Sashe 2
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya duƙufa seda ya kammala mata class work ɗin, kasancewar yana da yawa , yana kammalawa ya miƙe ya tafi ajinsu Farhan, kamar kullum tana zaune a gefe ɗaya, 'yan ajinsu basa wani shiga harkarta kasancewarta ba 'yar masu kuɗi kamarsu ba, saboda ita scholarship ne ta samu, saboda wani competition da taci, aka bata scholarship ɗin, gata suna ganin bata waye ba kamar su, dan haka basa involving ɗinta a sabgarsu, itama bata musu shishshigi kullum tana gefe, ba ruwanta da kowa se karatunta, sekuma Yanzu da Prince ya shigo rayuwarta.
Duk hayaniyar da ake a ajin, Prince na shiga sukayi tsit, dan juniors suna tsoronsa, saboda akwai dealing, baya son raini sam.
Ya ƙarasa seat ɗinta ya zauna a kusa da ita Yace "Baby gashi na gama miki" yai maganar yana ajiye mata littafin.
Ta sa hannu ta É—auka tana dubawa, ta É—ago tai murmushi tace "Nagode sosai Prince"
Maimakon ya mata magana, seya kashe mata ido É—aya.
Sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya.
Yace "ya kika wani sunkuyar da kai? Ina fatan babu wata matsala dai ko?"
Ta jinjina masa kai alamar eh.
Yace "Ai idan ma akwai matsalr bazaki iya faÉ—a ba, ke naga maganar ma wahala take baki Farhan, nasan maybe yanzu malami ze shigo muku, bari in koma ajinmu, amma kisani zanzo musamman kimin hira, ina son dinga jin muryarki sosai, saboda tana sani nutsuwa"
Ji take kamar ƙasa ta tsage ta nutse dan kunya, gashi ya tsareta da idanunsa, gaba ɗaya nauyinsa take ji.
Corper Nazir ne ya shigo ajin, ɗaliban suka miƙe suna gaisheshi, banda Prince dake zaune, Nazir yabishi da kallo, yana tunanin meya kawo wannan fitsarraren yaron kuma Jss2.
Prince ya miƙe ya kalli Farhan yace
"Mu haÉ—u in an tashi'
Daga nan ya juya ya fice abunsa.
Corper Nazir Yace "Ke Farhan, meye haɗinki da wannan yaron mara ɗa'a?"
Farhan ji tayi kamar Nazir ya soketa, Sadik É—inta ne wai mara É—a'a.
Shiru tayi ba tace komai ba, "Am talking to you Malama" yai maganar cikin tsawa.
Sunkuyar da kai ta sake yi, jikinta na rawa amma ta kasa furta koda kalma É—aya.
Daga can gefe wani ɗalibi yace "sir saurayinta ne"
"Saurayi kamar yaya?"
"Ai duk makarantar nan, babu wanda be san budurwar prince bace, saurayinta ne" cewar É—alibin.
Aikuwa Cikin faɗa Nazir Yace "baki da hankali ne? Kina Jss2 harkinsan wani saurayi? Shi iyayenki suka turo ki yi? Kuma ma wannan shegen yaron mara ɗa'a kike kulawa, zakiga saurayi sena zauna da babanki na gaya masa, come out here and kneel down, stupid girl kawai, zaki ɓata rayuwarki kina jss2 amma kin san wani saurayi"
Gaba É—aya ido ya dawo kan Farhan, ta fito jikinta na rawa, kamar ta nutse tazo gaban class tayi kneel down.
Nazir ya ƙaremata cin mutunci tsaf a gaban 'yan ajinsu, taji zafin abinda malam Nazir ya mata, dan haka nan da nan se ta fara hawaye, wani na bin wani kuka sosai, kamar ƙaramar yarinya.
"Will you shut up your mouth, stupid girl kawai, a haka kamar mutuniyar kirki, kin biyewa wannan sakaran yaron"
Sadik daya koma ajinsu kuwa, ya tarar classmates ɗinsa maza sun haɗa kai suna kallo a waya, matan kuma suma sun ja nasu gurin, suna Magana ƙasaƙasa suna shewa.
Ya ƙarasa ya leƙa abunda su Amin suke kallo, sedai ƙirjinsa ne ya buga da ƙarfi, yaja uban tsakiya ja da baya.
Amin ya ɗago ya kalleshi Yace 'babban yaro ya dai, ku matsa masa yazo ayi dashi mana"
Cikin damuwa ya girgiza Kai Yace "Ni bazan iya kallon wannan shirmen da kuke kallo ba"
Nasir ya kalleshi yace 'ji banza sekace ba namiji ba, wannan ba shirme bane alaji, just come an enjoy"
Sadik ya girgiza Kai Yace "I can't, kuma Allah ya shiryeku, dan ubanku zaku makance da wuri ne, kawai ku kewaye waya kuna kallon blue Film, shegu zakuyi bayani idan Allah ya tona muku asiri"
Amin Yace 'dan Allah malam ƙara gaba, tunda bazaka kalla ba ai shikenan"
Sadik ya samu kujera yai zamansa ya É—akko wayarsa, yana Game.
Seniors ne suka shigo class ɗin Ss2, kansu ɗauke da colored ties, mazan kuma huluna alamun prefects ne, wata zaƙaƙura a cikinsu cikin harshen turanci kamar baturiya tace "who ever knows he spoke vanacular, should come out and pay his 500, before I call names"
Banza sukayi musu, basu ko É—ago kaiba balle su tanka musu.
Nan ta ƙame ta fara kiran sunayen wanda sukayi Hausa, Sadik yana ji aka faɗi sunansa, amma ƙafafunsa na kan benci yana cigaba da game ɗinsa.
Babu sunan kowa a ciki sena Sadik, dama shi duk wata doka a makarantar nan, shine ke fara karyata a makarantar nan.
ÆŠaya daga cikin prefects É—in yace "Sadik, magana fa ake maka"
"Bazan biya ba" ya basu amsa
"You Are still speaking vanacular , you know you must pay' cewar wadda ta kira sunayen.
"Ke wallahi bazan bayar ba, baza'ayi turancin ba, yaren uwatane kona ubana? Ko meye haÉ—ina da wasu turawa da senayi yarensu, har a wani dinga cewa wanda yayi hausa seya biya, baza ai turancin ba, kuma bazan biya ba tunda ba ubankine yake bani kuÉ—in ba"
Dukan benci tayi ta nuna Sadik tace "don't insult me Sadik"
'idan na zagekin me zakiyi? Jeki gayawa duk uban da zaki gayawa, yarene a makarantar nan se wanda naga dama zanyi, bazan turancin ba, uban turancin, ke uban mungo park da sarauniyar England, ƙaryar banza kawai ba za'ai turancin ba"
Fitina sosai Sadik yaso tayarwa, dan da an ƙyaleshi ze iya dukan yarinyar nan.
Wata ɗalibace ta shigo ajin tana faɗin "Prince, ga Farhan can an sata kneeldown a rana, tayi wa wannan corper ɗin laifi, kuma wai tayi vanacular ance ta biya kuɗin vanacular tace "bata da kuɗi".
Ashar Sadik yayi Yace "what! Farhan ɗin?"
Beyi wata wata ba yai waje, hakan yai daidai da shigowar wani malami, da aka sanar masa ana rigima da Prince a ajinsu, ya taho yai maganin abun, sukayi karo da Sadik a hanya, yana masa magana amma yayi masa shiru, ya ture malamin yai hanyar ajinsu Farhan da hanzari.
Baiwar Allah, Farhan tana ƙofar ajinsu tayi kneeldown tana ta zubar da hawaye, ga zafin rana.
Sadik yaji tamkar ya ɗora hannu a kai yai ihu, ya ƙarasa inda take da sauri Yace "waye ya saki wannan abun?"
Kasa magana tayi, se kuka da takeyi beyi wata wata ba, ya jata office É—in director.
Sadik se huci yake, director ya kalleshi Yace "Prince Sadik, what's wrong? Why is she crying?"
"Sir, ka shiga tsakanin mu da wannan new corper É—in, why Will he gave her such kind of punishment, and that stupid Tina humilate her because of 500 naira, is she not a human being?"
Director ya kalli Farhan dake ta faman kuka, idonta yayi jawur, shidai yasan Sadik bashi da alaƙa da Farhan, amma yana gudun ɓacin ran wannan yaron, Yaron fitainanne ne, akwai taurin kai da rashin ji, sedai uwarsa zata iya ɗaure malami akan sa, ana ji da shi a gidansu kamar ɗan gwal, sama baya taɓuwa yarin nan, dan haka Yace "is ok my Boy, zan ɗau matakin daya dace, kayi haƙuri , Farhan kiyi haƙuri kinji"
Farhan dai ba tace komai ba, se kuka da take yi, Sadik yai waje a zuciye tabi bayansa, ya rakata har bakin toilet,yace ta shiga ta wanke fuskarta, ya jirata ta shiga ta fito, ya kalleta YaceÂ
"duk wanda ya kuma saki wani purnishment a makarantar nan, koya miki ba daidai ba kizo ki gayamin kinji ko? Ko "
Ta jinjina masa kai, Yace "Akwai inda yake miki ciwo ne?"
Cikin muryarta me narkar da zuciya tace "kaina yana ciwo, da ƙafata"
"shikenan, muje class É—inmu ki huta in Baki paracetamol"
Ba musu ta bishi, dan bata iya kaucewa umarnin Prince Sadik, ko da wasa bata zaton zata iya kaucewa umarninsa.
Tabbas nickname ɗin nasa na Prince ya dace da shi, saboda gashi Young adult be gaza shekaru goma sha shida zuwa sha bakwai ba, amma yana jida kansa, giyar arzikin iyayensa da tashen balaga na matuƙar ɗawainiya da shi.
Suka je ajinsu, ya bata paracetamol, ta karɓa ta sha, ta kifa kanta akan benci ta lumshe idanunta.
Babu daÉ—ewa, aka kunna jiniya, alamar lokacin tashi yayi.
Farhan ta tashi, Sadik yaje class É—insu Farhan ya É—akko mata jakarta, suka fito harabar makarantar, inda dandazon motoci suke taruwa, domin É—aukar yaran gata.
Farhan tace "bani Jakar, zanje in hau napep in tafi gida"
"No ga motar gidanmu nan, muje semu saukeki a gida, kinga baki da lafiya"
A ɗan tsorace tace "za'ayi min faɗa fa a gida, idan aka ganni a motar ku"
"Karki damu, ba wanda ze miki komai"
Haka yasa ta shiga motar, shima ya shiga, ta gayawa direban inda gidansu yake, suna tafe Sadik yana jera mata sannu, Tare Da yin ƙwafa lokaci zuwa lokaci.
Aka zo bakin layin gidansu Farhan, ta kalli Sadik tace "Nagode sosai Prince"
"Ki kirani da suna irin na masoya mana, haba my Farhan" yai maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai tata.
Rufe fuskarta tayi cike da jin kunya, yace "idan baki faɗa ba, zamu yi ta zama a motar nan ne fa" yai maganar yana sake kafeta da idanunsa kamar wani babban saurayi.
"Toni me zance?" Tai maganar a shagwaɓe.
Kasa magana yay, se ido da yake binta dashi, a hankali yace "koma meye kice kawai my wife"
"Thank you my Love" ta faɗa cike da jin kunya, kamar wadda tai saɓo, kasancewar shine mutum na farko data furtawa kalma me girma haka.
Ya lumshe idanunsa Yace "ina sonki my Farhan, jeki gida kar ayi miki faɗa, idan aka yi miki faɗa bazanji daɗi ba"
Tai murmushi ta buɗe motar, ta fita har direban zeja motar, Sadik Yace "tsaya inga ta shiga gida mana"
Direban ya tsaya yana mamakin, wannan taɓara da ƙarfin hali gami da tsaurin ido na wannan Yaro, ko secondary school be kammala ba, amma yasan ya tsara yarinya ta soshi, itama kuma ta biye masa maimakon ta maida hankali akan karatunta, Koda yake duk RUƊIN ƘURICIYA ke damunsu.