← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 92

Sashe 50

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi ya yi sannan yace "Da gaske nake fa, Allah Aure nakeso, wannan ne ma Babban dalilin da ya sa na dawo."

Sakeenah ta ce "Kai Sagir yanzu a gaban su Hajiya da Abbhee kake wannan maganar, bakajin kunya, daɗin daɗawa ga yaranka a wurin fa."😅

Tayi maganar tana mishi nuni da ƙananan yara dake palon, ƴan dugui dugui dasu, su na wasannin su.

Murmushi ya kumayi yace "Aha to ai wannan dalilin ne ma yasa nake maganar a gurin, saboda naga suna wurin, kawai dan bakuga Suwaiba ta ba ce, da sai kun fini ƙosawa na Aureta kafin wani yamin snatching ɗin ta."😎

Ko kunya babu yake maganar yana kuma nuna musu pictures kala kala na Suwaiba, zai kuma magana kenan.

Sameen ya É—auki cushion na sofa ya jefa mishi yana faÉ—in

"Yi mana shiru É—an nema baka da kunya ko kaÉ—an, gashi kaje London ka kuma koyowa salo salo."

Dariya kawai Sagir ya ke yi yana faÉ—in "Wallahi Yah Sameen kai ma kasan yadda London É—in nan take, gaba É—aya sun mayar da bawan Allah kamana kullum sai dai nayita É—aukar azumi fa kuma....!"

"Au badai zakayi shirun ba ko, ka ci gaba ne ko?."

Cewar Sameen yana dariyar "Tu no wani drama da ya taɓa faruwa tsakanin Sagir da wata Baturiyar London 😍.

Sagir ya kalla duka mutanen palon yana faÉ—in

"Kunga ni ko tunda kukaga yana dariya shima Auren yakeso, saboda haka kawai a haÉ—amu dasu Yah Yusuf ayi lokaci guda."

Tashi Sameen ya yi daga zaunen da yake ya nufa Sagir zai kama ya naÉ—a.

Ai da sauri Sagir ya miƙe tsaye yana faɗin "Yah Sameen na fa taimaka maka ne, tunda naga kanajin kunyar faɗa fa."

Ya yi maganar yayin da suke zagaye palon shi da Sameen yana binshi zai kamo ya daka, shi kuma yaƙi bari hakan ta kasance, sai faman zagaye ƙaton palon suke cike da farin ciki kamar wasu ƙananan yara ko dama ba wasu shekaru na azo a gani bane a tsakanin su.

Saminu ganin Sagir wahalar dashi kawai yake ba tsayawa zayyi ba, yasa shi ya koma ya zauna yana faÉ—in

"Tunda haka ne sai na faÉ—a, kowa ya sa ni."

Sagir dake can gefa tsaye yana sauke haki yace

"Ka faÉ—amana so what.?"

Sameen yana dariyar mugunta Yace "Kai kyakyawar African Nigeria ka ce na faÉ—a komai ko?."

Jin abin da Sameen yake cewa ai Sagir bai san lokacin da ya yi wata super ba, sai gashi a gaban Saminu ya rufe mishi baki da duka hannayen shi, faÉ—i yake

"Haba my Yah Sameen ba kace ba zaka faÉ—awa kowa ba, indai ni ne na dena maganar Aure indai ba zakayi wannan maganar ba, to daga yauma zan dinga kiranka da YaYah Sameen shikenan, daga Yau haka zan dinga kiranka kaji ko my Yah Sameen?."

Gaba ɗaya Sagir Yana maganar ne a ruɗe tsoron shi Allah kar Sameen ya faɗawa su Abbhee dasu Yah Yusuf abin da ya taɓa faruwa a tsakanin shi da wata Baturiyar London.🤣

Murmushi kawai AL_HAJI SAMEER LAMIÆŠO. Yakeyi ganin yadda family É—inshi suke cike da farin ciki, ga haÉ—in kai, wannan ya nuna mishi kenan ko da bayan ranshi Ahalinshi ba zasu tarwatse da rashin zumunci ba.

Kallon matan shi dake zagaye gefan shi ya yi yana kuma sakin murmushin nishaɗi can cikin zuciyar shi kuwa tasbihi yake yana kuma godiya ga Allah da ya azurtashi da wannan kyakyawan Ahali abin kwantance fa ɗin Birnin Jigawa State dama ƙasa Nigeria baki ɗaya hadda ƙasashen waje.😘

*SARAUNIYAR KYAU*💓

_(The Glam Queen)_ 👑

```Takun Farko```

Story & Written By:

*_The Nainarh KD_*

____________________________________________👑

*THE ONGOING BOOK'S*

1. *SONKI NE ƘADDARA TA*

MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
_Batool Kamba_

2. *ZAN JIRA KA*

MALLAKAR
A'ISHA ALƘALI
_Mrs Aysib_

___________________________________________👑

Page*49&50*

Sameen dai ganin Sagir ba kyaleshi zayyi ba, yasa shi É—a ga hannu alamar surrender.

Ganin haka yasa Sagir ya koma tsakiyar palon ya zauna yana faÉ—in

"Amma Yah Sameen nagode sosai dan kuwa idan ka faÉ—a bansan ina zankai kunya ba Allah kuwa "

Ya yi maganar yana dariya sosai, shima dai Sameen dariyar yakeyi.

"Wai wannan wata kalar magana ce, da ba'a so muji ne?."

Cewar Zuwaira cikin murmushi, "Kedai bari, wata ƙila ba gaskiya a lamarin tunda kikaga yaƙi bari a faɗamana muji."

Jummai ta amshe zancen ita ma fuskar ta washe da farin ciki.

Abubakar ne yace "Tunda dai ba'a so muji shikenan mun haƙura, idan tayi wari maji ai."

Haka suka ci gaba da fira cikin fahimtar juna da maɗaukakiyar ƙaunar junansu, can wajajen magarib mazajensu Jawaheer suka zo suka ɗaukesu suka koma gida bayan sun shiga ciki an gaggaisa.

_____👑

Rayuwa ta ci-gaba da tafiya tana lulawa da mutane cikin Æ´an watanni da suka gabata, komai ya daidaita Abubakar ya koma Abuja da zama, domin kuwa a can yake kula da companies na AL_HAJI SAMEER LAMIÆŠO.

A yayin da shi kuma Yusuf ya wuce Borno State shima ya fara gudanar da.
S.L__ GROUP OF COMPANIES dake can BORNO STATE.

Shima Sameen ya yi nashi gurin Lagos yana gudanar da aikin na shi Likitanci a Babban Asibitin ƙasa dake Birnin Lagos.

Tuni aka saka ranar bikin Sagir da kyakyawar shi Suwaiba sakamakon yadda ya qwazzaba shi fa aure yake Buƙata, harda kwanciya rashin lafiya na ƙarya, duk dan saboda ah farko AL_HAJI SAMEER LAMIƊO Yaƙi Yarda, haka dole ba yarda aka saka ranar bikin nashi da Suwaiban shi, wacca ta kasance ɗiya ga Alhaji Saleh Sama'ila a Birnin Kano ta Dabo koda me kazo anfika Aha, wanda take cikin AREWA cin Nigeria yankin Africa.

Sameen shima da zankaÉ—eÉ—iyar shi Sadeeyah wacca ta kasance Æ´ar Gombe State ce ita, sai Yusuf da tashi gwanar Yusra Æ´ar asalin Kaduna State garin governor, mazauniyar Borno State.

Kaf cikin su Abubakar ne kawai bandashi a auren, shima dai lokacin da aka zaunar dashi ana tambayar shi ko yanada tashi gwanar, sai cewa ya yi bai isa Aure ba ai.🤣

A lokacin dariya AL_HAJI SAMEER da Æ´an uwanshi maza biyu dake wurin sukayi, sannan Alhaji Yahya da yake Yaya a gurin AL_HAJI SAMEER LAMIÆŠO.

Yace "Abubakar kenan ai shi Aure da kake ganin shi lokaci ne dashi, idan lokacin ya yi kai da kanka zaka nememu, amma tunda yanzu kace baka isa auran ba, mu zamu baka lokaci nanda watanni biyar, ka ga lokacin ya yi daidai da Auren su Yusufa wata biyu da yi kenan, tunda wata uku aka saka, lokacinzamu sameka da magana idan lokacin ya yi kace mana baka samu ba. Ka yarda mu aura maka ko wacece?."

Murmushi Abubakar ya yi sannan cike da girmamawa Yace "Na amince Alhaji sannan ina godiya."

Murmushin manya kawai sukayi sannan aka ƙulla Deal.

Rayuwa ta ci-gaba tafiya yayin da kullum kwanan duniya lokaci yake kuma raguwa, wanda hakan ke ƙara ƙarfin imani ga masu shi.

A can ɓangaren kuma hakan ya yi daidai da saura sati biyu, bikin mutane uku daga Babban Ahali yara ga shahararren mutumin da duniya ke damawa dashi AL_HAJI SAMEER LAMIƊO Jigawa State.

Gaba ɗaya ɓangarori biyun shiri suke ba kama hannun yaro, ba ga dangin amare ba, haka zalika baga dangin angwaye ba, shirin shan shagalin biki ake sosai waɗannan suna nunawa waɗancan wane ku ta fannin mutunta juna da nuna abin Alkhairi ga juna.

Lokaci naja sosai har aka wayi gari a ranar wata laraba, an ɗaura Auren Sagir Samir Lamiɗo, da zankaɗeɗiyar amaryarsa Suwaiba Saleh Sama'ila a Birnin Kano ƙarfe sha ɗaya na safe, Auren da ya sama hallartar duban jama'a na fa ɗin Nigeria dama wajenta.

Sai kuma Sameen Samir Lamiɗo, shima da tashi gwanar a Babban masallacin jumma'a na Birnin Gombe State, misalin ƙarfe biyu da rabi na rana.

Sannan Yusuf Samir Lamiɗo, shima a Kaduna State ƙofar gidan mahaifin amaryar sa Yusra, Alhaji Nazir Sani Sidi, misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma aka ɗaura Auren.

Daganan kuma Æ´an É—aurin Aure da kuma matan da sukazo tare, aka wuce da amarya Yusra Jigawa State wurin dangin ango, kafin daga baya ita da angonta su wuce Borno State wurin da yake zaune.

Sun isa Jigawa State can cikin dare wajajen ƙarfe sha ɗaya, dan haka ba'a tsaya jiran komai ba, aka musu tarba na ban girma sannan aka saukesu a masauki ɓangarena musamman.

Washe gari da ta kama Alhamis sannan kuma ranar cikan biki, aka tashi da sabon shagali wanda aka nuna ainihin al'adar mutan garin, ansha shagulgulan biki sosai kuma jama'a da dangin amare sun ƙayatu matuƙa.
Sai da aka kwashe kwanaki uku ana shan shagulgulan biki sannan komai ya lafa.

Zuwa rana ta biyar da bikin, gaba É—aya jama'a sun watse gida ya rage daga amare da angwayen su sai kuma surukai iyayen angwaye.

Zuwa dare bayan isha'i Alhaji Samir LamiÉ—o, da matan shi Hajiya Harirah da Dr_Raheemah da kuma da Hajiya Zuwairiya.

Gaba ɗaya suna zazzaune a ƙaton palon gidan, wanda ya gaji haɗuwa yasha kayan more rayuwa kala kala abin ba'a magana sai wanda ya gani.

Sai ga Yusuf ya shigo amaryar shi na take mishi baya, fuskar ta lulluɓe da lufaya mai shigen kayan jikinta, wuri suka samu daga can gefe a ƙasa, suka zazzauna, sai ga Sameen shima da tashi amaryar sanye cikin shiga kala ɗaya suke, ita himar ne dogo har ƙasa a jikinta, wuri suma suka samu suka zazzauna Sameen kusa da Yusuf yayin da da amaryar shi ta zauna kusa da Yusra matar Yusuf suma suka gaggaisa dasu Hajiya Zuwairiya.

Can sai ga Auta Sagir da kyakyawar amaryar sa Suwaiba suma sun shigo bakinsu ɗauke da sallama cikin shiga iri ɗaya, suka shigo sai faman baza ƙamshi da gyalli irinna amare sabbin suke.🥰

Kusa da Alhaji Samir Lamiɗo Sagir ya ƙarisa ya zauna, ganin hakan yasa Suwaiba ita ma ta ƙarisa wajen su Sadeeyah ta zauna tana Suna sakarwa juna murmushin yaƙe na rashin sabo.

Buɗe taro akayi da addu'a sannan AL_HAJI SAMEER da matansa suka shiga jero nasihohi akan zaman Aure da ladan dake ciki, muddin za'a daure ayi haƙuri to akwai riba a gaba, domin shi Aure akwai farin ciki a ciki sannan kuma akwai akasin hakan, daga ƙarshe dai aka kuma rufe taro da addu'o'i sannan aka sallami kowa.

WASH£ GARI
Chapter 50 · 0% Book details