← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 48

Sashe 21

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadik ya rasa abunda yake masa daɗi, ya taso da niyyar ya koma gurin zamansa ya zauna, sedai idonsa ya sauka akan Taslim, da ta ɓalle botir ɗin sama na rigarta, wanda hakan ya bayyana wani sashi na ƙirjinta, dan kana iya ganin jar kalar brezia dake jikinta, ta nutsu tana danna waya.

Wani uban tsaki Sadik yaja ya kauda kansa, wanda seda ya janyo hankalin wasu daga 'yan ajin kansa.

Cikin muryarta me cike da iyayi Taslim tace "Prince what's going on ne? Gaba É—aya yau ajin nan ba daÉ—i saboda mood É—inka, what happens ne?"

Be ce mata uffan ba ya É—auke kansa daga kallonta, mafarkansa na jiya ne kawai suke dawo masa kansa, zuciyarsa na ta raya masa abubuwa daban daban, na arziki da na banza.

Ganin Sadik ba shi da niyyar yin magana yasa Taslim ta ƙyaleshi, s cigaba da danna wayarta.

Mubarak Babba ne ya shigo class É—in, ya nufi inda Taslim take, yana zuwa ya kalleta yace "you look sexy today Beb, kinyi kyau sosai"

Wani killer smile tayi, ta ɗan kashe masa ido, ta cigaba da danna wayar, zama yai kusada ita yasa hannu ya karɓe wayar yace "kalleni mana, ina Magana kina danna waya"

Hararsa tai tace "dan bani wayata"

"Sekin kalleni zan baki"

Idonta cikin nasa ta kalleshi tace 'na kallka yanzu bani wayata"

Wani irin kallo yake mata sanna yai murmushi yace "kinga abunda na turamiki jiya?"

"Ban gani ba"ta bashi amsa.

"Why?"
"Z" ta faÉ—a tana hararsa.

"Naga dai alama haryanzu fushi kike dani, duk da na baki haƙuri, shikenan in kin huce ma daidaita, But before ya kamata a rufe nan"

Ya kai hannu ƙirjinta, ya rufe botir ɗin ta dake buɗe tare da kashe mata ido.

Zumɓura baki tai taƙi kallonsa, ya gama surutansa ya fita.

Meena kuwa safa da marwa ta dinga yi a sashen Office É—in da Corper Nura yake, can cikin sa' se gashi ya fito da litattafai a hannunsa, da marker da alama aji ze shiga.

Tace "good afternoon sir" waigowa yai ya kalleta yace "Afternoon how are you"

"Fine sir"be jira abunda za tace ba yai gaba abunsa, haushi n ya kamata na tafiyar da yai b tare da ya sake kallonta ba.

"Hey fine girl, what are you doing over there?"

Ta juya ta a wake magana, É—aya daga sababbin corpers É—n da suka zo tare da Nura ne, me suna George.

Ta É—an haÉ—e rai tace "Nothing"

"But you are suppose to be in your class now, Why are you here?" Yai maganar yana sake ƙare mata kallo kamar maye.

Tsaki taja ta bar gurin, shikuma yabi bayanta da kallo yadda take tafiya, ƙwaurinta duk a waje ga matsatsen skirt da ɗan ƙaramin veil.

Ya jinjina kai yace 'lallai makarantar nan akwai 'yanmata'

Tana tafe tana tunanin ya zata ɓullowa Nura kuma.

Ta koma ajinsu tana zancen zuci.

Farhan ana tashi ta tafi ƙofar ajinsu Prince ta tsaya, tana nan tsaye se gashi ya fito, ta kalleshi tace "Sannu"

Yace "yawwa"

"Kawo jakar in riƙe maka"

"No kar in ƙara miki nauyi mu tafi kawai"

"A'a ka kawo tunda ba ka da lafiya"

Ta karɓi jakarsa ta haɗa da tata, Nas yace "shege Prince, a ɓoye dai ka gama da zuciyar ƙwailar nan, ta gama faller maka wallahi"

Wata uwar harara Farhan taiwa Nas, Nas yace "ke ni kike harara? Dan kina zuwa ajinmu ki zauna na ƙara ganinki a ajin sena ɓallaki"

Prince yasa hannunsa ya kamo na Farhan, sedai yana yin hakan yaji zuciyarsa tana harbawa da sauri, ita ma nata ɓangaren hakan ne, bugun zuciyarta ya ƙaru sosai.

Sadik ya dake yaja hannun ta, su kai gaba.

Nas yace "Lallai Prince Mugun É—an rainin hankali ne, yanzu har wannan 'yar ta fara wayewa ni zata harara"

Mubarak babba ya shafa fuskarsa yace "Yarinyar nan ba ta taɓa burgeni ba sam, ni hasali ma haushinta nake ji, amma yau tunda na ɗora idona akan hips ɗinta raina ya biya, Uniform ɗinta na yau sunyi pitting ɗin ta sun mata kyau sosai"

Amin yace "kaifa Babba wani lokacin Akuya ne, Kamar ya ranka ya biya?"

"Kamar yadda na faÉ—a mana"

Nas yace "Allah yasa Taslim ta jika"

"To taji ɗin seme? Dole wannan yaron ya liƙe mata, shiyake ganin abunda ya gani, sedai na ga shi kamar soko ne"

Wani wanda suke aji É—aya da Mubarak me suna Ahmad yace "kai me kake nufi ne Babba?"

"Zan kauda damuwata ne" ya faÉ—a yana murmushi.

Nas yace "kai kamarya, wai kana nufin kai a yanzu haka kasan mata?"

"Me za'a fasa? Kana tunanin kowane ke iya tsallake sweet sixteens ƙalau? Ga wannan mata muna shiga muna fita a cikinsu, suna dressing kamar a turai, mu zauna guri ɗaya da su, mu ci Abinci tare dasu, muyi raye raye da wasanni tare, kai this is not easy fa"

Amin yace "taɓ ashe mu bamu san komai ba, ai mu iyakar mu romance da 'yan kallece kallace"

Nas yace "baka san komai ba dai, dan nima kawai dai eh"

Nan suka saka shewa, Amin yace "ashe ni kuka bari a tasha?"

Nas yace "tunin ma, amma fa nima zuciyata na ƙawata min budurwar Prince ɗin nan sosai wallahi"

Babba yace "What so ever, kan in graduation a school É—in nan, Wannan Yarinyar sena san abunyi a kanta, she looks sexy in her every movement"

AMIN AFUWA KWANA BIYU NAYI BUSY NE SOSAI, AMMA INSHA ALLAH ZAN ƘOƘARI IN CIGABA DA KAWO POSTING AKAI AKAI

You can start subscribing now @₦300 only, Free pages are not much.

DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:          🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

                            15_16

Suka sake kwashewa da dariya gaba É—aya.

Farhan kuwa har gaban mota ta raka Sadik, ya kalleta yace "shigo mu tafi mana"

Ta girgiza masa kai tace "A'a, na ga ba ka jin daÉ—i, gara ka tafi gida da wuri, Allah ya sawwake"

Ta miƙa masa jakarsa tai gaba, Sadik ya bita da kallo yana lumshe ido, a hankali ya koma ya jingina da seat ya rufe idanunsa, babban burin sa be wuce ace ya mallaki Farhan ba, abunda yake ji game da ita yana neman yafi ƙarfin sa gaba ɗaya.

Farhan ma harta tafi hanya tana tunanin Prince, ba ta san meya same shi haka wanda ya sa shi shiga wannan yanayin na damuwa sosai ba.

Ko yana cikin damuwa idan ya ganta ya kan saki ransa, yai ƙoƙarin ɓoye damuwar ta sa, amma yau kam ya gaza ɓoye damuwar tasa gaba ɗaya.

Da wannan tunanin taje gida, ta tarar da Umma suna cin Abinci tare da ƙannen ta, duk sun sanya Uniform ɗin islamiyya, suna hira Umma nata dariya, amma Farhan na sallama ta haɗe rai, ta dena dariyar da take.

Ta kalli Umman tace "Umma na dawo"

"Sannu" shine kawai abunda Umman tace.

Farhan ta shiga É—akin su ta ajiye jakar ta, ta canza kaya ta fito ta shiga wanka, bayan ta kammala tai salla ta shirya cikin Uniform É—inta na Islamiyya itama, ta fito da niyyar cin Abinci, sedai tasan za'a kwashe wa kowa Abinci idan baya nan a adana masa, amma ita kuwa nata sedai ta tarar da shi a tukunya ya sandare.

Haka ta zuba Abincin ta shiga É—akin umman nata ta zauna tana cin abinci.

Tana son tai hira da Umman, amma babu fuska sam.

Umman Farhan cikakkiyar ba fulatana ce, gaba da baya, kuma Farhan ita ce 'yarta ta fari, bisa ga al'adar Hausa fulani kuwa, dama ɗan fari ba'a jansa a jiki saboda kunya, sedai idan uwa tana da wata yaya wannan 'yar fari ko ɗan fari ya riƙi 'yar uwar uwa a matsayin uwa.

Sedai Umman Farhan ba ta da Yaya mace ko ƙanwa, duk se maza gashi ba'a gari ɗaya suke ba, dan haka abubuwa suna bawa Farhan wahala.

Wasu lokutan ta kanji a ranta anya kuwa Umma ce ta haifeta? Saboda abun ya wuce alkunya, abunda take mata tamkar tsana ne, har gara kwanan nan ta kan yadda su zauna a guri É—aya, amma a baya ko zama tai a guri Umma ba zata zauna ba.

Dan haka babu wata shaƙuwa ta mussaman tsakanin Farhan da Umma, tsakanin ta da ita sedai kallo da ido, duk da Mahaifin Farhan kan yiwa Umman nasiha akan ta rage wannan alkunyar da take akan Farhan, sedai shima a nasa ɓangaren, ba wani sakin jiki yake sosai da Farhan ba, kasancewar ta mace kuma 'yar fari, yafi sakewa da ƙanenta maza, hakan ya ƙara saka Farhan ɗin zama mara kuzari ko a cikin yara 'yan uwanta.

Dama a yanayin halittar ta ma ba Yarinya ce me hayaniya ba, ba ta iya sakin jiki da kowa, idan kaga walwalata to tare da ƙanenta ne, suma wasu lokutan Umma na musu faɗan be kamata ta girma ta dinga shiga  cikin ƙannenta maza ba.

Shiyasa haɗuwarta da Prince ba ƙaramar Ni'ima ce a gareta ba, yadda yake janta a jiki da nuna mata kulawa ta hanyar kyautatawa, shiyasa take matuƙar jinsa a ranta, take jinsa tamkar wani gurbi me girma a tare da ita.
Chapter 21 · 0% Book details