← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 92

Sashe 21

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zaune can sai gata ta fito yanzu riga ce na material ash doguwa a jikinta, sai hular saƙa irinna sanyi, da ta saka Ita ma ash color rigar taji duniya ba laifi, don harda faji gefan ta, wannan karon ba gurin su Lailah taje ba ƙarisawa cikin palon tayi wajen su Nailah tayi sannan ta zauna a saman kujera mai ɗaukar mutum biyu, ba ruwanta, kallon Nainarh tayi ta ce "Auntie Nainarh ina ne ɗakin momyn naku na gaisheta naji ɗazu Antie Zaynerb ta ce bata jindaɗi."
Nainarh da surutun yarinyar baya burgeta ta ce "sama zaki hau room na biyu zaki shiga," ta bata amsa a gajarce. "to" ta ce tana miƙewa ta nufa benen sai kuma ta tsaya tana kallon twin's staircase ɗin dake gaban ta ga kuma wani staircase daga right ɗin ta wanda shi ɗaya ne, bawai twin's ba.
Rasa wanne zata bi tayi, juyowa tayi tana kallon, Nainarh ta ce "Auntie wanne zanbi ne?, naga abin naku kashi uku ne," Nainarh ta ce "kibi Right kawai."

'To ta kuma cewa sannan ta fara taka staircase É—in, har ta hau sama, "Yauwa yanzu, na wuce room na É—aya, ta faÉ—a a lokacin da ta wuce gurin, É—aki na biyu ta shiga.
Da shigarta wani irin ƙamshi wanda tunda take a duniya bata taɓa shaƙar mai kala dashi bama, balle shi, ya ziyarci duka ƙofofin hancinta, ae ba shiri ta lumshe idanun ta tana kuma shaƙar ƙamshin da kyau, huh mutumiyar taku fa, ita da tazo duba mara lafiya sai ta ɓige da kallon irin kyau da tsaruwar bedroom ɗin, a fili ta ce "cabɗijan wannan ɗakin yasin kona matar shugaban ƙasa albarka, wannan kyau da tsaruwa haka, ah lallai birni ana murewa," haka dai ta dingi sambatu, tana ƙarewa ɗakin kallo, san ranta, Sannan ta fito ganin da tayi matar tana bacci.
Ƙasa ta sauko ta zauna a kujerar da ta fara zama, Nailah ta ce "duba mara lafiyar ne kika daɗe haka?," Deejarh tana ƙumshe dariya ta ce "na tsaya na tayata fira ne ae."

Ta farka ne?, Lailah ta tambaya, Deejarh ta ce "E, mana, amma ta koma, lokacin da zan fito," sannan ta kalla Nailah ta ce "Aunty wai ina waÉ—annan Æ´an biyun?, naga bangansu ba." Nailah ta ce "wai Fareeda da Fadeela kike nufi?," ta ce "E, su," "Allah sarki ae sun tafi gida, tun É—azu," Nailah ta bata amsa.
Deejarh ta ce "Allah sarki anan garin suke ne?," Nailah ta ce "E,

Afeefah ta kalla Deejarh ta ce "wai kina ganesu ne, ko kuwa kawai kina cinkai sunan nasu ne?," Deejarh ta ce "waisu Auntie Nainarh kike nufi?, ina gane su sosai ma," "Okay tunda kince haka, to nunamin Auntie Nainarh, a cikin su, cewar Lailah, dan ta ƙure ta.
Deejarh ta miƙe ta ƙarisa gurin Auntie Nainarh tana karɓar jaririn Nailah dake hannunta, ta ce "wannan ita ce Auntie Nainarh," Afeefah da ɗan mamaki a fuskar ta, ta ce "ya akayi kika ganeta?," Deejarh tayi murmushi ta ce "ae ita Auntie Nainarh tanada tawadar Allah a gefen fuskarta ta gurin kunen ta na hagu, ita kuma Auntie Nailah a akan hancinta tawadar nata yake, wannan shine abin da yasa, na gane ko waccensu." Lailah ta ce "aikuwa kin cinka dai dai, sai dai kuma!, maganar dake bakinta da take ƙoƙarin fito dashi waje, ne ya tsaya cak sakamakon mutanen da taga sun shigo palon kamar an korosu..
Zaynerb ce ita da Haleesat suka shigo palon a tare suna sauke haki da alama sun sha gudu, Zaynerb ta zube a saman sofa 1sieter tana faÉ—in "Huh sister mun tsira," Nailah ta ce "lafiyar ku, kuwa kuka shigo ba sallama kamar an je foku?."
Haleesat ta ce "ae gwara ace jefomu akayi, da dai wannan uban gudun da muka sha, kamar marasa gata."
"Ikon Allah meya faru ne wai," Afeefah ta tambaya. Zaynerb tana jire hijjab É—in jikinta ta ce "kedai barmu kawai, ina wannan karen gidan Sunainah É—in, tofah shine ya biyomu, unfortunately.
Lailah tana gyara zama ta ce "ah ah yau kuma, ita Sunainarh É—in, ta tashi daga Ummyn Farhana ne, ta koma 'Sunainah' ga tsau, ko dai duk cikin wahalar ne, nifa wallahi wannan, shegen karen ne, yasa banason zuwa gidan, kare kamar zai cinye mutum É—anye wai ma, ya akayi ma karen ya biyo ku ne, ba an É—aureshi ba?,"

Zaynerb tana galla mata harara ta ce "wani an ɗaureshi?, to mudai a kwance muka ganshi kuma fa, a ƙofar gidan, shine shi kuma bawan Allah, bamu kulashi ba, ba muyi komai ba, ya biyomu shine fa, ita kuma wannan matsoraciyar, Haleesat tayi gudu nima na mara mata baya, shima kare ya mara mana baya, nan aka shiga tsere."

"Kin ji ki, bake ki ka fara gudu ba, ni kuma da naga zayyo kaina, na biyo ki a tamanin?."

Haleesat ta faÉ—a Ita ma tana cire zumbulelan hijjabin jikinta.
Lailah tana dariyar shaƙiyanci ta ce "wai waya ga, su Auntie Zaynerb ana gudun kare, ga wannan zumbula zumbulan Hijjaban da kuka saka, ae dole kare ya biyo ku."

Haleesat tana dariyar abin da ta tuno ta ce "hahaha saima kinga yadda Zaynerb tayi lokacin da muka iso nan gidan, ƙofar gate a rufe, yi tayi kamar zata tashi sama, dan tsoro, aikuwa ina baki story, gate man yana buɗewa ta kusa haɗawa dashi wajen shigowa."

Zaynerb taja qwafa tana faɗin "ae kuma dai, ni da ƙara zuwa gidan Sunainah sai wani jiƙon wallahi....

Sudai su Nainarh ba abin da sukeyi sai dariya, Deejarh saboda tsaban dariya sai da ta kusa yarda jaririn Nailah dake a hannunta, yi take ba ƙaƙƙautawa.
GabaÉ—aya suka zuba mata ido suna kallon ikon Allah, Lailah ta ce "wannan fa?, kodai tanada aljanu ne bamu sani ba?, "ke Deejarh lafiyar ki qalau kuwa?," cewar Afeefah a É—an tsorace dan duk a zaton ta, kodai aljanun Deejarh É—inne na dariya, suka tashi...

Saida tayi ma'ishi sannan ta dakata, dan kanta....
"kingama, nace kingama?," Lailah ta tambaye ta, tana galla mata harara...
aikuwa kamar ta ce ta ci gaba ta kuma fashewa da dariyar, Lailah ta ce "Auntie Nailah ki karɓa ɗan ki, a gurin wannan susuwar yarinyar idan kuma ba, haka ba tom."
Sai a lokacin ta dakata da dariyar, Afeefah ta ce "miss laugh, to dariyar me kikeyi?," Deejarh ta ce "kawai na tuna lokacin da karen gidansu habbulle ne, ya taɓa biyomu ni da ƙawata Hameeda, ranar sallah lokacin munje gidan kaimusu abincin sallah, ƙarshe abincin nan a jikin Hameeda ya zube tass, shikuma kare yace wana kama a lokacin saida ya ciza Hameeda mugun cizo...."
"Ke kuma ya kika ƙare kenan?,"
Lailah ta tambaye ta, Deejarh ta ce "na zomo mana na ranta a dubu na bar gurin, sai gida....

Zata kuma magana sukaji ana knocking ƙofar palon tun kafin wani ya miƙe Deejarh ta miƙe taje ta buɗe, mai gadi ta gani "lafiya kuwa," ta tambaye shi, jaka ya miƙo mata yace "wannan na Madam Zaynerb ne tayar garin gudu," karɓa tayi sannan ta mishi godiya ta dawo palon ta miƙama Zaynerb tayi ta ce "gashi Auntie Zaynerb kinyar garin gudu, inji mai gadi."

Karɓar jakar Zaynerb tayi tana faɗin "aikuwa dai, garin gudu na manta nayar da ita wallahi naga mutuwa.
Haleesat ne ta kalla Nailah ta ce "Auntie yaushe zaki koma ERITREA É—inne?."

Kai tsaye Nainarh ta bata amsa da "bayan gasar su Afeefah mana," su duka kallon ta sukayi Lailah ta ce bayan gasa kuma, Nainarh ta ce "E. mana ko akwai matsala ne?,"
"Kema dai kinsan Daddy bazai barki ki zauna ba, bayan ga mijin ki can a wata uwa duniya ƙasar ERITREA ko?," cewar Zaynerb, Nainarh ta ce "to ya ya kukeso nayi sucan sunce tunda ni juyace aure zasu ƙara mishi, wacca zata haifa musu jika,"
"aure kuma, auran lafiya kwata kwata shekaru nawa ne da bikin naku da za'a ƙara mishi mata haba, sufa larabawan nan shiyasa ba burgeni suke ba, don sun cika nuna ƙabilanci."
Lailah tayi maganar da alama ranta ya ɓaci highly. .

"Shekaru uku ne kacal da auren," Nainarh ta bata amsa, Nailah ta ce "dama can sunada niyyar su ƙara mishi matar ne, ƴar ƙabilansu da zasu wani ce saboda bakya haihuwa inaga aishi haihuwa lokaci ne ko,"
Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke sannan ta ce "yanzu ba wannan maganar ya kamata ayi ba,"
"to maganar me za'ayi Haleesat ta tambaye ta, ta ce "kamata yayi ta samu ta koma ta gyara zaman ta da mijinta, tunda suna son junansu, wannan zuwan da tayi shine zaisa suji daÉ—in aura mishi balarabiya Æ´ar uwarshi ae a nawa tunanin."

"Ba laifi kin kawo shawara," cewar Zaynerb..
Lailah ta ce "ni dama shiyasa soyayya bata dameni ba kiga anyi auren soyayya daga baya anzo ana samun matsala kamar da ba'ayi soyayya ba kamar ba gobe.

Nailah ta ce "au wai har yanzu Lailah kina ɗauke da wannan ra'ayin naki naƙin soyayya?,"

"of course yes,"

Lailah ta bata amsa, Nailah ta kuma cewa "anya ke macece kuwa?, gaskiya ina tantama," zaro ido Lailah tayi ta ce "ni macece mana me kika gani?," É—an jim Nailah tayi sannan ta ce "banga alama ba, ke bakyajin irin wannan feeling É—inne da akeji?."

Kwashewa da dariya Lailah tayi harda clapping finger's, sai da tayi ma'ishi sannan buÉ—ar bakinta ta ce "banaji ni banma sanshi ba, Yasin.......
GabaÉ—aya palon suma suka kwashe da dariyarta, Zaynerb ta ce "anya kuwa Lailah kina lafiya qalau kuwa, Nailah ta ce

"yauwa sis tambaya mana ita dai."
Lailah ta ce "kai mai kuka mayar dani Yasin lafiya ta qalau ba zaku fahimta bane kawai, Afeefah ta ce "kece dai bazaki fahimtar damu ba," Nainarh ta ce "ke Afeefah ai inaga idan ana maganar masu lafiya baza'a sakaki ciki ba," tayi maganar tana É—aukar remote ta canza channel zuwa wani chinese drama LOVE DESIGNER....

Afeefah ta ce "saboda mene baza'a sakani a ciki ba?," Nailah ta bata amsa da "saboda gwara Lailah ma akanki ke ko maganar soyayya ni bantaɓa ji ko ganin kinayi ba,"

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke sannan ta ce "hakuri nasara ne! haka zalika aure lokaci ne!, Soyayya kuma sai nayi thinking akai😝..
Chapter 21 · 0% Book details