Sashe 48
Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin ƙanƙanin lokaci suka kammala jere komai akan lodojin, sannan Elina ta dawo ta faɗawa Momy Rafi'at sun kammala, kana ta koma ciki.
Magana Momy Rafi'at ta musu gaba É—aya mutanen palon suka tashi suka nufa wurin cin abincin, kowa ya zauna a wurin da ya dace dashi, yayinda Ummi take binsu É—aya bayan É—aya da roba da ruwa a hannunta suna wawwanke hannayensu a ciki, sai da suka kammala tsaf sannan ta koma ciki.
Su kuma suka fara ɗu'amun sannu a hankali cikin nutsuwa.🥳
A hankali Deejarh dake zaune gefan Afeefah, ta matsa da bakinta sai tin kunnen Afeefah É—in tana faÉ—in "Balarabiyar India, shin zan iya tambayar ki wani abu?."
Afeefah ta ce "Inajin ki."
Deejarh ta ce "WaÉ—annan matan da suka raba abinci, su kuma daga ina suke?, Naga ma harda arniya a cikin suðŸ˜."
Murmushi Afeefah tayi dama tuni ta rubuta ta aje cikin zuciyarta sai Deejarh ta ma ta wannan tambayar. Ita ma cikin ɗan ƙasa da murya ta bata amsa da cewa "Ma'aikata ne su, wa'innan da kike ganin su Degree, garesu akan fannin girge_girge anan gidan namu suke aiki ana biyansu Salary mai tsoka, duk wata."
Deejarh da mamaki ya kamata ta ce "To meyasa kusan kwanana goma anan, amma ban taɓa ganin su ba sai yau kuma yanzu?."
Afeefah ta bata amsa da "Saboda sun tafi gida hutun watanni har biyu ne, yau suka dawo shiyasa bakisan su ba."
Deejarh tana gyaÉ—a kai alamar gamsuwa da bayanan Afeefah ta ce "Ooho kice ba'a nan garin suke ba kenan?."
Murmushi Afeefah ta kumayi, ita fa Wallahi bata gajiya da shirmen tambayoyin da Deejarh take ma ta, saima sakata nishaɗi da suke yi🤣
Ta ce "E, ita Ummi anan kusa take amma dai bansan sunan garin su ba, sai dai wata ƙila ma, anan Abuja suke zaune. Ita kuma Elina Ƴar Lakwaja ce, ita ma dai bansan sunan ainihin garin da take ba..."
"Wai kam nace gossip É—in wa akeyi ne haka, naji anata qus qus fa?."
Cewar Husnee tana kallon su Afeefah É—in.
Dariya Deejarh tayi ta ce "Sirri ne, tsakani na da Balarabiyar India ta."🤥
"Oh tunda haka ne, bari na barku ku ci gaba, ayi gulma da kyau guy's."
Husnee tayi maganar tana mayar da hankalinta wajen cin abincinta.
Hayaniyar da suka ji, yana tashi ne daga can waje yasa duk sukayi shiru, suna so su fahimci abin da ke faruwa.
Jin da sukayi hayaniyar ba mai ƙarewa bane, yasa ba shiri gaba ɗayansu, suka mimmiƙe suka nufa waje domin ganin abin da ke faruwar.
Gaba É—ayansu fitowa sukayi waje, don ganin komai. Daga can tsakiyar compound É—in gidan suka hango gaba É—aya ma'aikatan gidan sunyi curko curko dasu, ga wani saurayi ya juya baya yana zuba musu ruwan masifa kamar wanda baya cikin hankalin shi.
Da sauri suka ƙarisa wurin su duka Daddy yana tambayar Peter mai bawa flowers ruwa abin da ke faruwa. Cike da girmamawa Peter yake faɗi cikin hausar sa wacca bata gama karyewa a harshen shi ba.
Yace.
"Sir wannan ne,"
Ya nuna saurayin dake faman zabga masifa kafin ƙarisowarsu wurin amma suna ƙariso yayi tsit sannan kuma yaƙi juyowa.
"Sir tun ɗazu yake ƙoƙarin shigowa ciki, yana faɗin gidan sune wai, mu kuma bamu sanshi ba, munƙi bashi dama, shi kuma ya dage, ya dage akan sai ya shigo, har yana marin Moses fa, shi ne mu kuma muka dage muka hanashi shigowa Sir."
Peter yana maganar ne, yana gwada musu yadda saurayin yakeyi wai. { kuma dai masu karatu kunsan yadda Yare suke Especially ma idan suna so a Yarda da abin da suke faɗa 😆 }.
Ɗan murmushi Daddyn Yayi ganin yadda Peter ya dage yana bayani, bayaji baya gani, ba kuma ƙaƙƙautawa.
Sannan Mister Mai Kyau É—in, ya mayar da kallon shi akan saurayin wanda
yake sanye cikin riga Top blue mai gajeren hannu, sai kuma wando Crazy Jean's wanda ya tsaya mishi iya gwiwa black color, ya saka p-cap black akanshi ga kuma face mask black, shima dai. Ya goya Backpack irinna na masu tafiya a bayanshi, ƙafafunnshi kuwa Boots ne blue color, ga kuma wani akwatu yashe a gefansa.
Cikin jin É—an faÉ—uwar gaba, wanda baisan dalili ba, Daddyn ya fara magana kamar haka.
"Yaka É—an saurayi, shin zaka iya jiyowa domin muga fuskarka da kyau kuwa?."
Shiru saurayin yayi kamar ba zai juyo ba, sai can ya juyo gaba É—ayanshi tare da cire face mask É—in dake a fuskarshi nan take kyakyawar fuskarshi ta bayyana.
Tundaga kan Momy Rafi'at wacca ko'a mafarki ba za ta taɓa manta wannan kyakyawar fuskar ba...
Da Nailah wacca gaba É—aya tsananin mamaki da ruÉ—ani ya bayyana a kyakyawar fuskarta.
Ga Haleesat wacca ko daga bacci ta tashi ba zata taɓa mantawa da wannan fuskar ba.
Ba re Lailah wacca kullum take kwana take tashi da tunanin wannan saurayi da kyakyawar fuskarsa a kullum.
Zaynerb kuwa, ita bama za'a iya cewa komai ba, domin kuwa, she was very thither shock.
Gaba É—aya suka haÉ—a bakunan su wajen faÉ—ar
"BUDDY."
Afeefah da ƙarisowar ta wurin kenan ita da Nainarh da kuma Deejarh, taji maganar a kunnuwanta tamkar saukar adu.
Da wani irin sauri take wuce mutane harta ƙarisa gaban shi ta tsaya cak tana kallon shi kamar yadda shima yake kallonta.
Cikin sarƙewar murya da wahalar fitar numfashi take faɗin
"YaYa Maleek..! kaine kuwa..?"
Lallausar murmushi ya saki, sannan yace
"Ni ne dai Yaya Maleek ɗinki mai ƙaunar ki, yau gani na dawo gareki, shin ba za ki zo kiyi Hugging ɗina ba kamar yadda kika saba a koda yaushe?. MY sweet Blood 6ter?."
Yayi maganar yana buÉ—e ma ta duka hannayenshi.
Da gudun tsiya Afeefah ta nufa gurin shi, da niyyar zata rungumeshi, kamar yadda ya buƙata.
Sai dai kafin ta ƙarisa wurin sa, ta zube a ƙasa sumammiya.🤕
🔥ᴛᴀsʜɪɴ sᴇɴsᴇ🔥
Ai da wani irin sauri Maleek ya jefar da Backpack dake rataye a kafaɗunshi, Yayo kan Afeefah da gudu yana kiran sunanta da ƙarfi ya kai Hannu kenan zai taɓa ta.
Cikin mugun buga tsawa Nainarh ta dakatar dashi da faÉ—in
"Kar ka sake ka taɓamin Ƴar uwata da wannan ƙazamin hannun naka.🤨
Cak Maleek ya dakata da niyyar taɓa Afeefah da ya yi.
Ya juyo da rinannun idanun shi waɗanda sukayi jajir lokaci guda, saboda tsananin ɓacin rai, yana kallonta.
Qarisawa wurin Nainarh tayi tana tafa hannu ta ce
"Sai Yau?, na ce yau ne ka tuna damu Buddy?."
Nuna Afeefah dake yashe maga shiyan a ƙasa tayi da hannayenta waɗanda suke tsananin rawa tana faɗin
"Dube ta baiwar Allah yau tana cikin farin amma da zuwarka kalla yadda ta ƙare fa. Yanzu ka Faɗamin meyasa zaka zaɓa wannan ranar. This is only our glamorous Day, not yours, Amma... duba ka gani, daga zuwanka duba baiwar Allah yadda ta ƙare a sume fa."
Maganar take cikin hargowa da tsananin ɓacin rai gaba ɗaya ta manta wanda yake tsaye a gabanta, ta manta Buddy ɗinsu ne mai ji dasu, ta rufe ido tana zazzaga mishi masifa, tana fitar da duka baƙin ciki da damuwar da suka daɗe suna caccakar zuciyarta.😰
Zubewa Maleek Yayi gwiwo winshi duka a ƙasa yana zubar hawaye.
Hawayen da bai zubar dasu ba ranar da yabar gidan, Hawayen da ya daɗe yana jiran fitowarsu sai yau suka ƙari so. Saboda tsananin kuka ya ma kasa magana.
Shikuwa Daddyn su wato Mister Mai Kyau, Ashe tuni ya daɗe da yin sumar tsaye ba'a sani ba tun lokacin da Maleek ya juyo, da kuma tun lokacin da Shalelen shi ta zube a ƙasa sumammiya alamar ciwonta ne yakeso ya taso.
Ganin za'ayi to ne to ne ne, a tsakiyar gida yasa Uncle Yusuf kallonsu gaba É—aya yana faÉ—in
"Ku shiga daga ciki a ƙarishe maganar zai fi."
Yayi maganar yana kamo hannun Daddyn wanda ya zama kamar mutum-mutumi, sannan ya kalla Auntie Yusra yace da ita.
"Ku kamo Afeefah ku shigo da ita ciki,"
Kallon shi ya mayar kan Maleek da har yanzu yake a durƙushe, cikin sanyin murya Uncle Yusuf Yace
"Ka ɗauko kayanka ka shigo ciki." sannan ya yi gaba.😞
{*Tofah.! masu karatu, wai shin Menene ainihin abin da yake faruwa ne, a wannan labarin, gadai Maleek ya dawo gida, kuma ga Daddyn Ya zama kamar baya cikin hayyacin shi, gefe guda kuma ga Jarumar mu tana sume cikin wani hali, shin dama akwai wani ciwo ne da Afeefah take dashi ba'a sani ba🤔 koma dai menene yanzu zamuji asalin labari }... INSHA ALLAH 💘*}
*SARAUNIYAR KYAU*💓
_(The Glam Queen)_ 👑
```Takun Farko```
Story & Written By:
*_The Nainarh KD_*
____________________________________________👑
*THE ONGOING BOOK'S*
1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
_Batool Kamba_
2. *ZAN JIRA KA*
MALLAKAR
A'ISHA ALƘALI
_Mrs Aysib_
___________________________________________👑
*TH£ B£GINNING OF THE STORY*
*MAFARIN LABARI*
*SOM£ Y£ARS £ARLI£R*
*AL_HAJI SAMEER LAMIÆŠO*
Page*47&48*
Shararren mai dukiya ne, wanda duniya ke ji dashi, a domin kuwa ba iyaka ƙasar Nigeria sunanshi ya tsaya ba, hatta da ƙasashen waje sunanshi ya zagaya, yana da tarin dukiya mai yawa, Wanda shi kanshi baisan adadi ba, ga companies kala kala gareshi, kaf faɗin Nigeria ba State ɗin da babu companynshi, sannan kuma shine mamallakin wannan shahararren Industry na sarrafa magani wato S.L__ Pharmaceutical Industry. Dake Babban birnin Nigeria Abuja.
__AL_HAJI SAMEER LAMIÆŠO.
Asalin shi cikakken É—an garin Jigawa State ne, gaba da baya, sai dai mahaifiyar shi da ta kasance cikakkiyar Æ´ar Adamawa state ce.
Matan shi na Aure uku, matar shi ta farko ta kasance Hajiya Harirah wacca aka musu auren gida, Hajiya Harirah bata taɓa haihuwa ba tsawon zamanta da AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.
Sai kuma matar shi ta biyu Dr_Raheemah wacca ta kasance Balarabiya ce ta ƙasar Sudan.
AL_HAJI SAMEER LAMIƊO, ya haɗu da matar shi ta biyu Dr_Raheemah ne, a wani taron manyan Likitocin duniya da ya hallarta a ƙasar Sudan Babban Birnin ƙasar wato KHARTOUM, a lokacin kallo ɗaya yayima Dr_Raheemah yaji ta kwanta mishi.
Aikuwa bayyi wata wata ba bayan kammala taro ya sameta da zance.
Tom da ya ke ita ma Dr_ Raheemah tun daga kallon farko taji ta kamu, sai ba'aja zancen da nisa ba, duk da dai da farko Ahalinta sunso su bada matsala kasancer AL_HAJI SAMEER LAMIƊO baƙar fata.