← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 48

Sashe 36

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya cigaba da kallo, daga episode É—in da ya tsaya a baya, Film É—in yana cigaba da nuni da tsantsar soyaya me tsuma zuciya, sedai ba ta sauya zani ba, akwai adult content a cikin Film É—in, kusa kaso arba'in É—ari na film É—in in da yafi karkata kenan.

Rikicin film ɗin na ƙayatar da shi, rikicin masarauta da na Soyayya.

Amma maimakon hakan ya É—ebe masa kewa daga damuwarsa, sema sake faÉ—awa wata damuwar da yayi.

Kamar wanda aka mintsuna, haka ya kashe socket É—in da system É—in ke jone, ya rufe System É—in ya ja wani uban tsaki, ya kife akan gadonsa yana sauke numfashi sama sama.

Haka yai ta juyi, tare da jera tsaki ba adadi, kan bacci yayi awon gaba da shi.

Da sassafe Inna ta fito falo, ta tarar da Mother ta fito ta na bada umarni ga masu aikinta, akan abunda za a girka.

Mother ta kalli Inna tace "Ina kwana"

Inna tace "lafiya ƙalau, nace Bawan Allah  ya tashi ne?"

"A'a be tashi ba" Mother ta bata amsa.

"Ta so min shi" Inna ta faÉ—a ta na zama.

Mother tace "ba ya son a tashe shi idan yana bacci, ya hana tashin sa idan ba shine ya tashi ba"

Inna tace "umarni na ne, a tasomin shi"

Mother ta juya tana É—an hura hanci, dan takurar Inna tayi yawa.

Kusan 10minutes se ga Mother ta fito, ita da Alhaji Abdullahi.

Sedai Inna ba ta falon, Alhaji Abdullahi yace "bari in duba É—akin su"

Ya nufi É—akin Inna, yana zuwa ya tarar da ita a gefen katifa a zaune.

Ya rusina yace "barka da safiya"

Inna tace "Yawwa, ka tashi lafiya?"

"Alhamdilillah, amma yana ga Kamar kin tattare komai?"

Inna tace "Ehh, dama nace ai maka magana ne da azahar kasa a maida mu gida, zaman ya isa haka na gama abun da ya zaunar da ni"

Alhaji Abdullahi yace "Amma Inna da wuri haka cikin gaggawa? Ko dai wani abun akai miki a gidan?"

"Babu É—aya, kawai ina son tafiya ne kawai"

"Amma Inna, ba ki gayan da wuri ba ba'a shirya muku komai na komawa ba"

"Ni ba wani abu da nake buƙata daga gurinka, abu ɗaya ne zan sake maimaitawa shine ka kula da tarbiyyar yaran ka, ka saka ido sosai ka gane meye damuwarsu sannan meye mafita ga damuwar ta su ba wai abunda kai kake so ba"

Shi dai Alhaji Abdullahi be gama fuskantar in da maganganun na Inna suka sa gaba ba, amma yace "Insha Allah za'ai yadda kika ce"

Tace "Yawwa da azahar zamu tafi Insha Allah"

Ya tashi ya fita jikinsa a sanyaye.

Yau sam Sadik yaƙi shiga cikin gidan, ko gurin Mother be je ba, saboda ransa a ɓace yake gaba ɗaya.

Yana zaune a falo yana video game, Faruk ya fito daga É—akin sa yace "kai Muje Abba yana neman mu"

Sadik ya kalleshi yace "ina fatan dai ba wani abun nai ba?"

Faruk yace "nima ban sani ba, kawai dai ya kirani a waya ne Yanzu".

Sadik yace "ina zuwa"

"Karfa ka ƙi zuwa ace ban gaya maka ba"

"Kayi gaba kawai, zan zo"

Faruk ya fice daga falon nsau.

Yana isa harabar Gidan yaga Alhaji Abdullahi ya yo wa Su Inna rakiya, an saka Akwatin su a Mota.

Da sauri ya ƙaraso yana faɗin "ya naga haka kuma?"

Abba yace "eh za su koma ne, shiyasa na kiraku kuzo kuyi sallama"

Cikin damuwa Faruk yace "tafiya ba sanarwa haka? Inna meyasa zaku tafi?"

"Gidanmu zamu koma, ai mun zaunu a gidan nan, kuma gashi za'a koma makaranta"

Faruk yace "Inna banji daÉ—i ba, ke ki tafi ki bar mana Nana a nan"

Inna tai murmushi tace "Inaa ai baze yuwu ba, tana katara ta"

Wani Mugun kallo Mother ta watsawa Faruk, wanda ya sashi mamakin me yai ake masa Wannan kallon.

Sadik ne ya ƙaraso in da suke ya gansu a tsaye, ya kalli Abba yace "Abba gani".

"Dama Inna ce za su koma, na kiraku kuzo kuyi musu sallama"

Sadik ji yai kamar yayi tsaki, amma ya maze ya kalli Inna yace "ku gaida gida"

Maimakon Inna ta amsa se kallon sa da take, Tun daga sama har ƙasa.

ÆŠan tsuke fuska yai yana basarwa, dan ya rasa dalilin da yasa Inna take masa irin wannan kallon a duk sanda suka haÉ—u.

Yana É—aga ido, sukai ido huÉ—u da Nana aikuwa ta galla masa harara.

Wani Mugun kallo yai mata, ya tsani Yarinyar nan kamar ya shaƙeta.

Kan su gama sallama Faruk yai sauri ya koma BQ, har sun shiga mota da sauri ya ƙaraso, ya sa hannu a Aljihunsa ya ɗakko kuɗi da wata leda, ya miƙawa Nana.

Nana ta kalli Inna sannan ta kalli Faruk.

Yace "karɓi mana"

Inna tace "ta karɓi ledar dai, amma banda kuɗin"

Faruk yace "Inna wai meyasa kike min hakane, ina ruwanki da mu ba zan bawa ƙanwata abu ba?"

Inna tai murmushi tace "Allah ya baka haƙuri me ƙanwa"

Nana ta sa hannu ta karɓa tace "Nagode".

Yace "yawwa Allah ya kai ku lafiya, ban san zaku tafi yau ba da na muku rakiya ai"

Nan suka cigaba da Sallama aka fara jan motar a hankali, Sadik yace "Allah raka taki gona" hakan ya sauka a kunnuwan Inna, amma tai kamar ba taji ba, aka ja motar suna É—ago musu hannu.

Mother ji tai kamar an yaye mata damuwar ta gaba ɗaya, dan tafiyar su Inna ze sa ta sake a gidan ta, dan zaman su ba ƙaramin takura ne a gareta ba.

Sedai ta ƙwafe Faruk a ranta, fan ba ta gane kan wannan rawar kan da yake ba.

Sadik be shiga gidan ba, ya nufi BQ Faruk ya bi bayansa, suna shiga Sadik ya koma kan game É—insa, Faruk ya zauna a É—aya daga kujerun falon Yace "Kai Allah sarki, É—an zaman su a gidan nan na saba da Yarinyar nan wallahi, zanyi missing jokes É—in ta, she's so Funny"

"She's crazy dai, yarinya kamar Mahaukaciya bazar bazar ba nustuwa, ga surutu kamar wata parrot, ni wallahi gara da suka tafi, dama ga tsohuwar nan kullum cikin samun ido take, tai ta min wani irin kallo wanda na kasa gane kansa"

Faruk yace "shut up Sadik, mahaifiyar babanmu ce kar ka faÉ—i abunda be dace akanta b, kome za tai ba dan ta takura mana take ba, yaushe rabonta da gidan ba zuwa take ba fa, kuma batun Nana, she's our blood sister like Khairat ban san meyasa ka tsaneta ba"

"Ni yarinyar ce ba tai min ba sam, ta fiye rawar kai da fitsara"

"Ni kam ba abunda tai min, ina jinta a matsayin ƙanwata"

"Lallai ƙanwa manya" Sadik yai maganar yana ajiye remote ɗin hannunsa ya bar falon.

Yana shiga É—akin sa, ya cire wayarsa dake caji, ya ga message ya buÉ—e message É—in ya duba.

"Assalam Alaikum, ina fatan kana lafiya, am missing You, kar kai min reply wayar Umma ce, idan na samu dama zan kiraka Farhan"

Jujjuya message É—in ya dinga yi yana murmushi kamar yana gabanta yace "am missing You too Princess"

Ya cigaba da kallon saƙon, mussaman kalmar am missing You, ba ta taɓa furta masa haka ba, ji yai tamkar ya shirya ya tafi gidan su.

Murmushi ya sake yi yana jin yadda shima yake kewarta.

Yana tuna yadda su kai da Mother jiya da yai nata zancen Farhan yaji ransa ya ɓaci, take yaji ze iya ɗaukar kowane risk dan ganin ya samu abunda zuciyar sa ke so.

Se Yamma sannan su Inna suka isa gida, duk da a motar gida suke, Inna ta gaji duba da yanayin jikin girma.

Nana kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, saboda sun koma gida ga Hakimi se taraiyar ta yake yi.

Tabbas Nana ta yi missing É—in Kakanta, me sonta da kuma ji da ita sosai.

Duk da ta wani fannin ta ɗan ji daɗin zaman birni, amma ta kasa mantawa da baƙin halin Mother da na ɗanta Sadik, mussaman Sadik da ke nuna mata tsana a fili.

Duk surutun Nana da wuri tai bacci, saboda ta kwaso gajiya sosai da sosai.

"Inna wuro kun sha birni, kun barni kamar maraya ba jikata ba ke"

"Hmm mun sha birni kam, Alhamdilillah gashi kuma mun dawo ai"

"Hakane, ya kuka baro min su?"

"Lafiya ƙalau, sedai akwai ƙura fa"

Hakimi ya sake nutsuwa yace "kamar yaya kenan?"

"Ranka ya daɗe, nifa sedai kace na cika ƙorafi, amma maganar gaskiya akwai gyara a gidan Bawan Allah, mussaman Ƙaramin ɗan sa, na rasa wace irin macece Hauwa"

Hakimi yai murmushi yace "ba zaki dena damun kanki akan yaron nan da iyalan sa ba ko?"

Inna ta girgiza kai tacee "ba damun kai bane, ina jiyewa bawan Allah abunda ka iya zuwa ya zo, akan wannan taƙadarin yaron nasa"

"To wai me yai miki ne? Ni kuma kinga nutsuwarsa nake gani, lokacin da naje É—aurin Aure mota É—aya muka shiga da shi muka dawo, banga wani abuba tare da shi ba"

"Hmm ni na gani ai, Allah ya kyauta kawai"

Washegari da Safe Sadik ya shiga É—akinsa da ke cikin babban falo, ya fito daga É—akin kenan se ga Mother ta fito hannunta É—auke da wata leda, ta kalli Sadik tace "wai kai uban me a kai maka ne? Ko zuwa gaisheni yau ba kai ba, tun É—azu Abba yake ta cigiyarka? Meye hakan ka ne, kullum ba ka da aiki se yin abunda zaka jamin laifi gun mahaifinka ko danginsa"

Mamaki ne ya kama Sadik, wato har Mother ta manta abunda ya faru, amma ya basar yace "Mother ba Komai fa, am not in mood ne kawai, amma ba wani abu"

Faruk ne ya shigo da sallama, hannunsa ɗauke da key Yace "Mother gani na shirya, kawo saƙon in kai"

Mother ta ƙarewa Faruk kallo sannan tace "Yawwa dama ba iya kai saƙo ne yasa na kiraka ba, ɗazu da ka shigo mahaifinka na nan, ba damar in maka magana a gaban sa kar yaji haushi"

Faruk cikin rashin fahimta yace "Mother wani abun ne ya faru ne?"
Chapter 36 · 0% Book details