← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 48

Sashe 14

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ya cinma ta tuni ta arta a na kare, kamar walƙiyya ta bar falon da gudu, ya bi bayanta sedai yana fitowa ya neme ta ya rasa kamar aljana, se kace iska ta kwashi takadda, ba ita ba alamarta.

Ya ja tsaki ya koma ɗakin, yana ƙoƙarin tuna in da ya taɓa ganin fuskarta.

Ganin hakan ba ze fushsheshi ba yasa ya shige bedroom É—insa yana tsaki, gami da jin haushin bikin nan na Yayansa, dalilin wannan bikin da yayime yayimen mutane ake a gidan, masu hankali, sekace akansa aka fara Aure.

Haka yana ƙunƙuni yana mita, ya cire kayan makarantar sa ya shiga yai wanka, ya fito yai sallar azahar, yana son shiga cikin gidan cin Abinci, amma ganin taron jama'a da ke gidan ya hanashi shiga, dan baya son taro sam.

Ya É—akko tsaleliyar wayarsa ya nemo lambar Khairat ya kirata.

Tana fara ringing ta É—aga tace "ya akayi?"

Seda ya É—an yatsuna fuska sannan yace "kina gidanmu ne?"

"Eh ina nan"

"Suwaye a cikin falon nan?"

Khairat tace "ji wata Magana, ta yaya zan iya lissafo maka wanda suke falon, mutane ne da yawa gasu nan a gidan"

"Wani taimako nake son kiyi min"

"Ok am all ears"

"Abinci na zaki kawomin BQ"

Kamar Sadik na gabanta ta É—an murguÉ—a baki tace "meya hana kazo ka É—auka da kanka?"

"Nifa kin san taron mutanen nan ne bana so, in ba zaki kawomin ba shikenan"

"Zan kawo maka ba dan halinka ba"

"In dan halin nawane karki kawomin, bana son wulaƙanci fa"

"Meye wani abun wulaƙanci kuma? Ina zaman zamana ka sani aiki"

Tsaki yayi ya kashe wayar ya ajiye yace "Aikin banza ayi a gama wannan bikin ya tafi ya bawa mutane guri, ko ma huta da wannan jarabar, kullum gida a cike mutum baze huta ba, Aikin banza kawai"

Se mita yake shikaÉ—ai, haka nan ya tuno Nana da ta zage shi É—azu a falo.

Wani dogon tsakin ya kumayi, ya ji ina ma ya kama Nana, da se ya kusa karyata, seya tataka ta ya koya nata hankali, daƙiƙiyar yarinya fusaka kamar ta yaron aljani.

ShikaÉ—ai ya cigaba da soki burutsunsa, yana zage zage.

Khairat tai sallama ta shigo bedroom É—in, ta kalleshi tace "lafiya kake tsaki kai kaÉ—ai, tun daga falo ana jiyoka kana masifa ciki ciki"

"Bakomai" ya bata amsa.

"Kai faÉ—an naka ya kai ka dinga yi kai ka É—ai ma a É—aki, sekace me aljanu?"

"Ke kika sani miƙomin Abinci na ni"

"Au in maka abun arziki amma ba godiya, se gadara da isa ko, wallahi ka canza hali Sadik, wannan ba halin shiga jama'a bane"

"Ina ruwana da wata jama'a, kawai an takurawa mutane, mutum da gidansu anzo an hanaka sakewa, wai ma dan Allah suwaye yau kuma a gidan nan, dan ni wata mahaukaciya ce ta shigo min É—aki yau"

Dariya Khairat tayi tace "wace irin mahaukaciya kuma? Gaskiya duk baƙin Gidan nan banga Mahaukaciya ba"

"Ni na ganta ai"

"Gaskiya ba wata mahaukaciya, Kakar ka ce fa tazo da 'yan ƙauyen ku za'akai lefen Dr."

"What!" Sadik ya faÉ—a yana yatsuna fuska.

" 'yan ƙauye kuma Farhan?"

Cikin mamaki Khairat tace "Farhan kuma? Ka manta sunan nawa ne?"

"Ohh sorry, Khairat nake so ince, meye haɗin 'yan ƙauye da kuma kai lefe? Kai Allah ya sa dai yau wannan tsohuwar zata tafi"

Khairat tace "kakar taku?"

"Ita ɗin mana, tsohuwar nan jarababbiya ce ta ƙarshe wallahi, faɗan tsiya ne da ita ga takurar masifa da sa ido, ni shiyasa ko ƙauyen nan bana zuwa, dama am allergic to the water of the village, ke nifa Even iskar garin nan is irritating me, Abincinsu ma ƙyama yake bani, sam bana zuwa garin nan"

"Taɓ aikuwa tace tana gidan nan har ayi bikin dr."

"Kut, wallahi Farhan barin gidan nan zanyi, ina zan iya da tashin hankali da takura?"

"Farhan again?"

"Ohh sorry, ke nifa Farhan ce a zuciyata da kuma harshena, shiyasa nake kiranki da sunanta"

ÆŠan haÉ—e fuska Khairat tayi tace "wace kuma Farhan?"

"Sirikar mother ce, ana auren dr. Se nawa da Farhan Yarinya"

"Aure kuma Sadik, waze maka Aure Yanzu?"

"Ke dalla ban isa auren bane, ke tashi ki ban guri ma kin sani a gaba, zanci Abinci"

"To ni meye haÉ—ina da cin Abincin ka?"

"Zaki tashi ki barmin É—aki ko sena ji miki ciwo"

Ta miƙe tace "kana cewa kakarka masifaffaiya, ai kaima masifaffaen ne da be san abun arziki ba, kuma gobe ma rana ce"

Share Khairat yai ya zuba Abincinsa ya fara ci.

Yaci ya ƙoshi ya miƙe tsam, ya haye gadonsa ya fara chatting, tunani yake ina ma Farhan ta na da waya, da ya kirata ya ji muryarta yaji daɗi.

Faruku na shiga falo, ya tarar da Inna ga Daddy da Usman duk a zaune a falon, dam be san da zuwansu ba, ya ƙarasa gaban Inna yace "Sannu da zuwa"

Ta É—aga kai ta kalleshi tace "Sannunka, ba'a ganinku se anzo inda kuke ko Faruku?"

Ya É—an shafi sumarsa yace "ba haka bane Inna, ya Hakimi yana lafiya?"

"Yana lafiya, sedai yana mitar baya ganinku"

"Abubuwa ne suka É—anyi yawa amma insha Allah muna nan tafe"

Inna tace "yadda ka tara wannan gemun ai kyawunta ace kaima da naka auren za'a haÉ—a"

Daddy yace "haba Inna, guda nawa Faruk ɗin yake? Dan ya tara gemu yarone ƙarami kawai abunsu ne na yaran zamani ya tara wannan uban gemun, amma haryanzu be kammala karatu ba"

"Haka dai, boko boko boko, to boko yana hana Aure ne, in dai yaro yana da yadda zeyi, ku dena yiwa 'ya'yanku kallon yara fa, zamanin nan se addu'a kawai"

Ran Mother ya fara ɓaci ds Inna, a ranta tace "da yake kowa irinku ne, Aure, Aure, da yaro ya fara tasawa besan komai ba se a hau Aure, se tara 'ya'ya nan da nan mutum yabi ya lalace ya tsofe da wuri, saboda ku dai Jima'i shikaɗai mutumin ƙauye ya sani" ta ja gajeren tsaki ta bar falon.

Inna tace "Ni haryanzu banga É—aya yaron naka ba Abdullahi"

Daddy yace "ina ga be dawo daga makaranta bane"

"Aikuwa dai ina son in ganshi dan rabona da shi na manta"

Daddy yace "a daiyi haƙuri ranki ya daɗe"

"Sadik! Sadik!"

Ya jiyo muryar Faruk na kiransa tun daga falo, tsaki Sadik yayi yace "sekace be san in da nake ba yake min wannan kiran daga waje"

Yai banza ya cigaba da danna wayarsa.

Faruk ya shigo bedroom É—in yace "kana ji ina kiranka amma kai min banza?"

Sadik yace "na amsa ba ka ji bane kawai"

"Kaje Inna tazo, tana neman ka kaje ka gaisheta"

Yatsuna fuska yayi yace "tana nemana kuma? Me nayi?"

"Se kayi wani abun tukuna? Kajeka gaisheta"

"Nifa yanzu na dawo daga school gaskiya na gaji, Yanzu ina zuwa zata fara ƙaƙalen abunda za tai faɗa a kai, dama ni ba ta sona wannan tsohuwar, kawai ka ƙyaleni"

"In baka je ba, kaga ta ji daÉ—in hucewa akan Mother, tace ita ke sangarta ka"

Tura baki Sadik yayi ya juya baya, dan karma ya cigaba da jin abunda Faruk ze faÉ—a.

Se bayan la'asar sannan aka kai kayan lefen nan gidansu Yarinyar da Usman ze aura, iyayenta duk da kasancewa suma masu abun hannu ne, amma sunyi murna sosai sunyi appreciating kayan da aka kawowa 'yar ta su na lefe.

Daga nan gurin kai kayan 'yan uwan su Daddy na ƙauye aka maida su, aka dawo da Inna da sauran ƙawayen Mother gida.

Sadik kuwa be fito ba se bayan la'asar, ya fita ya silale ya bar gidan, ya tafi nasa yawon.

Ɗaki aka bawa Inna ita da Nana a falon ƙasa, ɗakin ba laifi babba ne, da banɗakin sa a ciki, ga gado da katifa a ɗakin, se ƙaramar sif ta kaya.
Nana nata faman taka tsantsan akan abunda za tayi, dan kar tayi abunda Inna zata mata tijara a cikin mutane, dan ita Inna ba ruwanta koba gaban waye idan tai ba dai dai ba faÉ—a za tai mata.

Sadik kuwa Be dawo ba se dare, lokacin kowa ya kwanta, sannan ya shiga falo ya wuce Kitchen, ya É—akko Abincin sa ya koma BQ.

Ita kanta Mother ba ta ji daÉ—in zaman Inna a gidan nan wai se biki ba, dan sam bata son sa ido irin na Inna.

Mother na ta zuba ido taga É—an auta, amma sam auta be shigo Gidan nan ba, tasan dama ba lallai ya shigo ba saboda mutane da ke gidan.

Dan haka da safe tai niyyar zuwa ta ganshi kafin ya tafi Makaranta.

Nana kuwa ba ta gajiya da ƙarewa gidan nan kallo, saboda tsaruwar gidan ba ƙaramin burgeta yake ba, tana sha'awar cigaba da zagawa da ganin in da ba ta shiga ba ta gani, sedai tana tuno arangamar da su kai da Sadik tai tsaki tace "Aikin banza kawai, Allah yasa kar in kuma haɗuwa da wannan sakaran, idan na kuma ganinsa kuwa nima sena masa rashin mutunci"

Gari ya fara haske, Inna tana can tana laziminta, Nana ta lallaɓa ta fito, masu aiki se kaiwa suke suna komowa, suna ƙoƙarin tsaftace gidan, Suna ta ƙoƙarin gyara komai, Mother na fitowa suka fara ƙoƙarin gaisheta, amma se wani shan ƙamshi take tana amsawa da ƙyar tana cigaba da basu umarni.

Ɓangaren Daddy ta nufa, tarara ya tashi, ya kalleta yace "good morning sweetie"

"Morning dear, ka tashi lafiya?"

Kamar ƙaramin yaro ya ɗan ɓata fuska yace "not that fine, kin gujeni mun dena kwana tare"

"Mutane na kaiwa na komowa, kawai a ganni a É—akinka ga mahaifiyar ka a gidan nan"

"Ina ruwan Inna damu, ai ita ba ruwanta damu, yakamata kije ku gaisa, ni naje na gaisheta kuma tana mitar Sadik be zo ya gaida ita ba"

Mother tace "ai kasan halin É—an naka, shifa mutane ne ba ya so, ni kaina ban ganshi ba tun jiya, yanzu nake sa ran zuwa in dubi shi ma, zan sa yazo ya gaisheta"

"Ai gara yazo su gaisa, kar ranta ya ɓaci"

A ranta tace "jarababbiyar tsohuwa ba, yanzu se ta samu a gaba da É—ana da surutu" amma a zahiri tace "insha Allah zan tura shi, me zan dafa maka ne?"
Chapter 14 · 0% Book details