Sashe 42
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yau kuma tunanin me kike yi?"
Firgigit ta dawo hayyacinta, ta kalli Sadik dake kusa da ita a zaune.
"Bakomai"
"Bakomai kamar yaya? Kin san lokacin da na shigo?" Girgiza masa kai tayi alamar a'a.
"Ke kin ma yi min laifi ko ki neme ni balle ki bani haƙuri ko?"
"Lefi kuma?" Ta faɗa a ɗan shagwaɓe kamar za tai kuka.
"Eh laifi mana, na yimin gaddama"
"Ba fa haka bane, ni tsoro nake ji a gida kar ai min faÉ—a"
"Zam bi hanyar duk da ta dace, ba wanda ze san anyi, kawai za'a É—an yanka cake ne aci a sha, mu tayaki murna shikenan fa"
Sunkuyar da kai tai ba tace komai ba.
"Ko dai haryanzu ba kya so É—in"
Ta girgiza masa kai alamar a'a.
"Yarinya kin taimaki kanki, da faÉ—a za muyi"
ÆŠan murmushin gefen baki tai, dan ita yanzu halin da take ciki ne yafi damunta, na wannan ciwace ciwacen da take fama"
Idanunta ne suka kuma sauka a hannun Sadik, a ido kawai fatarsa abun sha'awa ga wannan gargasar ta jikinsa da take burgeta.
A hankali ta É—auke idonta daga kallon hannun nasa ta É—aga kai ta kalleshi, karaf sukai ido huÉ—u yace "me kike kallo a hannuna?"
Mamaki ne ya kamata, dama yaga hannunsa take kallo.
"Ni ba hannunka nake kallo ba fa"
"Yanzu kuma ƙarya nake kenan?"
"Wai kai komai nayi lefi ne" tai maganar kamar ta rushe masa da kuka.
Cikin kwaikwayon muryarta yace "kawai ina son in dinga tsokanar ki ne"
Littafin gabanta ta ɗauka ta kwaɗa masa a hannu, ya cigaba dai mata dariya yace "naga hannun nan kamar wani abun kike kallo a jiki, bari in ciro miki shi sosai ki gani" ya kama botir ɗin gabar rigarasa ze fara ɓallewa.
Zaro ido tai ta ja da baya daga kusa da shi, tana kallonsa dariya yai yace "ke da shagwaɓar ki, da tsoron ki, duk ba sa ɓuya, tashi muje ki rakani shop"
"Ni ba zani ba banda lafiya"
"Ke kullum ba ki da lafiya ne? To sekin rakani"
"Ni bana son bi ta wajen SS3 É—in nan"
Yace "meyasa?"
A É—an marairaice tace "Kasan wani abu kuwa?" Sadik yace a'a sekin faÉ—a.
"Kasan wannan Salma É—in ta SS3?"
Yace "eh na santa"
"Ita ce wai tace wai tana so in zama ƙanwarta, idan aka fita break wai inje"
Take ta ga annurin fuskar Sadik ya É—auke, wani gumi ya tsatstsafo a goshinsa, cikin kaushin murya yace "meya haÉ—a ki da ita?"
"Ni ba abunda ya haÉ—ani da ita, kawai ranar na gansu a toilet ne, wai wata ba ta da lafiya, Nasreen wai cikinta ya faÉ—i, naji tace ina burgeta shine yau tai min Magana"
"Cikin waye ya faÉ—in?" Ya tambayeta yana tsareta da idanunsa.
"Wai cikin Nasreen É—in" ta faÉ—a cike da rashin wayo.
"I hope ba abunda sukai miki?"
Ta girgiza kai "ba suyi min Komai ba"
Be jirata ba ya tashi fuuu yai waje, hakan ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba.
Kai tsaye SS3 ya nufa, hakan yai daidai da fitar malami daga ajinsu.
Ba shakka, ba komai ya kutsa kai ya nufi gurin zaman Salma.
Kallo É—aya tai masa tace "lafiya ka zo ka tsaya min a ka haka kamar wani É—an sanda?"
Dukan benci yai da ƙarfin gaske, sannan ya nunata da yatsa yace "kashedi na zo nai miki, nasan kin san Farhan, to idan kuna rashin mutuncin ku da ɓata yaran mutane, ku kiyayi abunda yake nawa, Farhan is my Asset, don't Cross your limit, kince kina son ta zama ƙanwarki, to ta gayamin, wallahi da wasan wasa kika kuskura wani abu ya sameta, wallahi tallahi I will show you what am capable of doing na gaya miki"
Miƙewa tsaye tayi tace "kai ɗan saurara, kar ka gayan maganar banza, idan kana wa saura hura hanci da tunƙaho karka kuskura kaimin, ni ba sa'ar yinka bace, shekara nawa na baka kamarni zaka zo kace za kaiwa warning?"
Nasreen cikin sauri tace "ke Salma, namiji ne fa wallahi akan 'yar nan ze iya yi miki illa, akan kuÉ—in vanacula É—inta ranar ba kiga tijarar da yai min ba"
Mubarak babba ne yace "calm down Sadik, dan Allah kayi haƙuri ka manta da ita kawai, insha Allah ba abunds ze samu beb ɗinka"
"Na rantse da Allah, da wasa ita da gangs ɗin ta sukaiwa Farhan wani abu senai musu illa wallahi, Ita ɗin tawace nikaɗai, nasan suwaye ku nasan abunda kuke aikatawa, kar ku kuskura shashancin ku yazo kan yarinyar nan, ba ruwana da 'yar kowa a makarantar nan, nima ban yadda a taɓa abunda yake nawa ba"
Da ƙyar Mubarak ya fidda Sadik daga ajin nan, sannan ya dawo ya kalli Salma yace "ke baki da hankali, wannan yaron kamar ta masa Asiri haka yake wannan zafin kan akanta kamar matarsa, babansa yana da ɗaurin gindi a ƙasar nan, zaki iya jawa kanki masifa"
"To shine se ya zo kaina yana min hauka?"
"Kibi komai a sannu, bake kaÉ—ai ba ni kaina Yarinyar nan tarko zan mata, dan wallahi ta burgeni, shi ba ya tsaya sokonci ba, ze ga tsiya sena watsa rayuwar yarinyar uban kowa ya huta"
Tace "Aikuwa sedai ya mutu, dan nima zan cigaba da bibiyarta.
Ita kam Farhan sam bata san ma wace wainar aka toya ba tana fama da kanta.
Ba tsammani sega Sir Nazir ya shigo ajinsu, kuma alhalin a ranar kwata kwata ba su da lesson É—in sa.
Gashi kowa yana tsoro balle suyi Magana, dan da wani malamin ne bore za suyi suce su ba zasu saurari lesson É—in ba.
Lilly tai ɗaiɗai ta cire jacket ɗin ta, ta ɗora ƙafafuwan ta akan benci, tana cin shawarma, hatta ɗan ƙaramin hijjabin jikinta ta naɗe shi baya, tana ciye ciyenta.
Yana shigowa ta sauke ƙafafuwan ta tana raraba ido, yayin da cikinta ya dinga wata uwar ƙara kamar ya ɓaci.
Ya shigo hannunsa É—auke da litattatafai, ya juya ya fara rubutu akan board, ita kuma tai maza ta cigaba da cin shawarmar ta, yana juyowa sukai ido huÉ—u.
Bece mata komai ba, ya cigaba da abunda yake, É—aya bayan É—aya ya dinga raba musu litattafan su, da yazo kan Farhan har seat É—inta yaje ya ajiye mata, ya kalleta yace "Congratulations, you got the highest score in my Assignment, And your note and digrams are well drawn And label, clap for her please"
Raf raf raf. Suka tafa mata.
Ya kalleta yace "yadda kike brilliant É—in nan Allah ya shirye ki, yasa ki dena biyewa wancan É—an iskan yaron kuna lalacewa"
Dumm haka ƙirjinta yai mata, dan maganar ta daketa, ta rasa meyasa yake son dizgata haka a gaban 'yan ajinsu.
Shi kam ko a jikinsa kamar beyi Komai ba.
"Fatima Hakeem, stand up and explain the assignment i gave you"
Gaban Lilly ya faɗi, ta miƙe tsaye tana zazzare idanu, dan ita ta manta sam akan me ma ya bada Assignment ɗin.
Ta kai mintuna uku ba tare da tace komai ba.
Cikin tsawa yace "Am talking to you my friend"
Ba ta san lokacin da tace "Ni i have no idea on it" tai maganar tana hararsa ta gefen ido.
"Wow you have no idea on it, na bada Assignment ba kiyi ba, ba ki submitting littafin ba, nace ki zo kin ƙi zuwa, na shigo class kin cire riga, kina ciye ciye, bagidajiyar ina ce ke?"
Shiru tai ta sunkuyar da kai.
"Oya bring out your notebook let me check"
Tana zumɓura baki ta ɗakko littafin ta miƙa masa.
Sannu a hankali ya dinga buÉ—ewa yana dubawa, ba uwar da takeyi a littafin ba ta note ba ta Assignment.
Ya ajiye littafin ya kalleta yace "Follow me to my Office, daƙiƙiyar banza da ta wofi, ba abunda kika iya, sedai ku dinga burga kuna hura hanci iyayenku n kashe maƙudan kuɗi, ana kawoku a manyan motoci amma kanku bakomai, hopeless girl"
Ƙunƙuni ta shiga yi, tana ƙoƙarin ɗaukar jacket ɗin ta, amma yai mata wata razananniyar tsawa, ba shiri tai waje da gudu.
Class rep yace "taɓ she kashin wata ze bushe yau"
Yasmin tace "Wallahi kuwa dan babu alamar imani a idonsa"
Yana fita Sadik ya shigo ajin su Farhan, tai mamakin sake ganinsa, yai mata alamar ta biyo shi.
Ba musu ta tashi ta bishi, kan barandar ajin su Farhan suka tsaya, ya kalleta yace "Farhan"
Ta amsa da "Na'am"
"Ba ke babu wannan 'yan SS3 É—in, duk wadda ta kuma samunki da zancen wai ki zama sister É—in ta ko makamancin haka, ki sanar dani Please"
Farhan tace "to ni dama ba saninsu nai ba, wai amma meyasa kace haka?"
"Babu wani abun kirki da ke tattare da su, galibinsu 'yan lesbian ne"
"Meye lesbian?" Ta tambaye shi tana kallonsa.
Lallai Farhan Yarinya ce, ba ta san ma'anar kalmar lesbian ba.
"No karki damu, ba ta da wata ma'ana kawai dai ki kiyaye kinji Babyna, ke tawace nika É—ai Please Farhan watch your self in this school, ni I thinks you are quiting this school as soon as possible, da na samu admission, insha Allah zamuyi Aure mu tafi tare, ba zan iya barin ki a makarantar nan ba"
Ajiyar zuciya ta sauke tana É—an kallonsa.
"Anjima da yamma zanje in duba hall ɗin da za'ai birthday ɗin nan, ko kina da wani zaɓi ko ra'ayi?"
Ta girgiza kai alamar a'a.
"Ni bana son wannan girgiza kan, talk to me"
"I have no choice, duk abunda kai shikenan"
"Ok to shikenan, I love you Baby"
Murmushi tai tana jin yadda zuciyar ta ta karɓi kalmar da ya faɗa ɗin, ta juya ta koma Class.
Nana kam da taje makaranta kasa haɗa ido tai da su Alawiyya, saboda yadda aka dizgata a gabansu, suka dinga yar mata da ƙananun maganganu, sedai duk iya faɗan Nana ba ta kulasu ba ta share su, ta cigaba da sabgarta.
Inna tana ankare da ita harta dawo daga Makaranta, ba ta sakin jiki ta kula Inna.
Har ɗaki Inna taje ta tarar da ita, ta ƙare mata kallo sannan tace "Nana gaba kike dani dan na hanaki bin ƙawaye ko?"