Sashe 41
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P. W. A
*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
Writer of
WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)
_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_
âš ï¸âš ï¸âš ï¸Æ˜IRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA âŒâŒâ€¼ï¸
  Â
SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.Â
 Â
             29
Bayansa Farhan ta bi da kallo, ta na shakkar bijirewa abunda ya ke so, da kuma hatsarin aikata wani abu ba da izini ko sanin iyayenta ba.
Muryar Lilly ce ta dawo da ita hankalinta.
"Haka kurum, zaki mana sagegeduwa, ai nasan in dai ya sani akwai shagali na gasken gaske, dan Prince akwai son harkar girma"
Ita dai Farhan ba tace uffan ba, se tsunduma kogin tunani da tai.
Haseena kam tsaki ta ja, dan ta tsani duk wani abu da ya danganci Farhan, haushin ta take ji nesa ba kusa ba.
"Fatima Hakeem Yola, lambarki ta fito" cewar class captain É—in su Farhan.
Lilly tace "lambata ta fito a ina? Me nayi?"
"Sir Nazir ke nemanki"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, kashina ya bushe nasani"
Kwashewa da dariya Yasmin tai tace "kaga 'yar iskar ƙarya, ke da kike cewa zaki dinga abun da zaki ɗaga masaa hankali, se kuma gashi kin tsure dan ance yana kiran ki"
Hararta Lilly tai tace "ke dalla ƙyaleni, ni mutumin nan wasu lokutan tsoro yake bani wallahi, gashi jarababbe"
Class rep yace "to yanzu zaki je ne ko kuwa?"
MurguÉ—a baki tai tace "wallahi ba zani ba"
"Au ba zaki ba, idan ya zo ya ritsaki fa?"
"Wallahi ba zanje ba, fecewa zan gida, sedai komai za'ayi ayi, haka kurum"
Suka dinga yiwa Lilly dariya, ta É—auki jakarta ta bar ajin gaba É—aya.
Ko da aka tashi daga Makaranta, ba wanda ya nemi wani a tsakanin Sadik da Farhan, sedai ta tafi gida tana ta zullumin abunda Sadik É—in ke shirin yi, tana tsoron iyayenta su gano, bata san wani irin hukunci zata iya fuskanta ba.
"Nana wai shirin me kike yi ne haka?"
"Inna kin manta ne, babar 'yar ajinmu ce fa ta haihu yau suna, nace miki zamuje, bana tambayeki ba kika ce kin barni ba?"
Inna tace "ai na manta ne, kuma baki tunamin ba, se ganin ki nai kina shiri kawai dole in tambaya ai"
"Ai na gayamiki kin manta ne"
Inna tace "Allah ya taimaka"
Nana ta cigaba da shafe shafen hodarta tana shiryawa.
Inna na aiki a tsakar gida, sega ƙawayen Nana sunyi sallama.
Inna ta amsa musu tana ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya. Daga bisani tai musu nuni da ɗakin da Nana take.
Kai tsaye suka nufi É—akin suka shiga.
"Ahh su Nana 'yan mata irin wannan ado haka?"
Nana tai fari da ido tace "to a garin nan idan ban ado ba waze yi?"
"A'a ba wanda zeyi ta Jamilu ba da kanki a sare, ai idan muka wuce ta hanyar gidan me unguwa ya ganki seya rikirkice"
"Wallahi kuwa, dan mun haɗu ɗazu na kai niƙa yace min ina Nana? Nace masa kina gida amma da yamma ta layinsu zamu wuce zamu suna, ina ga ma yana nan a bakin layin yana jiran mu"
Nana tace "ke Hannatu, kama kanki, ni ba sa'ar wannan yaron bace"
Hannatu tace "ke! Jamilun ne yaro?"
"Eh mana ban da ya rainawa kansa hankali ni zece yana so?"
"Ke Nana shikenan kowa yana da saurayi amma banda ke?"
Nana tace "To Alawiyya meye dan bani da saurayi? Ke nifa wallahi É—an Birni zan aura insha Allah, amma se nayi karatu me yawa, in auri saurayi É—an gayu É—an birni"
Hannatu tace "eh lallai kin É—akko da zafi, ko da yake kuna da 'yan uwa a Birni ai"
Alawiyya tace "Amma ki tsaya ku gaisa da shi, kinga ba daɗi wulaƙanci"
ÆŠan shiru Nana tai tana tunani, dan harga Allah ta na son taji ance ita ma ta na da suarayi, ta na son sanin me ake ji a soyayyar idan ana zance me ake cewa?"
Ba ta kuma cewa komai ba ta tashi, ta ƙarasa shirinta suka fito tsakar gida.
Nana tace "Inna zamu tafi?"
Inna ta kalleta tace "zaku tafi ina kenan?"
"Haba Inna, É—azu fa nace miki ga inda zamu"
Inna ta ƙare musu kallo tace "ba inda zaki"
Saroro Nana tai tana kallon Inna, Cikin rawar murya Nana tace "Inna meyasa? Na tambayeki fa kince kin barni"
"Yanzu kuma nace ba zaki ba"
Ƙwalla ta taru a idon Nana tace "Inna meyasa ba zani ba?"
"Saboda na isa, kin wuce kin ban guri ko senai fatali da ke a gurin nan? Ku kuma maza ku kama hanya ku tafi"
Sumi sumi suka nufi hanyar fita daga gidan.
Nana kam da gudu ta bar tsakar gidan tana kuka, ta rasa wace irin rayuwar takura ce haka, wasu lokutan gani take kamar Inna ba ta ƙaunarta Saboda yadda take takuramata, da hanata sakewa.
Su Alawiyya na fita suka fara gulmar Inna.
"Taɓ Hannatu, dama haka kakar Nanan take, wannan mata anyi jarababbiya, ji yadda ta koremu"
"Hmm kedai bari, shiyasa Nanan ma gata nan jarababbiya, wallahi idan nice ba zan yadda da wannan abun ba, ai kakata ce ba uwata ba"
"Wallahi kuwa balle kuma ni"
Suka tafi suna cigaba da tattauna maganganun su.
Nana da mayafinta, da jakarta da takalmin ta duk a tsakar É—akin ta watsar da su tana kuka.
Inna ta shigo ɗakin, ta kalli kayan da ta watsar ɗin, ta kalli in da Nana ta dunƙule ta na kuka tace "dan ubanki zaki tashi ki kwashe wannan kayan da kika zubar ko sena saɓa miki? Ni zan miki Magana ki min zuciya ki zubarmin da kaya a tsakar ɗaki, kiyi kukan jini ma tashi daga gurin nan ko in haɗa miki jikinki yanzun nan, mara ɗa'a kawai"
Nana tana share hawaye, ta miƙe ta shiga tattare kayan da ta zubar ta maida su mahallin su, ta cire kayan jikinta, ta ɗakko masu datti ta saka dan ita ma ta ɓatawa Inna rai, ta ɗakko hijjabi ta saka, ta tafi turakar Hakimi tai kwanciyarta.
Inna tai banza da ita bata tanka mata ba, ta cigaba da hidimomin ta.
Ko Abinci dare Nana ta ƙi ci, Inna kuma ba ta takurata taci ba.
A haka Hakimi ya dawo ya tarar da Nana, taci kukanta ta godewa Allah, tana kwance tai shiru a É—akinsa.
"Subhanallah shalelen ba lafiya ne?" Yai Maganar yana taɓa goshinta.
Girgiza masa kai tayi alamar a'a.
"To meyafaru?"
"Inna ce" tai maganar tana fashewa da kuka.
"Me Innar tai miki?" Kasa Magana Nana tayi, se cigaba da kukanta da tai"
Hakimi yace "shikenan, ya isa dena kukan haka share hawayen.
Suna cikin haka Inna ta shigo É—akin, É—auke da kwanukan kayan Abinci.
Kallo É—aya tai musu, ba tace komai ba ta ajiye ta cigaba da harkokin ta, yasa Nana a gaba suka ci Abincin su tare.
Seda ya tabattar ta ƙoshi, sannan yai mata umarnin taje tai sallar isha'i ta kwanta.
Hakimi ya saba da irin wannan rigimar ta Nana da kakarta, dan haka be takura akan se ya san meya haÉ—a su ba.
Har washegari Nana ta shirya za ta tafi makaranta, amma ba ta wani shiga sabgar Inna, saboda a ganin ta ta gama dizga ta a gaban ƙawayenta.
Tun da Lilly tai ido huÉ—u da Sir Nazir a gurin Assmebly gabanta yai mummunar faÉ—uwa, dan tasan tai masa laifi gagarumi, Allah kaÉ—ai yasan yadda ze da ita.
Ga mamakinta ko kallonta be sake yi ba, balle yai mata Magana ya shareta.
Ita ma share shin tayi, sedai ƙirjinta na ta dukan uku uku.
Aka watse daga gurin Assembly, suka nufi classes É—in su.
Farhan na tafe sannu a hankali, taji an riƙo hannunta ta baya, cikin hanzari ta waiwaya zaton ta Sadik ne, se dai ba kamar yadda tai tsammani bane.
Salma ce ƙawar Nasreen wanda suke a Ss3, wanda ta gansu tare da su Nasreen ɗin ranar da Nasreen ɗin tai ɓari.
Murmushi taiwa Farhan tace "Farhan ko?"
Farhan ta jinjina mata kai alamar eh.
"Dan Allah in ba zaki damu ba, ina son ki zama sister na a school ɗin nan, if you won't mind"
Saroro Farhan tai tana kallon Salma.
"Anyway, idan an fita break ki zo Class É—in mu ina son ganinki please"
Farhan ta jinjina mata kai, ta juya ta tafi tana tunanin ita kuma wannan meye haÉ—insu, da zata wani ce ta na so ta zama sister É—in ta?.
A ɗarare Farhan take gudanar da al'amuranta na yau, kasancewar ta na cikin period ne, wanda wannan shine karonta na biyu da farawa, gaba ɗaya ta kasa sakin jikinta, ga shi ƙasan cikin ta na ɗan mata ciwo kaɗan kaɗan, wani lokacin kuma ya ɗan tsananta takura mata.
Ga wata uwar kasala da ke damunta, babban abunda yake ɗaga mata hankali be wuce yadda take jin ƙirjinta wani iri ba, zafi zafi ciwo ciwo, ba ta san wa zata gayawa ba, tafi tunanin ko Cancer ce ta kamata, gaba ɗaya ta kasa gane kanta.
Ana musu lesson amma zuciyarta fal tunani daban daban, a ranta take addu'a idan mutuwa za tai Allah ya nuna mata ta auri Sadik kan ta mutu.
Har aka fita break tana wannan tunane tunanen.