← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 92

Sashe 68

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani Abun mamaki shi ne duk Yadda a kaso motar da Hajarah take ciki ta tashi Abu ya cutura.
Abu dai kamar wasa tun ana gwadawa cikin daÉ—in rai har aka koma gwada mota mota amma wani ikon Allah shi ne, duk motar da Hajarah ta shiga ciki ba zata tashi ba, amma kuma tana fita wannan mota zata tashi.

Abu fa kamar wasa anata abu ɗaya har wuraren ƙarfe ɗaya na rana ana kan abu ɗaya, sai daga ƙarshen ƙarshe ne, bayan Addu'o'i da suka dingiyi aka samu mota ta tashi.

Ajiyar zuciya ko wanen su yake saukewa gaba É—aya sun haÉ—a uban zufa barin ma dai Hajarah da takeji kamar me?.

Sallama suka kuma yi da kowa sannan suka ɗauki hanya, Bayan gate man ya wangale musu gate.💃

_____*

Sun bar Garin Abuja wuraren ƙarfe ɗaya da rabi na Rana sannan suka fara wuce garuruwa sun wuce Minna ba daɗewa ke nan suna shirin shiga Garin Kaduna.

Jikin Hajarah ya fara wani irin rawa ta ko'ina haɗa zufa take ga wasu ƙuraje da suka fara fitowa daga ko'ina na jikinta, da yake su uku ne a Motar ita da Dr_raheemah da kuma Hajiya Harirah, da Farko basu lura da abin da ke faruwa da ita ba, sai da suka ji ta fara nishin wahala, aikuwa nan take suka ba driver umarnin tsayawa.

Gefan kwalta ya samu sannan ya tsayar da Motar da yake suna a gaba ne, shiyasa suma sauran motocin da ke bayansu suka sama wuri suka tsai tsaya, sannan gaba ɗaya suka fiffito suna kallon Hajarah dake faman haɗa uban zufa ga wasu ƙuraje da suke feso mata tashi ɗaya, Abin gunin ban tausayi.😰

Da sauri Abubakar ya ƙarisa wurinta kana ya kamo hannunta cike da tausayawa ya kira sunan ta.

Kasa amsawa tayi saivma kallon sa da tayi cikin jin azaba ta ce

"Dan Allah mu koma gida, idan ba haka ba kuma mutuwa zanyi, zafi nakeji ta ko'ina a jikina jina nake kamar bani ba..."

Daga jin irin abin da take faɗa da kuma ganin yadda gaba ɗaya jikinta yake rawa ga wasu ƙuraje, Yasa Alhaji Sameer Lamiɗo Ya yi gyaran murya, gaba ɗaya suka juyo suna kallon sa, suna jira suji abin da zai ce.

"Ina ga mu juya gida kawai domin kuwa na lura wannan lamarin dasa hannun Jinnu a ciki, mu Fara komawa gida a ma ta magani sannan koma menene daga baya a yi."

Gaba ɗaya sun gamsu da maganar sa kuma sun fahimci abin da yake so ya fahimtar dasu, saboda haka ba tare da ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga motocin su suka koma.

Su Rafi'at suna zazzaune a palon gidan suna taɓa fira tsakanin ta dasu Zuwaira suka ji dawowar motocin.

Mamaki ne ya kamasu ganin su Hajiya Zuwairiya sun shigo.

"To kodai har sun dawo ne?."

Jawaheer ta tambaya tana miƙewa tsaye kamar yadda suma sauran suka mimmiƙe suna binsu Hajarah da kallon neman ƙarin bayani.

Gaba ɗayansu zama suka yi a saman kujerun palon jiki a mugun sanyaye, ganin haka yasa suma su Jummai suka zazzauna sannan ne kuma suka lura da Hajarah da ƙurajen da suka fara fiffito mata a jiki.

"Ya Allah.! Menene kuma wannan?."

Sakeenah ta tambaya cikin waro ido tana ƙarisawa wurin da Hajarah take

Ajiyar zuciya Hajarah ta sauke idanunta sunyi jajur na ɓacin rai sannan a fili take faɗin

"Dama nasan haka zata faru, tabbas nasan ba zata taɓa bari na koma gida cikin sauƙi ba, ni na sa ni, kuma nasan komai, nasan ko ita wacece."

Gaba É—aya mutanen dake palon suka zubo ma ta ido cike mamakin jin abin da take faÉ—a.

Abubakar da ya gaza jurewa sai da ya magantu.
"Wacece ita haka da kike faÉ—in kin san ba zata Bari ki koma gida lafiya ba?."

Ya tambayar idanun sa akanta, kamar yadda suma sauran jama'an palon suke ma ta kallon neman ƙarin bayani.

Numfashi kawai take fitarwa da sauri da sauri kana bayan wasu sakanni ta É—ago da kanta tana kallon jama'ar palon, kamar suma yadda É—in ita suke kallo Sannan ta fara magana kamar haka.

"Alhaji Haleed Mai Waje shi ne cikakken sunan mahaifin mu.
Asalin sa ÆŠan Garin Kaduna State ne.
Gaba da baya, su biyu a wurin iyayen su, shi da ƙanin sa Kamaludeen, sunan 'Mai Waje' kuma mutane ne suka saka masa.
A dalilin shiɗin ya kasance yana gudanar da harkokin kasuwancin sa ne a tsakanin ƙasashen waje.
Ya kasance cikakken Ɗan kasuwa kuma Mai Naira Wanda duniya take damawa dashi ta kowani ɓangare.
Matar sa ɗaya wacca ta kasance Baturiyar ƙasar Bulgaria ce, haifaffiyar Babban Birnin ƙasar wato 'Sofia'.
Tabar iyayen ta da Biyuninta a ƙasar su ta biyo sa.
Nigeria ne a dalilin son sa da take yi, kuma a kayi sa'a shima ɗin yana matuƙar ƙaunar ta.
Koda suka zo Nigeria a tare, batare da wani ɓata lokaci ba mahaifin sa ya ɗaura musu Aure, bayan ta karɓa Addinin Musulunci taci suna Haleematul Sa'adiya.
Yaran su huÉ—u a tare Hasheem shi ne na Farko, sai kuma wasu mata biyu da suka kasance twin's ne Mubashirah da kuma Munira, sai kuma Ni Auta Hajarah.

Mun taso ne cikin Tarbiyar iyaye, saboda duk da cewa mahaifiyar mu ta kasance Baturiyar da ta Musulunta, hakan bai hana ta jajir cewa ba ita da mahaifin mu wurin bamu Tarbiya mai kyau da nagarta. Mun kasance a gidan mu.
Muna zaune ne tare da ƙanin mahaifin mu da matar sa, suma suna da Yara uku a tare.
Matar ƙanin mahaifin mu mai suna Asabe ta kasance ta tsani mahaifiyar mu fi ye da kima, wai saboda ta kasance TUBABBIYA ce, kuma duk da haka surukan su sunfi ƙaunar mahaifiyar mu avkanta, wannan ne Babban dalilin da Yasa ta tsani mahaifiyar mu, a kullum cikin muzguna ma ta take yi, duk da cewa a cikin gidan mu suke zaune, kuma da dukiyar mahaifin mu suke ci suke sha.
Amma hakan bai hana ta neman kai mahaifiyar mu ƙasa ba. Da duka ƙarfinta.
Sai dai kuma duk Abin da take yi cikin salo da dabara take yi domin kuwa kaf gidanmu dama Ahali baki ɗaya babu Wanda Yasan Burinta a kan mahaifiyar mu domin ta kasance mace mai ƙissa da kisisina, a cikin mutane nunawa take tafi kowa ƙaunar mahaifiyar mu, amma kuma cikin zuciyarta ba haka bane.

Kaf gidan ba Wanda Yasan Burinta akan mahaifiyar mu sai ni kaɗai, domin kuwa na kasance tun ina Yarinya ina da matuƙar kaifin basira sosai, Wanda wannan dalilin ne ma Yasa nake karantar psychology ma'ana ilimin Tunani.

Ita da ƙanin mahaifin mu suna da wani Yaro mai suna 'Sama'ila' Wanda ya kasance tun daga tasowar sa mutum ne shi mara imani ko kaɗan domin kuwa ya kashe mutum har lahira ba damuwar sa bane, domin kuwa koda ya kammala secondary school kai tsaye ya wuce ƙasar China ya Karanci Astrology Wato ilimin Bokanci.💀💀💀

Wanda a dalilin baƙin cikin hakan ƙanin mahaifin mu Kawu Kamaludeen zuciyar sa ta buga ya mutu.
Sai dai a maimakon mutuwar sa tasa ÆŠan sa Sama'ila ya tuba ya koma ga Allah. A'a saima sabon salon abu da ya fito dashi. Domin tattarawa ya yi ya koma can kudu da zama.
Yayin da ƙannin sa biyu da mace dana miji da kuma mahaifiyar su suka ci gaba da zama a cikin gidan mu.
A lokacin ne kuma Asabe ta fito da nata sabon salon ita ma domin kuwa ta Yanke shawarar Auren mahaifin mu ta ko wani hali.
Nima a lokacin nazo gida hutu ne, sai na je ɓangaren nasu. Wajen ɗiyarta wacca ta kasance sa'ata ce shi ne fa naji abin da Yafi ƙarfina, a lokacin hankalina ya tashi sosai domin kuwa harji nayi tana faɗin, "Lallai zata iya kashe mahaifiyar mu har lahira indai ta nema kawo mata matsala."
"Lokacin ba ƙaramin tashi hankalina ya yi ba, sai dai kuma wani abun mamaki na kasa faɗa wa kowa abin da naji tana faɗa har hutuna ya ƙare na dawo Abuja domin kammala karatuna.

To a lokacin dana kammala karatuna ne a wajen dawowa ta daga wajen taro, na gamu da wannan Hatsarin da harna manta gaba ɗaya memory na akan Rayuwata da Ahalina..."😭

Hajarah ta na kawowa nan da maganar ta tayi shiru, Yayin da wasu zafafan hawaye suka wanke kyayawar fuskarta.

Shiru gaba É—aya palon ya É—auka tsawon mintuna goma, babu Wanda ya iya faÉ—ar wani abu, saboda tsananin mamaki da al'ajabi, sai can ne Alhaji Sameer LamiÉ—o ya nisa sannan yace

"Tabbas sosai mun tausaya miki fi ye da baya, da jin wannan labari naki mai cike da ƙalubale da chakwakiya game da rikitarwa, wannan yana nufin ke nan zargi na ya tabbata a kan cewa, da saka hannun Jinnu a wannan lamarin, to daga yau Insha Allah, zamu dage gaba ɗaya a haɗa ƙarfi da ƙarfe wurin ganin an nemo Ahalin ki, sun zo su ganki, tunda zuwan ki can bazai yiwu ba, kuma zamu ƙara dage wa wajen ganin an rabaki da waɗannan mutanen da suke a tare da ke Bi'iznillah.

***

Aikuwa Tun daga wancan ranar gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka ƙara zage damtse wajen kula da Hajarah fi ye da baya, kowa ƙaunar ta yake yi kamar me, hatta Rafi'at ba'a barta a baya ba, domin kuwa ba kaɗan ba labarin Hajarah ya taɓe ta. Ashe dai ko'ina da shegu😕
Ita babu abin da yafi ɗaga ma ta hankali sai ji da tayi wai musamman Sama'ila da yake Ɗan musulmi, ya ɗauki ƙafa wai yaje har can uwa duniya Ƙasar China dangin ifiritai, Karantar ilimin Bokanci ashe haka duniyar ta zama.😔

*MGNR PAYMENT DA NACE BOOK 2, YES IS PAID BOOK. SBD HAKA DUK WACCE TA SHIRYA BIYA TA TUNTUƁE WNN LAMBAR (08081129487) VIA WHAT'SAPP.

Zieey Jinjina mara adadi a gareki, ina godiya matuƙa da ƙaunar da kike yiwa wannan book, Allah ya barmu tare🥰

Page*79&80*

_____*

Rayuwa ta ci gaba da tafiya Yayin da ta gefe guda Abubakar ya kammala binkciken sa akan Ahalin Hajarah sai dai kuma wani Abin haushin shi ne.
Wai gaba ɗaya dangin sun koma ƙasar waje da zama kuma bai san wata ƙasa suka koma ba.
Chapter 68 · 0% Book details