← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 92

Sashe 72

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da gudu Zaynerb ta fito daga bedroom ɗin ta jiyo kukan Ƴar uwanta da tayi, saboda tsananin saurin da take yi ga tashin hankalin da take ciki, yasa da uku uku take tsallake staircases ɗin, tana saukowa Down, Aikuwa garin saurin da take yi ƙafarta ɗaya ta gurɗe gaba ɗayanta tayo ƙasa tun daga saman bene har sai da ta yo Down.

Aikuwa tasha azaba sosai, ga Bayanta da ya riƙe dama abu ga mara ƙiba, amma duk da hakan bata dan dara ba.

Da a zamar ta ta miƙe tsaye, sannan ta ƙarisa tsakiyar palon inda Afeefah take kwance kamar gawa ga Momyn har Yanzu bata haƙura ba, sai Faman dukan ta da marinta harda hamɓarinta take yi.

Tsuguna wa Zaynerb tayi a gaban Momyn tana bata haƙuri, amma ina Momy tayi nisa, bata jin kira da ta gata hakan ma bai isheta ba, sai ta ƙarisa wajen kayan wuta na Palon, ta ɗauko wayar wuta, sannan ta dawo ta haɗa da Zaynerb da Afeefah ɗin tana duka.
Gaba É—aya tabi ta farfasa musu jiki da duka, ko gajiya ba tayi ga Zaynerb sai faman kuka da kururuwa take tana ka re Afeefah ita dukan yake samu.

Ganin dai Momyn nasu zatayi kisa ne, Yasa Haleesat tashi da sauri ta ƙarisa tsakiyar palon tana kare su, sannan kuma cikin tsawa da ɗaga murya take faɗin

"Momy.! Momy! Are going to crazy or what?, ki barsu haka mana zasu mutu fa, wai Menene ma abin duka anan ne, wannan zalunci ne fa."

Kallon Haleesat Momyn tayi ita ma cikin tsawa da huci ta ce.

"Ki barni Haleesat ki barni na daka wannan shegun, in banda tsaban Rashin mutunci har Afeefah ce zata ce Lailah ta goge ma ta ƙafa, ita har wacece hakan, Wacece ita iye, How Dare Her?, ki matsa ko kuma na haɗa dake, duka dasu na daka."

Ƙin matsawa Haleesat tayi sai ma ƙara rufe su tana ka resu da tayi.

Ganin haka yasa Momyn dage wa iya ƙarfinta, ta ɗauke Haleesat da mari mai zafi.

Da sauri Haleesat ta dafe kun cinta cike mamaki take kallon Momyn, gaza jurewa tayi da sauri tabar wurin ta haye sama da sassarfa.

Ita kuma Momyn ta ci gaba da dukan su Zaynerb da ko motsi ba sayi zuwa Lokacin. 😭

For More Enquires
08081129487
The Nainarh Kd

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

*

Page *85&86*

"Rafi'at. Rafi'at. Ke Rafi'at.!!"

Duk wannan kiran Alhaji Abubakar Mai Kyau ne Yake ƙwalawa Momy Rafi'at Yayin da yake ta kowa palon hankali tashe, ganin irin dukan mutuwar da take yi wa marayun Yaransa.

Aikuwa Yana ƙari sawa shima bai tsaya komai ba. Ya yasa kyawawan Yatsun hannun sa. Ya bata zazzafan maruka a kumatu, bai tsaya ba ya kuma ƙara ma ta, ya ƙara, ƙara ma ta, har sai da ya ma ta sau Biyar ta ko'ina, sannan ya dakata cikin huci da ɓacin rai yake kallon ta yana faɗin.

"Rafi'at akan wani dalili kika daki waÉ—annan marayun Yaran?, dama Haka mukayi dake zaki dinga duka min Yara Iyyyee?."

Ya yi ma ta Tambayar ne damma bayaso ya yanke Hukunci kai tsaye.

Tana huci ita ma take basa amsa da faÉ—in

"A kan na isa na taɓa su, nace saboda na isa dasu ne, kuma sunyi min laifi mai girma, shiyasa idan kuma akwai abin da zaka iya kayi kai tsaye ina jiran ka Malam Abubakar."

Tayi maganar cikin tsawa da kururuwa tamkar batasan wanene tsaye a gabanta ba.

"Okay haka kika ce ko?."

"Eh Abubakar Sameer LamiÉ—o haka na faÉ—i kayi duk abin da kaga zaga iya."

Cikin Huci shima Yake faÉ—in

"It's okay a baya banso na yanke wannan tsatsaurar Hukuncin a kan ki ba, amma kuma tunda hakan kika zaɓa ki kwashi yaran ki, kije ni Abubakar Sameer Lamiɗo na sakeki, saki ɗaya ni Abubakar Sameer Lamiɗo na sakeki saki biyu..."😐

🔥🔥Kan Bala'i 😝 Taɓɓ, Tashin sense Wanda ba'a saka masa lokaci, Balle kuma Rana 🔥🔥 }

Cak... Momy Rafi'at ta tsaya galala tana kallon mijinta Abubakar wanda ya dan ƙara ma ta saki har biyu lokaci guda, gaba ɗaya wutarta ta tsaya cak, saboda tsananin tashin hankali, tama kasa magana, sam bata yi tunanin wannan tsatsaurar hukuncin Abubakar zai yanke a kanta ba, a tunanin ɗauke Yaransa zai yi daga gidan ya kaisu can wurin mahaifiyar sa ko kuma Ƴan uwansa.

Kallon Lailah da tayi tsuru tsuru da ita a saman 3sieter inda Momy Rafi'at ta jefa ta, Alhaji Abubakar Mai Kyau ya yi kana Ya daka ma ta wani uban tsawa Yana faÉ—in
"Tashi ki wuce wurin uwarki tun kafin na ya galgalaki a anan wurin... Wato ke ce mai cewa a ƙarawa Shalele ta ko?, zaku sani daga ke har uwan taki, sai nayi maganin ku."

Da gudu ta sauko daga saman 3sieter ɗin har tana tun tuɓe, ta ƙarisa wurin uwarta wacca ta zama Tamkar statue a wurin. 😹

Qari sawa wurin da Yaran nasa suke ko wacce a sume. Ya yi sannan ya kamo hannun Zaynerb ya ɗa ga ta ya saɓata a kafaɗa sannan Ita ma Afeefah da jini duk yabi ya ɓata rigar Ƴar kanti dake jikin ta.

Ko kallon wurin da Momy Rafi'at take bayyi ba, ya fi ce dasu kai tsaye parking lot ya nufi.

Da hango Mister Mai Kyau tafe, ga Yara jiki duk jini, driver Jacob ya tabbatar da babu lafiya.
Da saurin sa ya ƙarisa wajen da motocin gidan suke a fake, sannan ya buɗewa ogan nasa motar ya saka Zaynerb a back seat, sannan ita ma Afeefah ya sakata, kana shima ya shiga, ganin haka shima Jacob ɗin ya shiga sannan ya tayar da motar, da gudu suka bar gidan bayan gate man ya wangale musu gate.

Wani Emergency dake a nan kusa da yankin Jacob ya ƙarisa da su bisa umarnin Mister Mai Kyau.

Da sauri ya fito daga motar sannan ya fito da Zaynerb aka aurata bisa Stretcher sannan aka shiga ciki da ita. Yayin da ita ma Afeefah aka É—aura ta bisa gadon ko numfashi bata yi, gaba É—aya a kayi ciki da su domin basu a gajin gaggawa.
Yayin da Alhaji Abubakar ya yi ma Jacob umarni da ya koma can gida da motar.

Sannan ya shiga cikin emergency ɗin da yake Babban mutum ne kuma sananne a duniya, shiyasa ba tare da ɓata lokaci ba ko bincikan lamarin aka fara basu taimakon gaggawa.

Tuni Zaynerb ta dawo Hayyacinta sai dai kuma a dalilin faɗowar da tayi daga saman bene ta sama gocewar ƙashi a hannun ta na dama.

Sai dai kuma duk yadda aka so Afeefah ta dawo Hayyacinta Abu dai ya cutura, domin kuwa ba ƙaramin wahala ta sha ba. Wanda dalilin haka ne ma yasa ciwonta wanda ba'asan dashi ba tashi. 🙄

Fitowa daga cikin emergency room É—in Dr. Ya yi Yayin da wasu Nurses ma ta biyu suke bin Bayansa.

Da sauri Alhaji Abubakar da Zaynerb wacca taƙi zama a room ɗin da aka bata, suka miƙe kana suka nufi Dr. suna tambayar sa halin da Afeefah din take ciki.

Cire Nose mask dake fuskar sa Dr. Ya yi kana cikin girmamawa ya fara magana.

"Mister Mai Kyau. Please ko zamu iya tattaunawa da kai a office nawa?, domin maganar ba zata yiwu a tsaye ba."

Ajiyar zuciya kawai Alhaji Abubakar Mai Kyau. Yake saukewa domin kuwa ya fahimci akwai matsala, kallon Zaynerb dake faman hawaye Ya yi kana cikin muryar kwantar da hankali Yace

"Zaynerb Ɗiyata, please koma ki zauna, ki jirani kinji Ƴar uwanki zata sama lafiya soon, amma fa sai kin daina kuka kinji tawan?."

Share hawaye tayi kana ta koma ta zauna, bata ce komai ba, amma ta yanke a ranta ko ba yanzu ba sai ta Rama musu Abin da Momy Rafi'at tayi musu, tana gani Daddyn da Dr. Sun nufa Hanyar office na Dr.
Ta miƙe da sauri ta ƙarisa ƙofar room ɗin tana leƙen ƙanwarta ta wacca aka saka mata oxygen ta baki kamar babu Rai a jikin ta.

Wani kuka ne mai ƙarfi ya kuma zuwa ma Zaynerb ganin irin Halin da ƴar uwan nata take a ciki. 😭

Wuri Alhaji Abubakar Mai Kyau. Ya samu ya zauna a É—aya daga cikin kujerun da suke a office É—in, sannan shima Dr. Ya zauna sannan bayan sun gaisa, suka yi shiru na wani lokaci, kana Dr. Ya katse shirun da office É—in ya É—auka, bayan ya yi gyaran murya sannan ya fara magana kamar haka.

"A gaskiya Mister Mai Kyau bazan ɓoye maka ba, domin kuwa halin da ɗiyar ka take ciki ya tsanan ta, fiye da kima, domin ko a dalilin dukan mutuwar da aka ma ta a bisa binkciken da muka gunadanar a kanta mun gano cewar, ciwon ta ne, ya tashi wanda hakan ne yasa zuciyarta da gangar jikin ta sukaƙi kaɓar duka taimakon da muke bata. Sann..."

Katse sa Alhaji Abubakar Ya yi Cike da Tashin Hankali Yake faÉ—in

"Ban fahimta ba, dama Afeefah tanada wani ciwo ne. Wanda mu bamu san dashi ba?. Please Dr. Yimin yayani yadda zan gane."🥺

Ajiyar zuciya Dr. Ya sauke sannan yana amsa masa da faÉ—in

"Dama Bai zama dole ku san tanada wannan ciwo ba, domin kuwa ba ko wani lokaci yake tashi ba, sai lokacin da aka ɓata ma ta rai, misali dai kamar ace.

Yanzu tana cikin Mood na farin ciki, sai kuma wani abu na baƙin ciki, ya same ta, shi ne wannan ciwo nata zai tashi, ko kuma tana cikin Mood na baƙin ciki, sai wani Abu na Baƙin ciki ya kuma samun ta a lokaci guda, tofa wannan ciwo nata yana iya tashi, ko dai still tana cikin Mood na farin ciki sai wani Abu na farin ciki Ya kuma nin kuwa akan wannan farin ciki da take ciki. Tofa ciwon ta nan ma zai iya tashi."

Zugum Alhaji Abubakar Mai Kyau Ya yi Yana sauraron Dr. Yayin da hankalin sa idan Ya yi dubu, tofa ya tashi domin kuwa shi tunda yake a tayuwar sa. Bai taɓa ji ko cin karo da makamancin wannan ciwo ba.

Sai da ya tattaro duka Nutsuwar sa sannan Ya fara faÉ—in
Chapter 72 · 0% Book details