← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 48

Sashe 5

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna tace "kin wuce kin nemi riga kin saka, ko sena taso na iskoki a gurin nan, gaɓuwa kawai ba kya ganin yadda ƙirjinki ya tasa? Amma kike yawo a haka? Karki adana su ki bari su fito a wulaƙance, naga alamar idan banyi dagaske ba, haka zakiyi budurci ba kintsi, 'yar butar uwa da kai kamar gwai gwai"

Ummi ta faÉ—a É—aki, tana kumbura baki, dan bata son wannan faÉ—ace faÉ—acen na Inna, Gashi idan ta tashi yi bata rufe komai, haka za tai ta sakin bayani, ko a gaban waye kuwa haka za tai ta sakin zance da sunan faÉ—a.

"Sarkin faÉ—a, ke da waye kuma da tsakar ranar nan kike faÉ—a haka?"

Cewar dattijon da yake shigowa, jikinsa sanye da Alkyabba.

"Dawa zanyi faɗa banda wannan yarinyar, duk gidan nan wake sani magana banda Nana, yarinya kamar ba'ace mata bari, taɓara da iya shege sinƙi sinƙi a cikinta"

Dattijon yai murmushi Yace "haba ke kuwa, takwarar taki guda, Ki dinga haƙuri da ita, yarinyace har yanzu ke kike ganin girmanta, amma yarinya ce ƙarama"

'ko da yarinta, harda iskancinta wani lokacin, bata taɓa jin daɗi idan bata sani magana ba"

Yai murmushi Yace  "to yanzu dai ba wannan ba, zuwa wani satin insha Allah, gidan Abdullahi  zasu kawo lefen Usman ɗin, ina fatan kina nan kina shiri?"

Inna tace "eh ina shiri, naji yace bikin bada tsawo za'a saka ba, ina ga idan suka kawo Kayan, zan bisu se kuma anyi biki, dan bana son yawan tafiyar motar nan"

But Nana dta fito daga ɗaki da ɗaurin ƙirji tace "Alhaji wai waye zeyi aure ne? Wai su wannan ɗin nan na birni?, wanda basa dariya sosai masu tara gashin nan kamar ƙabilu? 'ya'yan kawun nan?".

Dattijon Ya buÉ—e baki Yace "yayyen naki ne baki san sunansu ba? Se masu tara gashi?"

"Ni a ina zan san sunansu, bayan ba kula mutane suke ba, kuma ma ba zuwa gidan nan suke ba"

Alhaji ya jinjina kai Yace  "ikon Allah, lallai wannan abu bemin daɗi ba, Dole a tafi da Nana, kuyi kwanakin Tare, dan ta ga 'yan uwanta sosai"

Ummi tai tsalle tana faÉ—in "yee, zani birni inje asha bikin 'yan gayu dani"

Inna tai tsaki tace "mara hankali, ai idan kikaje ma kallon kwantacciya zasu yi miki, musamman matar Abdullahi, me wa mutane kallon banza"

Alhaji Yace "ai haka nan za'aje da Ita, rashin zumuncin yayi yawa, ace ba tama san sunayen su ba, shikenan ace yaran nan ko garin nan basa zuwa, balle su shaƙu da 'yar uwassu?"

Inna tace  "to ya zamuyi tunda uwarsu bata so? Nace a kai maka furar turakarka ne idan an dama?".

"Eh, a kawomin turaka, ina so idan na sha na ɗan huta, zanyi baƙi da yamma"

Inna tace "to shikenan, Allah ya baka yawan rai, zan kawo insha Allah"

Ya nufi hanyar ɗakinsa, Inna ta tashi, ta wanke hannunta, ta shiga ɗaki, ta tarar da Nana da ɗaurin ƙirji tana shirin Dutse"

"Nana kinyi salla kuwa?"

"Inna ai da sauran lokaci fa"

"To kuma kafin kiyi wanka, ba lokaci yayi ba?"

Nana ta zumɓura baki tace  "wai Inna ba nayi wankan nan da safe ba? Shikenan ni kullum cikin wanka kamar wata tarwaɗa?".

Inna tace "kyaci ubanki, lokaci na nan zuwa da za kiyi medalili, wanka ba wataran da asubar fari, koman sanyi haka zakiyi shi"

"Wankan?" Nana ta tambaya cike da mamaki.

Inna tace  "ƙwarai kuwa wankan da ki ke gudu, kuma dole ki koyi wanka da tsafta tun Yanzu kina gida, gaba nake jiye miki, kuma Yanzu ki ke girma kina kan tashen balaga, warin jikinki daban ze dinga fita, kuma duk wanda ki ka bari yaji wari a jikinki kin faɗo, ze dena ganin mutuncin ki, kuma dan ubanki na sake ganinki da ɗaurin ƙirji Sena makeki, idan baki alkinta abubuwan nan ba haka zasu fito ba tsari, kiyi 'yan matanci amma nono a zube, kizo kiyi aure ba zasu dinga birge miji ba"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, waike Innarmu kiyi ta faÉ—an magana ba kyajin kunya"

Inna tace  "Naƙi inji kunyar, idan ban gayamiki ba wani a waje zan jira ya gaya miki?, kin tashi kin tafi wankan ko sena zo inda kike? Na watsar da ke"

Nana ta tashi tana bubbuga ƙafa, da takaicin yadda Inna ke sata wanka ba gaura ba Dalili, ta ɗebi ruwa ta tafi banɗaki.

Bayan shigar Nana banÉ—aki, Inna tace "A kula idan za'ayi wanka, a wanke hammata da kyau, wuya da duk wani lingu....

'innalillahi Inna na haddace wallahi, na haddace ko karatune wannan na iya ke kullum sekin nanata min yadda ake wanka wai?"

'rufemin baki, gara in nanata miki ai, dan banƙi in zuba ruwa in wankeki da kaina ba,wani warin jikin yana faruwa ne daga rashin iya wanka tun a ƙuruciya, in kin gama wankan ga ruwan alumun nan da miski ki shafe jikinki dashi"

Nana ta yiwa Inna banza, dan wannan karatuttukan na Inna basa ƙarewa.

Inna ta damawa Hakimi furarsa, ta shiga kai masa, ta tarar dashi yana dariya, ta kalleshi tace  "lafiya naga kana dariya?"

Yai murmushi yace  "dariya nake miki keda jikar taki, kina takura yarinyar nan da yawa fa"

Inna tace  "a'a ba takura bace, gara in gaya mata ai, duk da Allah be taɓa bani 'ya mace ba, amma ni ban yadda se an sawa yarinya rana, sannan a dinga gaya mata ƙabali da ba'adi ba, tun tasowar yarinya ya kamata a dinga koya mata yadda zata kula da kanta, da yanayin Rayuwar Aure"

Hakimi yai murmushi yace "eh to hakane, amma ai Nana tayi ƙarama da yawa, da wannan karatuttukan naki"

"Taɓɗijan, kai kake ganin tayi ƙanƙanta, ba tayi ƙanƙanta ba, ba dan karatun boko ba, ai da yanzu idan ba'ayi aurenta ba, ana nan ana shirin hakan, kuma karkayi mamaki suna tattaunawa a junansu, yaran zamani ka kallesu kawai, gara in horata da nawa karatun, da wanda za'a karanta mata a waje ta ɗauka"

Hakimi ya jinjina kai yace "hakane kam, naga zasu yi hutun makaranta, shiyasa nace ki tafi da Ita bikin nan, wallahi ina jin banƙin cikin rashin raɓata da jikokina basa yi"

"Ka dena damun kanka fa, ita uwar yaran nata halin kenan, yaranta baza suzo ƙauye ba, dan haka ka haƙura ka bar mata yaranta, shi shine ɗanmu kuma yans zuwa inda muke, meye na damuwa dan yaransa basa zuwa?, Baga Ummi nan Allah ya baka ba"

Ya ɗanyi shiru Yace  "na tabatta da baban Ummi na raye ba yadda ze hana yaransa zuwa inda muke, kin sanni da ƙawa zucin yara, Allah be bani su da yawa ba, duk ya karɓe abunsa, ina ƙaunar yaran nan, irin son da nakewa mahaifinsu, haka nake sansu"

Inna tace "ni dai nace kayi haƙuri, ka maida komai ba komai ba, Ummin nan kawai in Allah ya bamu yawan rai, seka ga ta haysyyafa, ta cika mana gida da jikoki"

Hakimi ya jinjina kai Yace "wai, idan ba wani ikon Allah ba, ina ni ina ganin 'ya'yan Ummi, 'ya'yan jika fa?"

"Eh mana 'ya'yan jikan, ai abun na Allah ne, kai dai Allah ya baka tsawon kwana me amfani Saraki"

Yai murnushi, yana jin daÉ—in yadda matar tasa take masa addu'a, ko kuma yi masa kirari.

Inna na nan zaune tare da megari, seda ya kammala shan furarsa, ya kwanta sannan ta fito daga turakarsa, tana zuwa É—aki ta tarar da mutuniyar tata, tana cin Abincin rana.

"Yawwa ta Nana, gaki nan fes dake se ƙamshi kike, haka ake son mace a ganki kullum cikin gyara, ga kayanki can na islamiyya an goge miki, idan kin gama seki shirya ki tafi Makaranta"

Nana tace 'to Hajiya Inna"

Shirye shirye suna ta nisa, na bikin Usman, Sadik ma yana ta nasa shirin, dan yana son ya gwangwaje da bikin nan, zasu yi shagali sosai shida friend's É—insa.
Yauma yaje school sedai har ya shiga aji be samu ganin abar ƙaunarsa ba, ana fitowa break ya tafi ajinsu Farhan, sedai ya tarar bata nan.

Cikin takunsa na isa ya shiga cikin ajin, ya kallesu Yace "ina Farhan?"

Lilly tace  "Ana fita break ta fita, bamu san inda ta tafi ba"

Be kuma cewa komai ba ya fita, yana tunanin ina ta shiga haka? Tun jiya be sake ganinta ba.

Ita kuwa bayan wani aji taje tai zamanta, dan karma su haÉ—u Sir Nazir yai mata faÉ—a, koya kira babanta, sedai sam itama zuciyarta a takure take, tana son ganin Sadik É—in nata.

Sadik yana zaune yayi shiru, Meenal ce ta zauna a kusa da shi, Tare da ɗan dukan cinyarsa tace  "Babban yaro, what's wrong ne? Ka wani yi shiru"

Cikin damuwa ya ɗan lumshe idonsa ya buɗesu, sannan Yace  "Farhan na nema na rasa, naje har ajinsu bata nan, kuma ita bata zo nan ba"

"Shine ka zauna kai wannan shirun haka? Lallai yarinyar nan ta kama zuciyarka fiye da yadda kake tunani"

Yai murmushi Yace  "ke dai bari kawai, yarinyar ta musamman ce, komai nata abun burgewa ne, I can't do without her"

Meenal tace  "Ranar daka bar makarantar fa?"

"Zan bita har gida mana"

"Hmm Sadik manya, banda abun so dai, banga me ka gani a jikin wannan Farhan É—in ba, ita gata bata wani cika mace ba"

Sadik yai murnushi sannan Yace  "Ni idona sun gane min abunda naku idon baya iya gani, ku kuke ganinta ƙarama, amma ni nasan me nake gani"

Yai maganar yana lumshe idanunsa.

Meenal ta kalleshi tace   "Allah me iko, kaga ni dai dan Allah yi mana ordern Abinci, yunwa nake ji wallahi"

Sadik ya zaro wayarsa yana faÉ—in "bari inyi, kuma fa nima yunwar nan nakeji, amma banga zuciyata ba, ban sani ba itama taci ko bata ciba, ba zan iya ci ba"

"Can ta nannaÉ—e muku kai da ita, ni dai dan Allah yi mana"

Seda aka kunna jiniya, kowa ya koma aji, Sannan Farhan ta fito daga inda ta ɓuya zata koma aji, zuciyarta nata raya mata taje ajinsu Sadik ta ganshi, amma ta danne zuciyarta ta tafi ajinsu.
Chapter 5 · 0% Book details