← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 92

Sashe 84

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Tayi shiru ganin waÉ—anda suka shigo, sai kuma da gudu ta koma cikin bathroom É—in tana faÉ—in

"Kai Balarabiyar India kun Bani kunya. Dan Allah ku fita na fara shiryawa."

Dariya Lailah tayi tana zama saman doguwar kujera dake cikin bedroom É—in sannan ta ce

"Ae Yarinya idan zaki fito kawai ki fito, dukkanin mu ma ta ne anan, sannan kuma mun riga ki shan iskan duniya gaba ɗaya, so banga abin da zaki ɓoyemin ba, bayan kuma nima ɗin, ina dashi, Yarinya ki fito kawai ki ci gaba da Raira waƙarki ta Sani Ahmad domin kuwa akwai daɗi, wato KUJERAR SO."

Afeefah kuwa murmushi kawai tayi sannan ta ƙarisa wajen study chair dake bedroom ɗin, ta zauna tana faɗin
"Kinji Deejarh fito abin ki bari mu rufe ido kinji tawan."🤓

Kamar zatayi kuka Deejarh ta ce "Please Balarabiyar India ku koma kafin na shirya, ko kuma kiɗan miƙomin doguwar gown ta Bacci a cikin wardrobe nawa pleased."

Jin haka yasa Lailah miƙewa da sauri tana faɗin

"Bari na kawo miki kinji."

Tayi maganar tana nufar wardrobe sannan ta buɗe ta zaɓo wata sleeping dress black color mai taushi, sannan ta ƙarisa bakin ƙofar bathroom ɗin tana faɗin

"To gashi ki karɓa, da sauri ki saka tun kafin nayi fushi na mayar."

Jin haka yasa Deejarh zuciyarta guda ta ɗan turo ƙofar bathroom ɗin da ta Rufe, a hankali sannan ta zuro hannunta tana amsa wa da

"To Auntie Lailah ga hannuna ki bani kinji."

Ganin haka ita kuma Lailah ta mayar da sleeping gown É—in Left hand É—in ta sannan tasa right hand nata ta kamo Deejarh gaba É—ayan ta tayo waje da ita tana dariya.

Da gudu Deejarh ta haye saman bed ta ƙudun duna da bedsheet tana mayar da Numfashi ta ce
'Dan Allah Auntie Lailah ki Bani."

Murmushi nishaɗi Lailah tayi sannan ta miƙa ma ta sleeping gown ɗin tana faɗin

"Riƙe badan halinki ba."

Da sauri ta karɓa tana dariya sannan ta ce
"To ki Rufe idon ki sannan."

"Wannan ne kuma baki isa ba, Yarinya ni banga Abin ɓoyewa ba, bayan kuma duka muna dasu."

"It's okay wato dai bakiga Abin ɓoyewa ba ko, ke muguwa kin saka ƙaramar Yarinya gaba kina zalunta ko?."

Cewar Afeefah.

Kafin Lailah ta sama damar magana Deejarh mai baki, ta ce

"Tabɗi jan, Balarabiyar India, kinji ki da Wani zance. Yanzu ni ce ƙaramar Yarinyar, aikuwa bakiyi dai dai ba, domin kuwa a ƙauyen mu ae kamata tanada Yara biyu ko uku."

Zaro ido Lailah dake zama a doguwar kujerar da ta zauna da farko tayi sannan ta ce

"Haba sai kace wani Rayuwar Jahiliya ni dai ban Yarda ba gaskiya."

"Okay Tunda baki Yarda ba Wani Lokacin ki gwada zuwa ghetto Area, ko kuma wani ƙauye dake kusa, kiga Abin mamaki, domin kuwa zakiga mace wacca a shekaru ba za ta wuce twenty five ba, da Yara shida ko bakwai tana fama."

Cewar Deejarh iya gaskiyar ta.

Kallon Afeefah Lailah tayi tana cewa

"Wai Haka ne?."

Tayi tambayar da alamar Rashin Yarda Riƙe da Baki.

Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Of course yes, da Yawa ana samun Hakan."

Daga faÉ—in Haka tayi shiru.

Ajiyar zuciya Lailah ta sauke sannan ta ƙariso wurin da Afeefah take zaune Ta ce

"To malama Feefah Yanzu sai mun roƙa za'aba mu secret gift box mu gani ko kuwa?."

Murmushi Afeefah tayi sannan ta miƙa ma ta duka box ɗin tana faɗin

"Gashin nan Miss Lailah ayi ta gani."

Da sauri Lailah ta karɓa box ɗin sannan ta koma saman doguwar kujerar ta zauna, tana buɗe secret gift box ɗin, da sauri Ita ma Deejarh da ta kammala sanya sleeping gown ɗin a jikin ta, ta ƙarisa wurin tana gani cike da farin ciki game da tsantsan nishaɗi da zaƙuwa. 😁

Qayataccen murmushi Mai kyau Afeefah mai kyau take ta faman saki ganin Yadda gaba ɗaya Lailah da Deejarh suka bi, suka shiga confused, na ganin wannan ƙayatattun diamond wristwatch da Diamond Ring, diamond chain and earings harda check na kuɗaɗe.

Ita dariya ma Lailah ta bata sai kace ba ɗiyar Mister Mai Kyau shahararren mai dukiya na ala tsine uwar mai ƙarya ba, koda yake ba ganin wa'innan abubuwan yasa ta wannan ruɗewar ba, harda na tayata murna, kuma taji daɗi mara misaltuwa da Hakan.

A hankali ta miƙe tsaye tana tafiya a hankali kamar mai tausayin ƙasa. Yayin da ƙafafunta suke nutsewa cikin carpet tattausa dake baje tsakiyar Room.

A hankali takai hannunta sannan in slow ta Ya ye curtains Milk color dake Rufe da Windows na room É—in.

Buɗe glass windows ɗin tayi duka, Yayin da Yanayin yadda iskan garin yake kaɗa wa Ya yi dai dai da Yanayin nishaɗin da take jin kanta ciki, zuciyarta cike take da nishaɗi sosai sannan kuma bata Fatan wani abu yazo ya gifta tsakanin wannan Rayuwar farin ciki da nishaɗi da take ciki, ita da Ahalinta daɗi da ƙari daga ƙarshen ƙarshe dai ga Yaya Maleek nata ya dawo Gida.

Bayan shafe tsawon shekaru Bayanan.

Tasa ni cewa dukkan wani ɗan Adam Yana tare da ƙaddarar sa, koda kuwa yana ƙarshen duniya ne.

So ita tana fatan ta ta ƙaddarar ta kasance ma ta a Yayin da take cikin Ahalinta, bata Fatan wani abu yazo ya rabata da Ahalinta, Especially ma Daddynta, Auntie Zaynerb nata, Lailahnta, Deejarh da kowa da kowa.

Koda kuwa Aure ne tofah tafiso ta zauna kusa da Ahalinta gaba ɗaya cikin farin ciki da ƙaunar juna.

A Wani mugun tsora ce ta zaro fararen idanunta cikin Æ´an sakannin da suka shuÉ—e tana cikin nishaÉ—i, amma kuma cikin Æ´an wa'innan sakanni da bazasu wuce biyu zuwa uku ba, ta shiga matsanancin violence sosai, dalilin Haka kuwa shi ne.

Hango Auntyn ta Zaynerb kuma abar ƙaunarta cikin swimming pool tana iyo ciki ba tare da numfashi shi ba, to abin da ya faru shi ne, sai da Zaynerb ta cike mintuna biyar cikin ruwan ba tare da numfashi ba, sannan ta fito.

Tofah Wajen fitowan ne aka so a sama akasi, Allah ya kare, domin kuwa wajen riƙe Banister's na madaidaicin Benen da zata fito daga cikin swimming ɗin ne, zata riƙe bata riƙe da kyau ba, shiine fah.
Tayi baya zata koma cikin ruwan ta baya, sai Allah ya kiyaye ta riƙo Banister's ɗin da Left hand nata.🤯

Wata kalar ajiyar zuciya afeefah ta sauke, tana dafe saitin ƙahon zuciyarta. Yayin da idanunta kuwa har wasu qwallan farin ciki ne, suka taru sai faman haki take saukewa, duk da cewa ba ita bace ta kusa anta yawa cikin Ruwan.

Tana tunanin da'ace Zaynerb ta faÉ—a cikin ruwan, idan ba wani ikon Allah ba, da wuya a ciro ta da rai.

Saboda Yanayin yadda tayi bayan, gaba É—ayanta ba wani abu da zata iya.

Shiyasa ita bata damu da wani iyo cikin ruwa ba, ko kuma ta dama kanta da saita Iya tsawon mintoci cikin Ruwa ba batare da numfashi ba.

Tasan Allah shike karewa amma gaskiya hanyar lafiya a bita da shekara.

Koma wa tayi wurin su Lailah suka ci gaba da fira sama sama. Yawancin firan nasu akan Yanayin rayuwar poor people ne.

A taƙaice dai sai wuraren can cikin dare sannan Afeefah da Lailah suka koma bedrooms nasu bayan sun sha fira cike da farin ciki.

*Haleesat Mai Kyau*

Ɓangaren Haleesat kuwa, bayan fitarta daga bedroom na Afeefah, kai tsaye bedroom nata ta wuce, wanka ta fara yi sannan ta shirya cikin sleeping dress fanjama Riga doguwa fara mai taushi.

Sai da ta kammala duk wani al'adarta kafin kwanciya Bacci, sannan ta kwanta saman royal bed nata Yayin da ta zuba wa kyakyawar fuskar wanda ke rufe cikin face mask Souvenir Abin tunawanta ido tana kallo, tamkar ba zane take kallo ba.

Duk da cewa sau ɗaya tak ta taɓa ganin sa.

Tsayin rayuwar ta sannan a lokacin wata kalar ƙaunarsa ta shige ta duk da cewa bata ga fuskar sa ba.

Confirm tasan wasu zasu kirata da zararriya, ko kuma wacca ta sama taɓin hankali, amma ita ba zata damu ba, domin kuwa kyawawan idanun sa, kawai take tunawa a ganin ta yin soyayya ko kuma faɗawa soyayya, ba dole sai da wani dalili ba, domin kuwa yin soyayya ko faɗawa cikinta baya buƙatar wani dalili.

A hankali ta furta a saman laɓɓanta

"My souvenir Yaushe, a'ina wani lokacin na ƙosa sosai, da na ƙara ganin ka na ƙosa highly, Ranar da zanga beauty face naka tazo a Ranar ko'a gaban waye sai Nayi Rawa da juyi."

"Ina son ka daga kallon farko, ina son ka daga haɗuwar farko, hallaudai, I LOVE MY SOUVENIR. Please! sweet Dream Good Night, My love."🥰

Ta daÉ—e hakan cikin magana ita kaÉ—ai da paper É—in hannun ta, har can bacci Ya É—auketa bata san lokaci ba.

_-_ To Miss Haleesat Mai Kyau Zararriyar Your Souvenir Good Night_-_💃💃

"MY Feefah Baby.!"

"My feefah baby..."

"Umhm, My Baby."

"Kin san wani abu kuwa?."

"Umm umhm."

I Love So Very much, Thither I Love For the All My heart, please, Say me. You Love Me please My feefah?."

"umhm umm No Way."

Juyi kawai Take yi gaba É—aya tabi ta haÉ—a uban gumi tamkar Babu a.c cikin bedroom É—in, sai faman faÉ—in "Umhm um."

Take yi tana ƙara wa da kalmar "No Way."😉

A hankali ta buÉ—e kyawawan fararen idanunta, kai tsaye ta sauke su saman haÉ—aÉ—É—en ceiling.

Shiru tayi tana tariyo gaba É—aya mafarkin da tayi.

Gaba É—aya yasha banban da kalar wanda take yi kwana biyu, wancan tana yi ne akan Haleesat da wata mummunar Mata take so ta cutar.

Wannan kuma wanda tayi a yau, wai ita da wani haɗaɗɗen ƙasaitaccen matashin saurayi ne, wai Yake roƙonta akan ta soshi, sai dai kuma bata samu ta kalla fuskar sa ba ta farka.😇

Juya idanun ta tayi tana ƙarewa bedroom ɗin kallo, gaba ɗaya pillows ɗin sun zube ƙasa, kowanne da ɓangaren da Ya yi shi Kanshi bedsheet Tayi dai dai saman mattress ɗin a taƙaice dai, gaba ɗaya saman bed ɗin nata ya koma tamkar ansha bidiri saman sa.💃💃

Murmushi tayi ganin yadda bedroom ɗin ma gaba ɗaya ya koma, sannan ta miƙe tsaye, juya idanunta tayi kan clock, ƙarfe Biyar saura wasu mintoci.
Chapter 84 · 0% Book details