← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 48

Sashe 27

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta zauna ta buÉ—e ledar ta fito da wani haÉ—aÉ—É—en wandon jeans, kai da gani kasan wandon me tsada ne sosai, sedai abun takaici duk an yayyaga wandon ta cinya zuwa gwiwa, kamar kare ya tattauna.

Nana ta kalli wandon a ranta tace 'wannan wane irin wando ne?'

Faruk da ke fitowa daga ɓangaren Mother yace "Khairiyya, wannan wandon fa?"

Khairat tace "Wandon Prince ne, yace in karɓa in bawa Mother ta ajiye masa, kuma ban ganta ba"

Faruk yace "wannan wandon na ganshi Online ana advertising É—in sa, yafi dubu goma a kuÉ—in Nigeria"

Khairat tace "Ai Sadik akwai rigima in yaso abu, amma wandon yayi kyau sosai"

Faruk yace "hakane, ina ga dai Mother ba ta nan, amma ki ajiye masa shi a wani gurin"

"Ko kuma in baka ka ajiye masa?"

Faruk yace "No, ajiye masa, Mother yace ko bawa, akan wandon nan se ya É—agamin hankali"

Khairat tace "ok bari in Ajiye masa kawai"

Nana kam jinjina lamarin ta cigaba da yi a zuciyar ta, yanzu wannan wandon me kama da tsumma ne wai yafi dubu goma, gaskiya mutan Gidan nan ba su san darajar kuÉ—i ba, wannan ai almubazzaranci ne"

Faruk kuwa tuni ya bar falon, Wayar Khairat ce ta fara ringing, dan haka ta miƙe ta fita waje dan ta amsa wayar.

Tana fita zuciyar Nana ta dinga raya mata abubuwa daban daban, dama a ƙule take da Sadik da Khairat ɗin gaba ɗaya, dan haka ta miƙe ta waiga falon taga babu wanda yake kallonta.

A hankali ta ɗau ledar da wandon yake, ta ciro wandon ta zura a hijjabin ta, ta zaga kan baranda ta samu wani ruwan mopping da aka gama mopping da shi yai baƙiƙirin saboda datti, ta zura wandon a ciki.

Seda ya naɗi ruwan dattin nan Sosai Sannan ta matse shi, ta yar a gurin ta ƙara gaba.

A ranta tace "gobe ma ka sake zagina da kai da wannan shashashar Khairat É—in, zaku gane kuren ku"

Ita kam Khairat ko da ta koma, ta cigaba da sha'anin ta, ta manta da batun wandon Prince.

WANDA SUKA RIGA SUKAI PAYMENT, IDAN FREE PAGES SUKA ƘARE SU KAWAI ZAN TURAWA TA WHAT'S APP, WANDA BE PAYMENT BA ZE IYA SA A MANHAJAR AREWABOOKS, DAN YAFI SAUƘI.

DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.

19_20

Nana kam zuba ido ta yi ta ga yadda za'a kaya da wannan rigima.

Wandon Prince kuwa tuni ya koma tsumman ƙarfi da yaji, saboda yadda aka dinga sauke tukwane da shi.

Wandon yai baƙi ƙirin ya fita daga hayyacin sa.

Sadik kuwa da ya tafi nasa yawo be dawo ba se wajen sha É—aya na dare.

Da takeaway É—in sa ya dawo, dan karma ya shiga cikin gidan su, ya haÉ—u da Yarinyar da yafi tsanar gani wato Nana.

Ya so ya shiga gidan ya ga wandonsa, amma ya fasa ganin dare yayi, ya wuce part É—in su.

Usman na kallon sa Sadik ya zo ya wuce, ya shige bed room ɗin sa, ya zauna yaci Abincin sa, yai wanka sannan ya nemi guri ya kwanta, sedai kwanciyar ta sa ke da wuya, yaji yanayin da ya saba ji ya fara bijiro masa, take bacci ya ƙauracewa idonsa, se tunanin Farhan da ya dinga masa yawo a ka.

Duk yadda ya so ya rintsa amma abu ya gagara, se juyi kawai da yake akan gado, ya rintse idanun sa sosai amma ba abun da ya sauya daga yanayin da ya ke ji.

Duk da yanayin da yake ciki, ba ya hana shi murmushi, lokaci lokaci idan ya tuna Wasu daga halayen Farhan, na tsoro da kuma tsananin Kunya.

Abu kamar wasa Bacci ya gagari Sadik, maimakon ya tashi ya É—au carbi, ko yai salla kawai se ya janyo laptop É—in sa, ya kunna.

Films É—in da su Nasir suka tura masa, ya buÉ—e ya fara kallo da nufin ko ze manta da abunda ke damun sa.

Sosai ya nutsu ya fara kallon film É—in, kamar wasa film É—in ya burgeshi yaji yana son ganin yadda za ta kaya.

Da ya gama episode É—aya idan yai niyyar kwanciya, se yaji lallai yana son ganin me ze faru a next episode.

A hankali Film É—in ya cigaba da burge shi, Soyayya ce me tsayawa a zuciya tsakanin Jarumin film É—in da jarumar film É—in, kasancewar film ne na masarauta, shi É—an sarki ita kuma baiwa ce a gidan.

A hankali kuma Film ɗin ya fara canza salo zuwa wani abu daban, yadda aka fara bayyanar da abunda ya zarce ƙa'ida.

Da fari ya fara jure kallon cuddling da kisses da ake nunawa, ya dake ya cigaba da kallon, a hankali kuma aka fara zarce wannan matakin aka shiga nuna romance tsakanin jaruman, da yadda yake samar musu da meeting point, a cikin wani lambu, yaje suyi hirar su ta masoya ba tare da kowa ya sani ba, wanda a nan ne a hankali suka fara da kissing.

Series ɗin yai matuƙar burge Sadik, sedai fa kansa ya soma cigaba da wuta, dan baze iya jure abunda yake cigaba da kallo a system ɗin ta shi ba.

Kashe system ɗin yayi ya saketa ta faɗa ƙasan gado, ya dafe kansa tare da cije laɓɓansa na ƙasa, ya firzar da wata iska yace "Subhanallah, Nas why? Meyasa zaku turamin irin wannan Film ɗin?"

A hankali ya tashi, ya tafi toilet yai wanka da ruwa me sanyi, ya dawo da ga shi se boxers ya kwanta.

Wayar sa ya laluba, ya nemo hotunan Farhan da yai mata É—azu.

He Just stat zooming her beautiful face, seda hoton fuskar tata ya cika screen É—in wayar ta sa.

Ya ƙara zooming ɗin hoton, kyawawan leɓenta suka bayyana Sosai, da fararen haƙoranta kasancewar ta yi murmushi a hoton.

He just start imagine himself kissing that her beautiful lips.

Ya dinga sauke ajiyar zuciya a jejjere, a hankali ya ajiye wayar ta sa, yai ruf da ciki a kanta, tare da ƙanƙame pillow, yana jin yadda zuciyar sa ke harbawa da sauri, ga wani abu da ke masa yawo tun daga kan sa har ƙafafuwan sa.

A haka bacci yai awon gaba da shi.

Seda Sadik ya makara sallar Asuba, dan be kwanta da wuri ba, ga tarin mafarkai barkatai da yai tayi.

Ya tashi yaje yai wanka yai sallar Asuba, ya koma bacci.

Se wajen tara da rabi Sannan ya fito falon su dan yin break fast.

A falon ya tarar da Faruk shima yana karyawa, ya nemi guri ya zauna yana ta wani ciccin magani, kamar wanda aka tursasa yai wani abu da baya so.

Faruk ne yace "naga wani wando a gurin Khairat, tace min naka ne, wandon yai kyau sosai"

Se yanzu wandon ya faÉ—owa Sadik a rai yace "Eh jiya aka kawo shi, se na shiga gidan yanzu zan nemota ta bani"

Faruk yace "good" daga nan ba wanda ya kuma cewa komai, Sadik ya É—ebi Abincinsa ya koma gefe.

Farhan kuwa da ta koma gida, kyakykyawar ajiya ta yiwa lambar Prince, ta na yi ta na murmushi idan ta tuna yadda ta ganshi cikin manyan kaya, ba ƙaramin kyau yai mata ba.

Haka ta ƙarasa wunin ranar cikin annashuwa da farinciki, lokaci lokaci ta kan ɗakko takaddar da ya rubuta mata lambar sa, dan jin ƙamshin turarensa da ke jikin takaddar.

Da safe kasancewar ba makaranta, yasa Farhan ta kammala ayyukanta na gida gaba É—aya, ta koma É—akinta tana karyawa.

Umma ce da Abban ta zaune a tsakar gida suna karyawa, can Abban Farhan yace "jiya yaran nan da suka kawowa wannan Yarinyar katin gayyata, 'ya'yan Alhaji Abdullahi me turare ne fa"

Umma tace "Ikon Allah, ina ta samo yaran wannan mutumin?"

"Ahh makaranta mana, kin manta makarantar da take yi ne?"

Umma tace "ban manta ba, ni dai ina fatan ta kammala Makarantar nan Lafiya a aurar da ita, dan ina jin tsoron cuÉ—anyar su ita da yaran masu kuÉ—i"

"Haba ki zama me kyautata mata zato mana, mun san tarbiyyar da muka bata ai, kuma ni yaran na gansu a nutse, ba rawar kai shiyasa na bar yarinyar ma ta shigo, kuma ni da ki kai zancen ta gama Makaranta a aurar da ita se ki ka tunanin da batun Yaron nan Sunusi"

Umma tace "Wane Sunusin kenan?"

"Sirikin ki mana, Wannan ba barbaren yaron, babban Almajirin malam Abbas. Na yaba da hankalin Yaron sosai, Malam Abbas ɗin ne da kansa ya zo min da zancen ya na son in bawa Sunusin Auren ta, ni kuma na gamsu da nustuwar yaron, nace masa ba damuwa amma ya bari ta ɗan ƙara girma kan ayi Magana"

Umma tace "Alhamdilillah, Allah ya tabattar da Alkhairi, tana gama wannan Makarantar se ayi Magana, Allah ya tabattar da Alkhairi"

Ƙosan da Farhan ke taunawa a bakinta, tafi ƙarfin mintuna tana kokawa da shi amma yaƙi haɗiyuwa, ji tai gaba ɗaya test ɗin bakinta ya ɗauke.
Chapter 27 · 0% Book details