← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 92

Sashe 76

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Kai masu karatu ✍🏻 Alƙalamin Nainarh Kd fa, Ya yi kaɗan wajen rubuto da bayyano muku kyau da tsari irin na Gidan Mister Mai Kyau, sai dai kawai kuyi imagine yadda Gidan mutumin Da ya kasance kaf duniya da ƙasar an san da zaman sa, kuyi hasashen Yadda Living Home nasa wanda Iyalansa suke ciki, zai kasance ina architectures ne?, ina ga ku zaku iya fahimtar yadda tsarin ginin gidan yake,☺️ Saboda Aikin kune Ni dai Nayi iyaka abin da zan iya a Bayani 🤓 saboda haka Nayi nan.*🏃🏃

**
Gaba É—ayan su zama su kayi a Royal sofa's dake zagaye da palon, nan suka shiga firan duniya a tsakanin Afeefah da Æ´an uwanta domin kuwa Alhaji Abubakar Mai Kyau. Tuni Ya yi gaba part nasa domin Ya basu damar surutun yadda ya kamata.

Ita ma Momy Rafi'at tabi sa, saiya kasance iyakar Nainarh, Nailah, Haleesat, Lailah, xixi ne, a palon sai kuma Afeefah wacca suka sakata a tsakiya sai faman fira suke yi. Abun nasu gunin ban sha'awa da ƙayatarwa game da tsananin Burgewa.🥰

Lailah gaba ɗaya tabi ta nanu ƙewa Afeefah domin kuwa duk inda tayi ita ma tana nan, har dariya su Nailah Suke ma ta amma ita ba Ruwanta.

Xixi ce sarkin Iyayi da surutu, ta gyara zaman ta saman 1sieter sannan ta kalla Afeefah cikin Iyayi da Yanga irin na Young Lady mai ji da tashen balaga.

Tana Yarfe hannu Ta ce

"Oh Sis feeefat baki bamu labarin Abroad ba, kin san ba ko'ina Momy take Bari muje ba Especially, ma ƙasar France Wanda shi ne Burina nayi karatu a can idan na kammala secondary school da nakeyi."

Dariya Afeefah tayi Sannan tana amsa ma ta

"Menene kuma wani feefat?, Afeefah nake ba wani feefat nan. Ƙasar france kuma Labiba ma ta ce na gaisheki da kyau."

Dariyar murna ita ma xixi tayi kana cike da zaƙuwa ta ce
"Dan Allah Sis feefat da gaske kike, oh my God nayi kewar Labiba da ƙasar faransa obaa."

Ke baki ji ba ko?, nace wannan feefat yabar kan laɓɓanki, domin Afeefah nake kuma karki ƙara cemin wani Sis ehe. Iya Afeefah ma ya isa."

Cewar Afeefah É—in cike da nata salon bala'in.

Ya mutsa Beauty face nata tayi cike da Yanga ta ce
"Oh Sis feefat..."

Sai kuma da sauri ta Rufe baki. "Oh na manta Sis Afeefah ni na É—auka ma keÉ—in wayayyi yace. Ashe ba haka bane yanzu Menene aibin kiranki da Sis feefat?, naga shi ne normal suna na zamani ko?."

"Oho dai ke kika sani kuma?." cewar Afeefah tana dariya, dama da gangar tayi.

**
Da Dare misalin ƙarfe bakwai da Hamsin.

A hankali ta turo ƙofar bathroom ta fito sanye cikin bathrobe coffee color, jikin ta na ɗugar Ruwa.
Sam bata lura da mutum saman bed ba, don haka gaban mirror ta ƙarisa sannan ta janyo swivel chair ta zauna kana ta shafa lotion kaɗan, tayi light make-up sai dai bata saka powder ba.

Closet ta nufa ta ciro kalar tufafin da zaka saka, kana ta shirya cikin sleeping dress, dogon wando purple and vest ita ma purple color. sannan ta saka hula ita ma purple color, kana ta dawo ta nufa ƙofa zata fita Bayan ta saka hijjab sky purple iya gwiwar ta.

"Afeefah.!
My only.."

Taji muryar Lailah tana kiran ta É—an juyowa tayi, aikuwa ta hangota baje saman bed tana dariya ta ce

"Ina ne kuma zakije da wannan Daren haka?."

Murmushi Afeefah tayi tana faÉ—in"Oh Allah, Lailat ke ce yaushe kika shigo bedroom nawa ban sani ba?."

"Tun lokacin da kika shiga bathroom fa."

Lailah ta bata amsa, ɗan waro Manyan idanunta tayi sannan ta gyara tsayuwarta tana riƙe ƙofar bedroom ɗin ta ce

"Okay wato dai kin gannn.."

Tun kafin ta ƙarisa Lailah tayi saurin cewa

"A'a Wallahi. Rufe idanuna nayi, ni wacece haka, da zanka Æ´ar uwata?."

Tayi maganar tana dirowa daga saman mattress É—in.

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke "Zo ki rakani wurin Daddy kinji?."

Dariya Lailah tayi sannan ta ce "Okay babu damuwa muje."

Fita suka yi a tare sannan suka nufa twin's staircases suka bi wanda zai sa dasu da part na Mister Mai Kyau.

"Ke Lailah.
Ke Lailah.! ina zakuje da Daren nan?."

Da sauri suka juyo jin muryar Momy Rafi'at tana magana, tsaye take daga tsakiyar palon sanye cikin sleeping dress kamar yadda ta saba tayi Rolling kanta da mayafi.

Washe baki Lailah tayi tana bawa mahaifiyar ta ta amsa da faÉ—in

"Momy Sister Afeefah zan raka wurin Daddyn za ta masa Good Night ne."

"Ba zakuje ba."

Momy Rafi'at ta faÉ—a hakan kai tsaye.

Gaba É—aya da mamaki suka tsaya suna kallonta.

"Because of what, Momy kinga Halin naki ko?, akan me zaki ce baza muje ba, Bayan kuma na faÉ—a miki cewa Afeefah ce zata je tayima Daddy Good Night?."

Cewar Lailah ita ma kanta tsaye.
"Saboda na isa daku, nace baza kuje ba, idan kuma ban isa daku ba, ku shiga na gani."

Ita ma Momy Rafi'at ta faɗa a zafafe, Lailah zata kuma magana da sauri Afeefah ta Riƙo hannunta sannan suka sauko Downstairs.

Kallon Momy Rafi'at tayi cike da girmamawa ta ce

"Shikenan tunda kince ba zamuje ba. Please Idan kin shiga ki faÉ—awa Daddyn Shalelen sa tana zai gashe sa, kinji our Momy?."

Afeefah tana gama faÉ—in haka ta kuma jan hannun Lailah suka yi Hanyar bedroom.

Da masifa Momy Rafi'at take faɗin "Ke Afeefah, How dare you, wato har Ni ce zaki bani saƙo?, keɗin wacece?, har Yaushe kika girma?."

Juyowa Afeefah tayi ta ma ta murmushin Tura haushi sannan ta Rufo ƙofar garamm. Kakeji.

Galala Momy Rafi'at ta bita da kallo saboda tsaban takaici tama kasa magana, qwafa taja sannan tayi gaba.

Jingina tayi da Bayan ƙofar tana sauke ajiyar zuciya na ɓacin rai.

"Please My only, wani lokacin fa sai kin dinga haƙuri da Halin Momyn domin akwai ta da shiga shara babu shanu."

Cewar Lailah Tana kwaɓe fuska, cike da Rashin enjoying na halin mahaifiyar tasu.

Murmushi Afeefah tayi tana faɗin "Babu komai wata ƙila shi Daddyn bacci Yake yi shi yasa ta faɗa, haka kuma nasan Halin Daddyn bayaso ana Tashin sa idan yana bacci."

Kallon bazaki fahimta ba, Lailah tayi ma ta kana ta nufa gefan bed ta zauna bata ce komai ba.

_-_Har Yanzu cikin free page's muke SARAUNIYAR KYAU_-_

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

Page *93&94*
_-_Free Page's Still_-_

"Yauwa dama fa akwai tambayar da nakeso nayi miki tun É—azu."

Cewar Afeefah cikin murmushi ita ma tana zama kusa da Lailah É—in.

"Okay Inajin ki Sister."

"Oh My Lailat, yanzu taya ya zanji daÉ—in magana dake bayan kuma kin É—aure fuska faÉ—a min?."

Murmushi Lailah tayi tana faÉ—in"Tofa ."

Washe fuska tayi "Hakan Ya yi miki?."

Murmushin ita ma Afeefah tayi "Haba hakan yafi ae, nima zanfi enjoying na fira dake fuska sake ko?.

Dama tambayar ita ce, naji kun iya Harshen Jamus da kuma Spanish sosai sosai. Ta yaya aka yi kuka iya?, Please?."

Dariya Lailah tayi sannan ta ce "Ai bama iya harshen Jamus da Spanish muka iya ba, hadda ma yaren Eritrea mun iya, Labarin da tsayi fa."

"Okay Inajin ki ake."

Afeefah tayi maganar tana gyara zama fuskarta a washe.
Lailah ta ci gaba da cewa abin da ya faru, shi ne duk ƙasar da kukaje muma sai Momy ta nemo mana Malamin dazai dinga koya mana yaren da akeyi a ƙasar ace warta gwara muma mu'iya kar sai kun dawo Naija, ku baku iya Hausa sosai ba, muma kuma bamu iya Harshen da kukeji ba, wannan shi ne a taƙaice."

Murmushin mamakin halin Momy Rafi'at kawai Afeefah take yi sannan a fili ta ce "Hakan ya yi fah gaskiya."

***
Washe gari ma haka suka tashi gidan a cike da Ƴan Uwa da Abokan arziƙi na nesa da kusa waɗanda suka zo domin ganin Afeefah da mahaifinta da suka dawo Nigeria Bayan shafe tsawon shekaru shida a Abroad.

Rayuwa ta ci gaba da tafiyar ma Afeefah tare da ƴn uwanta musamman ma Lailah da ba ƙaramin shaquwa ce ta fara shiga tsakanin su ba.

Yayin da a kullum cikin waya da Ƴar uwanta Zaynerb wacca take karatu a ƙasar Amsterdam suke yi babu dare ba rana.

Rayuwar ta ci gaba da lulawa cike farin ciki.
Watannin su Afeefah uku da dawowa Nigeria, tuni mahaifin su Mister Mai Kyau. Ya saka su a University ita da Lailah wacca Ita ma ta kammala secondary school nata, sun fara zuwa University tare. Yayin da suke karantar course ɗaya dukkansu wato karatun Likitanci ɓangaren na musamman surgery.

Sosai suka mayar da hankulansu akan karatun su, babu wasa. Yayin da tsakanin Afeefah da Momy Rafi'at babu wacca take shiga harkar wata, domin kuwa gaisuwa ce kawai take haɗasu, ita ma daga Afeefah ta gaisheta bata tsayawa saita amsa take warin wurin, sai dai idan taga Daddyn ta a wurin ne, tofa nan ne zata tsaya ta amsa daga haka kuma babu abin da yake ƙara shiga tsakanin su.

Wata Ranar Jumma'a wacca ta kasance watanni su Afeefah biyar da dawowa Nigeria.

Ranar suna zazzaune gaba ɗaya a palon gidan Yayin da Afeefah da Lailah suke karatu cikin wani ƙaton book irin na Likitoci daga can gefe kusa da Bene. sunyi kaca kaca da littafai a yayin suna karatun.

Sai kuma xixi dake hakim ce saman kujera tana kallon wani Nigeria Nollywood Drama, 'Recap Beyond The Veil, a plasma tv dake palon, can gefe kuma saman 3sieter Nainarh ce kwance tana chatting a wayarta. Yayin da Nailah take can kitchen tana Faman soya soye, dama ita É—in akwai son kwaÉ—ayi, ita kuma Haleesat sarkin bacci tana bedroom nata tana kwasar bacci.

Jin ana faman knocking na ƙofar palo ne babu tsayawa ko dakata wa ne, Yasa Nainarh ta kalla xixi dake faman ƙyakyata dariya tana cewa

"Ke xixi jeki buɗe ƙofar can, ƙarar ta yana disturbing nawa da yawa."

Tashi xixi tayi tana faman ƙunƙuni ta nufa ƙofar, domin tasan ubanta zata ci idan bataje ta buɗe ba domin kuwa Nainarh babu wasa.

Buɗe ƙofar tayi cike da masifa ta hayayyaƙo zatayi ma koma waye a ƙofar, sai kuma bakin ya mutu, ganin wacca take tsaye gaban ƙofar janye da akwati.
Chapter 76 · 0% Book details