Sashe 28
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaskiya Sunusi be mata adalci ba, gaisawa ce da girmamawa tsakaninta da shi, dan me za'ai mata haka?
Gaba ɗaya, ba ya cikin tsarin ra'ayinta, ba ta san me ake ji a so ba, se akan Prince ɗinta, gashi ɗan gaye me aji, gashi me kyau, ina zata kai Sunusi, ga baƙi kamar an rina shi, ga tsagu a fuskarsa kamar ƙwarya, seya shafe sati yana saka yadi ɗaya, dama batun gayu babu shi, sedai Sunusi akwai haddar Alqur'ani me girma, dan gwani ma ake cema sa, da ka yake Rubutun Alqur'ani.
Ya san Alqur'ani sosai da sosai, sedai bayan ilimin Alqur'anin nan babu na hadisi, babu na fiqihu, amma idan ya zauna ze iya gaya maka adadin ayoyi na kowacce sura a cikin Alqur'ani, sau nawa Allah ya ambaci kowane Annabi, sau nawa sunayen Allah suka zo a Alkur'ani, adadin sunan Allah nawa ne a Alqur'ani da in da aka ambace su, duk da ka yake irin wannan abubuwan.
Duk da fankar É—akinta na ta uban gudu ta na bada iska, Amma ita wata irin zufa takeyi, sam ta kasa samun nutsuwa.
Ummanta kuwa cigaba su kayi da hirarsu, yayin da Farhan kuwa ta shiga cikin zullumi da damuwa, dan ita a duniya yadda take ji a zuciyar ta, idan har ba Sadik ba, ba zata iya auren kowa ba.
Duk da ana yawan faɗa mata Soyayyar su RUƊIN ƘURUCIYA ce kawai, kuma babu lallai ya Aureta, amma ita yadda Sadik ɗin ke nuna mata ba ta jin ze kasa Aurenta, Amma idan aka haɗa ta Aure da Sunusi an gama cutarta, yanzu ta san ciwon kanta, ta gane menene so meye daɗin sa, sam zuciyarta ba zata iya karɓar Sunusi a matsayin mijin Aure ba!.
Sadik kam cikin gida ya shiga, yana zuwa ya tarar da Inna a falo Nana na kusa da ita, da sauran ma'aikatan gidan da ke ta shige da fice, da fara shirin karɓar baƙi, dan saura kwana biyu a fara biki, gidan a cike yake da mutane.
Sadik na ganin Inna ya ɗan ɓata fuska dan baya son damuwar tsohuwar nan, amma ya basar ya ɗan risina yace "Ina kwana?"
Inna ta ɗaga kai ta kalli Sadik, ta ɗan yi murmushi me cike da ma'anoni tace "lafiya ƙalau ka tashi lafiya?"
"Lafy ƙalau" ya amsa tare da miƙewa ze tafi.
"Su sauran jama'ar É—akin ba zaka gaishe su bane?"
Haushi ne ya kama Sadik, ita dai tsohuwar nan ba ta san zaman lafiya kwata kwata, tun da dai ya gaisheta meye na wani seya gaida sauran mutanen É—akin?"
Juyowa yai ya tsurawa Innan ido amma yaƙi magana.
Nana kuwa zuciyarta se dukan bakwai bakwai take, tana fargabar kar ya gano waitar da tai masa.
Ana haka sega Mother ta fito, akan Sadik ta fara sauke idonta tace "Sadik har ka tashi da safen nan haka?"
Inna ta kalli Mother, kusan ƙarfe goma na safe, amma tana kiran har ya tashi da safen nan.
Sadik cikin shagwaɓa yace "Mother, ina wandona?"
"Wane wandon?" Ta tambayeshi cikin rashin fahimta.
"Wanda Khairat ta baki ko ajiyemin" ya bata amsa.
Mother tace "A'a ba ta bani komai in ajiye maka ba, ni yaushe rabon da in sa Khairat a idona ma?"
Sadik yace "jiya fa nace za'a kawomin saƙo ta karɓa ta baki ko ajiyemin"
"To ni ba ta bani ba, kuje can ku ƙarata"
Sadik ya É—an fesar da iska daga bakinsa yace "yau a nan gidan ta kwana?"
"A'a a gidansu ta kwana, amma nasan anjima kaÉ—an zasu zo"
Be ce komai ba ya jinjina kai ya bar falon.
Inna ta É—ago ta kallesu kawai ta girgiza kai.
Nana kam cikinta ya fara É—urar ruwa, dan idan Asirinta ya tonu ta shiga uku.
Nan ta ga sam ba ta kyauta abun da tayi ɗin, be kamata ace tayi haka ba, duk da a ƙule take da Sadik da Khairat tayi hakan ne dan huce takaicin wulaƙancin da suke mata, amma kuma se taji gaba ɗaya ba ta kyauta ba.
Wajen ƙarfe sha ɗaya Khairat suka zo gidan, ita da 'yan gidansu, se iyayin yawon karɓar ɗinki da zuwa gurin Saloon take yi, gaba ɗaya ta manta da batun ajiyar Sadik.
Kamar an jefo shi se ga shi ya kuma dawowa, ya tarar da Khairat É—in a falo, ita da wasu 'yan uwansu zasu koma gurin tela, Mother na musu sautu.
"Malama ina kayana?" Shine abunda yace da Khairat ba tare da ya kula kowa ba.
Tana ganinsa gabanta ya faÉ—i, dan gaba É—aya ta manta, se kuma ta ga kamar ta bawa Mother ai.
"Na bawa Mother tun jiya"
"Na tambayi Mother ai, tace baki ba ta ba, ina kika ajiyemin kayana?"
Mother tace "Ni baki bani komai ba"
Nan Khairat ta shiga wulƙita idanu, dan gaba ɗaya ta manta da batun wandon nan ta shiga sabgar ta.
Cikin zafin rai Sadik ya daka mata tsawa "ina wandona malama?, ina miki magana amma kin tsaya kallo na"
"Am..wallahi Sadik ni kamar Mother na.."
"Dalla rufemin baki, wallahi sekin nemo min abuna, daga cewa ki karɓi abun ki bawa Mother ta ajiyemin seki ɓatarmin, a haraba fa naga ledar kamfanin wandon tana yawo, duk in da yake ki nemo min abuna na gaya miki"
Duk Wannan bala'in a gaban babar Khairat É—in Sadik ke zazzaga mata, ba ta ido ba Komai haka ya rintse ido yana masifa.
Mother tace "Kai dai ka cika rashin haƙuri, Khairat kiyi tunani ina kika ajiye masa?"
Khairat da idonta ya cika da ƙwalla tace "I can't remember, na zata na baki ne, kuma yan...
"Wallahi sekin nemo min, na gaya miki gobe in Allah ya kaimu zanyi amfani da shi, ki nemomin kayana kawai, careless girl"
Nana kam se hailala da salati take, kar a ɗago wannan ɓarnar da tayi.
Sadik kam yana uban huci, haka ya bar falon.
Mother tace "ohh ni Hauwa'u Allah ya shirya min Auta, Khairat kiyi ƙoƙarin tuna in da kika ajiye masa wandon nan dan Allah kar ya zo ya kuma ɗaga mana hankali.
Jiki a sanyaye Khairat tace "wallahi Mother na zaci na baki ne, wallahi na manta yadda nai da wandon"
Sadik na fita yaci karo da abu akan baranda, abunda ya É—au hankalin sa shine tambarin kamfanin wandon fa yai siyayya.
Tsayawa yai, yasa hannu ya ɗago wandon, aikuwa Tabbas shine, ya yi duƙun duƙun, da alama anyi goge goge da shi ha baƙin tukunya a jiki.
Wani abune ya soki ƙirjin sa, nan da nan jikinsa ya ɗau rawa.
A fusace ya koma falon yana wani irin huci, yana shiga ya jefawa Khairat wandon a jikinta.
Da sauri ta kauce, kasancewar yadda wandon ya koma tsumma, ya fita da ga hayyacin sa.
"Wannan shine abun da na baki ajiya, aka mayar da shi haka ko?"
Mother tace "ba dai wannan ne wandon ba?"
Tabbas shine, amma ya akai haka ta faru ya koma haka.
Cikin kuka Khairat tace "wallahi ban san yadda akayi ya zama haka ba, nasan a cikin ledar sa yake.
Mother ta É—aga wandon, ba shi da maraba da tsumma.
Inna da tun É—azu ba ta tanka ba se yanzu tace "Wannan ai tsumma ne, shine wandon da ake ta rigima a kai?"
Talatu me aiki tace "Ai wandon sabone"
Inna tace "wannan É—in, amma na ganshi duk a yayyage? Ya za'ai sabon Wando a yage haka kamar na mahaukaci"
Duk da halin da Nana ke ciki na regeretin, se da tai dariya jin abunda Inna tace, duk yadda ta so riƙe dariyar ta kasa, ta miƙe ta bar falon tana darawa.
Sadik kuwa ji yai tamkar zuciyarsa ta tsaga ƙirjinsa ta fito.
Mummy tace "Khairat baki kyauta ba gasky, careless É—in ki yayi yawa, nawane wandon Ni se in biya kuÉ—in wandon?"
Wata uwar harara ya gallawa ƙanwar mahaifiyar tasa yai waje yana fidda numfashi.
Inna ta girgiza kai, ganin yadda suke ta wani lallaɓa shi yana fizgar kai, sam ba ɗa'a.
Ita kuwa Khairat fashewa ta sake yi da kuka.
Mother ta janyota tana rarrashin ta, suna mamakin yadda a lamarin ya faru.
Farhan kam abun duniya ya hanata sukuni.
Tunda taji zancen Sunusi ko Abincin kirki ba ta iya ci, bacci ma gagararta yake yi, saboda tsabar damuwa.
Ba ta san meyasa iyayenta haryanzu suke rayuwar mutanen da ba, meze sa kawai ai mata miji ba tare da neman yardatta ba, shikenan an mata shamaki da kawo kowa tace ta na so.
"Yaya tunanin me kike ne?"
Muryar cousin É—inta Huzaifa taji, wanda ya dawo da ita daga dogon tunanin da ta tafi.
Murmushi ta yi tace "ba abunda nake tunani"
Ya kalleta yace "ba wani nan, kin san tun yaushe na shigo, ina ta magana kinyi shiru, na shigo Umma ma bata nan"
Farhan tace "Kaga ni ba wannan ba, dan Allah wayarka da kuÉ—i a ciki?"
"Eh da kuÉ—i, amma ba yawa me zaki da ita?"
"Waya zanyi yanzu zan baka"
Ya sa hannu a aljihunsa, ya ciro wayar duk screen ɗin wayar ya tsatsage, wayar ta sha jiki, ya miƙa mata yace "kuma ki ka cinyemin kuɗi sekin biyani, minti ɗaya da rabi na baki"
Murmushi tai tace "godiya nake gwani Huzaifa"
Abba na son a kirashi gwani, saboda a duniya ba shi da burin da ya wuce haddace Alqur'ani.
Yace "kai kin sa naji daÉ—i sosai, in Allah ya yadda se na wuce ki a hadda"
Farhan tace "bari fa, na riga na wuce ka"
Murmushi yai ya fita yana faÉ—in, 'aikuwa zan baki mamaki"
Bayan ya fita, ta fito tsakar gida ta duba, ta ga Umma bata nan ta fita.
A hankali take tafiya kamar mara gaskiya, ta je ta duba É—akin Abba ta tarar yana bacci, ta koma É—akinta ta kulle ta saka sakata.
Litattafanta ta zazzage, ta É—akko lambar Sadik, jikinta na rawa saboda rashin sabo, gani take kamar ana kallonta.
Jiki na rawa ta kwafi lambar ta sa, ta danna kira.
Sadik na kwance ya yi ruf da ciki, zuciyarsa na ta tafasa akan asarar da Khairat tai masa, wayarsa ta hau ringing.
Wani dogon tsaki ya ja ya É—auke kansa da ga kallon wayar.