← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 92

Sashe 65

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba É—aya suna zazzaune a palon gidan sunyi jigum jigum, barin ma dai ita Rafi'at da abin duniya ya ma ta yawa a kai.
Tunani take shikenan fa yanzu mijinta Abubakar yana can tare da Amaryar sa a wani gidan suna shan shagali an barta anan jigum gum. 😭

Suna cikin haka kowa da tunanin da Yake yi, suka ji dirar motoci ba É—aya ba biyu ba.
Sai shigowa suke yi, ba bu wacca tayi gigin tashi daga cikinsu, har zuwa can mutane suka fara shigowa, suna nan zaune.

Ba ƙaramin mamaki Rafi'at tasha ba, ganin dangin mijinta Abubakar sune suke shigowa ga kuma wata lulluɓe da mayafin da ya rufe ma ta fuska da jiki da alama ita ce amaryar.

Ko waccensu da buɗa ri-ri-ri take shigowa, har suka wuce ɗan wani korido Wanda kai tsaye zai sadasu da ɓangaren Amaryar.

Ita dai Rafi'at da sauran dangin ta da suke zaune a palon ikon Allah kawai suke kallo.

Sailuba ce da ta gaza haƙuri ta kalla Yayarta Rafi'at ta ce

"Wai Auntie Rafi'at kamar idona dangin mijin ki nake gani sun kawo Amarya, aikuwa indai haka ne, kin kaÉ—e daga ke har ganyenki wallahi."

Shiru kawai Rafi'at tayi bata kula surutun Sailuba ba.

Da dare wuraren ƙarfe Takwas su Sailuba suna zaune a palon Rafi'at suna taɓa fira. Yayin da ita kuma take daga cikin bedroom nata abin duniya ya ishe ta.

Sallamar su Jawaheer ne yasa su Badi'atu da Sailuba dama sauran matan dake Palon suka yi shiru da surutun da suke yi sannan suka amsa musu sallamar.

Ƙarisa shigowa matan wajen su biyar suka yi yayin da da Amaryar take tsakiyar su lulluɓe cikin mayafi kalar kayan jikin ta.
Gaba É—ayan su wuri suka samu suka zazzauna kana aka shiga gaishe gaishe tsakani, dama can Sailuba dasu Jummai sun san juna sosai.

Tashi Sailuba tayi tana faÉ—in "Bari dai na kira Auntie Rafi'at domin naga kamar bata san da shigowar ku ba."

Tayi maganar tana nufar hanyar bedroom na Rafi'at, gaba É—aya suka bita da ido bayan sun amsa ma ta.

Ba'a É—auki lokaci mai Yawa ba, sai gasu sun dawo tare, wannan karon Rafi'at sanye take cikin dogon hijjab blue color, dan haka, ba'a ce. ga kalar shigar jikinta ba.

Zama suka yi a 2sieter sannan Rafi'at ta gaisa dasu Jawaheer, dama can basu samu sun gaisa ba.

Sai kuma aka shiga bawa Rafi'at Amanar Amarya Hajarah.

Jinsu kawai take tana kuma bin su da kallo fuskar ta ɗauke da murmushin yaƙe can ƙasan zuciyarta kuwa

"Humm hmm hmn...."

Har suka gama abin da ya kawo su suka ƙara gaba, Rafi'at bata ce musu ko ci kanku ba, sannan kuma ko fuskar Amaryar bata gani ba, har suka koma inda suka fito, tana zaune tana saƙa abinyi.

Can ma su Sailuba suka ma ta sallama ko wacce ta kama gabanta.

Ita kuwa ta ɓangaren Amarya Hajarah Babban abin da ya hana ta buɗe fuskar ta a gaban Rafi'at shi ne, ba tasan da wani ido zata kalla Rafi'at ba, sannan kuma ba tasan wani kalar kallo Rafi'at zata ma ta ba, kallon mayaudariya na miki alkhairi kin sakamin da Auren miji?, ko kuwa kallon nagode da kika Aura mijina?.

Tasan dai Auren ta da Abubakar Wanda yake matsayin miji a gareta, wani ikon Allah ne kawai domin kuwa cikin wata biyar komai ya faru tun daga rescue nata da suka yi, da kuma komawar ta Jigawa State wurin su Hajiya Zuwairiya da zaman ta a can.
Dama Auran ta da Abubakar da ya biyo baya komai a cikin watanni biyar kacal ya faru.

Rafi'at mata ga Abubakar Mai Kyau kuma uwar gidan sa, ganin da tayi kowa ya watse an barta, gashi har wuraren goma Abubakar bai shigo gidan ba, to koma ya shigo bata sani ba.

Yasa ta kwashi Yaranta gaba ɗaya da suka yi bacci a nan palon ta shige bedroom ɗinta dasu ta rufe ƙofa.

Washe gari ma tunda ta fito da asuba ta girka ma Yaranta abincin da zasu ci ta kwashe a kula ta koma bedroom ɗin ta, ta kuma rufo ƙofa bata kuma buɗewa ba har wuraren sha biyu na Rana, tana jiyo hayaniyar su Jawaheer sama sama da alama suna shirin komawa Jigawa State ne.

Amma ko fita bata yi ba, har tayi baccin da bata samu tayi ba, a daren jiya, ta tashi taga Yaran gaba É—aya suma baccin wahala suke yi saman bed É—in kusa da ita, amma banda Abdulmaleek da Yake can gefe Yana wasa da Teddy Bear abin shi.

A hankali ta sauko daga saman gadon tana ji cikin ta Yana ma ta ƙugin Yunwa domin kuwa Rabon ta da taci wani abu, tana ganin takai kwana biyu, tana shirin shiga bathroom taji muryar Abdulmaleek Yana kiran sunan ta, juyowa tayi tana kallon sa kana ta ɗaga masa kai alamar "Menene."

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Page *73&74*

Gimtse kyakyawar fuskar sa yaron ya yi sannan yace

"Momy melaca kika kulle mu a bedroom, bayan Daddy ya yi Mana cabuwar Auntie?."🤔.

Cike da maÉ—aukakin mamaki Rafi'at take kallon Yaron nata, tana mamakin kaifin tunani irin nasa.
Ashe duk wannan abin da ake ciki yana kula da komai duk da cewa cikin qwarancin sa na yara ya yi maganar amma ta fahimci komai.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna a saman bed kana ta masa alama da hannunta naya ƙariso.

A je Teddy ɗin ya yi a gefe sannan ya ƙarisa wurin ta.

Kallon sa tayi kana ta fara magana cikin É—aure fuska

"Buddy Mine, faÉ—a min tsakanin ni da Daddyn ku waye kafi so?."

Da sauri Yaron ya kalleta jin abin da ta ce Duk da cewa shiÉ—in Yaro ne, amma ya fahimci wani abu daga cikin maganar ta, dariya ya yi sannan yace

"Momy ke can ai nafi con Daddyn a kanki." 🤪

ÆŠiif wutar Rafi'at ya É—auke na wani lokaci kana da kyar ta iya furta

"Saboda me kafi son Daddyn ku a kaina?."

Har Yanzu Yaron dariya yake sannan cikin qwaranci yace

"Caboda cima Daddy yana cona kuma baya min faÉ—a idan nayi wani kuch kuye cai dai ya min nasiha kuma ya bani chakuleti da yawa kuma yana kula dani cocai cocai."

Shiru Rafi'at tayi tana kallon Yaron a kullum kaifin basirar sa ƙara nin kuwa yake Yaron brain ɗin sa tana ja sosai.

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa sannan ta ce
"Saboda haka ne kawai kafi son Daddyn ku a kaina ko?."

Girgiza ma ta kai ya yi alamar "Eh," murmushin mugunta tayi kana tana faÉ—in

"Yanzu idan ni ma na dena maka faÉ—a, sai dai nasiha kuma ina kula da kai sosai, ina baka chakuleti cikin basket da komai da komai zaka soni fi ye da Daddyn ku, kuma zaka dinga jin magana ta?."

Abun ka da ƙaramin Yaro yaji maganar chakuleti cikin basket, Aikuwa da sauri ya shiga girgiza ma ta kai alamar "Eh, ya amince.
Murmushi tayi nan dai ta ci gaba da janshi da fira, tuni ta manta da wata Yunwa.

**
Wuraren ƙarfe Takwas na Daren Ranar Rafi'at tana zaune a palon dake ɓangaren ta Yaranta zagaye da ita suna ma ta qwaran cin su na Yara tana biye musu.

Abubakar Ya yi sallama yana shiga ciki, da kyar ta iya amsa masa sallamar dan ma kawai tasan matsayin ta ne a Addini shiyasa.

Ƙarisa shigowa ya yi sannan ya sama wuri ya zauna kusa da ita, aikuwa da ganin sa Yaran gaba ɗaya suka dawo wurin sa cike da farin cikin ganin sa, shima dai nan ya shiga nuna musu Kalar ƙaunar da yake musu.

Sai faman satar kallon sa Rafi'at take yi ta ƙasan ido. Ƴan kwanakin da tayi bata gansa ba, sai taga kamar anƙara masa wani kyau na musamman fi ye da Wanda ta sansa dashi a baya.

Ajiyar zuciya ta sauke tana danne kishinta a kansa tuno wai a halin Yanzu ba ita kaɗai bace matar sa akwai wata a gefe.🤨

"Matar Mai Kyau ina ga da kin dena satar kallona, domin ni ɗin gaba ɗaya naki ne, gwara ki fito fili ki kalleni san ranki, dan bamai hanaki kinji tawan."😅

Duk wannan maganar Abubakar Mai Kyau ne yake antayo ma Rafi'at a lokacin da ya juyo da kallon sa a kanta.

Ɗan murmushi tayi ko banza taji daɗin abin da ya faɗa wato hakan na nufin ke nan mijinta har yanzu yana ƙaunar ta duk da bai taɓa fitowa fili ya faɗa ma ta ba, ta fahimci Abubakar shiɗin na musamman ne a cikin mutane, domin kuwa baya bayyana abu da baki sai dai ya yi shi a aikace.

"Kodai matar Mai Kyau tana azumin magana da mijin nata ne. Yana ta magana babu amsa."

Abubakar ya kuma faÉ—a cike da Zoyala, murmushi tayi kana ta ce

"A'a kawai dai matar Mai Kyau tayi kewar My Lawful É—in ta ne obaaa."

"To gashi ya dawo sai matar mai kyau ta kwantar da hankalin ta domin kuwa Lawful ba inda zai ƙara tafiya Yabar matar mai kyau ita kaɗai."

Wannan karon murmushin da ya bayyana fararen haƙoranta tayi, wato dai su maza a kullum sun san takan mace ko. 😡

Ganin Yaran gaba ɗaya sunyi bacci ne, yasa ta miƙe ta ɗauka Nainarh tana faɗin

"Please My lawful taimaka min da Buddy ya cika nauyi wasu lokutan."

Tayi maganar a lokacin da take ƙoƙarin ɗaukar Nailah ita ma, da sauri Abubakar ya miƙe tsaye kana ya karɓa Nailah daga hannunta Yana faɗin

"Kudai mata akwai ku da kasa da. Yanzu idan kika yar da ita Nainarh wajen É—aukar Nailah fa, wato saboda qwiuya zaki haÉ—asu duka, salon ki yarda É—aya ko?."

Ya yi maganar ne shima Yana saɓa Nailah a kafaɗa sannan kuma ya ɗauki Abdulmaleek ya haɗa su ya nufa bedroom dasu.🤭.

Baki sake ta bisa da kallo tana murmushi, wato ya ma ta faɗa akan ɗaukar Yara biyu a haɗe, shikuma ya ɗauka ko?.🤓

Girgiza Kai tayi cike da nishaɗi kana tabi bayan sa ita ma kafaɗarta saɓe da Nainarh.
Chapter 65 · 0% Book details