← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 48

Sashe 13

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Karki damu dan wannan ba Matsala, yama za'ai ai bikin bro tawa matar va taje ba, kin san daga bikinsu se namu fa"

Zare ido tayi sosai kamar ya faÉ—i wani abun tsoro.

"Meye naga kina zare ido haka?"

"Ya za'ai amana Aure yanzu, mufa yara ne"

Ƙasa ƙasa suke hirara ba wanda yake jina bunda suke faɗa, amma jin abunda Farhan ɗin tace yasa Prince cikin ɗaga murya cewa  "What!".

Seda aka jiyo aka kallesu, Prince ya basar yai ƙasa da murya tare da ɗan haɗe rai yace "suwaye yaran?"

ÆŠan tura baki tayi tace "to ai naga ko makaranta ba mu gama ba, kuma base mutum ya girma yake Aure ba, waye ze mana Aure a haka?"

Seda Prince yai murmushi, ya jinjina wauta da ƙuriciya irin ta Farhan, sannan yace "waye yace miki shi girma a fili yake, waye yace miki sharaɗin Aure ne se mutum ya girma sosai za'a masa Aure?"

"Ai haka naga anayi"

"Hmm Farhan kenan, yanzu idan Dad É—ina yazo nema min Aurenki baza'a bni ba?"

Ya faÉ—a in a very serious tone.

Kamar za tai kuka tace "wallahi ina ga se ya kusa ɓallani, cewa ze ya akai nai saurayi har na fara Maganar Aure?"

"Hakane You Are still Baby, but looking so....

Se kuma yai shiru yana cigaba da ƙuara mata ido, har seda ta ɗan tsargu.

"Amma ai kina sona ko?"

ÆŠaga ido tai ta kalleshi, ta mayar ta sunkuyar.

"Hmm i understand"

Babba ne na ss3 ya shigo ajin, yana shigowa Taslim ta miƙe da gudu ta rungumeshi, ya ɗagata yana juyi da ita a tsakiyar class ɗin.

Mamaki ya cika Farhan, wannan wane irin rashin hankali ne da rashin ta ido.
A shagwaɓe Taslim tace "I miss You Honey"

"Miss you too dear, ai tunda na dawo tun lats week ba kya Zuwa bamu haÉ—u ba"

"Bama gari, munje Abuja that's why, you are well dear, amma dai ka warke ko?"

Babba yace "Alhamdilillah jiki yayi sauƙi sosai"

Farhan kama gaba ɗaya seta tsargu, wata kunya ta mamayeta, ganin haryanzu sunƙi sakin juna Taslim da Mubarak wato Babba.

Sadik yace "gaskiya Mubarak ku fita can waje kuyi, kun san Babyna jaririya ce kuna iskanci a gabanta karku ɓatamin mata ku sa mata wani tunanin daban"

Taslim tace "ba wani jaririya, ta san komai, don't mind them my sugar"

Tai maganar tana kissing Mubarak a kumatunsa.

Nasir yace "kaga in da ake abu, ba irin soyayyarku ba, soyayya irin ta zamanin iyaye da kakanni"

Farhan ta miƙe tace "Na tafi aji"

Sadik yace "sun kore ki ko? Banzaye kawai muje in kaiki class"

Ya miƙe suka jera suka fita, sedai Nas yabi bayan Farhan da kallo.

Amin ya daki cinyarsa yace "kai lafiyarka kuwa?"

"Lafiya ƙalau, ina kallon Yarinyar nan ne kawai, gaskiya ina ni zan sharewa Prince hanyar nan, kan uba ka ga abunda na gani kuwa?"

"Aikuwa da yaci ubanka la'ada waje"

"Kai dall ƙyaleshi, se wani abu yake waishi na Allah, this girl is looking so hot ka gane ai"

"Karka kuskure ya gano ka wallahi, dan karonku baze maka daÉ—i ba, nasan akan yarinyar nan ba abunda baze iya ba"

Nas yace "za'a cigaba da ɗora shi a layi, idan yaƙi ɗaukar haske zega aika aika"
Suka cigaba da hiararsu ta rashin É—a'a.

Kwanci tashi asarar rai, satin kayan lefe guda cif, duk 'yan uwa dangin Alhaji Abdullahi duk suka zo suka ga kaya, sannan Inna ta shirya ita da Jikarta aka kawo motoci aka kwashe su su da kayan.

Can gidan Alhaji Abdullahi suka tafi da kayan, Nana ta ware ido ta finga kallon gidaje kamar biscuit, kamar a É—auka a ci dan kyau da tsaruwa.

A ƙauye ana cewa ba gidan da ya kai na Hakimi ƙaruwa, amma yanzu idonta ya gane mata in da ake gidaje.

Da ana zuwa da ita tsohon gidan, amma Inna ta daɗe bata taka ƙafarta gidan nan ba se yau.

Hajiya Hauwa kuwa wato Mother, taji haushin yadda aka taho da 'yan ƙauye, wai za'a kai kayan lefe, abun nan ya baƙanta mata rai a nata faɗar zasu ɓata mata lamari dan ba hankali suka cika ba.

Ba yadda ta iya tunda ga uwar mijinta, kuma shikansa maigidan yana gari balle tai rashin mutunci, tun asalin kai kayan ƙauye ma abun be mata ba, balle kai kayan lefen tare da su, ga ƙawayenta da 'yan uwanta 'yan gayu amma za'a haɗasu da tarkace.

Aka kuma shishshsigo da Akwatuna, Inna tasa aka sassauke kaya aka sake buɗewa, Hakimi ya sa an ƙara atamfofi dozen a ciki, Inna kuma ta saka zobuna da sarƙoƙin azurfa.

Nan aka dinga guÉ—a ana Allah ya sanya Alkhairi.

Wata ƙawar Mother tace "kai Hauwa, dangin mijin nan naki duk da 'yan karkara ne, amma sun san abunda yakamata, wallahi da nawa dangin mijin ne, sedai a kaisu a haka inma basu saci abunda zasu sata ba, amma kalli aabun arziki kuma atamfofi masu tsadar gaske, su kansu azurfofin nan masu tsada ne sosai"

Tsaki Mother tayi tace "nifa duk abunda za'a saka da mutanen nan ba sonake ba, inma bayarwar ne a aiko dasu mana, kawai an kwashi kaya an kai musu, an kuma kwasowa an dawo, za'a kuma kwasa a kai kaya dasu, ni Allah yasa ba wani abun sukai wa kayan ba, dan ni ba wani yarda nai dasu ba"

"Ke Hauwa, meye aibun hakan? Taɓɗijan, a zaminin nan ki samu dangin miji suna son 'ya'yanka, ai wallahi banga aibun hakan ba"

Tsaki Mother tai, ta cigaba da cika tana batsewa, tana wani basar da su kamar taga bola.

Daddy ne ya shigo tare da Ango, wato Usman.

Take 'yan ƙauyen nan suka kaure da guɗa ana shewa, Alhaji Abdullahi ya dinga murmushi, haka shima Usman ya dinga murmushi.

Alhaji Abdullahi ne ya fara zubewa a gaban mahaifiyarsa wato Hajiya Inna, ya dinga mata kirari sannan ya gaisheta abun gwanin burgewa.

Ya cire hular kansa ya durƙusa a gabanta yace 'barka da zuwa farar uwa me farar aniya, 'ya ga Hakimi mata ga Hakimi, katangar sukari kowa ya jingina dake se ya lasa, farar uwa abun alfahri 'ya'yanta, shalelen Hakimi barka da zuwa uwata ta kaina"

Seda mutanen da ke falon suka saka shewa, saboda abun gwanin burgewa.

Murmushi Inna  tayi, wanda se fararen haƙoranta suka bayyana sannan ta amsa masa "Sannunka ɗan gidan Innarsa, mun sameku lafiya"

"Lafiya ƙalau Inna"

"An shab turai, Usaman Allah ya kawo mu lokacin Aure, Ubangiji Allah ya Sanya Alkhairi"

"Ameen Inna"

Usaman yace "Inna ina wuni"

"Ba zan amsa ba, bayan ba kwa zuwa inda nake"

Usman yace "ba haka bane Inna, kin san ba zaman ƙasar muke sosai ba"

"Eh kuna can kuna yiwa nasara bauta ba, ai shikenan ni gani nazo ai, ina nan har a yi biki ai, ga kaya nan Hakimi ya ƙara maka, yace yana maka murna, se kuma Allah ya kaimu Lokacin ɗauren Aure ze zo"

Alhaji Abdullahi yace "Masha Allah, muna godiya ranki ya daɗe, Allah ya ƙara arziki yasa afi haka"

Nana ce tace "Kawu ina wuni?"

ÆŠagowa Alhaji Abdullahi yai ya kalli Nana yai murmushi yace "ai ban kula dake ba, ni yakamata in gaisheki Uwata ta kaina, ina wuni Ummana"

Rufe fuska Nana tayi cike da jin kunya ba tare da ta amsa ba.

Inna ta nuna mata Usman tace "to kin san wannan? Ko kuma baki sanshi ba se me tara gashi?"

Nana tace "Nasan shi mana"

"To ya sunansa?"

Shiru Nana tayi tana tunani, amma ta kasa tunawa.

"Kaga abunda nake faÉ—a ko ko Abdullahi, bata san sunan 'yan uwanta ba, sedai tace 'ya'yan kawunmu masu tara gashi"

Alhaji Abdullahi yace "Ayi haƙuri Inna, insha Allah za'a san abunyi"

Nana gajiya tayi da zaman, ana ta hira ta tashi dan fitowa harabar gidan ta sake ganin abubuwa.

Ta fito tana ƙarewa motocin dake harabar gidan kallo, bin motocin ta dingayi ɗaya bayan ɗaya tana shafawa, tana sake lelleƙawa.

Ta gaji da wannan ta nufi wani ɓangaren daban.

Leƙe leƙnta ta cigaba dayi, tana zazzagawa.

Motar Prince na shiga gidan, ya fuskanci da yauma da mutane a gidan, tun daga cikin motar yake jan uban tsaki yana cewa aikin banza anzo an cikawa mutane gida, an hanasu sakewa.

Ya saɓo jakarsa ya nufi BQ yana ƙwafa yana masifa, sedai yana shiga falo ya tarar da ita tana tattaɓa ƙatuwar plasma dake jikin bango.

"Ke wace wannan? Uban me kike a nan?!"

A razane ta waigo ta kalleshi tace "yi haƙuri ban san ba'a shigowa nan ba"

Gani yai kamar ya santa amma ya manta inda a santa.

'ke wace irin banza ce, daga zuwa gidan mutane kawai kije inda ba'a aikeki ba, dama kinga mutane na zuwa nan ne?"

Haɗe rai tayi tace "kar ka sake zagina ba nace kayi haƙuri ba" tai maganar tana tura baki.

'dalla zoki fita ki barmin É—aki, mahaukaciya kawai"

Nana tace "Kut, wallahi kaine mahaukaci bani ba"

"Ni kike cewa Mahaukaci?"

"To uban waye yace ka fara gayamin mahaukaciya?"

"Ubanki ne" ya bata amsa.

"Sedai ubanka bani ba"

Aikuwa ya nufi inda take gadan gadan....

Free pages are not much, hurry up and subscribe yours.

Ayshercool
07063065680.

[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

9_10
Chapter 13 · 0% Book details