Sashe 44
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru tai masa ta kashingiÉ—a a jikin seat É—in motar, tana jin yadda mararta ke É—an takura mata da ciwo.
Sadik yaita mata magana amma tai masa shiru, seda suka zo in da take sauka, sannan ta ɗau jakarta tacewa direban "Baba nagode"
Direban yace "Yawwa bakomai"
Sadik yace "Nifa?" Murguɗa masa baki tai ta sauka, sedai tana sauka yaga inda ta tashi yai staining na jini, ga shi ƙasan baban hijjabin da take sawa ma ya ɗan ɓaci.
Kwanciya yai a jikin seat É—in motar, ya É—an shafi sumar kansa yace "Babyna ta girma ba labari, sedai yana ganin kamar tayi yarinta sosai da farawar"
Murmushi ya cigaba da yi, wanda shi kansa be san dalilin yin sa ba.
Suna zuwa gida ya kalli direbansa yace"A wanken motar nan"
Be jira amsar da ze bashi ba yai gaba abunsa ya nufi BQ.
Lilly kuwa seda aka haɗa mata da ƙarin ruwa da allurai sannan ta dawo hayyacinta gaba ɗaya, Sir Nazir yayi regrating Punishing ɗinta da yai har yai leading ɗinta ga Wannan condition ɗin.
Amma a zahiri ya dake ya nuna ko a jikinsa, seda ta gama farfaɗowa sannan aka ɗakko mata jakarta daga aji, Madam Joy ta riƙota ta kaita motar Makaranta, ta shiga dan raka Lillyn gida.
Seda Nazir ya tabattar komai ya daidaita, sannan ya koma ya tattara kayansa shima ya tafi gidan da yake zaune.
Sedai lokaci lokaci da ya tuna yadda ya kasance da Lillyn a ɗazu dan ceto ranta, se yaji wata irin mummunar faɗuwar gaba, ƙirjinsa kuma na bugawa da ƙarfin gaske.
Ya dinga maimaita 'Innalillahi, wa innalillahi raji'un"
A ƙauye kuwa Nana ce zaune a can ƙuryar ɗakin Inna, ta samu ƙatuwar 'yar tsanarta tana ta taje mata gashi, dan sam taƙi kula Inna, hakan ya kasance ɗabi'ar Nana, duk da shegen surutunta, amma lokuta da dama idan aka ɓata mata rai, se tai shiri ta dena maganar se abunda ya zama dole.
Sedai kan tai irin wannan fushin tana daÉ—ewa.
"Nana" Inna ta kira sunanta, ba ta amsa ba sedai ta É—ago ta kalli Innan
"Ba zaki dena wannan fushin ba ko? Dani kike fushi ko Nana?"
Nana tace "A'a ni ba fushi nake ba fa"
"Ƙarya nai miki kenan, to dan ubanki wannan ba halin zuwa gidan miji bane, ba Namijin da ze ɗauki wannan iskancin da rashin mutuncin naki"
Nana tai shiru taƙi magana, can Innan ta kuma cewa "Nasan zakiga kamar ina takura miki akan wasu abubuwan, ba ina yine da cuzgunawa rayuwarki ba, ina yi ne dan ganin Rayuwar ki ta inganta.
Jiya duk hirar da ku kai da waÉ—anda suka zo gurin naki ina jinku.
Da sauri Nana ta kalli Inna, dan sam ba ta zaci taji hirar tasu ba.
"Ƙwarai kuwa, ko dan kinga na ƙyaleki? Naji suna gaya miki wani yana bakin layi yana jiranki, Nana ita rayuwa ba'a mata gaggawa, duk saurayin kirki da yake sonki saboda Allah, gidanku ze zo ya nemi izini, ba wai ya dinga laɓewa a bakin hanya yana tsare ki ba.
Nana ke yarinya ce, kina kan ganiyarki ta RUƊIN ƘURUCIYA, Shiyasa abubuwa da dama kike ganin kamar ina takuramiki.
Ba takura miki nake ba, so nake rayuwarki ta inganta, ki guji ƙawaye barkatai, idan kika fiye ƙawaye da yawa zaki zama baki da sirri, sannan ba kamun kai, dan zaki suffantu da ɗabi'u daban daban daga gurin su, masu kyau da marasa kyau.
Dan haka duk abunda ya shige miki duhu, wanda kike buƙatar ƙarin haske ni zaki samu ki gayawa, duk wata shawara da ƙawa zata baki, in dai zaki iya ɓoyewa ba zaki faɗa ba to ba shawarar Allah da Annabi bace, dan haka ki kiyaye kinji abunda nace miki?"
Nana ta jinjina kai alamar eh.
Inna tace "Yawwa".
Koda Madam Joy ta raka Lilly gida, ta gaya musu kawai ciwonta ne ya tashi, sun bata taimakon da ya dace a Clinic É—in Makaranta.
Maman Lilly ta karɓe ta cikin girmamawa tare da yi mata godiya.
Mamanta se jera mata sannu take, yayinda zuciyar Lillyn fal take da jin haushin Sir Nazir, babban abunda ya ƙara ƙular da ita be wuce yadda tana buɗe ido ta kalleshi, ya wani haɗe rai ya bar Clinic ɗin ba.
Ba ta san lokacin da tai ƙwafa a fili ba.
Mamanta ta kalleta tace "Lillyna meke faruwa ne? Nifa nayi mamakin yadda a kai ciwon nan naki ya tashi, ko dai an miki wani abun ne kinyi kuka?"
Cikin taɓara Lilly tace "please Mamma allow me to rest, am still feeling pain in my chest"
"Ohh God, ko a kira Doctor Kaseem ne?"
"No am ok, i just need rest"
"Ok rest my dear, amma zuwa magariba insha Allah zamuje Asibiti, bana son mahaifinki yaji ciwon nan ya tashi, ban kaiki Asibiti ba yaita sababi"
Lilly ba ta sake Magana ba se gyara kwanciyarta da tai.
(Cikakken sunan Lilly Fatima, itace 'yar Auta a gidan su, su huɗu ne a gidansu, babanta Babban General ne na Sojoji, yana matuƙar ji da ita, kasancewar sunan mahaifiyarsa ya samata, shine suke ce mata little daga baya kuma suka koma cewa Lilly, hakan yasa ba kowa yasan sunanta na gaskiya ba).
Da magariba ba yadda maman Lilly ba tai da ita ba akan suje Asibiti amma taƙi, se ƙyaleta tai.
Sadik kam Kamar yadda ya saba duk dare, hotonta yake ta zooming yana ƙare mata kallo, kamar a lokacin ya fara ganinta, yana jin wani abu yana cigaba da shigarsa a kanta.
Ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ya kalli agogon wayarsa, ƙarfe ɗaya da rabi na dare, a hankali yai juyi tare da ƙanƙame wayar a jikinsa yana sauke numfashi.
"Allah ka amince min na mallaki Farhan"
Wani irin gumi ne yake tsatsafowa a goshinsa, a hankali ya ajiye wayar ya miƙe ya fito falon su.
Faruk ya tarar yana kallon wani Nigerian Film, kusancin jarumin da jarumar Film É—in na nuna wani abu na shirin faruwa.
Tsakin da Sadik yai ne yasa Faruk É—agowa ya kalli in da Sadik yake yace "kai kuma kai da waye?"
"Wannan shirmen da kake kallo mana Sadik ya bashi amsa yana buÉ—e fridge, ya É—akko ruwa me sanyi.
"Ai seka tsaya ka gani kan ka yanke hukunci, tunda ba wani abun a kai ba"
Ɗan taɓe baki Sadik yai yace "Ni wannan ɗin ma shirme ne, mutum na zaman zamansa ya kallowa kansa damuwa"
Dariya Faruk yai yace "Allah nawan?"
Sadik ya zauna akan kujera one seater ya ɗora ƙafarsa, a kan ƙaramin teburin dake falon ya kalli Faruk yace "bro, am telling you the truth, wallahi bana iya jure kallon wannan fina finan, a simple Romance can put me in trouble, you understand what I mean"
Faruk yai murmushi yace "So, seka dena kallon Film gaba É—aya ka koma cartoon"
"Ba zaka gane bane" Sadik ya faÉ—a yana shan ruwan da ya zuba a kofi.
"Ya zakace ba zan gane ba, i went through same situation as you, kawai Lokaci ne da jiki ke girma, da alamu na zama cikakken mutum shine kawai, amma nan da wani lokaci zaka koma normal"
Ɗan guntun tsaki Sadik yai yace "ni bana tunanin wannan yanayi ne da zan iya fita daga gareshi lokaci guda, duk kallace kallacen fina finai da nayi a baya, bana jin komai se haɗuwata da Wata yarinya a makarantar mu, i really fall for her, gaba ɗaya na kasa gane kaina, nayi ƙoƙarin nusar da Mother ni Aure nake so, amma se ta shareni koma taimin faɗa"
"Hmm ai dole tai maka faɗa, Sadik dudu guda nawa kake ne? Shekarun ka nawa a duniya da har zaka fara zancen Aure? Ni ban yi wannan zancen ba se kai, kasan Aƙidar Gidan nan ko? Boko first before anything"
"Aƙidar banza, ai ba dokar Allah bace, ni wallahi idan aka cigaba da tafiya a haka, ba zan iya wani karatu ba" yai maganar yana tsuke fuska.
Faruk ya tashi daga in da yake zaune, ya dawo kusa da Sadik ya zauna ya dafa kafaɗarsa yace "Sadik, ita yarinyar da kace sanadinta ne ka shiga wannan halin, ba wani abu bane face RUƊIN ƘURUCIYA, wanda yake faruwa a lokacin tashen balaga, wani abune na ɗan lokaci, kuma abun da kake ji kowa ma yaji, amma dannewa ake, kar ka sake wannan feelings ɗin yasa ka rusa Rayuwar ka, kayi ƙanƙanta dafara ɗaukar stress na marital life, just forget about her, focus on your life, da zarar ka samu abunda kake so zaka dena jin wannan son, dan haka ka kula"
Shiru Sadik yai yana sauraron Faruk, a hankali ya sauke ajiyar zuciya, ya ajiye kofin hannunsa, ya miƙe tafi bedroom ɗinsa ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Safa da marwa ya shigayi, yana son tabattar da dagaske son da yakewa Farhan RUƊIN ƘURUCIYA ne? Ya rasa dalilin da yasa kowa yake ce masa ai Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai.
Sedai abunda yake ji akan Farhan ya wuce a kirashi RUƊIN ƘURUCIYA kawai, shikaɗai yasan meyake ji a kanta.
Da wannan tunanin ya kwanta, har bacci ya É—auke shi.
Kwana biyu Lilly ba ta Zuwa school, se ana uku taje, lokacin ta warware sosai, aikuwa tana zuwa su Haseena suka dinga ihu suna rungumeta.
Ture su Lilly tai tace "dalla can marasa mutunci, ba wadda taje dubani a cikin ku"
Yasmin tace "Wallahi yau muke cewa zamuje dubaki, jiya mutumin ki yazo yana tambayar ko kin zo?"
Lilly tace "waye mutumina?"
"Sir Nazir mana" Haseena ta bata amsa.
"Uwar mutumina, ai gayen nan Allah ya sakamin kneel down fa ya sani, na dinga kuka ina roƙonsa amma yaƙi saurarata, seda ya ga dama yace in tafi aji, kawai na faɗi a hanya"
"Dama ya za'ai ya saurareki, ai shi wannan ciwon naki gaba ta kaishi, ya samu abunda yake so"
Da mamaki ta kallesu tace "kamar yaya?"
Yasmin tace "ai ni zan labarta miki, da aka kai ki Clinic É—in nan, kin kasa numfashi bakinsa yasa a naki yana hura miki iska"
"What, dalla bana son ƙarya"