← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 92

Sashe 36

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi kawai Jiddarh tayi Ni'ima ta tono ma ta gurin dayake ma ta raÉ—aÉ—i, ita batasan menene matsalar ta ba, a baya can, ta fara É—inki mutane suna kawo ma ta tanayi abu kamar wasa har sunanta ya fara zagaye gari qwararriyar tela lamba É—aya a cewar mutane, saikuma batasan meya faru ba aka wari gari ko mutum É—aya an dena kawo ma ta É—inki haka kawai.

Ajiyar zuciya ta sauke tana mai amsawa da "shikenan ba damuwa zaki iya,"

Wani tsallen murna Ni'ima tayi kamar wacca aka ma ta bishara da aljanna, da sauri ta matso ta rungumo Jiddarh tana faÉ—in.

"nagode sosai Jiddarh thank you so much."

"Never mind, haba Aunty Beauty wannan godiya haka, ni zaki ɓallani fa."
Dariya Ni'imar tayi tana faɗin, "ai dole, yanzu kafin a samu tela irinki a wannan zamanin ai sai an tona😉

Jiddarh ta ce "to ai sai a tona ina ga za'a samu,"

Ni'ima ta ce "gaki ma ansamo, da aka tona ɗin😀

Dariya sukayi duka nan Ni'ima ta taimakawa Jiddarh sukayi fold ɗin rigar, sannan suka mayar sif, cikin ƙanƙanin lokaci saiga su suna fira kamar dama can sunsan juna.
Ita dai Jiddarh tana mamakin Ni'ima ashe ta iya surutu haka?, to meyasa da batayi, 'oho' taba kanta amsa.

ᴡᴀsʜᴇ ɢᴀʀɪ

Kamar kullum alarm clock dake a saman locker, a gefen bed É—in ne, ya tasheta.
A hankali take buɗe dara daran kyawawan idanunta, tana mai furta addu'ar tashi daga bacci, yaye tattausar blanket ɗin da ta lulluɓa tayi sannan ta sauko daga saman mattress ɗin, tana miƙa hannu ta ɗauki ribbons da hularta dake can gefen mattress.
Saida ta tufke dogon gashinta da ribbons É—in sannan ta saka hular ta shiga bathroom.

Wanka tayi haÉ—e alwala ta fito a gurguje ta saka doguwar riga da hijjab dogo sannan ta shimfiÉ—a sallaya a gurin da aka tanadar domin yin sallah.

Raka'atainul fajir ta farayi raka'a biyu, sannan ta jira aka kira sallan asuba, kana ta miƙe tayi, Bayan ta idar, bata miƙe daga saman sallayan ba, har sai da tayi azkhar bayan ta kammala tayi folded sallayar ta mayar ma'ajiyar ta.

Shiryawa tayi cikin wando three Quarter white color, da riga t-shirt mai garejen hannu fara, sai hula p-cap fara, sannan ta saka safa doguwa har gwiwarta ita ma fara, earpiece ta ɗauka shima fari ta maƙala a kunenta duka biyun, tayi connecting ɗinshi da wayarta, sannan ta saka wayar a trouser pocket ɗinta.
ÆŠauko takalman ta trainers farare a hannayenta tayi, ta fito palon É—akinta Club ta É—auka /wato sandar wasar golf/.

*💋💋ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ💋💋*

*ƚԋҽ ɠʅαɱ ϙυҽҽɳ*

*☆ʂƚσɾყ & ɯɾιƚιɳɠ Ⴆყ☆*

*~ƙԋαԃҽҽʝαɾƚԋ. ʂαႦι'υ. ყαԋყαԋ🤙~*

{ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ}😇

*page 35&36*

Palon sama ta fito ba kowa, dama ba tayi tunanin ganin kowa ba, tunda safe ne yanzu.
Cikin sauri take taka staircases ɗin harta sauko palon ƙasa Ajiyar zuciya ta sauke, hango Humaira da tayi tsakiyar palon ita ma cikin shigar wasan golf irinna ta.

"Good morning Humaira, hope kintashi lafiya?."

Jiddarh tayi maganar a lokacin da ta ƙariso gurin ta, murmushi Humaira tayi ta amsa da "lafiya qalau nake, fatan kema hakan.?"
Tayi maganar a yayinda suke fita daga palon. Jiddarh ta amsa ma ta, "lafiya nake garau ma."

Suna tafe suna taɓa fira har suka ƙarisa filin buga wasanni dake a can gefan gidan, ɓangaren buga wasan golf suka ƙarisa nan suka fara.
Jiddarh dayake qwararriyar ce, a ɓangaren sai cinye Humaira take ta fita sai ti.

Gefe Humaira ta koma tana sauke haki ta ce "a gaskiya yau, ba sa'a gabaÉ—aya sai faman cinyeni kikeyi, na hakura kawai."

Tayi maganar tana ɓalle murfin gorar ruwan ever dake a hannunta, ta kafa a baki.

Jiddarh tana dariya hadda tsalle ta ce "kiyi a hankali fa, karki qware, kuma ki gama ki nemo mana ball, don ta shige a tsananin bishiyu."

Harara Humaira ta galla ma ta ta ce "banayi, ko bakiji na ce yau ba ranar sa'ata bane?, dan haka, ja gefe kije ki Nemo ball É—in ki da kanki."

"mutane suna bani mamaki, sai kiga idan mutum yayi wata gasa ko kuma dai, yayi rashin nasara a wani al'amari, sai kaji yana faɗin wai ranar ba ranar sa'a bane, ko nasara a gareshi, sai kace shi yake zaɓawa kanshi abin da zai faru a ƙaddararshi...A gaskiya mutane da yawa suna irin wannan kuskuren na faɗin haka wai ba ranar sa'a ba, da'ace nasara fa, yayi bazaka ji bakinshi ba, sai dai yayi gum hum."

Jiddarh ce duk takeyin wannan maganar cike da takaicin halin wasu mutanen.

Ajiyar zuciya Humaira ta sauke ta ce "a gaskiya Jiddarh you are right, saboda da yawa mutanenmu na yanzu, haka ake ba godiyar Allah sai dai kawai Allah yasa mudace. gabaÉ—aya su biyun suka amsa da Amin.

ᴍᴀɪ ᴋʏᴀᴜ, ғᴀᴍɪʟʏ

Zaune suke a dinning table suna karin kumallo da ya ke glass dinning room ɗin yana ɗaukar kimanin mutane sha biyu ne, sai ya kasance Daddyn yana kujerar da take a miƙe, yayinda Momy Rafi'at ita ma take a ɗayar kujerar wacca ita ma take a miƙe saiya kasance Daddyn da Momynsuna suna fuskantar juna ne 😁.

Sannan kuma sauran kujerun ya kasance Nainarh tana daga ɓangaren hannun dama, ita kuma Nailah tana daga hannun hagu, saiya kasance suma suna kallon juna, gefan Nainarh kuwa Haleesat ce, ta ɓangaren hannun hagu, kuma Zaynerb ce suma kallon juna kenan.
Sannan kuma gefan Haleesat, Lailah ita ma suna fuskan tar juna ita da Afeefah, dake a hannun hagu sai kuma Deejarh a gefan Afeefan tana zaune ita ma.

Saiya kasance sauran kujerun dining É—in guda uku, babu mutane wayam suke.

Daddy ya kallesu gabaÉ—aya, kowa ya mayar da hankali ana kai loma, yayi murmushi wani abu yana tsaya mishi a qahon zuciya, kamata yayi ace akwai yaro Namiji koda É—aya ne, a gurin, amma haka Allah ya tsara kaddarar ta kasance.

Yana ina?, yana cikin ƙoshin lafiya, ko a kasin hakan, shin yana ma duniyar, idan ma yana raye a halin yanzu, wata kalar rayuwa yake gudanarwa, shin ya dena halayyar sa wacca ita ce sanadiyar da yasa shi barin gidan, ko kuwa bai dena ba, shin yaci abinci kuwa, shin akwai iyayen da suke kula dashi ne, shin yayi kewar Daddyn shi da Momyn shi da ƙannin shi kuwa, shin yana tunawa dasu a kullum.
Kamar yadda a koda yaushe yake maƙale a zuciyoyin su, shin zai dawo gida kuwa, kamar yadda suke fata.

shin shin shin kalar waÉ—annan tambayoyin sune cike da koda yaushe a zuciyar shi, bai sani ba, amma yanaji yana da kaso tamanin cikin É—ari na halin da Babban É—anshi, É—aya tilo Namiji ya fa É—a.

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kore tunane tunanen da suke so, su rinjayo zuciyar shi daga dogon fushin da yake a ciki, É—ago da kanshi yayi karaf suka shige cikin na sahibar Matar shi /Momy Rafi'at/ da tun lokacin da ya faÉ—a tunanin, take an kare dashi, dama jira take ya É—a go da kanshi..Girgiza mishi kai tayi alamar a'a.
Murmushi ya sakar ma ta kawai, ita ma ta mayar mishi da martanin murmushin.

Kallon shi ya mayar akan ƴa ƴan shi ma ta, farin cikin ko wani uba nagari😘

Ɗan jim yayi yana ƙare musu kallo kana yace, "ni banga hoton surukin nawa ba daɗin daɗawa, kuma ba'a faɗamin koda sunan shi ba, kodai rowan shi a keyi min?."

Ya ƙarishe maganar yana kallon Haleesat, fuskar shi cike da Annuri.

Wani irin tari ne mai haÉ—e da qwarewa yazo ma Haleesat, aikuwa nan tahau yi ba qaqqautawa.
Da sauri Zaynerb dake fuskantarta ta miƙa ma ta ruwa a cup, tana ma ta sannu.

Karɓa tayi ta kaba a baki ta shanye tas, sai faman sannu mutanen gurin sukeyi ma ta.

Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Daddyn nasu da ya zuba ma ta ido yana binta da kallon tambaya.

Da sauri ta ce "Daddy!," sai kuma tayi shiru, ta rasa abin cewa, dariya Zaynerb tayi ta ce.
"Allah Daddy komai za ta ce karka yadda saita faɗa maka sunan shi, sannan kuma ta baka hoton shi, mu ma mu gani, jiya ba kalar roƙon da ban ma ta ba, akan ta faɗamin ko da sunan shi ne. Amma taƙi."

Zaynerb ta ƙarishe maganar tana jefawa Haleesat hararar wasa.

Kafin wani ya kuma cewa komai, sai ga Lailah wacca ba wanda yasan lokacin da ta bar gurin, ta dawo hannunta riƙe da doguwar paper.

Gurin Daddyn ta ƙarisa da saurinta, ta tsaya ta gefan shi, sannan ta warware paper ɗin, sai ga zanen kyawawan matashin saurayi Gentle dashi, ya bayyana.

Lailah tana dariya tana faÉ—in "Daddy ga hoton surukin ka, wanda É—iyar ka Haleesat ta zana shi, jiya jiyan nan."

Ƙurawa zanen ido Mister Mai Kyau yayi, yana yima zanen kallon kamar ya san fuskar a wani guri.

Yayinda duk kallo ɗaya da zayyima zanen, sai zuciyar Haleesat ta buga da ƙarfi, tayi tsuru tsuru tana jiran tsammani, ita da ko magana ta fatar baki bai taɓa shiga tsakaninta da mutumin ba, amma aje ta zana shi, har tana nunawa su Lailah masu bakin surutu, gashi yanzu tajama kanta Daddyn ya gani.

"To ba'a faɗamin sunan shi ba, ko shima saina roƙa ne?."

Taji muryar Daddyn yana faÉ—ar hakan, da sauri ta É—a go kanta tana kallonsu, gaba É—aya sun zuba ma ta ido suna kallo, don suji abin da za ta ce.

Cike da in ina ta ce "sunan shi, wai sunan shi?, ohoo sunan shi, ae sunan shi 'MAHMOUD' ne fa." Tayi maganar tana cizan laɓɓanta na ƙasa da ƙarfi.

Gaba É—ayansu basu kula da halin da take ciki ba, sai Zaynerb ita kaÉ—ai.
Lailah ta ce "suna mai daÉ—i, ashe shiyasa kike mana rowar faÉ—a." Tayi maganar cike da zaulaya.

"Anfa takura wa yarinyata, gabaÉ—aya kunsa sai kunya takeji haba dai."
Cewar Momy Rafi'at tana É—an dariya. Suma dariyar sukayi Lailah ta kuma faÉ—in.
"Allah Momy ba wani kunya, hadda ma miskilanci." Tayi maganar tana komawa ta zauna gurin zamanta.
Ta ci gaba da cewa "ni ina mamakin a inda Auntie Haleesat ta samo miskilanci, nasan dai Daddyn mu ba miskili bane, haka zalika Momy."

"kika sani ko'a cikin dangi ta gado?."
Chapter 36 · 0% Book details