Sashe 30
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsuke fuska Sadik yai yace "mun shirya party ne da abokaina, 'yan makarantar mu, shine muka je da Khairat"
Usman yace "Amm ai seka sanar, duk ka É—aga mana hankali kun sa mutane a damuwa"
Khairat dai tai tsit tana rarraba ido.
Sadik kam ƙara haɗe rai ya fara takawa, ze nufi sashin su.
"Kai zo nan" Inna ta kira shi cikin bada umarni.
ÆŠan tsayawa yai yayi jim, se kuma ya juyo ya tako in da suke ya tsaya.
Inna ta kalli Khairat ta kalli Sadik, sannan ta kalli in da Mother ke tsaye tace "yanzu ke Hauwa tsakanin ki da Allah, Laifin da yaran nan sukai ba su isa hukunci me tsauri ba? Kalli shigar jikinsu, kalli jikin wannan Yarinyar, ta bishi cikin maza, tun safe ba sa gida se ƙarfe goma na dare suka dawo, maimakon ku tsananta bincikar su, ku san matakin da zaku ɗauka, kawai iya abunda zaku ce musu kenan? Kalli wandon jikinsa kamar mahaukaci duk a yayyage kamar wanda ya zare, kalli uwar sumar kansa kamar ɗan daudu, ita wannan Yarinyar kalli suturar jikinta.
Wannan wane irin riƙo kuke wa yaran nan? 'ya'yayenku fa se Allah ya tambayeku akan rainon su, suna shekarun su ne na RUƊIN ƘURUCIYA, Komai ze iya faruwa, amma har suje su shirya abu isu isu babu sa idonku a kai, wannan wace irin rayuwa ce, a tunanin ku wannan wayewa ce? Babu sa ido akan yaranku kun bar su suyi abunda suke so? Wallahi idan baku kiyaye kun kula da tarbiyyar yaranku ba watarn za kuga abun da ba kwa so"
Cike da ƙosawa Mother tace "Allah ya kiyaye ya tsare, dan Allah kima dena wannan maganar, kar ki musu baki yara idan ba'a bar su sun huta ba ya za'ai, a kirshe su, shima yawan takura yana lalata yara, kuma naga yaran nan sun saba da rayuwa da turawa ne, in Allah ya yadda ba abunda ze faru, yawan yi musu faɗa ma raini yake kawowa, kuma party a tsakanin su yara ba yanzu suka fara ba, kuma ba abunda ya taɓa faruwa, sunyi ne kawai dan taya ɗan uwan su murnar Auren da ze"
Inna ta jinjina kai tace "ba shakka, 'ya'yan turawa ko, shikenan Allah ya temaki turawa, Allah ya shirya"
Tana gama faÉ—in haka ta juya ta koma cikin gidan.
Shi kam Sadik kamar ya fashe, saboda yadda ya kumbura baki yana wani irin huci.
Mother tace "kaga abunda ka janyo min ko? Na gayamaka tunda Allah yasa tsohuwar nan ta tare a gidan nan kayi komai a hankali, in ba haka ba ido zata samana komai ta gani taita masifa"
Usman yace "Mother, dan Allah duk kuyi haƙuri dan Allah komai ya wuce, karki kuma yin wani lafin, kuma dan Allah idan ta ɗau zafi ki dena tanka mata, hakan yana tunzurata, Yanzu dai duk kuyi haƙuri"
Sadik bece komai ba ya wuce ɓangaren su, Khairat ma ta shiga cikin gidan tana sunkuyar da kai kamar munafuka.
Mother kuwa tana zuwa É—akinta, cikin 'yan uwanta ta hau masifa tana mitar Wai Inna tana ja wa 'ya'yansu masifa tana musu baki, ita Alla alla takema ayi bikin nan tabar mata gida duk tabi ta isheta.
Suka haÉ—u suka dinga yi da Inna suna zagin ta.
Ita kam Inna tunda ta koma É—akin da suke, tai shiru tana tunani al'amuran Sadik na bata tsoro da mamaki, tabbas idan aka cigaba da tafiya a haka da wannan sakacin ko sakarcin na uwarsa tabbas Yaron ze lalace.
Dan ta lura halayyar sa daban da ta sauran yayyen sa, tarbiyyar Sadik na buƙatar jajircewa da kuma sa ido, saboda kansa yana rawa fiye da shekarun sa.
Sadik kuwa gaba ɗaya ransa a ɓace yake, Alla Alla yake a gama bikin nan wannan tsohuwar ta bar musu gida, ya rasa me ya tare mata take masa wannan abubuwan, ba damar ya motsa se ta haushi da masifa.
Haka yana kumbure kumburen baki, yai wanka ya kwanta, amma bacci yaƙi zuwa.
Can kuma se partyn da su kai suka dinga dawowa kansa, take surorin 'yan matan nan suka dinga dawo masa kansa.
Ƙoƙarin banzatar da tunanin yayi, amma abu ya faskara, zuciyarsa ta dinga raya masa cigaba da kallon series film ɗin nan, amma wata zuciyar ta shiga gargaɗin sa.
Series ɗin yana ƙayatar da shi, amma kusan kaso arba'in na film ɗin yana bayyanar da very hot Romance ne tsakanin masoya.
Runtse idanunsa yai, amma se ya dinga Ganin Farhan a idonsa, da wannan kyakykyawan murmushin nata.
A hankali ya furta "Oh God"
Ya É—akko wayarsa, ya dinga kallon lambar da ta kirashi da ita, se kuma ya kalli agogo yaga kusan sha É—aya na dare, jiki a sanyaye ya ajiye wayar, ya nemi guri ya kwanta.
Da tunani barkatai cikin ransa da haka bacci yai awon gaba da shi.
Washegari Alhaji Abdullahi ya dawo daga tafiyar da yayi, wanda ya kasance ranar fara bikin É—ansa Usman.
Da yamma ya shiga gaida Inna, lokacin kusan duk jama'ar gidan sun yo ye sun tafi gurin biki.
Cike da girmamawa suke hira shi da Mahaifiyar sa.
Can Inna ta nisa ta kalli É—an nata tace "Abdullahi!"
Wani banbarakwai yaji, dan Inna ba ta sba kiransa kai tsaye da sunan sa haka ba, se idan ta na da wata mahimmiyar magana.
Hakan yasa shi tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan ta, yana sauraren me zata ce masa.
Cike da damuwa tace "Kamar yadda ka sani, ni mace ce me son haihuwa, Allah ya bani haihuwa, sedai duk sun koma, kaine ɗana na huɗu, bayanka na hayayyafa amma duk ba su rayu ba, ɗan uwanka Abubakar ya taso ina murna Allah ya barmin, se bayan yayi Aure ya haifi wannan Yarinyar ya karɓe shi ya karɓi mahaifiyarta"
Mamakin maimaita wannan tarihi da ta É—akko yake yi, wanda duk wannan abun da take faÉ—a ya riga ya san da shi.
Ta cigaba da cewa "Ni macece me son iyali na, fiye da tunani, duk da irin son da nake maka, Allah ya ɗaga ka, kayi Aure ka dawo birni da zama, sedai ƙawa zucina akan 'ya'ya ya ragu, tun bayan da Kai Aure, nasan dama namiji wataran mijin wata ne, mace ce duk inda take hankalinta na kan mahaifiyarta.
Na ɗora rai akan jikokina, saboda ganin suma duk tsastona ne, na ƙallafa rai akan su, sedai shima sena fuskanci matarka ba ta buƙatar hakan, ba ta son 'ya'yanta su raɓi ƙauyawa jahilai.
Sena maida hankalina kan Abubakar, ba dan zuciya ta ta dena sonka da 'ya'yanka ba, sedan bana son shiga cikin lamarin iyalan ka, saboda gudun matsala da zubewar mutunci.
Ashe Habu ma bame tsawon kwana ba ne, bayan yayi aure, an haifi wannan 'yar, matar tazo sake wata haihuwar Allah ya karɓeta, bayan rasuwarta nai ta fama da shi yai aure, amma be ba, har shima yai hatsari a hanyar dawowa daga gidanka zuwa ƙauye shima Allah ya karɓe shi.
Nasan za kayi mamakin sake maimaita maka abunda ka riga kasan shi, kuma ya wuce ban yi haka dan Komai ba, sedan sake jaddada maka irin so da ƙaunar da nake maka da 'ya'yanka, saboda dukkanin ku tsatsona ne, ba zan so inga wani mummunan abu ya sami zuriyata ba.
Ja da baya da nayi na zura maka ido kai da iyalan ka, baya na nufin na sallamaku bane bana kishinku.
Ka sani na sani, ni mace ce me zafi kuma da haka nai tarbiyyar ku, ba dan na dage da addu'a da jajircewa ba, da baka taso a haka har wani yai sha'awar Aura maka 'yarsa ba.
Abdullahi, kai da yaranka ba turawa bane ba, 'ya'yanka da kai Hausa Fulani ne masu kamala da tarbiyya, dan kayi boko, ko kun zuwa ƙasashen turawa ba shi ke nufin kuma turawa bane ba.
Bari in fito maka a mutum, yaranka ba su da tarbiyya!"
Da sauri Alhaji Abdullahi ya É—ago ya kalli Inna yace "Inna ba su da tarbiyya kuma?"
Cikin ƙwarin gwiwa, da nuna isa Inna tace "Ƙwarai kuwa, 'ya'yanka ba su da tarbiyya, mussaman me sunan Ƙarami ɗan Autan ka.
Allah ya sani ina ƙaunar yaranka fiye da yadda nake sonka, ka san yadda nake son jikokina duk da ba sa zuwa in da nake, amma hakan ba ze hanani faɗin gaskiya akan su ba.
Abdullahi ka sanya idanu akan tarbiyyar yaranka, kuÉ—i ba hauka bane ba, kafin kai dubun ka sunyi arziki kuma sun shuÉ—e babu su a duniyar nan, yana daga cikin sadaka me gudana bayan ran bawa, ya haifi É—a na gari da ze dinga aikata aikin Alkhairi.
Kana tunanin wannan? Ko kuma neman kuɗin kawai ka saka a gaba, yau kana Habuja, gobe kana gurin wancan gwamana, jibi ka na waccan ƙasar, ka bar mace da tarbiyyar gidanka matar da ita kanta tana buƙatar tarbiyya, wannan ganganci ne haihuwa da damuna.
Ba ina kushe maka iyali bane, ko ƙoƙarin haddasa maka husuma a cikin gida ba, bulaliya nake maka, naga shekaranjiya, naga jiya gashi ana damawa da mu a yau, ko kai da kai boko ka zaga duniya, ba zaka gayamin sanin duniya da zamantakewa ba, bar ganina bagidajiya bafullatanar ƙauye, shekarun da nayi a duniya naga abubuwa da dama, kuma ina iya fahimtar abubuwa da dama.
Dan haka ka kula da iyalinka, ka sa ido akansu sosai ka kula da tarbiyyar su, ka barsu da ingantacciyar tarbiyya da kyakykyawar rayuwa yafi wannan kuÉ—in da kake tara musu, da basu san ciwonsu ba, sedai su É—iba suyi ta bushasha"
Tun da Inna ta fara faÉ—an nan, ya sunkuyar da kai, bece uffan ba seda ta kammala, ya ja nannauyar ajiyar zuciya yace "Insha Allah Inna za'a kiyaye, in Allah ya yadda zan kula kamar yadda ki ka ce"
Inna tace "to Allah ya wuce mana gaba, ya kare dukkan zuriyar Annabi daga taɓarɓarewa da sharrin ƙarshen zamani"
Yace "Ameen ya Allah, Inna nagode Sosai"
Har ya miƙe ze fita tace "fita za kayi ne?"
Yace "eh Inna"
Tace "to zo in fesa maka turare"
Yai murmushi yazo gabanta ya durƙusa, ta ɗakko turare ta feffesa masa tace "yawwa duk da naji kana ƙamshin turare ai gara ka ƙara, ai ƙamshi rahama ne"
Yai murmushi yace "hakane Inna nagode"
Tai murmushi ta cigaba da laziminta.