Sashe 33
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Daf da magariba amma har a lokacin zuwa ake, har 'yan ajin su Farhan ma sun halarci taron bikin.
Sedai gaba ɗaya Haseena ta kasa sukuni, saboda kyan da Sadik yai a idonta, babban abunda yasa ta tsani Farhan bakomai bane illa kishi, gashi Sadik ɗin ba shi da fuskar da za tai masa shishshsigi, amma harga Allah yana matuƙar burgeta.
Yau ta ƙara tabattar da Sadik ƙyakyawa ne na gaske, dan ba ƙaramin cika ido da kwarjini yai a cikin manyan kaya ba, duk da ƙarancin shekarunsa, Allah yai masa ƙirar manya, dogo ne ga shi da jiki, wannan jikin ne ke ɓoye ainihin ƙuruciyar sa.
Yauma Inna ta ga taɓara kala kala, da rashin ta ido, wanda suka ƙara tsaye mata a zuciya.
Se wajen ƙarfe goma na dare, Sannan aka watse daga gurin bikin.
Farhan da ta koma gida, tayi zaton Umma za tai mata faÉ—an ta daÉ—e, amma ga mamakin ta ba abunda Umman tace mata.
Nan ta baje uban kayan da Sadik ya bata, ta bawa Umma, amma Umman taƙi ko kallon in da kayan yake, ƙarshe se bari tai da Abba ya dawo, ta kai masa ya sa albarka, yace suje su raba ita da ƙanen ta.
Ta rasa yadda za tai da ranta da wannan halin ko in kula da mahaifiyarta ke mata, kawai saboda tana 'yar fari, ita tafi danganta wannan abun da kawai ba ta santa ne, dan wannan abun ya wuce kawaici.
Tun da suka taho da Sadik, ta kasa gane me ke damunta, gaba É—aya jinta take wani iri kamar ba ta da lafiya, ta rasa takaimeme meke damunta, ga Wani yanayi da ta tsinci kanta, tun shigarta motar Sadik duk da ba yau ta fara hawa ba, amma ta kasa tantance yanayin da ta shiga.
Ga shi ƙasan cikinta yana mata ciwo kaɗan kaɗan, amma babu wanda ta gayawa, to wa ma zata gayawa? Ummanta da ba ta son taje in da take? Ko kuma ƙannenta maza?.
Jin ciwon be takura mata bane, yasa ta cigaba da sabgogin ta.
Tun bayan sallar isha'i da tai, ta samu guri ta zauna ta shiga tunani daban daban, a baya ko bisa kuskure Sadik ya taɓa jikinta, se ta nuna masa taji haushi, amma haka nan yau ba ta ji haushin hakan ba, sema kasa manta hannun sa da tayi, da irin ƙamshin turarensa.
Nan ta lalace a gurin da Tunanin Sadik,ba ta taɓa sanin haka akeji a soyaya ba, Sadik ya koya mata son sa.
Ji tai tana son yi masa bangajiya, amma da wace wayar?
Nan ta shiga tunani, can wata dabar ta faÉ—o mata, ta tashi ta tafi É—akin Umma, ta tarar da Umman na shirin kwanciya.
Cikin sanyin jiki tace "Umma, dan Allah aron waya nake so ki bani, zan duba wani abu a internet"
Nuni tai mata da in da wayar take, ta juya ta kwanta.
Cikin farinciki taje ta É—au wayar Umman, ta koma É—akinta zuciyarta cike da farinciki.
A gajiye sosai Sadik ya koma gida, sallar isha'i kawai yai, ya haye gadon sa, dan ya gaji sosai.
Cikin sa'a bacci yai awon gaba da shi.
Cikin baccin yaji wayarsa na ringing, a fusace ya É—ago wayar, amma yaga Farhan ke kiransa da layin.
Murmushi yai, ya katse kiran ya kirata.
"Assalamu alaikum" ta faÉ—a cikin sassanyar muryarta.
Shiru yai yaƙi amsawa, ta sake maimaita sallamar amma yai shiru.
"Hello ba ka ji na?"
Murmushi yai cikin muryar bacci yace "Ina jinki fa"
Dariya tayi tace "ji shi kamar wani Baby"
"Ummmm ai Babyn ne, dan na tashi daga Babyn Mother Babyn Princess ne"
Wata kunya ce ta lulluɓe ta, har mamakin Sadik take idan yana wani abun, ta rasa ina yake koyo manyance, da iya soyayya.
"Ya naji kinyi shiru? Ina fatan ba ai miki faÉ—an kin daÉ—e ba?"
Tai ajiyar zuciya tace "ba aimin ba"
"To Alhamdilillah, a ina kika samu waya?"
"Wayar Umma ce, nace mata zanyi abu a internet ne"
Wani murmushi Sadik yai wanda shikaÉ—ai yasan ma'anarsa.
"Ya naji kana dariya?"
"Dole inyi dariya mana, 'yar budurwata ta faller sona sosai, tunda zata iya ƙarya ta karɓi waya dan taji muryata"
"Nice nake ƙarya ko?"
"No, ba haka nake nufi ba, sorry bugun zuciyata, the only Moon in the sky, My little angel, my diamond Baby"
Dariya tayi tace "to ya isa haka, wai a ina kake koyo wannan abubuwan?"
Gyara kwanciyarsa yai yace "to ta ya bazan koya ba? A gabana Yayana ke ta sa soyayyar, lokacin muna tsohon gidanmu a ɗaki ɗaya muke kwana, a gabana yake soyayya, ga fina finai da nake kallo, ƙarewa ma Daddy da Mother ba sa ɓoye yadda suke son junansu ko a gabanmu ne, to meyasa ba zan iya soyayya ba"
Zare ido Farhan tai tace "kai! Mother kuma?"
Sadik yace "eh mana Mother, a gabanmu suke cewa suna son juna, basa ɓoye soyayyar su duk da sun tsufa maimakon su barmana" ya ƙarasa Maganar yana murmushi.
Shiru Farhan tai, ta ɗan tafi tunani anya tunda take ta taɓa ganin wani abu makamancin soyayya a tsakanin iyayenta? Iya abunda take gani shine law and order, biyayya da hidima amma ba ta ganin wani abu makamancin na so a tsakanin su.
"Kin tasheni daga bacci, kin ƙimin hira kinyi shiru"
Dawowa tai daga tunanin tace "au ka fara bacci ne?"
"Eh, na fara bacci wayarki ta shigo"
"To ba yanzu zaka koma baccin ba, cigaba da yi min hira"
Yanzu Sadik ke ƙara tabattar da Farhan ta iya hira, samun wanda za tai hirar ne babu.
A shagwaɓe yace "ni bacci nakeji"
"Ni kuma bana jin baccin"
"Ke gobe in Allah Ya kaimu za'a ɗaura Aure, da wuri zan tashi ki ƙyaleni"
"Aushhh" ta faÉ—a a raunane.
Da sauri yace "lafiya kuwa?"
"Cikina ne yake ciwo"
Sadik yace "ya salam, ko kinci wani abun ne?"
"A'a seda safe kawai"
Cikin damuwa yace "wait, ki sha magani karki kwanta kina jin ciwo kinji Babyna"
Da hmmm kawai ta amsa masa.
Ta katse kiran, cikin sanÉ—a ta je É—akin Umma, ta tarar tuni Umman tayi bacci ta ajiye mata wayarta ta fito.
Haka cikinta ya cigaba da yi mata ciwo, wanda ta rasa ina ne ma yake ciwon.
Sadik yai rigingine, a hankali ya furta ya rabbil izzati ka tsareni faÉ—awa halaka, Allah kasa iyayenmu su yadda su Auran yarinyar nan, ina sonta Sosai, Allah ka aurar dani da wuri.
Ya ƙarasa yana lumshe idon sa.
Inna kuwa bacci ɓarawo ne ya ɗauke ta, ƙarshe cikin dare ta tashi tai Alwala tai salla, ta dinga addu'oi tana nemawa zuriyarta da al'ummar Musulmi shiriya, amma ta girgiza da yanayin rashin tarbiyyar da ta gani a tsakanin yaran ƙarshen zamani, masu ji da RUƊIN ƘURUCIYA!
Sadik ya kwana da begen Masoyiyyarsa, cike da mafarkai masu tabattar da lafiya da nuna alamun girma ga É—an Autan na Alhaji Abdullahi.
Farhan kuwa da ƙyar tai bacci, gefe guda ciki na ciwo ga kuma tunanin soyayya.
Bayan sallar Asuba, Sadik ya koma bacci, kaÉ—e kaÉ—e da bushe bushen da suka cika gidan ne, suka sa ya farka.
Windown ɗakin sa ya buɗe ya leƙa, yaga manyan motoci anyi parking ɗinsu, ga maroƙa da manyan mutane sun cika harabar gidan, alamar ana shirin tafiya gurin ɗaurin Aure, kuma masu bushe bushen ya tabattar masa da Hakimi ya ƙara so.
Cikin hanzari ya shiga ya watsa ruwa ya fara nasa shirin shima, dan tuni hayaniya ta cika BQ É—in, abokan Dr. Sun cika part É—in suna shiryawa.
Rufe É—akinsa Sadik yai, ya cigaba da shirinsa cikin nutsuwa.
A babban falon gidan Hakimi ya zauna, ya sha kayan sarauta se zuwa ake ana kwasar gaisuwa, ana ta gaggaisawa cikin girmamawa kasancewar sa mutum me barkwanci.
Nana kam ta dinga murna, fa zuwan Hakimi taje ta maƙalƙale shi, ta zauna a inda yake, tana nuna yadda tai kewarsa.
Ƙarfe goma shaɗaya aka kammala haɗuwa, aka nufi babban masallacin unguwarsu Amarya Jidda in da za'a ɗaura Auren.
Nan ma Mother ta sha ado, tai kyau kamar itace Amarya se zuba ƙamshi take, ta sha shadda hannunta da wuyanta duk gwal, da ka ganta ka ga matar manya.
Ƙarfe ɗaya aka dawo daga ɗaurin Aure, aka dinga shigowa ana Allah ya Sanya Alkhairi ana ɗaukar hotuna.
Hakimi ne ya fara shiga falon, se Alhaji Abdullahi da 'ya'yansa, abun da yafi ƙayatarwa shine, duk sun ɗora farar Alkyabba me aikin blue, akan fararen shaddojin su, ga naɗi da akayi musu, sunyi kyau matuƙa gaya.
Inna ta kalle su tai murmushi tace "Allah ya shirya mana zuri'a" dan ganin su cikin wannan kamalar ba ƙaramin burgeta yai ba.
Nan aka zauna Hakimi ya dinga addu'oi, tare da Nasiha ga angon da kuma iyayensa, tare da yi musu gargaÉ—i akan shiga sabgar É—an da matarsa idan ba aka abunda ya zama dole ba.
Daga ƙarshe yace "Nagode Allah, sannan nai farinciki da Allah ya aramin rai na ga Auran jikana na fari, idan ina da rabo Allah ya nunan na sauran, na Faruku da na wannan abokin nawa, mara son mutane"
Yai maganar yana kallon Sadik, ba kunya Sadik ya gyara Alkyabbarsa yace "zama ka gani insha Allah, dan nawa za'a fara wata shekarar sannan nan wannan" yai maganar yana nuna Faruk.
Hakimi yai murmushi yace "Allah yasa"
Abba kuwa daƙuwa yaiwa Sadik yace "Ƙaniyar ka, mara kunya wayake ta taka, kaida ko sakandiren baka gama ba, next year by now insha Allah kana Amurka ko jamus kana karatu"
ÆŠan tura baki Sadik yayi, yayin da Inna take bin su da ido tana nazartar, duk wani motsi na Sadik É—in.
Da Yamma Hakimi ya ja tawagar sa ya koma, yayin da Inna tace ba zata bisu ba, za ta koma daga baya akwai abunda za tayi kan ta taho, ƙila se bayan sati da bikin.
Nana tace ita kuma za ta bi Hakimi ta koma ƙauye, Inna tace ba in da zata yadda suka zo tare za su koma.
Nana ba taji daÉ—in hakan ba, dan harga Allah ta gaji da zaman Gidan nan dan ba ta ga zaman me zasu yi ba bayan an gama biki.
Bayan sallar isha'i, 'yan uwan Amarya suka kawota gidan su ango gaida surikai, kan a kaita nata gidan.