← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 48

Sashe 15

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Komai ma kika dafa ni ci zanyi, am missing Your food, komai kika bani zanci"

Tai murmushi tace "shikenan ina zuwa"

Ta jiya ta fito, Nana cikin masu aikin nan su talatu ta shiga, tana tai musu surutu da tambayoyi, tace su bata ta taya su mopping, amma suka hanata.

Sedai surtun nata dariya yake basu, Nana Akwai baki, amma duk da dariyar da suke Mother na fitowa, suka nutsu suka cigaba da abunda suke.

Nana ta kalli Mother tace "Ina kwana"

"Lafiya" Mother ta amsa da ƙyar.

Ba ƙaramin haushi Nana taji ba da yadda Mother ta amsa nata gaisuwa, Nana a ranta tace "aikuwa za'a daɗe ban kuma gaisheki ba"

Ta jiya ta fita harabar gidan, abun sake burgeta yayi, duk yadda yake da hadimai a gidan Hakimi, amma wannan sun sha banban.

Saboda an fito da wasu daga cikin motoci ana wankewa, ga masu gyara flowers, suna basu ruwa komai gwanin ban sha'awa.

Nana ta ƙarasa gurin me wanke mota tace "Dan Allah ka bani abun zuba ruwan nan in wanke motar nima"

Dariya yayi ya kalleta yace "kina mace zaki wanke Mota, ai wannan aikin maza ne"

"To ai iya zuba maka ruwan kawai zanyi"

"A'a ba ruwana, ai ba aikin mace bane"

Nana tace "to me bawa bishiyoyin nan ruwa idan nace ya ban ze bani, ai naga mata ma zasu iya yi"

'je ki tanbaye shi kiji"

Ba musu ta nufi inda dattijon kewa Flowers ban ruwa, tace "dan Allah nima zanyi"

Waigowa yai ya kalli Nana yace "ke jikar Inna, wannan aikin ai ba naki bane"

"Kai ya akai kasan ni jikar Inna ce?"

Yai dariya yace "kai ai tun kina zanin goyo nasanki, kuma gaki nan kamar ki É—aya da ita sak"

Nan ta cigaba da zuba masa surutu kamar wadda aka ƙona a ka.

Faruk ne ya fito da gajeren wando da vest, da gani motsa jiki yayi yace "Baba Ilu sannu da aiki"

Baba yace "yawwa Faruku"

Nana a ranta tace "ikon Allah, ji wanan ƙato ba kunya ƙwauri duk a waje yana yawo a cikin gida, duk tsiraicin sa a waje"

Ya kalli Nana da ta ƙura masa ido yai murmushi yace "kin tashi lafiya?"

ÆŠaga masa kai tayi alamar eh, yace "Yama sunan naki?"

Tace "Nana"

Yace "Ohh yeah, Naana exactly, weldone Naana"

Yai maganar yana tafiya, ita kuwa binsa tai da ido tace "iyayi, Nanan ma baza'a faÉ—a yadda kowa ke faÉ—a ba se anyi wani iyayi, maganar ma da wani iyayi ake yinta, waisu lallai turawa'

Daga ƙarshe ta koma ƙirga motocin dake harabar gidan.

Mother ta shiga É—akin Sadik, ta tarar yana saka belt É—in sa na Uniform.

Yana ganin Mother yai murmushi yace "good morning mother"

"Ba zan amsa ba, yaushe rabon da kaje inda nake?"

"Hmm mother kenan, kema kin san bana son taron mutanen nan, kowa sekabi kana gaishehi ana wani kallon mutum, ana surutu that's why kawai naƙi shigowa, but am really missing you"

Yai maganar tare da kissing É—in hannun Mother.

Ta kalleshi tace "naji, but kasan Granny É—inku ta zo ko?"

Yatsuna fuska yayi yace "na sani"

"Amma ba kaje ka gaisheta ba? So kake tazo ta sani a gaba da masifa tace ni na hanaka zuwa ka gaisheta"

Cikin shagwaɓa da sangarta yace "Mother kin san fa ni matar nan ta tsaneni wallahi"

"Haka nan dai zakai haƙuri kaje"

"To yanzu na saka Uniform, kar in makara zanje school, idan na dawo zanje"

"Yawwa Son, safe journey ka kula da kanka"

Ya jinjina kai ya cigaba da shirinsa, ita kuma Mother ta fice daga É—akin.

Seda ya kammala shirinsa tsaf, ya fito Falo ya tarar Mother ta ajiye masa Abincin sa, ya zauna yai breakfast sannan ya fito dan tafiya makaranta.

An fito da motar da ake kai Sadik makaranta, motar tayi fes se ƙyalli take kamar sabuwa.

Tun daga nesa ya hango Nana a jikin motar, tana leƙawa tana zagaye motar tana shashshafa motar.

Prince na hangota ya tunkaro inda take a fusace, "Ke meye haka! Ƙazama a wanke motar kizo kina taɓawa, wallahi kika sa min datti sekin wanke ta"

Wata uwar harara tai masa tace "motar banza motar wofi, an shafa dattin, sedai ka mutu"

"Ke ni kike gayawa haka? Wallahi zan tattka ki banza Mahaukaciya kawai"

"Seka takanin in gani ai, kuma an shafa dattin, ta tofa miyau  a jikin motar ta zura da gudu tai cikin gidan.

Sadik ya tsaya soror yana kallon motar, ba abun yabi Nana ba ya sake makara, yai ƙwafa ya buɗe motar ya shiga, ranasa a ɓace yana tunanin kalar rashin mutuncin da ze mata.

Shikam Musa direban Sadik, kamar ya tuntsure da dariya, saboda abunda Nana tai masa, amma ya gimtse dariyar sa, kar yayi Sadik ya masa rashin Kunya.

Sadik na zuwa makaranta ya samu guri ya tsaya a gurin Assembly, yana jin yadda su Nas suke masa Magana, amma yai shiru yaƙi kulasu.

Farhan na ta leƙe ta hango abun ƙaunarta, sedai yadda ta ga fuskarsa tasan yana cikin damuwa, ransa a haɗa babu alamar fara'a sam a tare da shi.

Jikinta se yai sanyi ta shiga tunanin meya sami Prince haka yai wannan mugun haÉ—e ran haka?

Aka sallame su daga Assembly ground, suka tafi aji.

Suna zuwa aji, malamin da suke da shi ya shiga ajin, dan haka abokan Sadik basu samu damar tambayar sa abunda ke damunsa ba.

Har malamin ya koyar da abunda ze koyar ya fita, Prince yana tsaki lokaci zuwa lokaci, gaba É—aya ransa a jagule yake.

Taslim ce ta fara magana tace "Allah ya temaki Yarima, what's wrong with you know? You look somehow disturbed"

Tsaki ya kuma yi tare da É—an hura hanci, ya gyara zamansa.

Amin yace "yeah, that's what I want ask since, kika rigani meke going ne?"

Prince ya ɗan nisa sannan yace "wallahi mutane ne suka zo suka cika mana gida, harda wata mahaukaciyar yarinya, kidahuma 'yar ƙauye"

Nas ya kwashe da dariya yace "kai Prince, wannan cin mutuncin fa? Ba relative É—inka bace?"

"Ni nama san wacece? Ni na manta in da nasan ta ma gaba ɗaya, kawai ganinta nai a gidan nan, wata fitsararriya 'yar ƙauye"

Amin yace "kai harka kira wata 'yar ƙauye, ai budurwarka ce 'yar ƙauye"

Sadik yaiwa Amin wani warning glance, ba shiri yace "Ohh am sorry i dont mean to hurt you"

Sadik yace "Ai se nayi maganin yarinyar nan dan na tsane ta gaba É—aya bana son ganinta"

Taslim tace "to aini har Yanzu banji abunda tai maka ba"

Nan Sadik ya basu labarin abunda Nana tai masa, daga jiya zuwa yau, sosai suka dinga dariya, hakan ya ƙara bawa Prince haushi, dan haka ya tashi ya bar ajin.

Ajin su Farhan ya tafi, sedai suka haɗu a hanya, ya zuba mata idanunsa seda ta ƙaraso in da yake sannan ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta.

"Lovely meyasa ba ki zo ajinmu ba yau?"

"Na ganka ɗazu a gurin assembly kamar ranka a ɓace, shiyasa ban zo ba"

"Amma Farhan ki ganni a cikin damuwa amma ki ƙi zuwa in da nake, baki damu da halin da nake ciki ba kenan ko?"

"A'a ba haka bane, naga idan kana fushi baka son aje in da kake ne"

"Kuma se akace miki hadda ke? Da kinzo da tuni na manta da abunda ya faru, kin barni wancan Nasir É—in sun sani a gaba suna sake bani haushi, dan dai ban biye musu bane"

Farhan tace "am sorry, kayi haƙuri dan Allah"

Yai murmushi yace "bakomai, ai matata bata laifi"

Jin maganar tasa tayi wata uwar gundumemiya, wai matarsa ba ko kunya, shi baya jin kunyar wani yaji yana faÉ—ar irin wannan maganganun sam.

Suka jera suka tafi har ajinsu Farhan, a can ya zauna suka dinga hira, yana bata labarin kayan da aka kaiwa yayansa na lefe yace "ji nai kamar in ƙwace kayan nan a kai gidanku, ace na aurenmu ne Ni da ke Farhan"

Shiruu tai ba tace Komai ba, kuma ba ta É—ago idonta ba.

"Farhan, wai meyasa a duk lokacin da nai miki irin wannan zancen kike yin shiru ne, ko dai ba kya sona ne?"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"To meyasa ba kya son in miki Wannan zancen?

Tai shiru ba tace komai ba, ya gyara zama yace "Look Farhan, ina da kuÉ—in da zan iya yin Aure, kuma wallahi ni dagaske nake sonki Farhan, dan Allah ki dena doubting a kaina Please"

Ta sake jinjina masa kai yace "Yawwa,  zaki ci wani abun ne?"

Tace "A'a"

Ya zira hannu a aljihunsa ya É—akko dubu biyu ya ajiye mata.

Zare ido tayi za tai Magana amma ya haÉ—e rai yace "shhhh" ya juya ya fita ta bi bayansa da kallo.

A varrender ajinsu Farhan, ya haÉ—u da Sir Nazir, Nazir ya tsaya ya bishi da ido, Sadik ya haÉ—e rai sosai, ko kallon inda Nazir yake be ba ya wuce.

Tunani Farhan ta shiga yi akan ya za tai da wannan kuÉ—in da ya bata?

Ba tai aune ba taji mutum a kanta, tana É—aga ido ta ga Sir Nazir, yace "wato ba ki rabu da wannan yarn ba ko?"

ÆŠan tura baki tai, ta sunkuyar da kai.

"Wai ke dan Allah da ma haka kike da taurin kai ne? Waima meyake gaya miki da ya sa kika liƙe masa haka? Ko kuma me kuke yi da yasa kullum se yazo in da kike?"

Ƙin ɗago kanta tayi da ga sunkuyar war da tayi.

"Kije ki cigaba da biye masa karki fasa, nan gaba idan ya gama morar ki, ze watsar da ke ne, a lokacin ne zaki nadama mara amfani, wannan yaron sam ba tarbiyya ce da shi ba, ɓata miki lokaci ze a banza"

Babban abunda yake ɓatawa Farhan rai be wuce duk wanda suke soyayya a makarantar nan ita kadai ya sawa  ido ba, kuma abun takaicin be wuce yadda yake dizgata a gaban kowa ba, saboda Prince.

Nazir na fita Yasmeen ta ja tsaki tace "nifa wannan mutumin ya fara ɓata min rai akan abunda yake wa Farhan, ya fiye sa ido da takura wallahi"
Chapter 15 · 0% Book details