← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 92

Sashe 53

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Qwafa taja sannan a fili ta ce "Haleesat Rashid Rayyan You are die.! Wallahi."

Cikin gidan ta koma tana kuma imagine yadda zata ɓullowa wannan guy ɗin dan ta lura He was arrogant a nata tunanin.

___KWANAKI UKU GABA

Tun a ranar da Abubakar yaje gidansu Rafi'at, bai sama damar komawa ba, saboda bai ga amfanin komawar tashi ba, domin kuwa tun a ranar da yaje bayan ya koma gida, a maimakon ya yi tunanin Rafi'at, a'a sai dai kyakyawar fuskar Haleesat Rashid Rayyan take masa yawo a fuska, wannan dalilin yana daga cikin dalilan da ya sa bai koma ba.

Yau ta kama Sunday weekend Misalin ƙarfe biyar dai dai na marece. Ya shirya tsaf cikin shigar alfarma sai dai yau a maimakon ya yi shigar manyan kaya kamar yadda ya yi a ranar farko, a'a shiryawa ya yi cikin suit ash color.

Yauma dai shi kaÉ—ai ya É—auka motarsa mai kyau da tsada ba tare da escort ba, ya nufa gidan su Rafi'at, domin kuwa ya kasa jurewa, burinsa kawai ya yi tozali da kyakyawar fuskar Haleesat Rashid Rayyan, a dalilin da shi kanshi bai sani ba.

Cikin Motar ya tsaya bai fito ba bayan gate man ya wangale mishi gate isarsa gidan.

Wayarsa ya a trouser pocket sannan ya dannawa Rafi'at kira, bugu ɗaya ta ɗauka da sallama, amsawa ya yi sannan a taƙaice yace da ita

"Na ƙariso."

Kana ya kashe wayar ya fito ya jingina da motar yana latsa wayarsa sannan kuma yana ayyano yadda zai samu ya ganta a yau.

Yana tsaye jikin motar ya hango ta yauma kamar kullum sanye cikin Arabian gown white color mai adon flowers coffee color tayi rolling kanta da mayafi coffee color, tayi kyau sosai kamar a sace.

Qarisowa wurin tayi tana murmushi ta ce "Barka dai Mister Mai Kyau, ina Fatan kazo lafiya."

"Yeah am normal."

"Good please ga wurin zama daga can gefe fa."

Tayi maganar tana masa nuni da wani ƙayataccen balcony na hutawa wanda daga ciki kujerune na zama farare, ga glass table a tsakiya saman shi kayan marmari na alfarma ne kala kala.

"Okay shall we."
Qarisawa wurin su kayi a tare sannan taja masa kujera ya zauna, ita ma ta zauna tana É—an janshi da fira.
Amma shi gaba É—aya hankalinsa baya a kanta waige waige kawai yake ta inda zai hango Haleesat Rashid Rayyan sai dai Rashin sa'a, dan kuwa duk iya waige waigen shi ko mai kama da ita bai gani ba.

Duk waige waigen shi Rafi'at tana ankare dashi.

Murmushi tayi a fili a zuciyarta kuwa cewa take "Ai Malam Mai Kyau ka gama waige waigen ka, indai Haleesat Rashid Rayyan ce, ko mai kama da ita ba gani zakayi ba, a domin kuwa tana ciki na rufe ta a Bedroom."

Qayataccen murmushi ta kuma yi tana cizan laɓɓanta na ƙasa.

A hankali sannan cikin kashe murya ta ce "Mister Mai Kyau, please idan bazan takura ka ba, zaga iya ragemin hanya izuwa gidan Uncle Riyaz a domin na amso wani saƙo wajen matar sa Auntie Ramlat kuwa?."

Murmushi ya yi ke nan dai zai sama dama na ganin hasken Ranshi.🥳

"Okay babu damuwa shiga ki kira ƙannin naki, mu tafi tare."

Da wani irin mugun sauri ta kalleshi bakinta har wani rawa yake wurin faÉ—in

"Mene are You kidding me?."

Ta sauke ajiyar zuciya tana kuma danne abin da yake caccakar zuciyarta, cikin É—an sanyin murya ta ce

"Alright it's okay. Bari kawai na shiga na kira su, sai mu tafi taren."

Tayi maganar a É—an daburce sannan ta bar wurin cikin sauri sauri ta shige cikin gida.

AFT£R F£W MINUT£S

Su uku suka fito a tare Rafi'at Rafiq Rayyan, sai Haleesat Rashid Rayyan, sai kuma wata kyakyawar matashiyar budurwa wacca ba za ta kaisu a shekaru ba, Rafi'at da budurwar a tare sai Haleesat tana bin bayansu hannunta janye da wani madaidaicin Akwati.

Dukkansu suna sanye cikin shiga kala É—aya wato Arabian gown white color mai adon flowers coffee color, sai ma yafi coffee color da suka yi rolling kansu dashi.
Ƙari sawa wurin shi sukayi yana jingine da Motarsa yanzu kuma waya yake yi da alama abin da ya shafi harkokin kasuwancin sa ne.

Rafi'at babu abin da take saƙawa cikin Ranta fa ce duk yadda zata yi Haleesat Rashid Rayyan karta shiga cikin Motar Abubakar Mai Kyau, dan kuwa ba shi kanshi ba hatta da abin da ya shafeshi bata ƙaunar Haleesat ta raɓa.

𝗞𝗵𝗮𝗱𝗲𝗲𝗷𝗮𝗿𝘁𝗵 𝗦𝗮𝗯𝗶'𝘂 𝗬𝗮𝗵𝘆𝗮𝗵

𝗪𝗿𝗶𝘁𝗲𝗿 𝗢𝗳

Ŝ̬Â̬R̬̂Â̬Û̬N̬̂Î̬Ŷ̬Â̬R̬̂ K̬̂Ŷ̬Â̬Û̬
fιяѕт ѕтєρ

Ganin ya kammala wayar da yake yi ne, yasa cikin washe fuska ta ce dashi "Barka dai Mister mai kyau 2days Fatan kana lafiya?."

Murmushi ya yi cike da jindaÉ—in jin muryar ta na rashin dalili ya amsa ma ta da
"I'm very Normal, Fatan kema hakan, Ina Ƴan uku na?."

Murmushi Haleesat Rashid Rayyan tayi ta ce
"Oh Ƴan uku suna gidansu. Yanzu haka can zamu wuce ai."
"Okay harna ƙosa a ƙarisa domin kuwa nayi kewar Rashin jin su sosai."

Abubakar ya yi maganar cike da zoyala da nishaÉ—i kamar ba shike tamke fuska É—azu ba.

Kallon É—ayar budurwar dake tsaye gefe ya yi Yana faÉ—in
"Barkan ki ƙanwar mu kina lafiya?."

ÆŠan sosa kai budurwar tayi cike kunyar bata gaisheshi ba, sai shi ya gaisheta, ta amsa da
"Lafiya qalau Mister Mai Kyau, Fatan kaima hakan?."

Tayi maganar ne a Yayin da suka shiga Motar sa ita da Haleesat Rashid Rayyan a baya, sai Rafi'at a gaba, sai kuma shi bayan ya amsa ma ta sannan ya tada motar suka bar gidan.

A hanya a tsakanin Haleesat Rashid Rayyan da Abubakar Mai Kyau sai kuma wannan Budurwa mai suna Sailuba ne ake taɓa fira.

Yayin da gefe guda kuwa Rafi'at ta mayar da kanta tana kallon hanya amma can ƙasan ranta ji take kamar ta harbe Haleesat Rashid Rayyan kowa ma ya huta, daurewa kawai takeyi tana kuma ba kanta haƙuri, sai dai ta yanke a ranta suna komawa gida zata sama Dadynsu Alhaji Rafiq Rayyan da maganar Auren ta da Abubakar, kuma batason ya wuce sati biyu.

A haka har suka ƙariso gidan Uncle Riyaz! gaba ɗaya fitowa suka yi bayan ya yi parking a ƙofar gate na gidan.

Haleesat Rashid Rayyan da Sailuba suka yi gaba ita kuma Rafi'at ta tsaya suka yi sallama da Abubakar sannan ita ma tabi bayan su, shi kuma Yaja motar sa ya yi gida.

Haka abin dai ya ci gaba da tafiya kullum Abubakar sai yace gidan su Rafi'at fira, amma fa bawai dan ya yi fira da ita ba a'a.

Sai dai idan yaje ya saka ta kira masa Haleesat Rashid Rayyan suyi ta fira abin su, ita kuma a barta da kwasan Haushi.

Haleesat tun tana jin kunya harta ware sai abin ya zama idan zai zo ita take masa girki na musamman domin kuwa ita qwararriya ce ta fanin, shi kuwa haka zai ware ya kwashi gara.

Ana cikin hakan kuma aka saka Ranar Auren Rafi'at Rafiq Rayyan da Abubakar Mai Kyau, sati biyu a Ranar Rafi'at tayi kwanan farin ciki sosai, dan jinta take kamar wata amaryarsa ma.🤣

Shi kuwa ta ɓangaren Abubakar ba zai ce yana farin ciki da wannan Aure ba, haka zalika ba zai ce baya Farin ciki ba, abin dai ba yabo balle kuma wani Abu wai shi fallasa.

Haka Rayuwar ta ci gaba da wucewa ta ko wani ɓangare shiri suke, abin babu kama hannun yaro ta can Jigawa State ɓangarensu Hajiya Harirah ma duk shirya shiryen bikin Abu lele suke😘

Mutanen Lagos, France, Mai Duguri, Adamawa States harda ma mutanen Birnin London su Sagir da matarsa duk sun ƙariso, gaba ɗaya sun taho da matayen su haka su Zuwaira, Sakeenah, Jawaheer, Jummai.
Sai shirin bikin Abubakar Mai Kyau suke yi dama abu harka na masu Naira, ko da ba wani lokaci aka saka ba.
Abuja City nan ma dai shirin biki sukeyi amarya Rafi'at saboda tsananin farin ciki sai da ta zuba Ruwan sanyi a ƙasa tasha🤔.

https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20

*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*

*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*

*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*

{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}

💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>>

Page *53&54*

____*

Tun ana saura kwanaki takwas a ɗaura Auren, Abubakar ya dena zuwa gidansu Rafi'at domin kuwa bai ga amfanin zuwan nashi ba, ita ma dai Rafi'at ta wani ɓangaren jindaɗinta ne hakan, tunda dai wata magana zata dena shiga tsakanin shi da Haleesat Rashid Rayyan.

Rayuwa ta ci gaba lulawa kwanaki suna raguwa a kullum kwanan duniya lokaci daÉ—a ja yake yi domin shi baya jira sai dai a jira shi.

_____*

"An É—aura Auren Abubakar Sadeeq Sameer LamiÉ—o da zankaÉ—eÉ—iyar Amaryarsa Rafi'atu Rafiq Rayyan akan sadaki mafi daraja da cancanta lakadan ba Ajalan ba.'

Wannan maganar da wani maroƙi yake yi yana ƙarawa, ita ce ta dura a kunen Haleesat Rashid Rayyan tamkar Saukar Aradu.

Dafe kanta dake faman sara ma ta tamkar zai rabe gida biyu tayi da duka hannayenta babu abin da take furtawa a bakinta fa ce kalmar.

"Inna-lilahi-wa-inna-illahir-raji'un. Alhuma-la-sahla-illa_ma-ja'altahu-sahlan,wa-anta-taj'alu-l-hzana-idha-shi'ta-sahlan.

Ya Allah! Babu wani abu mai sauƙi sai abin da ka sanya shi ya zama mai sauƙi, kuma kai kana sanya tsanani idan ka so ya zama sauƙi.''

Haka kawai take iya furtawa a bakinta zubewa a ƙasa tayi tsakiyar Bedroom ɗin.
Wai meke shirin faruwa da ita ne?. wannan wata kalar makauniyar kaddara ce, ta rasa wanda zata so sai Saurayin Yayarta, a halin yanzu kuma miji a gareta...

"Kai! Kai!! Ya Allah! Allah na tuba, wannan wata kalar makauniyar soyayya ce?."😭

Ta furta a fili cikin matsanancin kuka, baiwar Allah gaba É—aya tabi ta fita a hayyacin ta, komai abin mutum ya ganta cikin halin da take ciki sai ya tausaya mata.

Ta daɗe a wurin tana gurzar kuka kamar ranta zai fita. Kafin daga baya jin an fara knocking bedroom ɗin, yasa ta miƙe tsaye da kyar, ta shiga bathroom wanka tayi sannan ta fito zuwa lokacin kumburar da idanunta suka yi, sun ɗan ragu ba laifi.

Cikin kayanta na Anko ita ma ta shirya tsaf, sannan tayi kwalliya sama sama ba domin ya ƙara ma ta kyau ba sai dan ya rufe kumburin idanunta.

Ɓangaren da Amarya da ƙawaye da Ƴan uwa suke ta wuce kai tsaye.
Chapter 53 · 0% Book details