← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 92

Sashe 14

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aje mata plate na noodles ɗin jieddarh tayi a gabanta "gashi Bilkisu mai gadon zinare muci ko," ƙara gyara zaman ta tayi sannan ta ɗauki spoon ta ɗi ba takai bakinta tana rumtse ido, ae ba shiri ta fito dashi jin wani uban yaji ga gishiri game da uban maggi da yayiwa abincin yawa tari ta fara ba qaqqautawa kamar zata shiɗe, Da sauri jieddarh ta miƙa mata gorar ruwa na Mr. V.

Hannu na rawa ta karɓi ruwan saida ta shanye ruwan tas sannan ta sauke gorar daga bakinta tana sauke ajiyar zuciya da sauri ta ɗauki maltinar data ɗaukowa jieddarh bata shaba, ta kafa a bakinta tas ta shanye maltinar harda karkaɗe kwalbar, Dariya ma taba su jieddarh ganin yadda take karkaɗe robar , na gode Bilki ta faɗa da sauri lokacin da ta ɗauki plate ɗin indomie ɗin tabar gurin kitchen ta shiga da sauri.

jieddarh na kiranta amma ina tayi gaba ko juyowa batayi ba, dariya jieddarh takeyi dama shiyasa taƙi cin indomie ɗin dan kuwa tasan da wuya idan Bilki bata shirya mata mugunta a ciki ba gashi abinda take zargi ya tabbata, Ita ko Bilki koda ta shiga kitchen ta ƙofar kitchen ɗin ta fita ta koma sashen su na ƴan aiki cike da takaicin jieddarh da ta sa ta shan yaji ba tare tayi shiri ba, gashi ko gama kallon masoyinta Heesham ba tayi ba, A fili ta ce Allah ya isa na Jieddarh'

****

Da yamma wuraren ƙarfe biyar dai dai jieddarh na zaune a wasu ƙayatattun kujeru na hutawa daga gefan compound ɗin gidan tana karanta wani English Short Novel Mai Taken The Power Of The Silent, Gown ce doguwa a jikin ta na atamfa brown mai ratsin milk sai mayafin da ta yafa akanta milk color gabanta kayan mar mari ne kala kala sosai takejin daɗin karatun saboda yanayin weather na garin iska na kaɗawa kaɗan kaɗan gashi garin yayi luf luf💔

*Hauwa'u Ma`ana ☆🄺🅈🄰🄺🅈🄰🅆🄰🅁 🅈🄰🅁🄸🄽🅈🄰 🄼🄰🄸 🄹🄰🅁 🄵🄰🅃🄰☆ shi ne cikakken sunanta kyayawar budurwa ce mai kimanin shekaru goma sha tara zuwa ashirin a duniya.
Fara ce sosai hasken ta mai haɗe ja ne, Don zan iya cewa ma Jan yafi yawa akan farinna fatarta, Kyakyawa ce ajin farko duk wani qualities na kyau jieddarh tana dashi gashin kanta dogo mai tsayi highly highly...domin kuwa har mazaunan ta ga santsi sumar kanta mai kala biyu ne daga sama BAƘI ne suɗuq daga kasa kuma brown color ne mai haske idanun ta farare tas gasu dara dara masha Allah ga hancin ta mai tsini wanda Yayi daidai da kyakyawar fuskar ta, Bata da faɗin fuska don fuskar ta is Normalcy ne, Ga ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da launin dark pink tana da gashin gira highly highly gashi baki ga gashin idonta gazar gazar gunin ban sha'awa tana da tabon Allah a kasan gemunta baƙin ƙirin wanda ya ƙarama kyakyawar fuskar ta kyau highly highly😍.....Doguwa ce dirarra gata da duri ba'a magana saboda akwai ta da kayan alatu....Akwai ta da Yawan murmushi gata da dimples a duka gefe da gefen fuskar ta koyaya tayi magana saiya lotsa, Jieddarh akwai ta da son wasa da dariya ba ruwanta...Ta kammala Primary da secondary school ɗin ta a private schools masu masifar tsada a ƙasashe daban daban na duniya, Don bazai yiwu na ce ƙasa ɗaya ba...saidai kuma har wannan Lokaci bata shiga University ba ace war ta secondary School ma ya isheta tunda ta iya turancin ta Shikenan, Jieddarh tun tana da shekaru sha shida tayi saukan alqur 'ani mai girma tana da hazaqa highly highly🤓

Abba Yaya ne agurin mahaifin ta mahaifin ta ya rasu tun tana ciki ba`a haifeta ba..Jieddarh bata taso tasan mahaifiyar ta ba, ko'a hoto mahaifin ta dai wannan ta sanshi a hoto sannan tasan sunan shi "JURAEJ" amma mahaifiyar ta ko tayi ma Auntie ko Abba maganar ta sai suce mata mahaifiyarta bata sonta ta tsaneta bata ƙaunarta tunda ta haifeta ta bar gidan basu sake sannin inda take ba.

Saboda haka ko`a wani lokaci tayi musu magana akan mahaifiyar ta haka suke faɗa mata, Wannan ne yasa bata ma musu maganar mahaifiyarta ta saboda ta lura idan tana musu maganar ta ransu ɓaci yakeyi, Jieddarh ta taso sam batasan Menene soyayyar iyaye ba duk da cewa su Auntie ba takura mata suke ba amma soyayyar iyaye na daban ne, Burin Jieddarh ɗaya a rayuwa shi ne a wayi gari ta zama SARAUNIYAR KYAU sannan kuma tana son wasan golf obaa da kuma gasar tseren🤐.
.......................................................................................................................

𝕎𝕒𝕟𝕟𝕒𝕟 𝕜𝕖𝕟𝕒𝕟 𝕒 𝕥𝕒𝕜𝕒𝕚𝕔𝕖 𝕟𝕒𝕟 𝕘𝕒𝕓𝕒 𝕫𝕒𝕞𝕦 𝕛𝕚 𝕕𝕒𝕝𝕚𝕝𝕚𝕟 𝕕𝕒 𝕪𝕒𝕤𝕒 𝕞𝕒𝕙𝕒𝕚𝕗𝕚𝕪𝕒𝕣 𝕁𝕚𝕖𝕕𝕕𝕒𝕣𝕙 𝕥𝕒 𝕥𝕒𝕗𝕚 𝕥𝕒 𝕓𝕒𝕣𝕥𝕒 𝕕𝕒 𝕜𝕦𝕞𝕒 𝕕𝕒𝕝𝕚𝕝𝕚𝕟 𝕕𝕒 𝕪𝕒𝕤𝕒 𝕁𝕚𝕖𝕕𝕕𝕒𝕣𝕙 𝕓𝕒𝕥𝕒 𝕤𝕠𝕟 𝕜𝕒𝕣𝕒𝕥𝕦 𝕕𝕒𝕞𝕒 𝕕𝕒𝕚 𝕤𝕒𝕦𝕣𝕒𝕟 𝕤𝕦
.......................................................................................................................

{ 🅺🆄 🅳🅰🅸 🅺🅰🆆🅰🅸 🅺🆄 🅱🅸🆈🅾 𝕿𝕳𝕰 𝕹𝕬𝕴𝕹𝕬𝕽𝕳 𝕶𝕯 }

***

Ji𝖊ddarh Bilkisu ta hango zata shiga ɓangarensu na ƴan aiki da alama daga garden take ƙwala mata kira tayi da ƙarfi juyowa Bilki tayi jin ana kiran ta kuma tasan ba kowa bane sai Jieddarh, ƙarisowa gurin tayi, " Malama Bilki zauna mana" Jieddarh Ta ce tana murmushi, zama Bilki tayi a ɗaya daga cikin kujerun gurin harda ɗaukar Tufa tana ci.

"Gani kiran me kikamin aiki zanyi fah bakiga É—akina ba kacaca saboda haka faÉ—i abinda da zan miki ko nayi gaba abina" Bilki tayi maganar tanacin tufa É—inta hankali kwance, aje tsadaddiyar wayar dake hanunta Jieddarh tayi tana kallon Bilki ta ce "kinason YaYa Heesham ko?."

Da sauri Bilki ta kalli Jieddarh jin abinda ta faÉ—a dan kuwa batayi tunanin wannan kalan tambayar zata mata ba, É—an gyara zaman ta tayi tana sosa kanta kamar wata mara gaskiya, Ita kuwa Jieddarh ta zuba mata ido tana kallo, ÆŠan É—agowa Bilki tayi zatayi magana saita fasa ganin yadda Jieddarh ta zuba mata ido tana kallo "ina jinki fah, kiyi magana nifa zan taimaka miki wajen YaYa Heesham É—inne," É—agowa Bilki ta kumayi jin abinda Jieddarh ta kuma cewa magana ta fara cikin inda inda "ni nnifa Jieddarh kin zuba min waÉ—annan idanun naki mai kalar Ash bazan iya magana ba ae."

Dariya Jieddarh tayi ta ce "miye kuma idanu na suka miki da bazaki iyamin magana ba idan ina kallon ki?,"

"Hhmmm bazaki gane bane Yasin Jieddarh," "to ki ganar dani mana cewar Jieddarh.
Hm hum hum hmm Bilki taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta fara cewa "kinga idanun naki kalar su Ash dasu su suke hana mutane haÉ—a ido dake dan kuwa ina faÉ—amiki ko mijin kine kika zuba ma wannan idanun naki mai kalar Ash mai Shaining to Yasin ina faÉ—amiki baisan lokacin da zai baki kuÉ—in Lalle ba kona anko ba Yasin."

Dariya Jieddarh tayi har jejarrun teeth É—inta farare tas suka bayyana cikin dariyar take cewa "Allah da gaske kike ki rantse Bilki ta ce kicema ya mallaka miki gabaÉ—aya dukiyar shi tofah da gudu zayyi hakan.
Bilki hadda kuma gyara zaman ta a kujera ta ce "Allah kuwa ae ina faÉ—amiki keÉ—in mai sa'a ce a rayuwa."

Jieddarh ta ce "to mudawo topic É—in mu kinason YaYa Heesham ko a'a?.

Bilki ta ce "kema dai Jieddarh kinsan ba kunyar ki zanji ba, ko E' ina son shi," ta faÉ—a hadda rufe ido wai kunya bayan kuma yanzu ta gama cewa bata jin kunya ta ci gaba da cewa amma fah karkiga na rufe fuska kije ina jin kunyar ki a'a duk acikin soyayyar da nake mishi ne, To in ma ji kunyarki akan me bayan nasan ke sa'a tace dan kuwa nasan bazaki girmeni ba sai dai muzo sa'anni amma dai yanzu ba wannan maganar ce agaba na ba.

"Na Menene" Jieddarh ta tambaya "ah ae kema kinsani kawai dai ni bansan ta yadda zan janyo hankalin YaYa Heesham ya dawo kaina bane gashi É—an gayu ina faÉ—amiki idan naje kusa da shi har wani shiÉ—ewa nakeyi na manta kaina na manta wacece ni gabaÉ—aya a duniya."

"Tofah kice abin ya girmama?," cewar Jieddarh Bilki ta ce kedai Jieddarh ba zaki gane bane kawai amma na miki uzuri saboda baki taɓa soyayya ba, Bakisan Love bah amma duk ranar da kikasani zaki tuna abinda nake faɗa miki amma yanzu mu aje maganar ki a gefe aji da matsala ta ki faɗamin abinda yafi so da kuma wanda bayaso da sauransu.

Jieddarh ta ce "na farko dai abinda zan faÉ—a miki ki dena mishi wannan mayen kallon da kike mishi kamar zaki cinyeshi idan kinganshi saboda bayason kallo, Ke bamashi kaÉ—ai ba akwai mutane da yawa basu cika son a kalle su ba haka suke su, Na biyu kuma ki dinga tsafta highly highly saboda YaYa Heesham yana son tsafta highly highly ke bama shikaÉ—ai ba duka maza suna son mace mai tsafta daÉ—in daÉ—awa kuma tsafta cikon addini ne.

Jieddarh ta É—an yi shiru tana ganin yadda Bilki ta zuba mata ido tana kallo "kina fahimta kuwa?," Jieddarh ta tambaya, ajiyar zuciya Bilki ta sauke ta ce "ina fahimta sosai ma", "yauwa haka akeso ae" cewar Jieddarh nan dai Jieddarh ta dinga koyawa Bilki yadda zatayi Heesham ya sota acewar su.

Wasu danƙararrun motoci ne masu kyau da tsada suka shigo gidan guda biyu Yayinda Bilki ta saki baki da hanci tana kallon mutanen da suke fitowa daga motocin a fili ta ce "cabɗi jan yau muke ganin ƴan gayu anan gidan nan Yasin Yasin😇.

"Kalle su Mata su huɗu masu kama da Hajiya Jamila Wato Auntie da alama ƴan uwanta ne" cewar Bilki ta ci gaba da cewa gasu da yaransu suma ƴan gayu kamar su saidai ɗaya ce naga ba Yaro a tare da ita wata gila bata haihu ba ta tsaya tsarin iyali aikuwa za'a tsareta da kishiya duk ranar da mahaifarta ta sama problem "😅😂🤣.

Ɗan murmushi Jieddarh tayi bayan matan sun shiga ainihin gidan ba tare da sun kula su Jieddarh dake zaune a gurin ba, Bilki ta kalli Jieddarh da fuskar ta ya nuna alamar rashin jindaɗi ta ce "Jieddarh su kuma wa'innan fah kamar basu ga mutane a guri ba suka wuce hadda binmu da kallon banza hala ƙanin Hajiya Jamila ne naga suna kama da ita.
Chapter 14 · 0% Book details