Sashe 4
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Banza Sadik yayi musu, suka gama surutunsu 'yan matan class É—in ma sukazo kan Sadik suna nasu surutun
"Babban yaro waye ya taɓo mana kaine?"
Kamar da Dutse suke Magana, yai musu shiru ƙarshe se haƙura suka yi suka ƙyaleshi.
Farhan kuwa gaba É—aya ta kasa nutsuwa, ta kasa samun kwanciyar hankali saboda rashin ganin Sadik, É—alibai kowa yana harkokinsa amma banda Farhan.
Ganin da tayi zaman baze fishsheta ba, yasa ta miƙe ta nufi hanyar ajinsu Sadik.
Tana zuwa gaba ɗaya ta kasa shiga, ta tsaya a waje tana leƙa ajin, ba zata iya shiga ajin ba, saboda na Seniors ɗintane, gashi bata san kowa a ajinba se Sadik, dan haka tana jin nauyi sosai.
Ta window ta tsaya, tana leƙawa dan taga ko zata hango Sadik ɗinta.
"What are you doing here?" Da sauri ta waiga dan ganin me Maganar, Nasir ne abokin Sadik, ya kalleta yace "ko kina Neman Sadik ne?"
Farhan ta É—an sunkuyar da kai, cike da jin kunya.
Nasir ya ɗan tsaya yana ƙare mata kallo, da jinjinawa mugun jin kunya na Farhan, se dai babu mamaki irin wannan halayyar ga 'ya'yan talakawa, sam basu da wayewa.
Yace "to ki shiga mana, yana ciki ai"
Kamar wadda aka yiwa dole, ta shiga ajin can ta hango Sadik, zaune ya kifa kansa, gabanta ne ya faÉ—i tai tunanin ko bashi da lafiya ne?
Da ɗan hanzari ta ƙarasa bencin da yake zaune.
Jin mutum a kusa da shi ne yasa ya É—ago da sauri dan yiwa wanda yazo kusa da shi É—in masifa, sedai kuma yayi tozali da fuskar Farhan.
Ajiyar zuciya ya sauke, bece komai ba.
A hankali tace "baka da lafiya ne?"
"No Farhan, lafiyata ƙalau"
"Amma ban ganka a gurin assembly ba?"
"Nazo a makare ne, kuma wancan corper ɗin ya ɓatamin rai, sena gyara masa zama tukuna"
Farhan tace "me yayi maka?"
"Yana min shishshigine, dan yana saka wannan koÉ—aÉ—É—un uniform É—in na NYSC, idan be kiyayeni ba zan koya masa hankali"
Farhan tace "kasan meyasa ya sani punishment jiya?"
Sadik ys girgiza mata kai, tace "wai saboda kaje gurina, ya tambayeni meke tsakanina da kai, shine 'yan ajinmu suka faɗa masa, shine yaita min faɗa ya sani kneeldown"
Sadik ya daki benci yace "har akwai wani sakaran daze sawa soyayya ta ido a makarantar Nan? Wallahi idan mutumin nan be kiyayeni ba sena sa an karairayamin shi" yai maganar a harzuƙe wanda seda hankalin 'yan ajin ya dawo kansu.
Aminu Yace "wai kai Sadik meke damunka ne?"
"Wannan Nazirun ne, da gemu kamar soson wanka wallahi ya cigaba da shiga sabgata kota Farhan wallahi sena masa illa"
Farhan ta kwantar da murya tace "dan Allah kayi haƙuri, dana sani ban gaya maka ba"
Wata cikin 'yan class ɗinsu Sadik me suna Amina amma suna cemata meenal ta taɓo ƙawarta tace "Taslim, kina ganin wani abu kuwa, wannan budurwar Sadik ɗin akwai iya barikanci, kalleta saliha kuma yarinya amma ta dabaibaye zuciyar ɗan mutane ji yadda take masa magana"
Taslim tace "ke dai Bari, kina gani Tun ɗazu muke tambayarsa meya dameshi, yai banza damu amma tana zuwa ya ɗago kansa, na rasa meya ja ra'ayin Sadik akan yarinyar nan, kaf class ɗin nan Sadik bashi da budurwa, ya rasa a inda zeyi budurwa se a Jss2, duk wannan iyayin nasa.
Meenal tace "lallai ma ke ɗin nan, Sadik wayone da shi ya samo yarinya fresh, wadda bata san komai ba ya koya mata sonsa, zeyi tattalin kayarsa kuma ki ƙare mata kallo, yarinya ce amma me ƙirar manya, tana da zubin halitta me jan hankali sosai"
Suka cigaba da gulmarsu a gefe, Sadik kam se banbami yake akan Corper Nazir, Farhan tace "ni ka dena wannan faɗan ko in tafi"
"Farhan ya bazanyi faÉ—a ba, yana nema ya kassaramin soyayya, ina ruwansa damu?"
Nasir Yace "Sorry Prince, ai komu ba zamu bari a kassara wannan soyayyar ba, wadda muke saka rana ta shiga kundin tarihi kamar ta su Laila majnun"
Kamar Farhan za tayi kuka tace"dana sani ban gaya maka ba, nace fa kayi haƙuri"
Sadik yai shiru yana cigaba da huci, Farhan tace "kayi haƙuri mana, dan Allah ka dena fushi Kaji, ka ga malamnmu ne, koba komai ya koyar damu, ka dena zaginsa"
Sadik Yace "ke dalla ƙyaleni, na tsani mutumin nan wallahi"
Miƙewa Farhan tayi zata tafi, jin yadda yayi mata magana a tsawace, ya riƙo hannunta da sauri, wanda hakan ya haddasawa Farhan mummunar faɗuwar gaba, taga kamar kowa suyake kallo.
Tace "ka dena taɓani, meye haka?.
Sadik yace "am sorry, na dena amma dan Allah kiyi haƙuri, zauna"
Farhan ta nemi Guri ta zauna, yace "kiyi haƙuri bazan sake ba insha Allah"
Ta zauna tana ɗan tura baki, taƙi kulashi, ya sake kashe murya yace "haba na face kiyi haƙuri"
Tai murmushi tace "Na haƙura ai"
Suka cigaba da hira ita da Sadik, yama manta da maganar wani Nazir.
Har aka koma class Farhan bata sani ba, tana zaune tana hira da Sadik cike da nishaÉ—i, duk da mafi yawan hirar shi yake mata, ita murmushinta yafi yawa akan magana.
"Ke Farhan!" Sukaji muryar Sir Nazir.
A rikice Farhan ta waiga, dan ji tai an kira sunan nata tamakar saukar Aradu, Kamar yadda ta zata sir Nazir ne ba wani ba.
"What are you doing here? Is this your class?" Ya tambayeta yana zazzaro ido.
Cikin tsoro Farhan ta girgiza kai, alamar a'a yayinda attention ɗin class gaba ɗaya ya dawo kansu, kowa ya zubo ido.
"Me kikeyi a kusa da namiji a zaune? Ajin ku ne nan? Tashi ki bar ajin nan ki koma ajinku"
Sadik ya fusata ze yi magana, Farhan ta girgiza masa kai, ta tashi da sauri ta fita, Sadik ya tsaya yana kallon kallo da Nazir.
Naziru yai ƙwafa ya fice, yana fita Sadik ya daki benci yana muzurai, Nasir Yace "easy Prince, kayi haƙuri"
"Mutumin nan yana wuce gona da iri fa, zanyi masa kaca kaca a makarantar nan wallahi"
"Kayi haƙuri, zamu san matakin da zamu ɗauka a kai"
Farhan kam da Kusan gudu ta ƙarasa ajinsu, ai kuwa Nazir ya rufa mata baya, a gaban 'yan ajin ya shiga zazzaga mata bala'i.
"Ke wace irin yarinya ce ne? Abunda kike kin kyautawa kanki ko iyayenki? Gurin wannan É—an iskan yaron aka turoki? Me kike zuwa gurinsa yi?" Yai maganar yana tsatstsareta da ido.
Farhan ta girgiza masa kai, alamar ba komai.
"Wallahi idan baki shiga hankalin ki ba sena haÉ—a miki assembly, kuma in kira mahaifinki in gaya masa abunda kike aikatawa, gara tun wuri ki fita harkar wannan É—an iskan yaron, tun be lalata Rayuwar ki ba"
Farhan tana jin zafin cin mutuncin da Nazir yake mata, sedai jinsa kawai take dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik,sum sum taje ta zauna a gurin zamanta tana sunkuyar da kai, Nazir na cigaba da zazzaga Mata cin mutunci.
"Irinku ne masu komawa iyayensu da ciki ,ku lalace tunda ƙuruciyarku, saboda RUƊIN ƘURUCIYA na ɗibarku, sun turo ki kiyi karatu amma kina biyewa 'yan iska, a haka gaki kamar saliha amma baki da hankali, in sake ganin kinje inda yake, sena zaneki a makarantar nan"
Farhan tai shiru, ta sunkuyar da Kai tana jin yadda maganganun nasa ke mata dirar mikiya a ƙirjinta, taji zafin yadda yake cin mutuncin ta a gaban 'yan ajinsu, dan seda tayi kuka, sedai sam maganganun nasa basuyi tasiri a zuciyarta ba, dan bata tunanin zata iya rabuwa da Sadik, tun da ita dai bata ga aibun Sadik ba, a barshii da zafin rai dai wasu lokutan da rashin son raini, amma yana da sauƙin kai sosai, sedai ta yanke shawarar zata yi duk me yuwuwa ta nesanta kanta da Sadik ko dan kaucewa cin mutuncin Sir Nazir da dizginsa da kuma gudun kar ya haɗa ta da mahaifinta, dan a duniya tana tsoron Allah, tana tsoron mahaifinta sosai.
Nazir ya gama faÉ—ansa san ransa sannan ya shiga gabatar da lesson É—insa.
Har ya gama karatunsa Farhan kuka take yi, dan sam na ta fahimci komai ba har yai ya gama.
Bayan ya fita wata daga cikin'yan ajinsu wadda ake cewa Lilly tazo ta dafa kafaÉ—ar Farhan, Farhan ta É—ago kanta ta kalli Lilly.
"Ki dena kuka ki rabu da wannan É—an rainin hankalin kinji, ki dena kuka"
Farhan ta jinjina mata kai alamar to.
Koda aka tashi daga school, Farhan bata jira kowa ba ta silale ta tafi gida, Sadik yaita nemanta be ganta ba, haka ya haƙura ya tafi gida, yana mamakin yadda aka yi ta tafi basu haɗuba.
**********
Gudu gudu sauri-sauri haka ta faÉ—o makeken tsakar gidan, hannunta É—auke da jakar makaranta, tana zuwa ba tayi wata wata ba, tai jifa da jakar a tsakar gida, ta faÉ—a banÉ—aki.
Dattijiwar dake zaune tana mulmula fura, ta kalli jakar makarantar da yarinyar ta jefar a tsakar gida, ta girgiza kai ta cigaba da aikinta, kusan mintuna biyar sannan ta fito daga banɗakin, ta tsaya a tsakar gida ta shafa cikinta tace "wayyo Allah, fitsari idan ya matseka ba arziki, ina tafe a hanya kamar zanyi hauka, saboda yadda ya matseni"
Dattijuwar ta kalleta tace "zaki zo ki ɗauke wannan jakar da kikayi jifa da ita a tsakar gida, ko kuwa se nayi yaƙi da bakina"
Ɗan tura baki tayi, taje ta ɗauke jakar Tata, ta kai cikin ɗaki ta ajiye, ta cire duk kayan jikinata, ya rage daga ita se dogon wandon makarantar ta, ta fito tsakar gida tana faɗin "Innarmu, wai yau me aka dafa ne?"
Inna ta É—ago zata yi magana, amma taci karo da yadda yarinyar ta fito tsakar gida.
"Nana waike wace irin sha3 ce ne haka? Kalli fa a yadda kika fito, kowane lokaci za'a iyayin sallama a shigo gidan nan, amma kika fito tsakar gida a haka"
Ummi ta ya mutsa fuska ta kalli kanta tace "to ni innarmu me nayi?"
"Dan ubanki baki san kin fara girma bane? Dubi ƙirjinki kin fara ƙigar dangi, amma kin fito a haka bako Kunya, ko 'yar shimi ba ki saka ba"
"Meye kuma ƙirgar dangi?" Ummi ta tambaya cike da wauta.