← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 92

Sashe 7

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Okay natsu kwantar da hankalinki sai kimin magana" Haleesat ta faɗa tana ƙara waro ido tana bin xixin da kallo gabaɗaya ta fita hayyacinta kamar ba ita ba, ajiyar zuciya ta kuma saukewa a karo na babu adadi sannan ta kira sunanta.

A Hankali "xixi! faɗamin abinda ya faru kinji?, kodai baƙyajin daɗin zaman gidan Uncle Yunus ne?, girgiza kai xixi tayi alamar a'a, "to menene ko a school ne?", nanma girgiza kanta ta kumayi alamar dai a'a. "to kin gaji da paris ɗinne kinaso ki dawo Nigeria gurin mu?.

Girgiza kai tayi, sai kuma da sauri ta É—aga kanta alamar eh Hakane, murmushi Haleesat tayi sannan ta ce "wato kewar mu kike yi ko?", eh xixi ta faÉ—a tana sauke ajiyar zuciya to yanzu me kike nufi Haleesat ta Tambaya tana jiran amsa.

Dan kuwa tasan xixi ɓoye mata kawai tayi wannan dalilin bashi zaisa ta rame haka ba akwai dai wata a ƙasa.
"Okay kinsan menene ki daure ki kwantar da hankalinki ki samu ki ƙarisa wannan term ɗin kinga yanzu kina level one going to level two ki daure ki ƙarisa kin san dai daddy baya tolerating nonsense ki daure ki ci gaba karatun ki nasan ba gaskiya kika faɗamin ba amma na miki uzuri duk time ɗin da kikaga ya miki zaki iya faɗamin abinda ke damun ki, kinji ko Tawan," Da to xixi ta amsa tana sakin murmushin ƙarfin hali.

"Okay to sharre hawayen naki kinji baby xixi na Autar momy kuma Autar gidan mu daga ke ba ƙari ko anaso ko ba`aso," Fashewa da dariya xixi tayi, ita ma Haleesat ɗin dariyar takeyi.

Muryar Labiba taji ta bayanta da sauri ta juya tsaye take, ta harÉ—e hannayenta ta baya tana sanye cikin Turkish gown riga doguwa milk color bata sa mayafi ba sai veil da ta yafa a kanta fuskar nan nata a É—aure tawau.

Qarisowa tayi saman gadon ta zauna sannan ta ce "Aunty leesat karki bi ta wannan yarinyar tunda ta iya zurfin ciki tun one week da ya wuce take wannan kukan anyi lallashin duniyar nan ta faɗa abinda ke damunta taƙi faɗa," Labiba ta ƙarishe tana hararar xixi.

Dariya Haleesat tayi sannan ta ce "ae kunfi kusa ko kin manta saboda ke ta dawo nan ƙasar da karatunta ta barmu Anan,"

Dariya Labiba tayi ta ce "gashi kuma taƙi faɗamin abinda ke damunta gabaɗaya na shiga damuwa," "ae rabu da ita kawai idan taji wuya zata faɗa ne" Haleesat ta faɗa tana murmushi, "ke dae Aunty Leesat barta kawai karma ta faɗaɗin zamuga wanda zai bari ta dinga yin ƙunci a gidanan," Labiba ta faɗa tana ƙara tamke fuska alamar bada wasa take bah, nan dai Haleesat da Labiba suka ci gaba da fira tsakani,ita kuwa xixi idan taga dama ta saka musu baki idan kuma bata ga dama ba sai dai tabi su da ido, sun ɗauki lokaci suna wayan kafin suyi sallama Haleesat ta kashe wayarta a hankali ta lumshe kyawawan idanun ta.

Tunani ta faɗa lokacin da xixi ta kammala secondary school ɗinta, lokacin xixi dagewa tayi sai ta koma paris da karatu wajen Uncle Yunus ɗinsu wai tare takeso su ci gaba da karatun tareda Labiba ɗiyar Uncle Yunus a paris dayake, Age mate Suke Labiba taba xixi wata biyu a duniya, alokacin har ciwo ta kwanta dan daddy ya hanata zuwa paris karatu saida ƙyar aka samu ya barta ta tafi shine yanzu wai kuma zata dawo itama tasan ba'a take dan daddy ba yarda zayyi ba har saita kammala degree tukunna, murmushi Haleesat ta saki a fili tace xixi rigima silly girl kawai kuma autar gidanmu😝

Tashi tayi ta faÉ—a wanka takai tsawon mintuna talatin kafin tafito É—aure da towel White color.
Gaban dress mirror ta tsaya tana busar da dogon gashinta da handDrier saida ta busar da gashin, sannan ta aje Drier É—in a mazaunin shi.

Shiryawa tayi cikin indian dresses gown iya gwiwarta pink mai adon stones purple da wando jeans pencil dogo pink and purple shima, ribbons tasa ta tufke sumarta da ƙyar don yawan da sumar take dashi domin kuwa kaf gidan daga Zaynerb sai Haleesat sune masu tsayi da yawan gashi over highly,ita dai Afeefah sai dai ta nuna musu yawan gashi sosai domin gashinta akwai yawa sosai don ya wuce gadon bayanta ya sauka har mazaunanta.
Ɗaukar mayafin kayan tayi ta yafa akanta ba tare da tasa hula ba tana shirin ɗaukar wayarta domin kiran Wata Maryam classmate ɗinta domin su tattauna akan Bikin maryam ɗin daya kusa, Ta tajiyo muryar momy a palo tana ƙwala mata kira.
Palon ta fito ta sama guri ta zauna a saman two siter ita ma momy Rafi`at É—in guri ta samu ta zauna tana fuskan tar Haleesat É—in "Haleesat".

Momy ta kira sunan ta ba tare da ta É—ago daga latsa wayar da takeyi ba ta amsa da "na'am momy akwai wani abune?"

Gyara zama Momy Rafi'at tayi bata damu da yanayin yadda Haleesat ta amsa mata ba ta fara magana.
Haleesat ki natsu magana mai muhimmanci nakeso muyi dake Yanzunnan.
Mayar da wayar dake hanunta gefanta Haleesat tayi sannan ta fuskan ci momy Rafi`at É—in "Yeah! inaji wata magana ce wannan ?".
"Haleesat yanzu haka zamu saka ido a Gidannan wannan shegiyar Yarinyar nan ta dinga juya kowa yadda takeso kamar wasu bayinta ki duba ki gani ɗazu da zata fita a gaban mu taba wancan kucakar House maid ɗin can sa'adah dubu ɗari biyu, to wallahi idan muka bari irin haka ta ci gaba da faruwa tofa wata rana Gidannan sai yafi ƙarfin mu gashi ɗazu naji wai ana maganar an zaɓe ta a gasar 𝐒𝐀𝐑𝐀𝐔𝐍𝐈𝐘𝐀𝐑 𝐊𝐘𝐀𝐔 matakin jaha kuma naji ana maganar saura one month.....
ÆŠan tsagai tawa da maganar Momy Rafi'at tayi tana kallon yadda Haleesat ta mayar da hankalinta gabaÉ—aya kanta tana sauraronta.

Murmushin gefan fuska Tayi sannan ta ci gaba da cewa "Kuma tana cin gasar nan nasan ba za ta tsaya ba saita je na ƙasa daganan kuma saina duniya,mu kuma Zuwa Lokacin baƙin ciki Ya kashe mu"😱

"Yanzu na yanke shawarar kota halin qaqa bazan bari taci gasar nan ba gobe zanbi Flight zuwa China gobe."
"Na Rantse da Allah Mai girma indai ina numfashi a duniya bazan bar yaran haajarah su huta a duniya ba yaran da mijina ya fifitasu sama da nawa yaran" ta ƙarishe maganar tana huci kamar wata kububuwa..

Miskilin murmushin gefen baki Haleesat tayi sannan ta ƙara gyara zaman ta akan Royal sofa ɗin kana ta fara magana, momy kenan wani lokacin kina bani mamaki saiki dinga abu kamar yarinya yanzu wannan ƙaramar alhakin ne saikin Tafi har can China akanta, irinsu makirci ma kaɗai ya ishesu yanzu ga YaYarta Zaynerb duk da bansan ko Menene ainihin abinda ya sakata a Halin shayashaye ba amma nasan da saka hannunki ciki sabosa nasan wacece ke sama da kowa right, ɗan shiru Haleesat tayi yayinda suka shiga kallan kallo tsakanin ta da mahaifiyartata Momy Rafi`at,wai akuya ta mari kura, wani ƙayataccen Murmushin gefan fuska Halessat ta kuma saki sannan bata damu da kalar fitinannen kallon da Momy Rafi`at take mata ba ta ci gaba da cewa, "Ae koshi kaɗai ya ishesu a Rayuwa ma ba sai an ƙara musu da komai ba,Haleesat ta ƙarishe maganar tana kuma sakin shu'umin murmushin gefen baki...

Wata Kalar Dariyar Bosawa Momy Rafi'at ta fashe da ita tana tafa hannu tace yanzu nasan na haifa Æ´a duk sauran yarana duk wawayene yanzu nasan na haifa Yarinyar da zata maramin baya a duk shirina. Haleesat É—iyata Allah Ya suburbuÉ—a miki Blessed highly highly kuwa.

Dariya Haleesat tayi ita ma harda ba momy hannu suka tafa kamar wasu yara ba ƴa da uwa ba { T⨳o⨳f⨳a⨳h⨳ T⨳o⨳ A⨳l⨳l⨳a⨳h⨳ y⨳a⨳ k⨳y⨳a⨳u⨳t⨳a⨳ }

A hankali Zaynerb dake laɓe a bakin ƙofar bedroom ɗin ta fara Ja da baya tana rufe bakin ta da duka hannayenta jin wani irin kuka nason qwace mata, Yayinda gabaɗaya Jikinta babu inda baya rawa na tsananin tashin hankali data shiga, Da gudu ta shige ɗakinta ta rufe da key.

Ta faɗa saman bed tana sakin wani marayan kuka ta na ƙarajin mamakin hali irin na Momy Rafi'at, ita batasan me ita da ƴar uwanta suka tarema matar nan ba tabi ta tsanesu a Rayuwa duniyar su, share hawayenta tayi ganin ba kuka ne abin yi ba tashi tayi ta zauna a saman bed tana ƙara tuno yadda taji firan Momy Rafi'at da Haleesat ɗin, Farkon Abin ta fito da niyyar tafiya ɗakin Haleesat suyi magana akan matsalar xixi taji magana ƙasa ƙasa shine ta tsaya dan taji me ake cewa dan ita da farko ta ɗauka Haleesat ɗince take waya da ƙawayenta ashe abin ba haka bane, Gashi taji abinda yafi ƙarfin tunanin ta ashe Haleesat kallon kishe akema rogo muguwar makira ne ba'a sani ba, murmushi tayi sannan a fili furta China ko zanga yadda za'aje china kuwa, Ubangiji Allah ya kaimu goben da rai da Lafiya😇.

Miƙewa Tayi sannan Takai dubanta ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta ƙarfe ɗaya da kwata na rana.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta nufa gaban dress mirror ta cire agogon hannun ta sannan ta shiga bathroom, Alwala ta ɗauro ta fito ta shimfiɗa sallaya sannan tayi sallar azahar bayan ta iddar da sallar ba tare da ta cire hijjab ɗin da tayi sallah ɗin ba ta fito daga bedroom ɗinta, kai tsaye kitchen ta wuce Auntie sa'adah ta samu tana aikin abincin Rana, Da murmushi ɗauke a fuskar ta ta ce "Auntie sa'adah sannu da aiki baki wuce ba kenan?", Ita ma murmushi tayi ta ce "sai zuwa ƙarfe uku na rana zan wuce insha Allah.

"Okay aunty akwai wani Abu na musamman a kitchen ɗinnan kuwa wanda mai ƙaramin ciki zata iya buƙata na marmari?".

Murmushi Auntie sa'adah tayi sannan ta ce "eh mana Zaynerbu Abuuu akwai, baza`a rasa ba. "Yawwa Auntie a haɗomin akwai mai buƙata cewar Zaynerb tana murmushi, "Ae inaga zatafi son kwaɗo ko bari nayi ma ta shi kinsan mai ciki akwai son kwaɗayi, "Aikuwa dai Auntie sa'adah ita wannan cikin nata wata huɗu ne shigan na biyar, Zaynerb tayi maganar tana zama a ɗaya daga cikin chairs ɗin dining da aka qawata kitchen ɗin dasu.
Chapter 7 · 0% Book details