Sashe 45
Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kashe T.v É—in Jiddarh tayi sannan ta kalla su Humaira tana faÉ—in "Abin akwai ban tausayi fa, ace mutum bai samu ya cika burin da ya sama rai ba, a gaskiya yarinyar ta bani tausayi ba kaÉ—an ba."
Ajiyar zuciya Humaira ta sauke tana mai faɗin "Ni ma dai hakan ne, amma ya zatayi wannan ita ce ƙaddarar ta gashi abin ya yayatu a social media ta ko'ina maganar ta akeyi fa."
Auntie ta ce "ai kunji irin matsalar yanzu tajama kanta da iyayenta tonon qwaqwaf kenan fa."
Ci gaba da tattaunawa akan lamarin sukayi gaba É—aya jikin Jiddarh yayi laqwas duk tausayin budurwar yabi ya addabeta a zuciya.
Suna cikin haka sai ga Bilki ta shigo bugujin bugujin da ita ga yarinya a hannunta tana tsotsar madara a fida.
A tsakiyar palon ta zube sannan ta kalla Jiddarh tana faÉ—in "Sannu SARAUNIYAR KYAU ta jahar Kano, gaskiya ina tayaki murna sosai."
"Ke tayaya kika san ita tayi Nasara a Gasar bayan kuma bakije Gasar ba?."
Auntie ta tambaya tana kallonta, dariya Bilki tayi ta ce "Hajiya kenan Auntien mu kin manta ina da waya ne.?"
Humaira ta saka baki, "Malama Bilki mai raino, to ya ya yarinyar taki take,?"
Bilki tana washe baki ta ce "Ga yarinyar bata da rigima sam, inajin daÉ—in wannan yayen da nakeyi, ni dama mutane zasu gane su dinga kawomin raino ai dana zama Auntyn Yara."
Jiddarh ta ce "Aikuwa zaki dace da Autyn Yaran highly."
Bilki ta bata amsa da "Kedai bari ai abin ba'a iya cewa komai wallahi."
Jiddarh ta kuma cewa "To ya zakiji idan akazo tafiya da Khausar ranar da kika gama rainonta?."
Bilki ta ce a gaskiya abin babu daɗin faɗa ko'a baki, dan zanyi kewar ta sosai banama fatan ranar da zata zo karɓanta tazo, dan idan tazo sai nayi zazzaɓin yini ɗaya yasin."
Tayi maganar tana zuba uban tagumi.
Humaira ta ce "Ba kewar ta zakiyi ba kenan, tunda dai zazzaɓin yini ɗaya zakiyi kacal?."
Bilki ta amsa da "To ai na yini É—ayan yafi daÉ—in faÉ—ane a baki fa, shiyasa nace hakan."
Dariya sukayi jin irin wautar Bilki fira suka ci gaba dayi sama sama Bilki tana basu dariya da shirmen ta.
*SARAUNIYAR KYAU* 💓
_(The Glam Queen)_ 👑
```Takun Farko```
Story & Written By:
*_The Nainarh KD_*
_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._
*THE ONGOING BOOK'S*
1. *SONKI NE ƘADDARA TA*
MALLAKAR
FATIMA ABDULLAHI
_Batool Kamba_
2. *ZAN JIRA KA*
MALLAKAR
A'ISHA ALƘALI
_Mrs Aysib_
Page *43&44*
ABUJA_NIGERIA
M.M.K, FAMILY💓
Sun isa gida lafiya, cike da farin ciki dukaninsu suka fito daga cikin motocinsu sannan suka miƙa hanya, palo suka shiga bayan Momy Rafi'at ta danna lambobin sirri ta buɗe.
Gaba É—aya saman kujeru matan suka zube cike da gajiya, dama shi M.M.K tuni yayi part É—inshi.
Lailah ta nisa tare da faÉ—in "A gaskiya mun kwaso gajiya, ba kaÉ—an ba, domin kuwa jina nake kamar anyimin dukan tsiya fa."
Tayi maganar tana kwance igiyoyin takalmin ƙafarta da bata samu ta cire ba, saboda tsaban gajiyar da tayi.
Zaynerb ta ce "Kedai bari kawai, dan gajiya akwaita kam sosai, dan yanzu banajin zan iya zama, har saina ji ni ina take shower ko zanji daÉ—i."
ÆŠagowa lailah tayi tana shirin yima Momynsu magana taga ta nufi staircase's ta fara takawa saboda sauri da bibiyu ma take taka staircase's É—in.
Dukansu da kallo suka bita baki sake, amma basu kawo komai a ransu ba, dan kuwa sunfi tunanin gajiya ne, da kuma tunanin Asibiti wata ƙila za'a iya nemanta a ko wani lokaci yasa tayi hakan.
Sai dai banda Zaynerb wacca kanta kawai ta girgiza sannan ta shige Bedroom ɗinta tana saƙa abubuwa da yawa a zuciyarta.
Wani wawan bugu ta kaima ƙofar Bedroom gaba ɗaya tama manta a kulle ƙofar take, har sai da taga ƙofar taƙi buɗuwa, sannan ta zuge zip ɗin jakarta dake rataye a kafaɗarta ta ciro key's ta buɗe ƙofar ta shiga ciki a mugun fusace, zuciyarta har wani tafasa take saboda tsaban ɓaccin rai.
Tana shiga bata tsaya komai ba tayi jifa da jakar hannunta a saman gado mayafin kanta ma cireshi tayi shima tayi throwing ɗinshi saman mattress, gaba ɗaya perfumes da cosmetics ɗin dake saman mirror tayi watsi dasu har ƙasa, nan masu tarwatse suka farfawashe a ƙasa, hakan ma bai ma ta ba ɗaukar wani kwalbar turare tayi da ƙarfi ta jefa shi saman Dress Mirror, aikuwa nan take Dress Mirror ɗin ya tarwatse a gurin.
Huci kawai take fitarwa tana zagaye Bedroom ɗin, da sauri ta ƙarisa gurin da ta jefar da jakarta, buɗe jakar tayi sannan ta ciro wayarta, kai tsaye contacts ta shiga ta lalubo wata lamba wanda akayi saving da rubutun CHINESE, kira ta danna amma abu ɗaya wannan Baturiyar mai baƙin jini take faɗa shine, wayar da take kira a kashe take.
Bugun zuciyarta ne ya ƙaru fiye da kima, wai meke shirin faruwa ne?, kardai ace wannan matar yaudaranta tayi bata ma ta aikin da ta sakata ba, aikuwa bazai yiwu ba, ita bama uban kuɗaɗen da ta bawa matar takeji ba, a'a wahalar da ta sha kafin ta samu ta sama..."Kai bazai yiwu ba wallahi, No Way.! wallahi bazan yadda ba, ina! sai dai kuwa idan ba ni ce Rafi'atu Rafiq Rayyan ba.
Gaba ɗaya maganar takeyi idanunta a rufe kuma a fili take maganar cikin hargowa saboda mugun ɓacin ran da take ciki.
Wani irin jifa tayi da wayar hannunta a jikin bangon ɗakin sai ga wayar a ƙasa tayi tatsatatsa ta tarwatse a ƙasa, da gudu ta ƙarisa gurin wayar faɗin take "Ina bazai yiwu ba, bai kamata nayi haka ba, wannan wayar tana da matuƙar muhimmanci a gurina."
Gaba ɗaya saboda tsananin tashin halin da take ciki, saya tana abu kamar wacca bata cikin hayyacinta faɗi take "Please an waya ki kawo, karki yimin haka ina buƙatar amfani da ke, please please..."
Ganin dai wayar ba kawowa zatayi ba, yasa ta kuma jifa da ita, ba abin da takeyi a Bedroom É—in sai faman kai kawo daga nan zuwa can.
Tsayawa tayi cak da kai kawon da takeyi, juyawa ƙofa baya tayi, sannan daga tsayen da take ta fara magana a fili cikin ɗan ɗa ga murya take faɗin "Wallahi bazai yiwu ba, ace yarinyar nan ta sama Nasara, to wai ina inane lokacin da hakan ta faru?..."
Ɗan shiru tayi kamar mai tunani, sai kuma can bayan wasu mintuna a fili ta kuma cewa "Na rantse da wanda raina yake hannunsa sai naga ƙarshen zuri'ar Hajarah mudin ina raye a duniya koda kuwa zanyi yawo tsirara ne, waɗannan mutanen guda uku bazan bari su sama sa'ida ba a rayuwa, indai ni ce Rafi'atu Rafiq Rayyan tabbas anwuce gurin."
"Da gaske kike zaki iya yawo tsirara akan cikan burinki, ko kuwa faÉ—a kawai kike na kuri.?"
Da mugun sauri ta juya tana kallon wacca tayi ma ta wannan tambayar.
"Ke kuma tun yaushe kike anan?."
Tayi ma ta tambayar tana zama saman Bed ta ci gaba da cewa "Menene ya kawoki nan.'
Qarisa shigowa Haleesat tayi ita ma ta zauna a saman bed ɗin tana fuskan tar ta sannan ta mayar da kallonta kan bedroom da yayi kaca kaca, tana ƙarara ko'ina kallo, har sai da ta gama nazartar Bedroom ɗin tsaf, sannan ta ce fa idanunta zuwa ga kallon Momy Rafi'at dake faman huci, da alamu har yanzu ɓacin ran da take ciki, bai gama sakinta ba.
"Na tambaye ki kinyi shiru, shin zaki iya yin yawo tsirara a domin cikar burin ki?, sannan naji kina faÉ—in mutane uku zaki É—auka fansarki akansu, nidai nasan mutum biyu shin wanene ko kuma wacece ta ukun?."
Shiru Momyn ta ma ta kamar ba zatayi magana ba, sai kuma ta ce "Lokacin da zakisan ko wacece ta ukun bayyi ba, amma duk ranar da burina ya gama cika, tabbas zan faɗa miki ko wacece ta ukun, a ranar zakisha mamaki kalar wanda baki taɓa sha ba tsayin rayuwar ki Haleesat."
Tayi maganar tana sakin shu'umin murmushi kamar ba ita ce wacca ta haÉ—e rai ba, sannan kuma idanunta qur akan Haleesat kamar yadda ita ma Haleesat É—in ta zuba ma ta nata kyawawan idanun tana kallo ba tare da ta ce da ita komai ba.
Ajiyar zuciya ta sauke har yanzu idanunta akan Momy Rafi'at suke, da kyar ta iya haÉ—iye yawun bakinta domin kuwa yanzu Momyn ta dena bata mamaki, sai dai tsoro, sannan ta ce "Shin Momy zan iya tambayar ki wani abu kuwa?."
ÆŠan murmushi Momyn tayi sannan ta ce "Go ahead,"
Haleesat ta ce "Wai shin menene ainihin abin da yasa kika tsana maragayya Mamy Hajarah, bayan kuma ba abin da tayi miki, kuma naga ai ta mutu ko, amma baki rabu da yaranta biyu ba, da Allah ya azurtata dasu kafin rasuwarta, sannan kuma naga Daddyn har da kowa a cikin dangi harke kanki ba wanda ya taɓa faɗar hallayar ta mara kyau, kowa sai dai ya faɗi alkhairinta. Shin ko zaki iya faɗamin dalilin da yasa kika tsaneta haka?."
Haleesat ta ƙarishe jero ma ta jerin tambayoyin, tana kuma kallon Momy Rafi'at ɗin da kyau tana jira taji ta bakinta.
Ajiyar zuciya kawai Momyn take saukewa tana kuma ɗaure fuska, tuno abubuwan da suka faru fiye da shekaru Ashirin baya. Tunosu take kamar yanzu suka faru, tana tuna yadda Hajarah taci amanarta ta aure ma ta miji, yayinda take tuno hakan zuciyarta take ƙara ma ta zafi.
Sun É—auki fiye da mintuna biyar a haka suna kallon kallo.
Kafin can Haleesat ta katse shirun da faÉ—in ''Ina jinki fa Momy, ko dama ba wani abu da tayi miki, kawai kinaso ki É—auki fansa ne, ba tare da ta yi miki wani Babban laifi ba?."
Da sauri Momy Rafi'at ta katseta da faÉ—in "Dakata Haleesat badai kinaso na faÉ—amiki abin da Hajarah tayimin ba, to yanzu zakiji komai, zakiji kalar cin amanar da tayimin. Sannan sai ki tantance wacece mai gaskiya tsakanin ni da kuma ita."
Gyara zamanta Momyn tayi sannan ta fara magana haka.