← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 92

Sashe 77

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ware duka muryar ta tayi cike da tsananin mamaki Ta ce "Sister zaynerb ke ce?, kodai gizo kike min me kike yi a Nigeria, kodai har kin kammala karatun ne?."

Jin abinda take faɗa ne yasa ka daga Afeefah da Lailah wa'inda suke karatu harda Nainarh mai chatting dukkan su suka mimmiƙe tsaye a tare suka nufa ƙofar gudu gudu, Lailah na faɗin "Ke xixi banason hauka fa. Menene kuma zai kawo Sis Zaynerb Naija mutumiyar da take Amsterdam karatu?."

"Wallahi Siister zaynerb ce ai na santa a pictures, kuma ma idan baki yadda ba gata nan ki ganta, face to face." Cewar xixi tana basu hanya.

Gaba ɗaya da tsananin mamaki suke kallon kyakyawar budurwar dake tsaye bakin ƙofar palon gabanta akwatu wajen guda uku.

Saboda tsaban mamaki ma sun kasa magana sai kalloncta kawai da suke yi kamar sun sama tv, duk da cewa a lokacin basu san Zaynerb a fili ba, sai'a pictures amma sun gane ta.

"Auntie Zaynerb ɗina, kece kuwa me kike yi a Nigeria bayan kuma a ƙasar Amsterdam kike karatu, kodai kin sama hutu ne ki-ka-zo mana?." Cewar Afeefah Tana kallon Zaynerb ɗin.

A maimakon Zaynerb ta bawa Afeefah amsar tambayoyin da take jero ma ta, a'a da gudu ta ƙarisa shigewa palon, sannan tayo hugging Afeefah ɗin tightly a chest nata, tana fashewa da matsanancin kuka kamar ranta zai fita, ganin haka yasa gaba ɗayan su jikin su ya yi sanyi laqwas.

A hankali Afeefah ta riƙo hannun Yayarta ta suka nufa cikin Palon. Bayan ta sake ta, ganin haka yasa Lailah da xixi suka ɗauko akwati nan Zaynerb da ta bari a wajen, suka shiga dasu cikin palon.

Gaba É—aya zama suka yi akan Royal sofa's dake palon, sannan Lailah ta ce "Sis Zaynerb lafiya kuwa, naga kamar bakya cikin hayyacinki sosai..."

"To sarkin surutu sai ki bari ta huta ko, daga zuwa ko zama baki bari ta kammala yi ba, harkin sako ta gaba da tambayoyi haka?."

Cewar Nailah da take ƙari sawa palon hannunta riƙe da plate ciki shaƙare da kayan maƙulashe, ƙari sawa palon tayi Sannan ta miƙawa Zaynerb ɗin plate dake hannunta tana faɗin
"Gashi sister zaynerb fara cin abinci tukun na koma menene, daga baya a yi maganar."

Karɓa Zaynerb tayi sannan cikin muryar ta mai daɗin sauraro ta ce da Nailah ɗin
"Thanks to You."

Cikin Baturiyar Muryar ta, murmushi Nailah ta ma ta sannan ta koma ta zauna tana amsa ma ta da "Never mind enjoy."

Sai da Zaynerb ta kammala cin abinci da Nailah ta bata tas. Tasha Ruwa ta huta sannan ta kalla Ƴan uwanta duka da suka sakata gaba suna kallo kamar sun sama TV.

Ta ce
"Barkan ku dai Æ´an uwa na."

"Kema barkan ki dai."

Suka haÉ—a haÉ—a baki wajen faÉ—in hakan, amma banda Afeefah wacca ta tsurawa Yayarta nata ido tana kallo.

A hankali ta buÉ—e bakinta ta ce "Auntie Zaynerb tawa, zuwa Yanzu nasan kin dawo nutsuwar ki please zaki iya faÉ—a mana abin da yake faruwa, kona samu na sama nutsuwa."

Ajiyar zuciya Zaynerb ta sauke tana tariyo duka abin da ya faru da ita tun daga ranar da ta taka ƙafafunta a ƙasar Amsterdam har izuwa rana mai kamar ta ranar da suke ciki.

Sannan ta kallesu gaba É—aya kana cikin tsananin rawar murya gunin ban Tausayi take faÉ—in

"SOYAYYA CE. Sanadi Soyayya ce Sanadin duka Halin dana tsinci kaina, soyayya ta wahalar dani fi ye da tunanin mai tunani, soyayya tasa na tsana kaina, soyayya tasa na fita hayyacina, soyayya tasa a shekarar Farko na karatuna na tashi da c.o. Soyayya ce da kuma Namiji sun wahalar da zuciyata fi ye da kima. Dan Allah Ƴan uwana karku min tambayar dalili na dawowa, domin kuwa banason na ƙara tunawa dashi a rayuwata, saboda na tsane sa, na tsana duk wata alaqar da zata ƙara haɗani dashi. Ya Yaudareni da sunan soyayya Ya.. Ya..."

Kasa ƙari sawa tayi saboda kukan daya zo ma ta nanta shiga yi abin gunin ban tausayi, zafi zuciyarta take ma ta, ji take ba za ta iya jurewa ba, kwara ta mutu kawai ta huta.

Tsuru tsuru suka yi suna kallonta gaba ɗaya jikin su ya yi mugun sanyi ba kaɗan ba. Jin abin da Zaynerb take faɗi, sai aka rasa wanda zai rarrasheta, a cikin su, domin kuwa ba ƙaramin sanyi jikin su ya yi ba da wannan sarƙaƙaƙƙen labarin.

Lailah ce tayi ƙarfin halin cewa "Sis Zaynerb kinji kiyi shiru, ki dena kuka, domin kuwa babu amfani, ba dai kun rabu ba, to ni banga amfanin sakama rai damuwa ba, ina ce dai yanzu kin tsane sa, bakya ko son ganin sa ko?."

Da sauri Zaynerb ta É—aga ma ta kai alamar hakane.

Sauke ajiyar zuciya xixi tayi sannan ta ce
"Sis zaynerb please zaki iya faÉ—a min sunan sa?, kuma musulmi ne ko kuma ba musulmi bane?."

"Amma dai xixi kinji kunya wallahi, yanzu ana so a lallaɓata ta manta dashi gaba ɗaya a cikin rayuwar ta, amma ke ta sunan saurayin da ya wahalar mana da ƙanwa kike ko?. Da bakin ki a gurin kamar na Angela ko?."

Cewar Nainarh cike da Bala'i.
Turo ƙaramin bakinta tayi cike da shagwaɓa ta ce.

"Allah sis Nainarh akwai ki da tsaban ƙarya, amma in banda haka, ta'ina kika ga ɗan ƙarami madaidaicin siririn bakina ja dashi ya miki kala dana Angela ne, in banda tsaban ƙarya da rashin kula da faɗin gaskiya irin na ki, haba dai Sis Nainarh a duba lamarin fa chabb, wai bakin Angela."

Tashi Nainarh tayi zata kaima ma ta mugun bugu, lura da hakan da xixi tayi ne. Yasa ta miƙe da gudu ta shige jikin Zaynerb tana faɗin "Please Sis Zaynerb ki ce ceni, zata kashe ma Daddyn mu Auta shikenan fa idan ta dakeni sai nayi ciwo, wayyo ni Zeenaru..."🤣😅

Biyo ta Nainarh tayi tana faÉ—in "Yau ko cikin, cikin Zaynerb zaki koma saina dake ki, badai baki da kunya ba?."

Qara shigewa jikin Zaynerb xixi tayi faÉ—i take "Please, please sis Zaynerb ki taimake ni zata dukeni fa."

Dariya kawai Zaynerb take yi na drama ɗin xixi da Nainarh, ta fahimci Yarinyar akwai tsokana, sai tsaban tsoro, ita kuma Nainarh babu haƙuri, riƙe girma.😕

Tun daga wannan ranar Rayuwa ta dawowa Afeefah sabuwa fil, don gata ga Yayarta Zaynerb wuri guda. Rayuwa suke cike da farin ciki da ƙaunar juna mara misaltuwa.

Watan Zaynerb É—aya da dawowa Nigeria tuni ta koma school sai dai kuma ta canza course, domin kuwa koda mahaifin su Alhaji Abubakar Mai Kyau, Bayan Yaji dalilin ta na dawowa Nigeria Ya fahimce ta domin kuwa Yasan Menene so. To koda ya tambaye ta abin da zata karanta kai tsaye ta ce masa "LAW" take so ta karanta yanzu.

Aikuwa nan ba tare da wani ɓata lokaci ba, aka samar ma ta da Admission anan wata katafariyar University dake birnin tarayya, na Yaran Manya ta fara karatun ta cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin komai ba, domin kuwa makarantar ma da take yi na mata zalla ne, sannan kuma maganar soyayya ta a jeta a gefe

_-_Masu karatu nan gaba zamu san ainihin abin da da ya faru da Zaynerb a ƙasar Amsterdam Insha Allah, kudai kawai ku biyo wannan Ƙayataccen Labarin *💋💋SARAUNIYAR KYAU💋💋* Much Love_-_😘

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ_________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅_

Page *95&96*

_-_Uhum nayi maganar payment banga ana layi ba🥺. Kar fa ku manta Discount ɗin na sati ɗaya ne kacal 👌. Kwana ɗaya ya wuce, saura kwanaki shida kacal. Ku gaggauta biya fa, kafin Discount ya ƙare. 🥳🥳

***
Rayuwa ta ci gaba tafiya ta kowani ɓangare cikin nasara da kuma farin ciki sakanni suna tafiya Yayin da mintoci suke wuce wa, suma awanni suzo su wuce, haka ma kwanaki wucewa suke su suna bawa satikai damar suma suzo su wuce kamar ba'ayi ba Yayin da watanni suke tafiya suma shekaru suzo su wuce.

To haka ma Ahalin Alhaji Abubakar Sameer Lamiɗo _-_Mister Mai Kyau_-_ suka kasance Bayan shekaru biyu da dawowar Zaynerb Nigeria shima Abdulmaleek ya kammala karatun sa a ƙasar Rasha ya zama cikakken gynaecologist _-_Likitan mata_-_

*NAMADI-INT£RN@TIONAL-AIRPORT-ABUJA*

Tafiya yake cikin nutsuwa irin na sa. Tafiya kalar na Manyan Gayu masuji da Kyau ga hutu da jindaÉ—in duniya daÉ—i da kari kuma ga Naira.

Dogo ne shi sosai, kuma fari wanda farin sa yake haÉ—e da gauranyen ja, kyakyawa ne shi, first class domin kuwa duk wani qualities na kyau yana dasu, ga hutu da jindaÉ—i da yake ciki tsundum ta ko'ina.

Kyakyawar fuskar sa zagaye take da stubble beard. Wanda ba ƙaramin kyau madaidaicin stubble hair da ya tara a kyakyawar fuskar sa ta ƙara masa ba.

Yayin da sumar kansa mai tarin yawa gashi baƙi sidiq ya ma ta wani kalar gyara na musamman in stylishly sai shaining take.

Sanye yake cikin T-shirt black color mai gajeren hannu, wacca ta zazzago masa har kusan gwiwa, gefe da gefen Rigar Yanayin style na wurin sai Ya yi kamar a tsage.
Kalar wannan Riga dai wacca Manyan Gayu wa'inda suka san darajar Gayu da wanka suke sakawa, daga ƙasa ƙasan Rigar, gaba da baya Anyi wani Rubutu da farin kala cikin harshen farasanci, sai kuma trouser jeans pencil Black color wandon ba ƙaramin kamasa Ya yi ba, amma haka yake takawa ba ruwan sa, sai kuma wani farin Boots dake sanye cikin ƙafafunsa irin Takalmin nan wanda ake Ya yi sannan, kafin kaganshi a ƙafar wani tofa ƙaton aiki ne, saboda tsadan Takalmin sai wanda Ya isa ko kuma aka san da zaman sa ko uban sa a ƙasar sannan...
Chapter 77 · 0% Book details