← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 48

Sashe 26

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tashi taje ta canza kaya, ta fito ta tarar da shi in da ta barshi.

Yau Sadik da kan sa yake driving, suna tafe yana tsarawa Khairat abunda za su faÉ—a.

A bakin layin su Farhan yai parking, gabansa se faɗuwa yake, ya hango mahaifin Farhan zaune a kan dadduma, yana tilawar Alƙur'ani.

Khairat kuwa ganin gidan da Sadik ke dosa ya sa ta ɓata fuska, tun daga farkon unguwar kasan ta talakawa ce, ko ina kwata, se wari kwatocin ke yi, ga wasu gungu gungun awaki da tumaki da ke kaiwa suna komowa a tsakanin layukan.

Ga kaji da ke ta sake haƙe kwatar da aka kwashe aka zubar a gefen hanya, gaba ɗaya haushin Sadik Yakamata, gasky Prince ya faɗo ya rasa in da ze samo budurwa se a wannan unguwar talakawan, sedai ba ta da ikon Magana, yanzu ze hayayyaƙo mata, haka tai shiru ta cigaba da bin sa.

Suna zuwa in da Mahaifin Farhan yake, Sadik ya samu guri ya É—an risuna.

Mahaifin Farhan ya rufe Alƙur'anin gabansa ya kalli Sadik da Khairat, yace "Sannun ku da zuwa"

Sadik ya ƙara nustuwa yace "Abba ina wuni"

Baban Farhan yace  "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, ya gida?"

Sadik ya ƙara nutsuwa yace "Lafiya ƙalau Alhamdilillah, dama ni ɗan makarantar su Farhan ne, wannan ƙanwata ce ajinsu ɗaya da Farhan a Makaranta, Yayan mu ne ze Aure, shine muka kawo mata katin gayyata ko za'a barta taje"

Sadik yai maganar tare da ɗakko katuna a aljihunsa ya miƙawa Baban Farhan.

Ya sa hannu ya karɓa ya duba, ya kalli Sadik ya jinjina kai, dan sunan mahaifinsa d sananne ne, ya ƙara tabattar da Allah ne kawai ya yi Farhan za tai wannan Makaranta, ban da haka ina ita ina karatu da 'ya'yan Alhaji Abdullahi.

A fili yai murmushi yace "Masha Allah, ai komai da sanarwa yana da daÉ—i, Allah ya sanya Alkhairi, shiga ki kai mata katin"

Khairat ta karɓa, ta nufi gidan da mahaifin Farhan ya nuna mata, tana sake tsantsame jikinta, dan ita ƙyamar gurin take.

Baban Farhan yana da kirki sosai, ya din ga jan Sadik da hira, tun Sadik na jin nauyin sa, harya saki jiki suka cigaba da hira sosai.

Yadda Sadik ya zo cikin shiga ta mutunci da girmamawa, ba ƙaramin burge mahaifin Farhan yai ba.

Khairat kuwa sallama ta yi tana ƙarewa gidan kallo.

Gidan tsaf da shi, ko tsinke ba bu a tsakar gidan, se ƙamshin turaren wuta da ke tashi.

(Dama ita tsafta ai ba se me kuÉ—i ba)

Sallama Khairat ta yi, ta tsaya a tsakar gida, Umman Farhan ce ta amsa mata, sannan ta bata izinin shiga.

Ta shiga ta gaida maman Farhan, ta amsa mata cikin kulawa.

Khairat tace "dama gurin Farhan na zo, na kawo mata katin bikin yayan mu"

Umman Farhan tace "Allah sarki, Allah ya sanya Alkhairi.

Ta nunawa Khairat É—akin da Farhan ke ciki.

Ta shiga ta tarar da Farhan, sanye da dogon hijjabi ta na karatun Alqur'ani.

Khairat ta samu guri ta zauna, Farhan ta dakata ta kalli Khairat, dan ba ta santa ba "Sannu da zuwa"

Khairat tace "Yawwa, Farhan ko?"

"Eh, sedai ban ganeki ba"

"Ƙanwar Sadik ce"

Kunya ce ta kama Farhan, tai murmushi tace "Allah sarki, sannu bari in kawo miki ruwa"

Khairat tace "No, ba se kin kawo ba, dama katin gayyata ne na bikin Yayan sa, yace mu zo mu kawo miki yana waje, idan da hali yana san ya ganki"

Shiru Farhan ta É—anyi tace "ai ban san yadda zan fitan ba ne, ina jin tsoro Abba na yana nan"

Khairat ta ɗan ƙare mata kallo a ranta tace 'taɓ, rayuwar yaran talakawa ba tai ba sam, wace irin jaraba ce wannan dan baban ka yana nana ace ba zaka fita ba?'

A fili tace "ai ba daÉ—ewa za ki ba, kice kawai zaki rakani ne, se muje ku gaisa kawai"

Har ga Allah, Farham na son ganin Sadik, cikin sanyin jiki ta miƙe ta tafi ɗakin Umman ta, ta nemi iznin raka Khairat, ga mamakin ta se Umma ta amince, har da bawa Khairat ɗin kyautar turare, zaton ta ƙawar Farhan ce.

Khairat kuwa a ranta mamakin irin wannan rayuwa take, saboda tsabar abu Yarinyar ko wayon yadda zata fita ba ta da shi, fita rakiyar ma seta tambaya, lallai 'ya'yan talakawa na rayuwar takura da rashin 'yanci.

Cike da faragaba ta bi Khairat suka fita, cikin sa'a da suka fito baban Farhan ba ya ƙofar Gidan.

Ta hangi Sadik zaune akan barandar da ke gefen gidan su, ya sha shadda dark blue, harda hula kai kace wani babban mutum ne, ba ta san lokacin da ta saki wani ƙasaitaccen murmushi ba, shima ɗagowa yayi ya kalleta yai mata murmushin, tare da sauke ajiyar zuciya a jejjere.

Suna zuwa in da Sadik ke zaune ta sunkuyar da kai, tana wasa da yatsun hannunta.

Sadik yace "Madam kawai se nemanki nai na rasa a makaranta, ki ka dena zuwa why? Ki ka bari ina ta cigiyar ki"

Kasa Magana tayi, saboda fargabar kar wani ya ganta ko babanta ya dawo, ga Khairat a tsaye a gurin.

Ganin yadda ta kasa sakewa, ya sa Sadik yace "zo muje daga bayan layin ku naga You are not comfortable here"

Duk da Farhan na cikin fargaba, amma ba zata iya yiwa Sadik musu ba, ta bisu suka nufi in da sukai parking.

Suna zuwa Khairat ta buÉ—e gaban mota ta shige, ta bar Sadik da Farhan.

Ganin Khairat ta basu guri, yasa Farhan yin ajiyar zuciya tace "ina wuni?"

"Se Yanzu zaki gaishe ni, kin ƙi ko kallona se wani ƙasa kike da ido kina kallo na, ki ɗago ki kalleni sosai"

Murmushi tai, ta rufe fuskarta tace "kayan nan sun maka kyau"

Sadik yace "dagaske?"
Ta jinjina kai alamar eh.

Yai murmushi yace "Alhamdilillah, Tunda sun burgeki, na haÉ—u da Abba a waje, munyi hira da shi sosai, Your father is very kind, Allah yasa idan aka zo nema min Auren ki ya bani, kar yace nayi yaro da yawa"

Shiru tai ta sake sunkuyar da kanta tana murmushi.

Shima murmushin yai yace "Anyway, meyasa ki ka dena zuwa school?"

Gaban ta ne ya faÉ—i, da tuna abunda sir Nazir yake zarginta da shi, a zahiri ta basar tace "Nothing naga ba'a komai ne a school É—in"

"Shine, kika dena zuwa duk tunanin ki ya dameni, ga shi ba ki da waya balle in dinga kiran ki a waya"

Tai shiru ba tace komai ba.

Sadik yace "yanzu dai zaki zo bikin yayan nawa?"

Farhan tace "Ai ka kawo katin gayyata, za'a barni insha Allah"

Murmushi Sadik yai, wani farinciki ya kama shi, yace "Alhamdilillah, naji daÉ—i sosai"

Farhan tace "meyasa kake murna dan zan zo?"

Ya so ya gaya mata dalilin sa, amma se ya fasa dan yasan tsaf zata fasa zuwa,  ya gyara tsayuwar sa yace "My dan Allah ya zan dinga samunki a waya ne? Kin ga hutu za'ai ina son in dinga jin muryar ki, ko in dinga zuwa gida in ganki?"

Zare ido Farhan tai, ta girgiza masa kai tace "A'a, Abba ze tambayi dalilin zuwanka"

"To meye a ciki? Se mu faÉ—a masa gaskiya"

"A'a dan Allah kar ka dinga zuwa"

Sadik yace "to naji, yanzu ki bani lambar da zan dinga kiran ki in same ki a waya"

Farhan ta É—an yi shiru, dan tabbas ita ma tana son hanyar da zata dinga waya da shi, dan ko ba komai a yanzu bayan karatun ta ba wanda yake É—ebe mata kewa sama da Sadik.

A hankali tace "ka bani lamabar wayar ta ka, idan na samu waya ni se in kira ka"

Yace "ki min ko flashing ne, ni kuma zan kiraki insha Allah"

Ya É—akko jotter ya rubuta mata ya bata.

Tace "Bari in koma gida, kar a fara nema na"

"Ok to shikenan, amma tsaya muyi hotuna, wand zan din ga kalla ina jin daÉ—i"

Ba tace komai ba se murmushin nan nata me É—aukar hankali.

Ya ciro wayarsa yai mata hotuna, sannan ya kalle ta yace "se Allah ya kaimu Lokacin bikin, i love You, take a good care of yourself"

Juya tai tana murmushi ta na jin yadda kalaman nasa ke sake tasiri a zuciyar ta.

Shi kuma ya koma motar su.

Yana shiga Khairat tai tsaki.

Ya kalleta yace "ke kuma lafiya?"

Khairat ta yamutsa fuska tace "kai kam me ka gani a wannan bagidajiyar 'yar talakawa?"

A hargitse Sadik ya kalleta yace "wallahi ki ka kuma zaginta sena miki rashin mutunci, a haka nake sonta"

"Allah ya baka haƙuri, amma gaskiya ta fiye kidahumanci, ace dabarar da zatai ta fito ma se da na gaya mata, ta fiye tsoro gashi kamar ba wayayyiya ba, ga ta yarinya sosai"

Sadik be ce mata uffana ba ya fara jan motar, jin yai mata banza ya sa ta ja bakinta ta tsuke, dan ta san idan ta matsa kuma, faÉ—a za suyi.

Suna tafe lokaci lokaci, seya shafi sumar kansa yai murmushi, yana jin so da ƙaunar Farhan ɗin na ratsa shi.

Kai tsaye gidansu suka wuce, suna zuwa yai parking a waje ya kalli Khairat yace "sauka, ni zani wani guri ne yanzu, maybe za'a kawomin wandon jeans, ki karɓa ki bawa Mother ta ajiyemin"

Khairat ta ɗan taɓe baki tace "to" ta buɗe motar ta fice, shi kuma ya ja motar yai gaba.

Khairat kuma ta shiga cikin gidan, sosai gida ya fara É—aukar harami, saboda shirin shiga hada hadar biki.

A falo Khairat tai karo da Nana, tana ta hira ita da talatu me aiki, ta kalli Nana tai tsaki.

Nana ta kalli Khairat tace "Sannu tsaka"

Ba ta kuma kula Nana ba, ta shiga Kitchen ta É—akko madara a roba, ta dawo falo ta na sha.

Dawowarta babu daÉ—ewa, Sadik ya kirata a waya.

Ta É—aga tace "Yaya ina jin ka"

"Kije gate ki karɓo min saƙon nan ki ajiyemin"

Khairat tace "to"

Ta ajiye robar hannunta ta fita, ba daÉ—ewa ta dawo hannunta É—auke da wata leda me kyan gaske.
Chapter 26 · 0% Book details