Sashe 7
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadik ya girgiza kai yace "Ina son Farhan ne ba dan in ɓata mata rayuwa ba, hasalima ni kamun kanta, sanyin halinta da kunyarta ne yasa na fara sonta, kuma ni sam bani da interest akan aikata abunda be dace ba, ni bazan kalli filma na batsa ba, bashi da wani amfani Sam, bayan ya toshewa me kallonsa ƙwaƙwalwa ga kuma zunubi, sannan nafi ƙarfin ku kirani yaro wallahi, cox i always have dreams, ina jin feelings kamar kowane lafiyayyen namiji, sedai ni ina son Farhan ne dan Allah ba dan wani abu ba"
"Taɓɗijan, aikuwa in dai dagaske kana jin feelings, and you even have dreams ma, to tabbas a hankali watarana seka so kasancewa da mace, kuma ga Farhan a kusa da kai, tunda ba aure za'a maka yanzu ba, Yawan kasancewarku tare komai na iya faruwa"
Nasir yace "dalla bar ɗan rainin hankali, wai shi na Allah, se iskanci a baki amma baze gani ba koya aikata, my friend you better enjoy your life, that girl can do anything you ask her to do, gara ka gwada kanka kaji capacity ɗinka, ko ka ƙare a kame Kame, ƙishirwa ta addabeka, ga ruwa a kusa da Kai amma kaƙi maganin ƙishirwar"
Aminu yace "rabu dashi, taso mu tafi Baba, duk ƙaryar banza ce ba namiji bane, har yanzu yarone".
Suka kwashe da dariya, suka tafi suka bar Sadik cikin tunani.
Nzarin maganganun sa ya dinga yi, gaba ɗaya yaji kansa yai dumm, yama rasa wane tunani zeyi? Su Nasir sun caza masa kai, suna ƙoƙarin cusa masa wani tunani, ga ɓacin ran Fargan kuma.
Farhan kam harta je gida gaba ɗaya bata hayyacin ta, bata san ma daya taje gida ba, saboda tunanin ta ɓatawa Sadik rai, mussaman yadda ya dinga faɗan nan, ta san tabbas ransa ya ɓaci sosai, nan ta fara tuhumar kanta meyasa ma ta biye maganganun Sir Nazir, ta fara gujewa Sadik, ƙila ma barazana kawai yake Mata, ba wani Babanta daze kira ya gaya masa, dan gara ma a gayawa Babanta, ta san baze wuce ayi mata faɗa ba shikenan, amma idan Sadik ya dena kulata bata san ya zata yi ba.
Jiki a sanyaye take yin komai, har seda mahaifiyarta ta lura da hakan, tace "Farhan meke damunki ne? Ko a makarantar ne akai miki wani abu?"
Farhan ta girgiza kanta tace "A'a Umma, ba abunda akayimin"
"To idan ma wani abun akayi miki, kiyi haƙuri, ki iya talaucin ki nasan duk makarantar babu ɗan talaka kamar ke, kema Allah ne yayi zakiyi wannan makarantar, saboda scholarship ɗin nan, dan haka sedai kiyi ta haƙuri"
Har Umman Farhan tayi maganarta ta gama, sam Hankalin Farhan baya kanta, tunanin ta kawai yadda zata shawo kan Sadik, dan ta lura yana da kafiya wasu lokutan da zafin zuciya.
Salla kawai tayi ta nemi Guri ta kwanta, Ummanta ta shiga ɗakinsu ta ganta a kwance "Islamiyyar ce ba zaki ba, ko kuma wani sabon salon wulaƙancin ne haka?"
"A'a Umma, kaina ne yake ciwo"
Daga nan Umma bata sake cewa komai ba, ta fita daga ɗakin, bin bayan Ummanta tayi da kallo taji ina ma Ummanta tana sauraren ta, kasancewar ta 'yarta ta fari sam bata wani shiga sabgarta, ko hirar kirki ba ta yi da ita, lokuta da yawa abu na damunta, amma ba zata taɓa iya tunakarar mahaifiyarta da maganar ba, duk da ƙanƙantar shekaru na Farhan, tana son hira da mahaifiyarta, amma sam mahaifiyarta bata bata lokaci,ba ta raɓar duk wani abu da ya shafi Farhan saboda kunyar ɗan fari.
Ajiye wannan tunanin tayi, ta shiga neman mafita akan yadda zata shawo kan Sadik, shiru tayi ta shiga tuna haÉ—uwarta da Sadik, da yadda suka fara soyayya.
Bayan an sanar da iyayen Farhan ta samu scholarship, a makarantar su Sadik saboda ƙwazonta, sunyi murna sosai dan makaranta ce ta 'ya'yan manya, kuna akwai karatu sosai a makarantar.
Sedai Ranar farko da Farhan ta fara zuwa, ta tsorata da ganin yaran dake makarantar, saboda duk yadda ake zuzuta makarantar ta yaran masu kuɗi ce, bata zaci zata ganta haka ba, Yarane na alfarma a makarantar, 'ya'yan hutu rainon AC, gaba ɗaya tsarin rayuwarsu ya sha bamban da wanda ta taso taga anayi, kalar fatarsu kawai idan ka kalla ka ga yaran hutu, dan kaso mafi yawa na yaran farare ne ƙal.
Suna da cikakken 'yancin aikata abinda suke so a makarantar, da ƙalubalantar duka' wani malami da yayi musu ba daidai ba, saɓanin makarantar data baro, Wadda ta kasance ta gwamnati, baka da wani kataɓus se Abinda malami yaga dama.
A makarantar data baro ta saba da idan an fita tara, suje su kashe kuɗin makarantar su da idan yayi wuta naira hamsin, amma a wannan Makarantar idan aka fita tara masu zuwa da abinci zakaga Abinci ne na alfarma, kaji ko nama yanka zuƙu zuƙu akan abinci, ko kuma tarkacen kayan cake da chocolate da sauran kayan kwaɗayi, se kaga ɗalibi da sama da naira dubu guda.
Ta saba a makarantar data baro, in an fita break, wasansu baya wuce 'yanta, 'yar gala gala da sauran wasannin yara, amma a wannan makarantar daga basket ball, football, volleyball irin wannan wasannin suke, sannan suna bawa birthday mahimmanci da sauran bidi'oi wanda bata saba dasu ba, suna da manyan gangaunan kiɗa da manyan speaku na disco, har clubs clubs ne na koyarda rawa ta zamani, da waƙe waƙe a makarantar.
Ga uwa uba dressing, ita makarantar da ta baro dukda a Jss1 ta baro makarantar, amma hijjabinta ya wuce gwiwarta, manyan hijjabai suke sawa, amma a wannan makarantar, skirt ne gajere daidai jikin ka, ka rufe ƙwaurinka da safa idan kana buƙata, ga ɗan ƙaramin hijjabi, sam bata iya Ratsa unguwarsu da wannan ɗan guntun Hijjabin, seta saka babba a kai.
Wannan banbance bambancen ne yasa Farhan ta sake takure kanta a makarantar, komai nasu ganinsa take daban takasa sabawa da abubuwan makarantar, saboda sun sha banban dana wadda ta baro, ta 'ya'yan talakawa.
Sam bata da wasu ƙawaye a nan, dama dai bame kwashe kwashen ƙawayen bace.
Gaba ɗaya yanayin makarantar da Al'adun makarantar se sukayi mata wani iri daban, babban abinda yake ƙara ɗaure mata kai be wuce yadda ɗaliban da wasu daga malaman ke mu'amalantar juna tamkar jinsinsu ɗaya ba, ta hanyar yin wasanni tare, kamar na ƙwallon ƙafa da sauransu, cin Abinci tare, gaisawa da juna ta hanyar musabiha tsakanin maza da mata, rungumar juna da dai sauransu, wanda a normal al'adar malam bahaushe hakan ya saɓawa tarbiyya da addininmi, dan haka gaba ɗaya Farhan take baya baya da lamuran makarantar nan dama ɗaliban, ta kama karatunta tunda shi tazo yi, suma ɗaliban ba kowa ke shiga harkarta ba saboda suna mata kallona wadda bata waye ba sam.
Wataranar juma'a, lokacin kusan satinta uku a makarantar, Sadik ya dawo aka ce yaje Umra shida 'yan gidansu, anyi rabon kayan dabino bagaruwa, zam zam carbi agoguna, haka aka dinga rarrabawa, abunda Farhan ta lura shine, Ana matuƙar son Sadik, baga malamai ba baga ɗalibai ba, saboda barkwancinsa da yawan kyautarsa, dukda duk yaran masu kuɗine abokan nasa, amma yana musu ɓarnar kuɗi sosai.
Gashi yana da ƙoƙari sosai, sedai ta lura bayan sonsa da akeyi kamar abun harda tsoronsa akeji, seniors ɗinsa na shakkarsa, haka juniors ɗinsa, ko gaban assembly ne ake surutu kafin a fara assembly malamai suzo, daya hau kan stage kowa yake yin shiru, Sadik akwai tsafta da gayu sosai da sosai, gashi baya son raini ko kaɗan, ko tahowa yayi Junior ya taho se an bashi hanya ba'a haɗa hanya dashi, koda kuwa 'yan SS1 ne, sedai Wasu lokutan yakan shiga cikinsu yayi Wasanni kamar ball da sauransu, sabida bayan kasancewar sa gwarzo a aji, ƙwararren ɗan wasa ne, dan ba dan mahaifinsa yaƙi bashi goyon baya ba, da ƙasar waje ze tafi makarantun koyan tamaula.
Wata ranar juma'a, duk 'yan makarantar na gurin wasanni, wasu na wasa, wasu na gurin kaɗe kaɗe, Sadik ya shiga cikin makarantar ɗakko ATM card ɗinsa, ze fita cin Abinci, yazo wucewa ta ƙofar ajinsu Farhan, ya hango ta a zaune ita kaɗai a ajin, tunda ya dawo daga Umra ya ganta a makarantar, baƙuwar fusaka ce dan be santa ba kan ya tafi, sedai yana lura da yadda sam ba ruwanta da kowa, abinda ya dameta shi kawai take yi.
Tura ƙofar ajin yayi, wanda hakan yasa ta ɗago da sauri, ya ɗan ƙura mata ido sannan Yace "ke bazaki gurin wasan bane?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To saboda me?"
"Bakomai" ta faÉ—a a sanyaye.
"Amma You Are new in this school ko?"
Ta É—aga kai alamar eh.
Sadik yace "Yayi kyau, amma Yakamata ke ma ki fita gurin wasanni, ki dinga motsa jiki"
Farhan ba tace masa komai ba se binsa da kallo da tayi, Sadik dogo ne chocolate color, kana ganinsa ka san ɗan hutu ne, yana tara suma a kansa, Afro style ko yaushe sumar tana ƙyallin mai, da wuya ka ga kansa a bushe babu mai, gashi da dogon hanci sosai, masha Allah ɗan kyakykyawan matashi ne Prince Sadik.
Tun daga ranar da yai mata magana, duk in da suka haÉ—u se yai mata murmushi yace mata "Sannu"
Wasu lokutan ta kan mayar masa da murmushin tace "Yawwa"
Haka nan take burge Sadik, saboda shiru shirunta, kusan kullum se sun haÉ—u ko a hanya ko kuma a gurin assembly.
Watarana ana birthday party na headgirl É—in makarantar, gaba É—aya an tare a gurin da ake raye rayen, Sadik ya duba duk gurin partyn amma be ga Farhan ba, ko a gurin assembly be ganta ba, haka nan yaji yana son ya ganta, dan haka ya tafi ajinsu.
Ita kaɗaice a ajin, ta kifa kanta a kan benci, Sadik ya ƙwanƙwasa ƙofar clss ɗin, hakan ya sa tai saurin ɗagowa, kamar kullum yau ma musayar murmushi suka yi.
Ya ƙarasa ya zauna a kusa da ita, zaman da Sadik yai a kusa da ita se taji tamkar wani babban zunubi ne, take fargaba ta shige ta da tunanin idan aka zo aka gansu a haka fa?
Prince yace "meyasa baki je gurin birthday É—in ba, Why do you always like to isolate yourself from the people?"
A hankali tace "bakomai"