Sashe 18
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsit sukayi suka gayara zamansu, Director yace "my dearest And beloved student, can't you greet?"
Seda yai Maganar, sannan suka gaishe su gaba É—aya.
Nan ya gabatar musu da 'yan bautar ƙasar nan, a matsayin sababbin malamai.
Nan suka gabatar da kansu É—aya bayan É—aya ga 'yan ajin, bayan sun gama gabatar da kan nasu ne, Director da kansa ya dinga gabatar musu da É—aliban da kansa, kowanne ya gabatar da shi da matsayin mahaifinsa.
Seda suka kammala yai musu jawabin da ze musu, akan su bawa malaman haÉ—in kai, dan samun ilimin da ya dace.
Meena ce cikin harshen turanci da iyayi, ta wakilci 'yan ajin ta yi musu barka da zuwa, da tabattar musu da za su basu Dukkan haɗin kan da suke buƙata, dan gudanar da aikinsu.
Wani fari daga cikinsu wanda ya gabatar da kansa a matsayin Nura daga Kogi state, shima cikin harshen turanci ya wakilci 'yan uwansa, yai musu godiya da irin karɓar da a kai musu.
Daga nan kuma suka bi Director suka fita suka nufi wani ajin.
Suna fita Meena tai murmushi tace "Subhanallah"
Taslim tace "ke lafiyarki kuwa?"
Meena tai murmushi tace "Taslim kinga abunda na gani kuwa?"
"Me kika gani?"
"Wallahi I fall for that guy"
"Wane guy kuma?"
Taslim tai maganar tana kallon Meena.
"That fair and tall Man, Nura looking very beautiful and energetic, wallahi yai min"
"Ke bana son iskancin banza fa"
"Ke wallahi ba ƙarya nake ba, before nafi ganin kyan corper Nazir, Amma yanzu naga abunda zuciyata ke so wallahi"
Taslim tace "Nifa daɗina da ke 'yar bala'i ce ke, ki rage leƙe leƙe wallahi"
"Ba wani leƙe leƙe ƙyaleni kawai"
Nasir kuwa cigaba da batun bikin yayan Sadik sukayi.
Yau Farhan ba ta zo gurin sa ba, dan haka da kansa ya kuma tafiya nemanta, sedai ya tarar ta kifa kanta akan benci, kamar me bacci.
Ƙarasawa yai a hankali, ya ɗagota da ga kwanciyar da tayi.
Hakan ya firgita ta sosai, ta shiga rarraba ido amma ba tace komai ba, yace "Am sorry na miki laifi, na firgita ki gashi na taɓa ki ko?"
Ba ta masa ba, ya samu guri ya zauna daf da ita yace "Honey meke damunki ne? Naga idonki yai ja"
Ji tai kamar Sadik ya taɓo mata inda yake mata ƙaiƙayi, tana da damuwa But she has no one to discuss with, she's developing some changes in her breast, suna mata zafi wasu lokutan, sedai ta kasa ganewa, is it the normal stage of puberty, ko kuma wata matsala ce daban, dan tana jin ana wayar da kai akan breast cancer, dan recently anyi taro a makarantar, na wayarwa da mata kai, akan ciwon sanƙaran mama, amma ita ta kasa gane a wani hali take? Gashi ba yadda za'ai taiwa Ummanta zancen, gashi ba wanda za ta iya gayawa damuwarta, a yanzu haka duk da ta na kwana guri ɗaya da Ummanta ta tashi, amma Babu wanda take da kusanci da shi a yanzu kamar Sadik, sedai shima ɗin Maganar tayi matuƙar nauyin da ba zata iya tambayarsa ba.
"Lafiya naga kin yi shiru kina kallona? What's wrong ki gayamin please"
Ajiyar zuciya tayi, cikin sassanyar muryarta tace "bakomai fa"
Ya kwaikwayeta yace "ban yadda ba gaskiya"
Hakan ya bata dariya da seda tai murmushi, yace "oya gayamin ina jinki"
"Dagaske nake bakomai, bacci nake ji ne"
'ba kya bacci sosai ne a gida?"
"Eh ina yin karatu da daddare"
"Wow that's very good ai, amma ki dinga rangwantawa kanki kinji Hubby na, bikin yaya na ya kusa, za'ayi events da aka shirya a gidan mu, amma akwai party da zan organising, so akwai kalar outpit É—in da za'a saka, ayi order dake zaki saka?"
"A'a baza'a barni ba a gidanmu"
"Ok ba damuwa, nasan dama ba lallai a barki b, but I just decided to tell you ne, amma dai ko sau É—aya zaki zo ko?"
"Eh Insha Allah"
"Yawwa my wife"
Sunkuyar da kai tayi ƙasa, dama yasan hakan ne ze faru, dan wannan kalaman nasa nauyi suke mata.
"Farhan" ya kira sunan ta.
"Na'am" ta amsa.
"Next week zan karɓo exams card ɗina, na kusa Barin makarantar nan Insha Allah"
Ai da sauri ta É—ago ta kalli Sadik tace "dan Allah dagaske ka ke?"
"Am serious, zanyi Waec ne in kammala karatuna akan lokaci"
Take jikin Farhan yai wani irin sanyi, ta kasa cewa uffan se dai damuwa ta bayyana ƙarara ta mamaye fuskarta.
"Farhan" ya kira sunanta.
A sanyaye ta kalle shi, yace "kin san meyasa nai haka? Duk cikin planing É—ina ne na in mallake ki, dan Allah Farhan kar ki kalli hakan da wata fuska daban, i really love you wlh, duk saboda nake wannan fighting É—in, kimin addu'a samun nasara, bari in tafi aji kar Wannan jarababben mutumin yazo yai min masifa"
Ya tashi ya kalleta yace "I love You baby" ya kashe mata ido É—aya ya juya ya fita.
Ai yana fita ta bawa hawayen da take ta kokawa da su damar zubowa, ta kifa kanta kawai ta fara kuka ƙasa ƙasa.
"Yanzu idan Prince ya dena zuwa Makarantar nan ya za tayi, a duk ranar da ba ta ganshi ba, tana shiga mummunar damuwa, se gashi ze bar makarantar gaba É—aya, nan hawaye suka cigaba da zarya a kuncinta, ta sa hanky tana gogewa, tun a lokacin taji ta fara kewar masoyin nata, take ta manta da damuwar ta ta farko dake damunta.
Shi kansa Sadik tunda ya gaya mata yaga damuwa a fuskarsa, ya shiga damuwa shima, take yaji wani irin tausayinta ya kamashi sosai, shikansa ya san zeyi missing É—inta, sedai barinsa makarantar ba yana nufin ya bar Farhan ba, akwai yiwuwar ya fara neman Hanyar cinma burinsa, na aurar wadda yake so a Wannan shekarun.
"Idan ka aureta Yanzu tata rayuwar fa? Karatun ta fa?" Wata zuciyar ta tambayeshi.
'ta ƙarasa a gidana' ya bawa kansa amsa.
Da gudu ta sheƙo ta kan varrender, tana ƙoƙarin ƙarasawa ajinsu "Lilly! Lilly" tsayawa Lilly tayi tana kallon Sir Nazir dake ta ƙwala mata kira kamar mafarauci.
"Why are you running like this? Where is your jacket?"
Ta kalli jikinta daga ita se inner shirt, da skirt É—in ta iya gwiwa, ta cire jacket É—in ta ajiye a aji, ta kalleshi tace "tana aji"
"Meyasa kike yawo a haka? Baki san kin fara girma ba, kuma kina gudu a cikin yara haka? Ga hijjabin ki ƙarami, Why are you exhibiting childish behavior, don't you know you are at your Adolescents period, you have to maintain your body?"
A ranta tace "ji É—an iska, seka gayamin a Adolescents period nake, ai nima na sani"
Ta tura baki cike da sangarta.
Yace "idan na kuma ganin kin kuma cire jacket É—inki kina gudu haka, sena zane ki, wuce ki ban guri"
Tafiya tayi tana yatsuna fuska.
Tana zuwa Ajinsu tace "hmm ƙawayen amana kun san abunda ya faru kuwa?"
Haseena tace "ya za'ai mu sani se kin faÉ—a"
Lilly tace "mhmm wannan sir Nazir É—in ne na taho da gudu ya wani tsaida ni, wai meyasa nake yawo ba jacket nake gudu, wai ban san na fara girma bane na shiga Adolescents period, kuji min É—an air mutum"
Shewa suka yi Haseena tace "Ya ƙyasa ne yaseen, shine ya gaza shiruu seda ya tanka, ya tsaida ke ne kawai dan kawai ya sake kalla sosai"
Ihu suka saka gaba ɗaya, tai wani juya tai girgiza tace "gani ba taɓawa ba asarar ido, nan gani nam bari ɗumamen mayya, kuma wallahi yawo ba jacket yanzu na fara, ke ni fa na kusa dena saka wannan ɗan hijjabin ma, haka zan dinga yawo, mutum ya kalla ko kuma ya runtse idonsa"
Yasmin tace "to Allah ya temake ka abubuwa sun fara fitowa ace ba zakai gayu da abunka ba, wani abun ma se munje Final year lokacin sun gama fitowa, lokacin ne zega yadda ake abu, yadda zamu addabi makarantar nan, ai ya gani ya kasa shiru shine ya tanka miki, sun tsole masa ido"
Lilly tace "aikuwa in hakane ya shiga tara mutumin nan, dan sena ganshi ma zan dinga kasawa da gud"
Yasmin tace "ai base kinyi gudu ba, kya yiwa kan ki ɓarna ai, kina tafe kina ɗan bada style ma ya isa, ban gaya muku ba ma, na fa samo mana littafin nan, ku kunji abubuwa a ciki kuwa"
Haseena tace "dan Allah dagaske ko da wasa?"
"Wallahi dagaske nake, ke kunga yadda aka fayyace komai ban dai karanta ba, page É—aya kawai na karanta, amma naji sena zo da wayata mu karanta tare, kai akwai tafasassun abubuwa a littafin nan"
Lilly tace "shegiyar kaya, ai a kawo mana littafin nan, muji abubuwa kawai"
Su kaita shewa, ita kam sam Farhan hankalinta baya kansu, hankalinta kacokan yana kan maganar da sukayi da Prince É—inta.
Shikansa Prince har aka tashi jikinsa a sanyaye yake, yaje ƙofar makarantar ya tsaya yana jiran fitowar Farhan.
Aikuwa ya hangota ta fito daga cikin makarantar, idanunta sunyi jawur sosai, tana tafiya a hankali, daga inda yake tsaye yake kallonta, kullum ƙara girma take tana kyau abunta, sheɗan ne ya fara ƙawata masa ita, da ɗarsuwar wani abu daban a ransa, take yace "Subhanallah" ya dawo hayyacinsa.
Tana É—aga ido sukai ido huÉ—u da shi, murmushin dole tai masa, yace "ke muke jira taho mu tafi gida"
"A'a zan tafi ai"
"Bana son gaddama fa"
Ba yadda ta iya haka ta bishi ta shiga motar, suna tafiya yace "Anya ba kuka ki kai ba, naga idonki ya ƙara ja"
"Ba kuka nai ba, dama ina ciwon ido wani lokacin"
"Ciwon ido, lallai ma ashe makauniya ce matar tawa, gaskiya sena rage sadakin da zan bayar" yai maganar yana murmushi.
Direba ko a ransa yace 'ikon Allah, ji wani kwaɗo da fitsara wai ita game saurayi ta shiga motarsa yana mata kalaman banza na RUƊIN ƘURUCIYA, banda haka ina Sadik ina wata budurwa dan kawai yana ganin ya na da tsawon ƙafa!?"
Seda suka kai Farhan gida sannan suka wuce gida, babban abunda yaiwa Sadii daÉ—i be wuce yadda yau gidansu ba mutane ba, hakan yai masa daÉ—i sosai.