← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 48

Sashe 47

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mafita ɗaya ce, ke dama ɗabi'arki ce zama da English wears kullum kamar 'yar turawa, tunda he's no more appropriating ita, ki koma masa ƙabilarki ta Hausa Fulani, ki duba kayan lefenki ki dinga masa wankan atamfa da leshi, idan yaso ki dinga saka English wears ɗin lokaci zuwa lokaci, Sannan shaƙuwar da ku kai a waje kar ta sa ki dinga kallonsa kamar mate ɗinki, ko ki dinga masa magana ba wani respect, no matter how close you are to each other, he deserves a respect from you shi namiji namji ne, ki dena wannan maganar taki cikin gadara, ki fara da jarraba wannan mu gani, se muga meye next abun yi"

"Ka besty i love You lodi lodi, ina yinki Sisyna, insha Allah zan jarraba Allah yasa a dace"

"Ameen Allah ya daidaita, kice ina gaishe shi"

"To zeji insha Allah"

Jidda ta fara tunanin maganganun bestyn ta, wato duk abun nan da suke a school suna ganin wayewa ce ashe yana da negative impact a gaba? Dama duk abun nan da take dan burge Usman kuma a kirata wayayyiya ze zo ya dena burgeshi? In Kuwa hakane Lallai a rayuwar ƙuruciya ana tafka shiirmen da ze zo ya zamewa mutum abun dana sani a gaba.

Daga Sadik har Farhan sukuku su kai Weekends É—in, damuwar Sadik É—aya kukan da suka rabu tana yi, ya dimga fatan Allah yasa karta rabu da shi a dalilin abunda ya faru.
Sedai baze iya misalta zallar nishaɗin da tsananin shauƙin soyayyar da ya shiga ba, a lokacin da yake sumbutar Farhan, wani abu ya dinga ji from no where yana ratsa ilahirin jikinsa, dan gaba ɗaya mantawa yai da batun wani ƙyanƙyami ko wani abu me kama da haka, hakan ya ƙara kwaɗaita masa son Auren Farhan, sabida wani irin sonta da ya ƙara shigarsa.
Amma ba ya jin ze kuma yadda ya aikata makamancin wannan kuskuren, dan shi kansa yayi nadamar biyewa su Nas ya aikata abunda be taɓa aikatawa ba a rayuwar sa.

Duk yadda ta so jin tsanar Sadik a ranta saboda abunda yai mata amma abu ya gagara, sam ba taji ta tsane shi a zuciyarta ba, mussaman idan tai la'akari da shima be san abunda su Nas suka shirya ba, sedai a jikinta tana jin abunda suka aikata ɗin ba daidai bane, kuma kasancewar sun aikata a gaban mutane, ba za'a taɓa dena kallon su da abun ba.

Ba zata iya misalta yanayin da ta shiga a lokacin da abun ya faru ba, dan Tamkar a mafarki haka ta dinga ganin lamarin, kuma ta kasa tantance halinda ta shiga, saboda taji wani abu da jikinta be taɓa bata ba a tsawon rayuwarta se a wannan karon da abunda ya faru ya faru, lokaci lokaci idan ta tuna abunda ya farun ta kanji ta tsani komai, sedai ƙarƙashin zuciyarta na hasaso mata wani yanayi ne me wuyar mantawa.

Ranar Monday kuwa Sadik shirin Makaranta yake, amma cike da zullumin yadda ze tunkari Farhan ta saurare shi.
Itama nata ɓangaren tunanin yadda zata shiga makarantar take tayi ido huɗu da wanda akai abun a gabansu, dan tana ji a jikinta ta rasa wata kima da daraja da take da ita a idon wasu daga cikin abokan karatun nata.
Jibtaka tamkar ta fasa zuwa makarantar, amma idan ta fasa tasan se a tambayi ba'asin hakan, dan haka jiki a sanyaye take aiwatar da shirin makarantar.

Seda aka gama Assembly sannan ta shiga makarantar, ta wuce ajinsu tana sussunkuyar da kai, duk wanda suka je gurin tsirarun mutane ne, dan a 'yan ajinsu Lilly ce kawai taje se wasu daga 'yan ajinsu Sadik se Khairat, du du du ba su fi su goma ba, amma gaba É—aya ta rasa sukuni.

Sadik na shiga ajinsu suka hau yi masa ihu da shewa.

Be kula su ba yaje ya nemi guri ya zauna a mazauninsa, Nas da Amin sukaje suka zauna kusa da shi, Nas yace "Mazaa, ya ake ciki ne? Munyi ta kiran wayarka ba ta shiga, kuma ka barmu a gurin partyn ba ka dawo ba, ya kaji abun?"

Sadik ya É—ago idanunsa ya kalli Nas, kallon da Nas É—in ya kasa tantance kallon meye.

Amin yace "wallahi you did it in the most passionate way, naji haushi da ka hana É—aukar hotuna ku bada kala fa"

Nas yace "ai mun tabattar da namiji ne yanzu, yanzu zaka fara soyayyar morewa ba irin wadda kake yi ba da, ta ƙauyanci, nasan ko yanzu ka samu chance you want do it again ko ba haka ba?"

"Shut up!" Sadik ya faɗa da ƙarfi yana dukan benci.

"Dan Allah ku ƙyaleni inji fa abunda ya dameni, ku tashi ku ban guri"

Binsa su kai da kallon mamaki, meke damunsa hakane?

Kasa jurewa yayi, ya tashi ya nufi ajinsu Farhan amma ya tarar Madam Joy na ciki na musu lesson dan haka ya koma ajinsu.

Bayan fitar Madam Joy, Lilly taje in da Farhan ke zama ta zauna a kusa da ita tace "mutuniyar ya gajiyar taro?"

Wata ƙwalla ce ta zowa Farhan, da tuna a gaban Lilly Sadik yai kissing ɗinta, ta san maybe Zuwa yanzu duk ta gama bawa 'yan ajin labari.

Lilly tace "yana ga kamar zaki kuka? Meyafaru?"

Aikuwa maganar Lillyn tasa hawayen da Farhan ke maƙalewa ya gangaro kan kuncinta.

"Yasalam, Farhan menene?"

Cikin kuka Farhan tace "bakomai"

"Bakomai amma kike kuka?"

Farhan ta jinjina mata kai.

Lilly tace "anyway shikenan, bari in ƙyaleki kar in takura miki"

Har Lilly ta miƙe Farhan ta riƙo hannunta, ta dawo ta zauna tace "ya akayi?"

"Fatima dan Allah kin gayawa wani abunda ya faru agurin nan?"

Lilly ta riƙe hannun Farhan tace "i understand you ƙawata, karki damu ni ba wanda na gaywa, ni ba haka nake ba, and is something common in this school, no one will cares, amma duk da haka ni ban gayawa kowa ba, in abunda ya saki kuka kenan ki kwantar da hankalinki"

Farhan ta jinjina kai tace "Nagode sosai"

"Bakomai karki damu"

Ana haka, aka kaɗa jiniyar fita break, Lilly ba ta jira kowa ba ta ɗau littafinta, da kayan ciye ciyenta ta tafi ofishin malam Nazir, fan wata irin ƙishirwar ganinsa ke damunta, tun incident ɗin nan da yafaru, idan har bata sa shi a idonta ba, ba ta jin daɗi.

Kan tai sallama yaji ƙamshin turaren ta "Assalam Alaikum" tai Sallama.

Be É—ago ya kalleta ba ya amsa.

"Good morning Sir"

"Morning how are you?"

"Fine Alhamdilillah"

Ta ja kujerar da ta saba zama ta zauna, ta fara ƙoƙarin kwafar note ɗin ta, so take ko sau ɗaya su haɗa ido, amma yaƙi kallonta aikinsa kawai yake, wanda seda hakan ya ɗan bata haushi.

Sir Nazir kam yana sane yaƙi kallonta, saboda ya kasa gane kansa akan 'yar ƙaramar yarinyar nan.

Yayi rayuwar University cikin manya manyan 'yan manta, yai yawace ywacensa, amma be taɓa cin karo da wadda yake jin wannan bugun zuciyar akanta ba se wannan yarinyar me shegen iyayin tsiya.

Yayi mata kyau sosai, ji take tamkar ta gaya masa yayi kyau, amma tai shiri da bakinta tana tunanin me za tai wanda zesa ya kulata?

Can tai gyaran murya, tare da miƙa hannunta kusa da inda hannunsa yake ta ɗau biro.

ÆŠagowa yai suka haÉ—a ido, ta É—anyi luuu da nata idanun cikin wata irin murya tace masa "Nawa biron ya tsaya, shine na É—auka aron naka"

A hankali ya jane idonsa daga nata, ya cigaba da abunda yake yi.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya kalli wayar sannan yasa hannu ya É—auka ya kai kunnensa.

"Assalam Alaikum" yai Sallama.

Lilly ba ta iya jiyo me ake cewa a wayar amma taji yace "like serious, congratulations my dear, am missing you, very soon zan shigo nima insha Allah"

Ya É—anyi shiru Sannan yace "yadda kike so, idan ta idar ki bata wayar in kwashi gaisuwa"

Tunda ya fara wayar Lilly ta ƙura masa ido harya ƙare, gaba ɗaya Annurin fuskar ta ya ɗauke bata san lokacin da tace "Sir fa wa kake waya?"

"Da ƙaniyarki" ya bata amsa.

Sunkuyar da kai tayi ta cigaba da rubutunta, haka nan taji haushi ya kamata.

Mintuna kaɗan aka sake kiransa ya kuma ɗagawa, cikin wata nustuwa da girmamawa yace "Ina kwana Umma, duk kuna lafiya, ai insha Allah na kusa shigowa, Auta tace min ba ta da carryover a exam ɗinta, baki yaƙi rufuwa"

Murmushnsa ya faÉ—aÉ—a yana shafar gashin kansa yana wayar, wata nustuwa Lilly taji da ta fuskanci da 'yan gidansu yake waya.

Babban abunda ya bata mamaki da kusan dariya be wuce yadda yakewa Mamansa shagwaɓa a wayar ba, se taji ya wani ƙara burgeta sosai da sosai, ta dinga kallon sa tana murmushi.

Yana Ajiye wayar ta kalle shi tace "Sir is she your Mum?"

Ya jinjina mata kai alanar eh.

Tai murmushi tace "Amma Babba da kai kake shagwaɓa"

Murmushi ne ya ƙwace masa ya shafi gemunsa yace "Ai su iyaye ba a girma a gurinsu"

"Eh hakane, amma kai kayi girma da shagwaɓa"

Yace "Allah ko?"

"Eh mana, ai mata ne kawai suke shagwaɓa"

Murmushi yai ya cigaba da dannan System.

"Sir kana da ƙanne mata ne?"

"Eh ina da ƙanne mana, shiyasa bana don inga kuna rashin ji, idan na tuna da ƙanne na, bana jin daɗin ganinku kuja rashin ji, sedai ku kuma ba kwa son ace muku bari"

"Sir ba haka bane ba fa?"

"To yane Fati, ke kanki na san kina jin haushi na saboda hukunta ki da nayi ko?"

Lilly ba zata iya misalta farin cikin da ta shiga ba, kasancewar Sir Nazir yana mata Magana cikin nutsuwa ba hargowa da zare ido.

Ta É—ago idonta ta kalleshi, ta ga shima kallonta yake, ga wani cikar zati da kwarjini da ya sake yi masa ado.

A hankali ta sauke ajiyar zuciya, a ranta tace "ohhh God" ta fara tunanin ko ba duka ba za'a samu Sir Nazir da Mafi rinjayen siffofi da ake kamanta mazan littafi da shi, ba abunda yake tsole mata ido irin sajensa da wannan faffaɗan ƙirjin da yake da shi, she wish to hugs him even once, ta shafa wannan sajensa kamar yadda take karantawa a littafi.

"Fatima ya kira sunanta"
Chapter 47 · 0% Book details