← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 92

Sashe 59

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saboda haka bai sama damar Raka maragayya Haleesat Rashid Rayyan izuwa makwancinta ba.

Da yake a wancan lokacin waya tayi ƙaranci yasa ba kowa ya sama damar zuwa ba cikin Ahali wa'inda suke da nisa, sai washe gari suma mutanen Jigawa State suka ƙariso.

Rafi'at gaba ɗaya ta ɗauki damuwar duniya ta sakawa kanta domin kuwa koda abinci bata iya ci sosai ta saba kafin suyi aure da Abubakar Mai Kyau a kullum tare suke da Haleesat Rashid Rayyan koda wani wuri zasuje to tare suke zuwa, bama ita kaɗai ba gaba ɗaya ɓangarorin abin sai a hankali.

Satin Haleesat Rashid Rayyan biyu da Rasuwa Rafi'at ta koma gidan mijinta Abubakar zuwa lokacin kuma an sallami Alhaji Rafiq Rayyan daga Asibitin.

/RAYUWA KE NAN😭/

_*BAYAN_WANNI_BIYU*_

Rayuwa ta ci gaba da tafiya sumuluquii ta wasu ɓangarorin amma banda ɓangaren Rafi'at da mijinta Abubakar domin kuwa zama suke zaman doya da manja tun rasuwar Haleesat Rashid Rayyan komai ya taɓarɓare tsakanin su ko ɗan kulawar da Abubakar yake bata a Sanadin cikin jikinta Yanzu babu, domin kuwa wani miskilanci Yake ji dashi haka suke zaman abin sai addu'a.

Ranar wata litina Rafi'at ta tashi da naƙuda ba'a ja lokaci ba da yake da wata tsohuwa Babah Ladii ƙanwar Kakansu a gidan saita taimaka ma ta zuwa Yamma lokacin Abubakar ya dawo ya tarar da halin da ake ciki, bai ɓata lokaci ba, ya kira Hajiya Zinaru ta waya ya sanar da ita abin da ke faruwa.

Ko kafin Hajiya Zinaru ta ƙariso Rafi'at ta haifo kyakyawan Jaririn ta ƙato mai kama da ubansa kamar an tsaga kara komai iri ɗaya sak, Like father Like son 🤓

Koda suka ƙariso ita da wata ƙanwar ta sai kuma Sailuba nan suka haɗu da Babah Ladii suka shiga kula da mai jego da kuma Jaririnta.

Zuwa kwana uku da haihuwa gaba É—aya Ahalin Alhaji Sameer LamiÉ—o dana Alhaji Rafiq Rayyan ba Wanda baizo duba lafiyar mai jego da kuma Jaririn da ta haifa ba, kowa yazo sai ya yaba da kyau irin na wannan jariri.

Ranar suna Yaro Yaci suna

ABDUL'MALEEK.!

/THE KING/

Mutane na kiran sa da Maleek Yayin da iyayen sa suke kiran shi da

BUDDY

Wato Aboki
Duniya sabuwa fil a wurin Rafi'at da Jaririn ta Abdulmaleek domin kuwa tun a Ranar da ta haihu wani kulawa na musamman Abubakar Yake bata ita da Jaririn su sunyi ƙiba sunyi ɓulɓul abinsu.

ABDUL'MALEEK Ya taso Yaro ne shi mai ƙiriniya sosai da sosai domin ko Asibiti Rafi'at ta tafi dashi tofa Ya dingi dukan Yaran mutane ke nan gashi ita kuma Likitar Yara ce, gashi daga ita har uban sa suna ƙaunar shi sosai ƙaunar da ta sa basa ganin laifin sa koya yake.

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

Page *63&64*

Duk da cewa shiɗin ɗan fari ne amma wannan bai hana Rafi'at da Abubakar nuna masa soyayya ba koda kuwa a gaban waye ba ruwan su ƙaunar ɗan su suke kamar Rayuwar su.

Tun Bayan Haihuwar Abdulmaleek Rafi'at bata kuma haihuwa ba sai da Abdulmaleek yakai shekaru uku a duniya sannan kuma ta haifa twin's duka mata Ranar suna, aka raɗawa Yara suna Hasana Babbar taci suna Nainarh Yayin da ita kuma Hussaina ƙaramar taci suna Nailah.

Sai kuma lokacin Sabuwar ƙauna da kulawa ta ninku fi ye da baya saboda Yadda Abubakar Yake ji da Yaransu uku a duniya shi da matar sa Rafi'at.

Abdulmaleek, Nainarh, Nailah Rayuwa ta ci-gaba da tafiya ko wani ɓangare hankali kwance sai dai abu ɗaya dake tokarin Rafi'at Rafiq Rayyan mata ga Abubakar Sameer Lamiɗo uwa ga Abdulmaleek Nainarh Nailah shi ne.

Tunda suka yi Aure har izuwa Yau da Yaran su uku.
Abubakar bai taɓa yi ma ta kallon soyayya ba, ko kuma ya furta ma ta kalmar so, wannan abu ba ƙaramin ci ma ta tuwo a qwarya yake ba.
Kawai dai haƙuri takeyi a kullum tana masa uzuri saboda ita ɗin mai ƙaunar shi ne, shiyasa bata ganin laifin sa ko kaɗan.

_______**

Rayuwa ta ci-gaba da tafiya ta ko wani ɓangare abin masha Allah.

Ana cikin haka su Rafi'at suka sha bikin Sailuba da mijinta suma anan Abuja suke zaune da yake mijin nata É—an kasuwa ne.

____*

Tafe suke cikin motar Abubakar, Rafi'at da Yaran Yayin da Abdulmaleek Babba Yake a back seat Yana wasa ga Nainarh na kusa dashi, sai Nailah a hannun Rafi'at da take zaune gaban mota ita da mijinta Abubakar Mai Kyau.

Tafiya sukeyi ta gefa gefan titi suna ɗan taɓa fira sama sama daga gidan Sailuba suke sun dawo daga kai ma ta ziyara zasu koma gidan su.

Suna firan ne Yayin da Rafi'at take kallon gefan titi cike da NishaÉ—i kamar ance ta kalla can gefe wajen wasu bishiyu aikuwa tayi kyakyawan gani, domin kuwa kamar mutum ta hango cikin jini.

Ba tare da fargaban komai ba ko tunanin wani abu ba, ko É—arsawa zuciya tunanin komai.

Rafi'at ta kalla mijinta Abubakar Mai Kyau cikin murmushi ta ce

"My lawful naga kamar mutum ne fa kwance cikin jini a can gefan wasu bishiyu, please ka tsayar da Motar nan muƙarisa domin mu taimaka ma ta naga kamar macece fa."

Tayi maganar cikin Rarrashi domin kuwa tasan halin abin ta.

Duk da cewa cikin Rarrashi tayi maganar sannan kuma cike da shgagwaɓa amma hakan baisa Abubakar tsayawa ba, saima cewa da ya yi

"Ba wani mutum cikin jini kawai dai idanun kine basu gani dai dai ba."

"Wallahi Ras idanuna suke gani, please ka tsaya mu taimake ta domin naga alamar jini take zubarwa sosai."

Rafi'at ta kumayin maganar kamar zatayi kuka.

Habba jama'a ai fa nan aka shiga ja'inja a tsakanin Abubakar da Rafi'at shi yana faÉ—in "Ba wani mutum kawai idanunta ne basu gani dai dai ba."

Yayin da ita kuma ta Rantse masa ta kuma Rantsewa akan tabbas mutum ta gani.

Ganin dai bazai saurareta ba idan bata haɗa masa da wani hadisi ko Ayya ba, yasa Rafi'at tayi gyaran murya sannan ta kalleshi da kyau yana tuƙin sa hankali kwance ta ce

"My Lawful a kullum muka zauna zaman fira da Daddynmu abu É—aya yake faÉ—a mana, wannan abu É—ayan shi ne "Ku taimaki wanda yake neman taimakon ku, ba tare da tunanin samun wani abu daga garesa ba." Ko kuma Yace mana "Ku taimaki wanda baku sani ba, batare da sa ran wani sakamako ba daga gare shi ba wannan shi ne mutun taka."

"Shin baka mana kwaɗayin samun ladan wannan taimakon da zamuyi a wurin Allah, tunda nake a Rayuwata banajin na taɓa taimakon wani na ƙasa da ni, shin Yau ba zakamin kwaɗayin samun lada ba?.
Yau É—aya nayi niyyar taimako ba zaka goyamin baya ba, haba mijina haba jarumin jarumai miji a wurin Rafi'at ita É—aya ka taimaka please pleased..."

Ba ƙaramin sanyi jikin Abubakar Ya yi ba, jin abin da Rafi'at take faɗa shima tunani ya fara shin wai Yaushe Rabon shi da ya Taimakawa wani ɗan adam?. a gaskiya shi kanshi bazai ce ga tsawon lokacin da ya ɗauka ba.

Ba shiri Ya yi Reverse sannan ya yi baya da Motar ya juyo dama tuni sun wuce wurin.
Murmushi Rafi'at tayi tana sauke ajiyar zuciya batasan dalili ba, amma kawai Yau taji tanaso ta taimakawa budurwar da ta hango cikin jini, wacca ko fuskar ta bata hango sosai ba.

Tsayar da Motar Ya yi a dai dai sai tin budurwar dake kwance cikin jini kayan jikinta da suke farare suma sun koma ja saboda tsananin jinin da ta zubar.

Fitowa suka yi shi da Rafi'at daga cikin Motar suka bar Abdulmaleek da Nainarh.

Rafi'at ta Riƙo Nailah a hannunta sannan cikin sauri gaba ɗaya suka ƙarisa gaban budurwar dake kwance.

Sai kuma lokacin tsoro ya fara kama Rafi'at, wannan tsoro bana komai bane saina ganin wani kalar masifaffen kyau da wannan budurwa wacca ta gama yin kaca kaca cikin jini duk da cewa cikin jini take amma wannan bai hana Rafi'at hango tsantsan kyau na musamman da wannan budurwa ke da shi ba.

Cikin zuciyarta tana mai tabbatar wa koda za'a bar wannan budurwa a haka ba tare da tayi wani kwalliya ba a haÉ—asu Gasar kyau Rafi'at tana da tabbacin duk da itaÉ—in tana da masifar kyau tofa wannan budurwa sai tayi ma ta zarra.

A fili Abubakar ya furta kalmar

"Masha Allah."

"Allah mai hallita yarda ya so..."

Ya yi maganar yana kuma ƙarewa kyakyawar fuskar ta kallo domin kuwa zai iya cewa tunda Yake a duniya bai taɓa ganin macen da kyau ya yi mata kyau ba sai wannan budurwa dake kwance gaban sa, cikin jini ga idanunta a rufe da alama suma tayi.

Ita ɗin mai kyau ce cikin masu kyau. 🤠🏃👑

Ganin Yadda mijinta Abubakar mai kyau ya tsuguna yana ƙarewa wannan budurwar dake kwance cikin jini dake gabansu kallo, ya sa Rafi'at jan ɗan ƙaramin tsaki cike da jin haushi na Rashin dalili ta ce

"Malam Mai Kyau ka taimaka mu kamata a sakata a mota domin a kai ta Asibitin saboda naga jini take zubarwa fa."

Rafi'at tayi maganar cikin ƙunƙuni ganin kamar bai jita ba yasa ta dage iya ƙarfinta ta ɗaka masa duka a baya tana kuma maimaita masa abin da ta faɗa.

A maimakon taga Yaji haushin dukan da tayi masa, a'a sai ma tsadadden murmushi Ya yi ma ta kana ya miƙe yana gyara hannun rigar sa, ganin haka yasa ta aje Nailah a gefe ita ma ta fara kici kicin gyara mayafin kanta.

"Ke kuma mai zakiyi?."

Taji Abubakar ya tambaye ta, murmushi tayi kana ta ce

"Zan tayaka ne mu cicciɓeta a kaita Asibitin ai."

Tayi maganar tana dariya.🤣

"Saboda kin mayar dani Rago ko me?."

Ko kafin ta nema amsar da zata bashi tuni taga ya ɗauki wannan budurwa da duka ƙarfin da Allah ya bashi ya nufa motar shi da ita🧐.

Baki wangame 😨 Hanci sake 👃 ido warwaje 👁️👁️fuska ɗauke da matsanancin mamaki 🤔 Rafi'at tabi mijinta Abubakar da kallon ikon Allah.

Ai bata tsaya tunanin komai ba ita ma ta mara masa baya, har ta kusa motar, ta jiyo kukan Jaririyarta Nailah da sauri ta juya Ashe wai saboda tsananin mamaki da matsanancin kishi ne yasa ta manta da jaririyarta a wurin.🤣
Chapter 59 · 0% Book details