← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 92

Sashe 31

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Deejarh tayi sannan ta ce "burina shine naga wata rana, an wayi gari na zama babbar likita wacca take taimakon talakawa da marasa ƙarfi, SO I WANT TO BE A DOCTOR.

Tafi class ɗin ya ɗauka rafraf suna faɗin munayinki wallahi our new comer { kuma kunsan students idan malami baya class 😁 }

Deejarh tayi murmushi a takaice sannan ta ce "nima dai zanso naji Burin ko wannenku ko?,"

Budurwar da tayi magana ne ta miqe dama bencin farko take kuma ita kaÉ—a ce.

Ta tsaya gaban blackboard kusada Deejarh, Sannan ta miƙawa Deejarh ɗin special hand ɗinta ta ce. "AM FALILAT KHAM££S, AND I WANT TO A DOCTOR TOO."

Murmushi Deejarth tayi sannan ita ma ta miƙa ma ta hannunta dake sanye cikin handglove ash color ta ce "nice to meet you miss Falilat,"

Falilat ta koma ta zauna, wata ma tazo sukayi kamar yadda sukayi da Falilat, haka suka dingi yi har aka gama da ɓangaren mata.

Wani saurayi ya fito ya miƙowa Deejarh hannu, wai su gaisa, murmushi tayi sannan ta juya hannunta ta baya ta karkaɗa mishi ta ce "haka akeyi saboda ni ba muharramarka bace."

Murmushi yayi yana faɗin "na gode da tuni, And am Farhad Khamees, i want to be a perfect £ngineer

Deejarh tana dariya ta ce "amma dai ku, twins ne da Falilat ko?,"

Amsa ya bata da faÉ—in, "E, haka ne, tayi murmushi haka suka ci gaba da yi mazan suma ba'a gaisawa sai dai a karkaÉ—a hannu. inji Deejarh.

Bayan sun gama ta sama guri a bencin farko, ta zauna kusada Falilat suna taɓa fira sama sama akan karatu, suna haka saiga wani malami ya shigo, miɗewa sukayi aka gaisar dashi, bayan ya amsa suka zauna.

Deejarh ta kalla Falilat dake ciku cikun ciro littafi a jakarta ta ce "wani darasi wannan malamin yake koyarwa?,"

Falilat ta amsa "£nglish language," jin haka yasa Deejarh ta ciro book ɗinta a jakarta ita ma.
Saida ta tsallake pages É—in da aka wuce ta sannan ta fara copyn writing É—in da malamin yakeyi a blackboard.

Bayan ya kammala ne yayi musu dogon explaining saida period É—inshi ya fita sannan ya bar ajin.

Wani ma ya shigo bayan ya fita, aka kaÉ—a bell lokacin Break, ganin kowa yana fita, Banda su yasa Deejarh ta kalla Falilat ta ce.

"nace ke banda kene a fita Break É—in?,"

Murmushi Falilat tayi sannan ta bata amsa, "ki tsaya kiga ikon Allah mana."
Jin haka Deejarh tayi gum, can saiga Farhad da snacks da kayan maqulashe kala kala ya duresu a gaban su, sannan ya kalla Falilat yana faÉ—in.

"Auntina waÉ—annan hadda qawarmu," yayi maganar yana kallon Deejarh da ta saki baki tana kallon su, yayi murmushi sannan yace "mamaki kike ko?,"

"Sosai ma," cewar Deejarh, yace "to ai ba abin mamaki bane, auntina ce ita idan kuma baki yadda ba, ki tambaye ta yana faÉ—in haka ya fita waje, wajen abokanshi.

Deejarh ta kalla Falilat zatayi magana, Falilat ta rigata da faÉ—in "haka ne ni ce babba awa É—aya tsakanin mu, kuma yana girmama ni, nima ina bashi girmanshi."

Deejarh ta ce "amma kuma ana ganin shi, aka ganki za'a ce shine babba,"

Falilat ta ce "Eh mana saboda shi namiji ne ae."

Haka suka cigaba da fira suna taɓa snacks ɗin gaban su har aka dawo class.

Wannan karon macece ta shigo ta koyar dasu Hausa language, 'Malama Fateema' bayan ta gama ta fita wani ma ya shigo a haka har aka tashi sallah bayan sunje sunyi, sun dawo islamic aka koyar dasu dayake haka tsarin makarantar yake.

Ƙarfe uku dai dai aka tashe su, a tare Deejarh da Falilat da kuma Farhad suka fito.

Tsaye suke a bakin gate na makarantar, Falilat ta kalla Deejarh tana faÉ—in.
"to kodai zamu rage miki hanya ne, tunda drivern naki bai ƙariso ba?."
Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "an karki damu fa, kuje kawai nasan nan bada ɓata lokaci ba zai ƙariso,"

"to shikenan,"

Falilat ta amsa ta sannan ta shiga motar su driver yaja suka tafi.
Akalla takai minti biyar a tsaye sannan ta hango wata farar mota ta parker, a kusa da ita, da sauri Moses driver ya ƙariso yana faɗin.
"am sorry ma'am Mrs mai kyau ce ta aikeni shiyasa ban ƙariso da wuri ba."
Murmushi Deejarh tayi sannan ta ce "ba komai Moses yanzu shiga mu tafi gida, dan Yunwar da nakeji ba za ta faÉ—u ba, shiga motar tayi bayan shi ma ya shiga yaja suka bar gurin sai gida.

KANO

Da Gudun tsiya ta taho saboda tsananin saurin da takeyi, in twin's take taka staircases ɗin da sauri ta ƙarisa tsakiyar palon tana sauke haki.

"Ke Jieddarh lafiyar ki kuwa?,"

Auntie da Humaira suka haÉ—a baki wajen tambayar ta ganin yadda ta sauko kamar wani abu ya biyota.
Tana sauke haki ta musu nuni da haÉ—aÉ—É—iyar princely gown dake hannunta.

Cike da farin ciki take faÉ—in Auntie na kammala, a yau na kammala haÉ—a gown É—innan.

Da sauri Humaira ta karɓa rigar tana faɗin.

"nicely Jieddarh barkanki dai, wannan aiki haka, shimfiɗa rigar tayi a tsakiyar palon tana bin haɗaɗɗiyar rigar da kallo ta haɗu sosai ba ƙarya.

Ɗinki ne irinna ƴa ƴan sarakuna, yaran sarakunan ma ba ƙanana ba.

Da wani kalar tsadadden yadi aka tsara É—inkin rigar, yadi mai masifar kyau da tsada, sky blue color mai haske.

Rigar bata da hannu, daga sama wajen ƙirji an matse rigar, daga ƙasa kuma ta buɗe, amma ba sosai ba, yanayin tsarin dai irinna ɗinkin yaran sarakai.
Wasu kyawawan stones farare da kuma sky blue color da aka jeresu jikin yadin, da aka ƙawata saman rigar dasu sai sukayi kamar sarƙa.
Daga tsakiyar rigar kuma ta wajen ƙirji wasu haɗaɗɗun flowers ne, sirara sosai aka taho dasu har izuwa ƙasa, yayinda wasu guda bibbiyu kuma aka jasu ta baya ko wani ɓangare biyu.
Sai kuma wani haɗaɗɗen yadi fari ta bayan rigar, doguwa ce rigar sosai, dan sai taja ma ta ƙasa, duk da cewa ita ma Jieddarh ba baya ba akwai ta da tsayi ba ƙarya.

Sai kuma wani haɗaɗɗe kuma kyakyawan yadi fari da aka ƙawata shi da stones sky blue color, sannan aka ɗinke, shi aka zagaye ma'ana dai zayyi kamar shine hannun rigar amma shi daban yake ba haɗe da Rigar ba.

Gefe ma ga wasu Beautifuls hand Gloves farare suma masu É—auke da adon stones sky blue color, suma sak, ko ince fiye da na yaran sarauta suma daban a gefe ba'a jikin Rigar ba.

Kallon Jieddarh Humaira tayi Bayanta kammala ƙarewa gown ɗin kallo obaa highly.
Tana murmushi ta miƙawa Jieddarh hannunta tana mai faɗin "a gaskiya na yaba da wannan haɗaɗɗiyar Rigar tayi ɗari bisa ɗari 100%. Jieddarh tawa sannu da ƙoƙari fa."

Sannan ma zatayi ma wacca ta É—inka kyau É—ari bisa dubu, dariya Jieddarh tayi tana faÉ—in.
"wayyo Humaira bakiji yadda nakeji ba, jina nake kamar nayi tsuntsuwa, naje na yanjo Ranar gasar nan ya dawo yau, kuma yanzu sannan kuma adai dai wannan lokacin a wannan gaɓar" 😝

Humaira ta ce "kisa ranki a inuwa kamar kinyi, babban baƙo ya mutu da dare.

Championship day É—in aita kusa nan da jibi ne ae."

Kallon Auntie Jieddarh tayi tana washe farare kuma ƙananan teeth ɗinta ta ce.
"Auntie ya kika ga wannan Rigar tayi kuwa?,"
Auntie dake zaune a saman three sieter ta ce, "sosai ai saima Ranar gasa É—iyata zata fito a cikakiyar princess ta fasa Taro da kyawunta mai ban mamaki."

Fashewa Jieddarh tayi da dariya tana faÉ—in "wayyo Auntie kuna fasamin kai fa, da wannan ya bawar,"

"Yoo ai gaskiya ake faÉ—a keÉ—in kyakyawa ce, a cikin kyawawa ina faÉ—amiki, mutumiyar keÉ—in, tauraruwa ce, a cikin kyawawan taurarin dake haske guri," Humaira ce take kwararo wannan zancen a yayinda da take ninke haÉ—aÉ—É—iyar gown É—in.

Jieddarh ta ce "wow it's so very very amazing oh my glamorous Time."

Please Humaira can you imagine, yadda zan kasance a ranar gasar kuwa?."
Ta faÉ—a tana yin zaman Æ´an bori a tsakiyar palon tayi tagumi hannu bibbiyu tana lumshe ido, ga fuskar ta har yanzu a sake take, wanda hakan yaba kyawawan dimples É—inta duka biyun damar bayyana, dama kuma can koda tayi murmushi ko batayi ba a haka fuskarta take koda yaushe dimples É—inta a bayyane suke.

Humaira ta ce "komai yayi zam zam, sai dai abu É—aya da kika manta da shi."

Da sauri Jieddarh ta ce "Menene shi wannan abun?,"

Murmushi Humaira tayi sannan ta ce "banga kin nuna mana, wannan ƴar sandar da yaran sarakuna suke riƙewa ba."

Jieddarh ta bata amsa "ina nan da ita, tana bedroom gata ita ma launin ta sky blue ne, nd White color,"

Humaira ta ce "na lura da gaske kike wannan shirin fa,"

"sosai ma," cewar Jieddarh tana washe baki kamar gonar auduga.

Tashi Humaira tayi ta koma saman two sieter tana faÉ—in "da kikace 'glamorous' ma tunomin da wani chinese drama mai suna 'OUR GLAMOROUS TIME', kikayi, inason dramar sosai,"

Jieddarh ta ce "ni kuma wacca take cikin dramar nake so, Humaira ta ce 'Zhao liying' kike nufi?,"

"E, mana ta iya act sosai da sosai take burgeni I LIKE HER SO VERY MUCH." Jieddarh ta faɗa tana nufar staircase hannunta riƙe gown ɗin.

ABUJA

Da sallamarta ta shiga palon tana cillah school bag É—inta sama ta cafowa.
Amsa ma ta sallamar Lailah dake zaune saman two sieter gabanta laptop tayi.
ÆŠa go da kanta tayi daga kan laptop É—in, ta sauke akan Deejarh daketa faman washe ma ta baki.

"ah ah barkanki dai Æ´ar school, to ya ya school É—in?, ina fatan dai anyi karatu sosai da sosai?," cewar Lailah cike da fara'a kamar ba ita ba.

Zama Deejarth tayi a tsakiyar palon tana amsawa da "yauwa Auntie Lailah, hala ke kaÉ—ai ce a gidan?,"

"Me kika gani?,"

Lailah ta tambaya tana kallon Deejarh ɗin, dan kuwa ba ƙaramin kyau yarinyar tayi ma ta cikin school uniform ba.

"naga kamar banga kowa bane sai ke, " ta bata amsa, Lailah ta ce "Auntie Zaynerb da Haleesat suna school, sai zuwa anjima zasu dawo, su kuma Auntie Nainarh da Nailah suna up, Momy kuma ta fita hospital kinsan bata cika zaman gida ba."
Chapter 31 · 0% Book details