← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 92

Sashe 6

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan Suka ci gaba da cin breakfast ɗin su, can saiga Momy Rafi'at ta sauko ƙasa daga Upstairs dayake can bedroom yake, bata kula kowa ba ta zauna a kujerar dinning ɗin da sauri Auntie sa'adah ta ƙariso gurin tayi serving ɗinta.

Ina kwana momy!!. Afeefah ta faɗa tana kallon abincin gabanta, ba ta re da da Momy Rafi'at ta kalleta ba ta ce lfy a taƙaice ita ma, suma su Lailah gaisheta sukayi ta amsa da sakin fuska.

Kallon zaynerb Afeefah tayi ta mata alama da ta gaisar da Momy Rafi'at, Zaynerb tana sane taƙi kulata ɗan gyaran murya daddy Yayi yana kallon zaynerb ɗin a hankali ya ce "daughter bakiga momynki bane?",.

Zaynerb tana kallon Momy Rafi'at dake mata kallon ƙasan ido tayi smile ta ce "oh oho ae daddy karka damu, har ɗaki nabi ta muka gaisa fa", ta faɗa tana kashe wa Momy Rafi'at ido Wanda Hakan daya faru ba wanda ya gani ko ya lura.

Kallon Momy Rafi'at Daddy Yayi cikin murmushi yace haka akeso daganan ya cigaba da cin breakfast É—inshi.

Ita kuwa Momy Rafi'at da ɗumbin mamaki Take kallon Zaynerb data shirga ƙarya amma ko'a jikinta Domin kuwa basu haɗu ba sai yau kuma yanzu, amma shine harda iya cewa tazo ɗakinta sun gaisa qwafa taja bata ce komai ba, ta ciga ba cin abincin ta.

Gyara zama Zaynerb tayi tana fuskan tar daddy cikin murya irinna zumuɗi ta ce "daddy nanda wata ɗaya fa, za'a gudanar da zaɓan S͓̽A͓̽R͓̽A͓̽U͓̽N͓̽I͓̽Y͓̽A͓̽R͓̽♥︎K͓̽Y͓̽A͓̽U͓̽ matakin jaha kuma sannan sunan Afeefah ya fito ma ina tunanin baka sama Labari ba,ko na ce SARAUNIYAR Gidan namu bata faɗa maka ba" Zaynerb tayi maganar ne tana kallon reacted ɗin gabaɗaya mutanen dake a dining ɗin aikuwa dai tana lura da yadda saura kaɗan Momy Rafi'at ta qware da juice ɗin da take sha saboda tarin da yazo mata yi take ba qaqqautawa.

Da sauri Zaynerb ta miƙa mata ruwa tana mata sannu, ko kallon ruwan da zaynerb ke miƙa mata Momy Rafi'at batayi ba dan takaici gorar ruwan ever dake kusada da ita ta ɗauka sai da ta kwankwaɗe shi tas sannan ta aje gorar tana ɓallawa Zaynerb harara kamar idonta zai fito waje tsaban takaici da tsanar da tayi mata.

Ita ko Lailah kasa haɗiye abincin bakinta tayi Dan kuwa maganar da Zaynerb ta faɗa a bazata ya zo mata da Ƙyar ta iya haɗiye abincin bakinta tana kallon daddy dan jin abinda zaice.

To Bangaren Haleesat ma Hakane sai dai ita ko a fuska bata nuna ba balle ka zargi wani abu ita ma dai zuba ma daddy ido tayi dan jin abinda zaice.

Afeefah kuwa murmushi kawai take saki tana kallon ko wannensu kana ta sauke idonta akan daddy ita ma.

Qayataccen murmushi na musamman daddy ya saki yana kallon kyakyawar Yarinyar tashi Afeefah daya ci buri akanta, sannan a hankali ya ce "na sama labari tun last week kawai dai ina jira kuda kanku kuyimin tuni sannan,yanzu saiku fara shiri ko.

fuska washe Zaynerb take faɗin Hakane daddy zamuyi list ɗin abubuwan da ake buƙata duk da dai ita Afeefah ɗin bamusan ko wani kalan kaya zatayi amfani dashi a gurin ba Zaynerb tayi maganar tana maida hankalinta akan Afeefah.

Murmushi tayi sannan ta canza zancen da faÉ—in nayi waya da xixi tace min nan Nijeriya zata dawo da karatunta ba za ta iyayi a abroad ba.

"Zinaru ɗin ce ta faɗi hakan da kanta?", daddy ya tambaya cikin kaɗuwa suma dai su Haleesat baki wanga me suke kallon Afeefah xixin da ko one Year ba ta cikasa ba da zuwanta faransa karatu, zatace zata dawo bayan ita ta takura a paris take son yin karatu wajen Uncle Yunus harda su rashin lafiyar ƙarya dan daddy yaƙi Yarda daga farkon Lamarin....

Afeefah ta cigaba da cewa ta ce idan ta dawo zata faÉ—a dalilinta fa, inaga kawai Kewar mu Takeyi highly shiyasa.

Shiru sukayi jin abinda da ta ce ita ko Momy Rafi'at takaici ya isheta wai ace É—iyarta guda zata dawo ita bata sani ba sai a bakin wata banza Afeefah waya sani koma ita Afeefah É—innne ta zugata tabar karatun a acan.

Ba wanda ya kuma cewa komai a cikin su har suka kammala cin breakfast É—innasu.
Ta re da Lailah Afeefah suka fita dayake school ɗaya sukeyi Suna karantun likitanci M.B.B.S. a Babbar university dake birnin tarayya ɗin wato madinatul Abuja😎.

Haleesat bata fita ba dan yau batada lecture ita micro biology take karanta tana matakin ƙarshe.
Zaynerb kuma itama ba ta da lecture gabaɗaya satin dan kuwa LAWYER take karanta tana matakin kusada Ƙarshe.

{ 𝔹𝕪 𝕋𝕙𝕖 ℕ𝕒𝕚𝕟𝕒𝕣𝕙 𝕂𝕕 }

*💋SARAUNIYAR KYAU💋*

*ⓟⓐⓖⓔ 9&10*

🄺🄰🄽🄾

🅹🅸🅴🅳🅳🅰🆁🅷♥︎🅚🅞🅜🅐🅘♥︎🅝🅐🅚🅐

A gurguje take shirin tana jin Humaira na ƙwala mata kira zasu tafi airport ɗauko "ABBA" zai dawo daga ƙasar Australia. Da sauri ta ƙara murza Jan baki a laɓɓanta tana kallon kanta a dress mirror saida tayi juyi sannan ta ɗauki wayoyinta da handbag ɗinta ta fito tana yafa scarf ɗinta.

A palo kuwa Humaira ta cika tayi fam fam domin kuwa saura kaɗan ta fashe, da sauri ta ƙarisa saukowa downstairs ɗin da sassarfa ta ƙariso wajen Humaira bata tsaya jin abunda Humaira za ta ce ba ta jawo ta tana faɗin "afuwan my sis zo muje" ba yanda Humaira zatayi haka tabi bayan Jieddarh suka fita dan tuni Auntie tana jiransu a mota ita da Heesham da yake shi zai kaisu airport ɗin.

***
Sun isa airport lokacin saura five minutes jirgi Yayi Landing, dan haka suka tsaya jira basu wani daÉ—e suna jira ba jirgi ya sauka, a hankali fasinjoji suke saukowa duk gabaÉ—aya su jieddarh sun bada hankulansu suna jiran fitowar sa.

A hankali farin dattijo wanda akalla bazai wuce shekaru Hamsin zuwa da uku ba yake taka mattatakalan jirgi yana saukowa, Humaira ce ta fara hango shi aikuwa da sauri ta ƙarisa gurin shi bata tsaya jiran wani Abu ba ta rungumeshi tana faɗin "welcome Abba we miss you highly."

Murmushi kawai yake saki yana bubbuga bayan ta, lokacin ne su Jieddarh suka ƙariso gurin fuskar ko wannensu ɗauke da walwala.

"To ae saiki sakeshi ya huta ko, kin wani maƙalƙale shi, Like a baby girl!, Jieddarh ta faɗa cike da barkwanci dan kuwa duk, wanda yasan Jieddarh yasan ta da barkwanci,She`s flirting girl.

Dariya Humaira tayi tana faÉ—in "nayi kewar ABBA obaa highly shiyasa", ta faÉ—a lokacin da take sakin shi.

A haka dukansu suka yi hugging ɗin shi cike da farin ciki da Nishaɗi, Auntie ce ƙarshen yi da akazo kanta sai taƙi yin hugging ɗinshi wai tayi fushi saida aka gama da yara sannan za'a tuna da ita?.
Dariya sukayi dukansu hadda Abba Jieddarh ta ce "haba Auntie ae yanzu ba take akeyi ba tamu Abban mu yake ke kinyi tsufa kalli yadda kike tafiya kamar zaki yi kasa fah, habah Auntyn mu kinyi zamanin ki fah wannan ƙarnin mune fah."

Dukan wasa Auntie ta kai mata da sauri ta ɓuya a bayan Abba tana dariya qwafa Auntie taja tana faɗin "zan kama ki ae fitinanniyar Yarinya kawai hmm hmm."

Dariya Abba yayi ya ce "ba ganewar da zatayi ae gaskiya ta faÉ—a dan haka a qyale min É—iyata.

Heesham ya ce "da kunzo antafi gida a ƙarishe drama ɗin acan."
"Aikuwa dai da zaifi armashi" cewar Humaira Ita ma.
Gabaɗaya suka ɗunguma gurin mota suka ƙarisa Heesham ya shiga mazaunin driver, Humaira kuma a gefan mai zaman banza, Yayinda Jieddarh dasu Auntie suke a kujerar baya Jieddarh tana nanuƙe da Abba a Haka har Gida.

ⒶⒷⓊⒿⒶ

🅷🅰🅻🅴🅴🆂🅰🆃♥︎🅜🅐🅘♥︎🅚🅨🅐🅤

Bayan fitan su Lailah school ɗaki ta koma kai tsaye Wayarta ta ɗauka ba tare da Wani ɓata lokaci ba, ta lalubo lambar xixi na ƙasar faransa ta danna kira, Sai dai a kashe wayar take.

Yanzu ma Bayan tsawon mintuna Talatin, ta kuma kiran tana mai addu'ar Allah Yasa xixi ta ɗauka, saboda akwai maganar da take so ta mata, shin ko akan meyasa takeson dawowa Nigeria da karatunta bayan kuma ita ta zaɓa karatu a Abroad.

Cikin sa'a kuwa wannan karon xixi ta É—aga kiran.

Wata nannauyar ajiyar zuciya Haleesat ta sauke tana mai zama akan Royal bed É—inta.

"Hello!! xixi," Haleesat ta faÉ—a Cike zaquwa.
On the Other hand ƙasar faransa, xixi ta amsa da....
"Hello!! Aunty leesat ya kike?"....
"Am so Normalcy," "kefah naji muryar ki kamar ta mai kuka meke faruwa?", aikuwa kamar ta ce ma xixi ta ƙara volume ɗin kukan ta ne, ƙara sautin kukunnata tayi, cikin kukan take faɗin "Aunty leesat ni gida kawai zan dawo na gaji da wannan ƙasar ta faransa,muguwar ƙasa,ni kawai Nijeriya zan dawo soon.

cikin rarrabewar murya Haleesat tace "xizzixi! xixi!! calm down just relax, natsu ki faÉ—amin abinda ya sameki kinji,"
Still cikin muryar kukan xixi ta ce "ni kawai gida nakeso na dawo, na gaji da wannan muguwar ƙasar wallahi." ta ƙarishe maganar tana mai fashewa da kuka higher.

"Tofah" Haleesat ta faÉ—a tana furzar da huci tunda taji xixi na kuka tasan abin ya cutura, a hankali cikin muryar lallashi ta ce "xixi shiga video call kawai domin zamufi enjoying na maganar okay!!."

"Tom" xixi ta ce tana kashe wayar sannan ta shiga video call ɗin ita ma Haleesat kan sofa ta koma ta zauna sannan ta shiga video call ɗin ita ma, nan take wata kyakyawar matashiyar budurwa ta bayyana wacca ba za ta wuce shekaru goma sha tara ba, tana kwance saman royal bed jikinta sanye da top red color da wando jeans pencil dogo black color ta ɗaure dogon gashin kanta da red nd black Ribbons tayi style in ponytail idanun nan nata kuwa sun koɗe sunyi jajur, fuskarta ta kumbura alamar dai taci kuka ta godewa Allah, dogon hancinta shima har wani ja, yayi saboda matsan da yasha. pillow rungume a chest ɗinta ta ƙanƙame shi cikin muryar kuka ta ce "Aunty leesat!".

Zaro ido Haleesat tayi tana bin xixi da kallo ganin yadda duk tabi ta rame tayi zuru zuru da ita. "xixi kece kuwa?"xixi Menene meke faruwa dake haka ne duk kinbi kin rame". Haleesat ta tambaya cikin shiga tsananin violence.

Qara ƙanƙame pillows ɗin dake ƙirjinta xixi tayi ta rufe bakin ta da duka hannayenta ta kasa cewa komai saima kukan dake ƙara taho mata.
Chapter 6 · 0% Book details