← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 92

Sashe 27

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ta rasu a washe garin ranar da ta haifeni," Afeefah ta faɗa tana kuma share hawaye ta ci gaba da cewa "ni da ƴar uwata Zaynerb mun taso kwata kwata bamusan Menene soyayyar mahaifiya ba, mahaifin mu kawai muka sani kuma dashi kaɗai muka shaƙu sai kuma kakarmu AMMA Zaynerb ce ma ta shaƙu da ita fiye da dani,"
"to ita AMMA É—in tana ina ne, halin yanzu?," Deejarh ta tambaya.
"Tana KANO STATE," Afeefah ta bata amsa, Deejarh ta kuma cewa.

"to meyasa bata dawo nan ba, ta zauna tare daku," Afeefah ta ce "tana zaune a gidan ƙanin mahaifin mu Uncle sagir ne da yake zaune a KANO ɗin shida iyalan sa, shiyasa bata dawo nan ba, kumaa, shiru tayi ganin Deejarh tana hawaye "Menene kuma ya sakaki hawaye?,"
Afeefah ta tambaya, cikin kuka Deejarh ta ce "ba komai kawai dai na tuna kakanni nane dukansu sun rasu Ummata ma ta rasu, Abbana kuma baya sona,"
Janyota zuwa jikinta Afeefah tayi tana rarrashi ta ce "addu'a zaki musu ba kuka ba, kuma Abbanki yana sonki, kawai dai ki bashi lokaci shida kanshi zai nemeki kinji ko?," gyaÉ—a ma ta kai tayi alama taji.

"Good girl haka nake so" Afeefah ta faɗa tana miƙewa ta nufa wardrobe dake bedroom ɗin, tana faɗin "bari muga kayan ƙawantawa ƙilama sunfi nawa kyau da tsari highly," 😍

Ba shiri Deejarh ta fashe da dariya tana faÉ—in "kai Auntie Afeefah,"
Dariya ita ma Afeefah tayi ta ce "E, mana da gaske nake wata ƙilama sunfi nawa kyau, ta ce kuma gobe ki shirya zamu fita shopping, Daddy yace gobe muje ki zaɓa duk abin da ranki yakeso, kijido baki da wata damuwa koma duka kayan SHOPPING MALL kikace kinaso yace a kwaso a kawo miki gabaɗaya😂
Haka Afeefah ta ci gaba da janta da fira saboda ta mantar da ita damuwarta.

*~💅💥💅~*

*𝑯𝑨𝑳𝑬𝑬𝑺𝑨𝑻*

Fitowar ta daga bathroom kenan, jikinta sanye da bathrobe, ta hango wayarta dake saman mirror tana haske alamar shigowar kira, dayake a SILENT wayar take.
Da sauri ta ƙarisa ta ɗauka ganin 'JENNY' ce mai kiran nata yasa tayi murmushi, picking tayi sannan ta kara kunenta shiru tayi domin jin abin da Jenny zatace, sai kuma taji bata jin abin da Jenny ɗin take faɗa hayaniya yayi yawa a gurin.

"Hello Jenny, banaji fa, akwai hayaniya a gurin da kike," shiru taji, da sauri ta duba wayar gani tayi Jenny ta katse kiran.

Taɓe baki tayi a fili ta ce "wata ƙilama suna jira na a waje ne, duba clock ɗin dake manne a wall na bedroom ɗin tayi, taga ƙarfe sha ɗaya saura na dare "Kan ubancan ashe lokaci yaja haka huh," ta faɗa tana zama akan stool na dress mirror lotion ta shafa sama sama sannan ta miƙe closet ta nufa ta zaɓo kayan da zata saka, sannan ta dawo ta aje saman bed, zama ta kuma yi kan stool ɗin, light make-up tsantsara sama sama.
Sannan cikin ƙanƙanin lokaci ta shirya cikin Floral Dress Gown blue black mai zanen flowers pink color, sai belt pink color da ta ɗame Tummy ɗinta dashi, rigar hannun vest ce da ita saita gyara hair ɗinta in 'punky ponytail' 'straw hat' ta ɗauka pink color ta riƙe a hannunta sannan ta ɗauko zundumeman hijjab blue tasa ta ɗauka ƙaramar handbag ɗinta blue black.

*~𝑻𝒐𝒅𝒂𝒚 𝒊'𝒎 𝒊𝒏 𝒔𝒊𝒄𝒌, 𝒚𝒐𝒖 𝒔𝒉𝒐𝒖𝒍𝒅 𝒎𝒂𝒏𝒂𝒈𝒆 𝒇𝒐𝒓 𝒕𝒉𝒊𝒔 𝒍𝒊𝒕𝒕𝒍𝒆 𝒑𝒂𝒈𝒆, 𝒔𝒐𝒓𝒓𝒚 𝒇𝒐𝒓 𝒊𝒕 😎~*

*~✦𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉✦~*

🥳𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅🤙

*💋💋SARAUNIYAR🎀KYAU💋💋*

______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

*𝑷𝒂𝒈𝒆 25 & 26*

Sannan ta fito daga bedroom ɗin, cikin sanɗa kamar yadda ta saba take wuce palon duk girman shi, a hankali ta tura door ɗin kitchen ta shiga, haka kawai taji gabanta na faɗauwa, da sauri ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta fita, da sauri sauri take tafiya har ta dan gana da ƙaramar ƙofar garden ta fice da sauri.

Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke daga inda take a bakin window na bedroom ɗinta, zuge curtains ɗin tayi, a zuciyarta ta yanke shawarar gobe kawai koma miye zai faru, sai tayi ma Haleesat maganar wannan satar hanyar da takeyi tana tafiya Night Club, koma miye zai faru ya daɗe bai faru ba, wani yanki na zuciyarta kuma faɗa ma ta yakeyi kawai ta sama Momy Rafi'at ta ma ta Bayanin komai, yayinda wani ɓangaren yake gargaɗinta akan idan tayi haka Haleesat ba zataji daɗi ba.

Da tunanin ya isheta a fili ta ce, "toh kartaji daÉ—in mana miye nawa tunda bani na sakata fitar dare ba ae."

Haleesat kuwa tana fita tun kafin ta ƙarisa gurin motar ta cire hijjab ɗin jikinta, sannan ta saka straw hat ɗin hular hannunta, akanta, sam bata lura da wata farar mota acan gefe dake fake ba, saboda duhun dare da gurin da motar yake dashi.

Tana shiga motar Zuree taja suka bar gurin, saida ta saita nutsuwar ta sannan ta kalla motar da kyau, bataga Jenny ba 'dum dadam' taji gabanta ya faÉ—i na rashin dalili, gabaÉ—aya motar mutum uku ciki, hadda ita Zuree dake driving sai Feenah dake gefenta tana shafa wayarta sai kuma ita Haleesat É—in ta uku.

*__🏪__*

'𝑷𝑨𝑹𝑻𝒀 𝑨𝑳𝑳 𝑵𝑰𝑮𝑯𝑻'

A hankali Haleesat ta furta sunan saman laɓɓanta tana ɗan murmushi ganin irin tsadadden club ɗin da sukazo a yau.

Night club ne wanda yayi ƙaurin suna cikin garin Abuja kuma da kewaye, guri ne na manyan yara, don masu zuwa girin sai wane da wane don ba guri ne na ƙananan qwari ba, shi kanshi kuɗin parking mota na da ake biya a Club ɗin ya ishi wani talakan Najeriya jari mai ƙarfi, don zunzurutun kuɗaɗe ne bana wasa ba, aƙalla ana biyan kuɗin parking mota a haɗaɗɗen parking lot na Club, sama da Dubu ɗari uku parking kawai, sannan yanayi yanayin mota ake bi, don idan motar ka/ki mai masifar tsada ce tofah kuɗin da mutum zai biya sai haure hakan 😎

Har yanzu ƙayataccen murmushin fuskar ta bai ɗauke ba, ta kalla Zuree da ta ƙariso gurin bayan tayi parking a gurin da aka tanadar domin yi.

Ta ce "it's pleasure babe muna wuta fah highly higher kuwa, Yau kuma nan akayo damu ne?,"
Dariya Zuree tayi tana karkaÉ—a car key's É—in dake hannunta ta ce, "Yeah I you enjoy this ko kuwa a canza wani Club É—in?," ta tambaya Haleesat É—in tana ma ta nuna da gabaÉ—aya haÉ—aÉ—É—en Club É—in.

Dariya ita ma Haleesat tayi sannan ta ce "Yeah Yeah I enjoy this special Club, 'PARTY ALL NIGHT',"
Kallon Feenah tayi tana faÉ—in.
"yane wai Feenah yau kamar bakya walwala fah, what happening to you?,"
Tun kafin Feenah tayi magana Zuree ta rigata da faÉ—in, " ae barta kawai kinsan halin ta fah, ko'ince kinsan halin ku guda na miskilanci."

"Toh ina kuma Jenny take?," Haleesat tayi tambayar tana kallonsu su duka, Still Yanzu ma cikin sauri Zuree ta ce "Yau batajin daÉ—i shiyasa fah, that's All ta faÉ—a tana É—an sosa fuska game da inda inda.
"Alright kuzo mu shige fah guys, don anayi bamu," cewar Haleesat.

Ba wanda ya kuma magana acikin su suka shiga ciki, Haleesat cikin tafiyar ta juya tanayima Feenah magana, sam bata lura ba, taji tayi karo da mutum gamm, a tsiwace ta juyo dan taga wani shafaffe da mai ne ya bugeta, bai iya bada hakuri ba, maganar da tayi niyyar yine ya tsaya cak a maqwogwaronta sakamakon ganin irin mutumin dake tsaye gabanta, dum dadam daram taji gabanta ya tsananta bugu a dalilin haÉ—a kwayar idanu da sukayi.
She was very Thither shocked, saboda yadda taga yanayin shi dogo fari, ga faffaɗan ƙirji, ga kyakyawan suffa irinna asalin jaruman sadaukai, ba za ta iya cewa ga yanayin fuskar shi ba, sakamakon sanye yake da face mask.

A hankali ta lumshe kyawawan idanun ta, in few secs, sannan ta buÉ—esu tana mai addu'ar sake kallon kyakyawan surar dake gabanta, sai dai me?.
Da buɗe idanun da zatayi, wayam ba kowa a gurin sama da ƙasa, da sauri sauri cikin zafin nama ta juya bayanta, can ta hangoshi a ƙofar fita zai fita da alama wani yake nema ko yake bi.

Da ƙarfi ta ciji pink lip ɗinta na ƙasa har saida ya fashe, da sauri Feenah ta ƙariso gurin tana tambayar ta, ko lafiya ta tsaya a gurin.
Bata ce mata komai ba, ta kama hanyar fita daga gurin, harabar Club É—in ta fita, amma bataga kowa ba, koda kuwa mai kama dashi ne.

Wannan karon hadda Zuree suka ƙariso gurin da take, ita taƙi gaba haka zalika taƙi baya.
Zuree da É—an mamaki ta ce "wai Baby Leesat lafiyar ki kuwa, menene kike nema haka?,"

Sai lokacin Haleesat ta É—an dawo cikin nutsuwar ta, kallon ta tayi cikin lumshe idanu ta ce.
"me kika gani ne, kika ce haka?," Zuree ta ce "naga kina abu kamar wata mai iska mana, gashi yau naga kamar akwai abin da ke damunki ko?,"
Murmushi Haleesat tayi ta ce "ba komai, kawai dai yanayin garin ne, amma ba komai, So no need to worry your self, nagode da kulawa fa."

Ciki suka koma Zuree na faÉ—in "gabaÉ—aya sai naji Club É—in yau babu, daÉ—i dukanku bakwa cikin walwala," Feenah ta ce "share kawai."

Suna shiga basu tsaya komai ba, kai tsaye suka haye wajen Rawa dama ba'a rabasu da ita rawar, yi suke kamar ba gobe, kuma kamar basa gajiya da ita rawar 😇

IN BRIEFLY

A taƙaice dai basu suka fito daga club ɗinnan ba, sai wajen ƙarfe biyu na dare.

A mota Haleesat ta kalla Zuree dake driving cike da nishaɗi ta ce "Babe ya naga baki ɗauka hanyar gidanmu bane, naga kin miƙa wata hanyar daban, ko dai kin manta dani a motar naku ne?."

Ƙin kulata Zuree tayi saima ƙure volume da tayi, ganin haka yasa Haleesat ta mayar da kallonta kan Feenah zatayi magana.

Da sauri kamar tana jira ta kalleta, ta jefa mata wani farin handkerchief a fuska, ko sakan bata ƙara ba, wani bacci mai nauyi ya ɗauketa.

Dariya suka sheƙe da ita a tare hadda tafawa, Zuree tana murza steering ta ce.
Chapter 27 · 0% Book details