← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 92

Sashe 24

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙayataccen murmushi Bilki tayi tana wani fari da ido ta ce "to ya san ranki, yauwa Jieddarh dama inaso kifaɗamin abinda zance mishi ne, idan ya dawo, kinga yanzu ya kusa dawowa fa,"
"ke Bilki kifa dinga bi aslowly, idan ba haka tom, shawara ce,"
cewar Jieddarh dan ta lura idan ba tana dakatar da Bilkin a wasu abubuwan ba, tofah ita Bilkin ita ce zata sha wuya ba kowa ba.
"kedai malama kawai ki faÉ—amin abin dana tambayeki kinji," Bilki ta faÉ—a ko'a jikinta da abin da Jieddarh ta ce ma ta.

"inaga kawai kice mishi welcome yayi,"

"haba Jieddarh wani 'welcome' kuma?, ai welcome ya zama tsohon yayi gaskiya."
Cewar Bilki tana kyaɓe fuska.
Jieddarh ta ce "toni kinga dai ba soyayya nake ba, balle nasan me zance miki ko," Bilki ta ce "amma kuma, ai kinyi karatu kinfi ni nida na tsaya iyaka secondary school,"
Jieddarh tayi dariya tana faÉ—in "ai duk kanwar ja ce, don nima dai iya kana secondary school É—in."
Waro ido Bilki tayi ta ce "haba yanzu kamar ke haka kin kammala secondary shine saboda jin daÉ—i, kika tsaya a haka baki É—aura ba, ni ina mamakin abin da ya hanaki shiga University, gaskiya da walaki,"
Jiiddarh ta ce "bana ra'ayine kawai, that's why, ba wani abu ba,"
Bilki tana ya musta fuska alamar ita bata yarda da abin da Jieddarh É—in ta ce ba, ta ce.
"haka kawai saboda iya shege kice bakya ra'ayi kawai dai da wata a ƙasa ki yarda da wannan madam,"

Zata kuma magana taji durar motar Heesham zumbur ta miƙe tsaye, ɗaukar gyalenta tayi ta nufi cikin gidan babu magana.

Girgiza kai Jieddarh tayi kurum a fili ta ce "gaskiya ni bansan wani kalan soyayya Bilki take ma Heesham ba, sai kace aikin sihiri?."

Ita kuwa Bilki da sauri ta ƙarisa parking lot a daidai lokacin da Heesham ya fito daga motar hannun shi riƙe da briefcase, har zai wuce ya jiyo muryar ta tana faɗin.

"yaya Heesham," juyuwa ya É—anyi, aikuwa sukayi four eyes da Bilki zuba mata kyakyawan idanun shi yayi yana jira yaji mai zatace, gabaÉ—aya sai taji ta ruÉ—e ta duburburce da kyar ta iya haÉ—o kalmomi ta haÉ—asu guri guda.

Tana ɗan inda inda ta ce "amm uhm yaya Heesham 'welcome back home' ya gajiya?, umm dama nace kawo jakar naka na riƙe maka kaji?," da kyar ta iya haɗa kalmomin ta faɗa saboda yadda ya zuba mata ido ba ko kyaftawa.

Baice komai ba ya miƙa ma ta briefcase ɗin, hannun ta na rawa tasa ta karɓa, shikuma yayi gaba tabi bayan shi hadda ɗan saurinta.

Gabaɗaya Bilki ta manta da babin wata Ni'ima da irin laifin da ta mata har, saida suka shiga palon sukayi ido huɗu da ita, zaune saman 2sieter ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, tana taunar cingum
Hango shigowar Heesham ne yasa ta wani taso da saurinta zata rungumeshi.

Da sauri ya matsa gefe yana kwaɗa mata harara sannan ya fara magana kai daga jin maganar kasan ranshi ya fara ɓaci da irin halinta.

"Ni'ima meyasa bakyajin magana ne, dubi shiga ki fa, ya miki kala da shigar yaran musulmai?, kuma na faɗa miki ba sau ɗaya ba, akan, ki dena ƙoƙarin hugging ɗina, cuz keba muharrama ta bane, amma ba kyaji ko, so this is the last warning da zan miki akan wannan ugly ɗabi'ar taki.

Cike da shakwaɓa Ni'ima ke faɗin, "haba my world, mana yanzu miye laifin wannan shigar tawa?, sai kace baka waye ba, come on mana, ka shigo zamani mana,"
Ta faÉ—a tana kuma yin juyi a gaban shi. cike da takaici ya kalle ta.
Ya juyo ya kalla Bilki da tayi tsuru tsuru, yace "duba nan, dubeta, a tsakanin ita dake wacece tayi shigar rashin da'a fisabilillah faɗamin?," kallon Bilkin ita ma Ni'imar tayi taga shigar jikinta ya mutsa fuska tayi tana faɗin, "haba my world dubeta fa, wannan ai shigar ƙauyawa tayi.

Da sauri Bilki ta kalla Ni'ima jin abin da ta ce lallai ta latsa ta, ita Ni'imar sanye take cikin €nglish gown black color, mai hannun vest ko gwiwar ta rigar bata kaiba gashi ta ɗameta ɗam numfashi ma, da kyar takeyi.

Bai tsaya jin abin da zata kuma cewa yayi gaba abin shi, da sauri Bilki tabi bayanshi, suka bar Ni'ima a tsaye kamar gunki.
Suna shiga bedroom ɗinnashi dake upstairs ta aje mishi briefcase ɗin a palo ta dawo down ta sauko bataga Ni'ima ba dan haka batama damu ba garden ta koma gurin Jieddarh zuciyarta qhal💦

D̬̂â̬ĝ̬â̬ Â̬l̬̂k̬̂â̬l̬̂â̬m̬̂î̬n̬̂

*🌼ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ🌼*

🅰🅱🆄🅹🅰

**
Yau juma'a wanda yayi daidai da kwanakin Dije {Deejarh} biyar da zuwa gidansu Afeefah kuma yaune gwaggon ta wato Auntie sa'adah zata koma ƙauye, Zuwa yanzu Deejarh ta fara fahimtar kaɗan daga cikin halayen mutanen gidan, farko dai kamar:

'𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉' ta fahimci mace ce ita, mai masifar rashin son shiga jama'a bawai kuma miskila bace, a'a ita haka halinta yake, sannan kuma ta fahimci tana masifar ƙaunar ƴan uwanta sannan kuma tana da kirki sai dai bata nuna kirkinnata kamar AFEEFAH ita NAINARH nunawa take kamar bata da kirki, amma idan ka zauna da ita zaka fahimci ko wacece ita.

'𝑵𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉' ta fahimci itaɗin mace ce ƴar bin ra'ayin kanta kamar mahaifiyarsu MOMY RAFI'AT sannan kuma kirkinta ragagge ne bisa kowa na gidan.

'𝒁𝒂𝒚𝒏𝒆𝒓𝒃' ita kuma Deejarh ta fahimci ZAYNERB mace ƴar komai saina shiga ma'ana ita dai ZAYNERB akwaita da neman rigima amma ga ƴan uwanta kuma rigima irin wacca za'ayi wasa da dariya.

'𝑯𝒂𝒍𝒆𝒆𝒔𝒂𝒕' cabɗi sarkin miskilanci kenan yadda Deejarh ta mata laƙani, don ta fahimci a rana guda ma za'a iya ƙirga adadin magana da HALEESAT tayi, sannan ta lura Haleesat mayyar Bacci ce, sannan kuma na lura Haleesat tana tafiya Club, sai dai bata yi gigin faɗawa kowa ba, sakamakon dalilai.

'𝑳𝒂𝒊𝒍𝒂𝒉' ta fahimci ita kuma ƴar Ji_ji da kai ce, ga kuma mugun iyayi, da alfahari da dukiyar iyayenta, sai dai ita ma tanada kirki iya nata, sannan kuma ta iya yaɓa magana babu taunawa ko wata kala ce kuwa.

'𝑨𝒇𝒆𝒆𝒇𝒂𝒓𝒉' uwar gayya kenan, a gaskiya Deejarh ta kasance tanajin daɗin zama da AFEEFAH fiye da kowa a cikin gidan MISTER MAI KYAU har shi kanshi dama matar sa MOMY RAFI'AT
Deejarh ta fahimci Afeefah mace ce ita mai masifar kirki highly domin kuwa ba ruwanta da kowa bata faɗa da kowa, haka zalika kowa nata ne ba ruwanta, sannan bata ɗaurawa kanta Ji_ji da kai ba sam, sosai akwai bambanci mai yawa tsakaninta da ƴan uwanta especially ma LAILAH, sam Afeefah bata wulaƙanta kowa akan dukiyar da mahaifinta yake dashi. ko kuma wai irin ta nuna bambanci tsakaninta da ƴan uwanta akan ƙaunar da mahaifinsu MISTER MAI KYAU yake nuna ma ta sama da kowa sam bata haka, sannan tun zuwan Deejarh gidan bata taɓaji Afeefah tayima wani ko wata daga cikin ƴan aikin gidan tsawa ko masifa ba. ba kamar Lailah ba da a gaban Daddynsu ta mara ƴar aiki akan 'As depleted ta zubo mata tea a jiki ba tare da ta sani ba.

Afeefah tana da kirki fiye da tunanin mai tunani, sannan Babban mafarkinta a duniya shi ne zama SARAUNIYAR KYAU ta duniya gabaɗaya, Burinta kuma shine zama Babbar Likita da ƙasarta zatayi alfahari da ita, Fatan ta kuma shi ne zama House Wife ta gari💃

________________________________________________________________________________

Tun safe ake abu ɗaya da Deejarh, ta maƙale akan sai tabi gwaggon ta ƙauye ita kuma gwaggon ta ta ce, ba za ta koma da ita ba, yanzu ma haka abin da ake ciki kenan da ita.

Tsaye suke a parking lot Afeefah, Deejarh, Auntie sa'adah sai kuma Zaynerb da Lailah dake gefe suna kallon ikon Allah.

"Deejarh ki bari ta shiga mota, mana driver yaja su tafi, kinga lokaci yana ƙurewa fa, ko kinaso tayi dare a hanya ne?,"
Duk wannan maganar Afeefah ne takeyi ma, Deejarh a hankali kuma cikin rarrashi.
Deejarh tana sha re hawaye ta ce "to zata dinga zuwa dubani, a koda yaushe, da yaushe 😳.
Da sauri Auntie sa'adah ta ce "E, mana Dije na, ai duk wata zandinga zuwa duba ki ba fashi,"
"toki rantse min," cewar Deejarh iya gaskiyar ta.
Dariya Afeefah tayi ta ce "ai ba seta rantse ba, idan ma bata zoba nida kaina zan kaiki ƙauyen, ki ganta ko," da kyar dai akasamu Deejarh ta bari Auntie sa'adah ta shiga motar driver yaja, suna ɗagama juna hannu har suka fice daga gidan.

Su kuma suka koma ciki suna shiga Deejarh ta É—are saman 3sieter kamar ba ita bace ta gama kukan rabuwa yanzu, zama Afeefah tayi a gefan Deejarh tana faÉ—in "dubeki kamar ba kece mai kuka yanzu ba,"
Dariya Deejarh tayi ta ce "to ai ni haka nake, yanzu zakiga ina kuka anjima kuma dariya."

Zaynerb ta kalla Afeefah lokacin da ta zauna a kujerar kusada ita ta ce.
"ni banga kina wani shirye shiryen gasa bane fa, kallon Zaynerb Afeefah tayi ta ce "shirya shirye kuma sai kace wacca zatayi aure?,"
Lailah tana shafa wayarta ta ce "bawai haka ba, amma ai ya kamata ko É—an gyaran jiki kiyi ko?."

Baki Afeefah ta saki tana kallon Lailah sai kuma tayi dariya, "lallai Lailah bakiji da kyau ba, kawai saboda wahala sai naje ina wani gyaran jiki saboda gasa, a'a to bada ni ba,"
Lailah ta ce "Wallahi da gaske nake fa,"

Afeefah ta ce "nima ai da gaske nake,"

"nifa yau banga wulƙawan Auntie Nailah ba kwata kwata, Zaynerb tayi maganar.

Deejarh ta ce "ai lokacin da kika tafi makaranta ne suka fita ita da wannan ƙawan nata mai kama da jarumar india 'Pooja Hegde' ɗinnan, ni banmasan sunanta ba,"

"amma wallahi baki da kirki sadiqqa ce take kama da Pooja É—in?," cewar Zaynerb tana dariya.

Dariya ita ma Deejarh tayi ta ce "Yasin Auntie wannan ƙawar Auntie Nailah ɗin, da pooja take kama har tsayin da hasken ɗaya, yanayin gashinta ne, kawai bansani ba."

"ke kuma a'ina kikasan tsayin pooja É—in?, uwar Æ´an sanin kamanni?,"
Lailah ta tambaya, Deejarh ta ce "a cikin film mana,"
"wanne a ciki?," Lailah ta kuma tambayarta.
Chapter 24 · 0% Book details