Sashe 31
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Maganganun Inna sun damu Alhaji Abdullahi Sosai, duk d aba ta fito ta gayamasa ƙarara meyafaru ba, amma maganganun nata sun tsaye masa a rai sosai.
Se dare sannan aka din ga dawowa daga gurin kamun da aka tafi, wanda zasu kwana a gidan duk suka taho nan gidan, dan a tare motocin suka dinga dawowa.
Wajen ƙarfe sha ɗaya na dare, Mother tayi wanka ta canza kaya, ta nufi sashin Megidanta da coffee.
Tun da taje take zuba masa hira, tana nuna masa hotunan biki, sedai ta lura kamar yana tunanin wani abun ne.
"Yallaɓai ya na ganka wani iri ne? Kai da Yakamata ace kana farinciki zaka aurar da ɗanka na fari"
Kallonta yayi sannan yace "Akwai wani abu da Sadik yaiwa Inna ne na rashin kyautawa"
Haushi ne yakama Mother, wannan takurarraiyar tsohuwar ta isheta.
A fili tace "wani abun tace ya mata ne?"
"No, ba tace min yamata Komai ba, sedai tamin hannunka me sanda a cikin Magana, dan haka dan Allah idan ma da wani abu na rashin ɗa'a ko kyautawa da yake, ki ja masa kunne, nima zan masa magana bana son ranta ya dinga ɓaci akan wani abu"
Ajiyar zuciya Mother tai tace "ni dai iya sani na ba abunda yai mata, sedai kasan ba su fiye jituwa ba, amma zan masa magana insha Allah"
Yace "yayi"
Yana É—auke kai ta dalla masa harara, gaba É—aya haushin Inna take ji, ta fiye sa ido da son hanasu rawar gaban hantsi ita da 'ya'yanta.
Aka cigaba da gudanar da biki cikin bajinta, da kuma wadata.
Ranar Dinner Inna tace ba in da Nana za taje, wani irin bikine baza'a fara shi ba se dare dan watsewa, waye ze sa mata ido akanta.
Nana hadda kuka, tana son zuwa amma Inna ta hana.
Faruk ne ya shigo cikin shadda coffee colour, se sheƙi take kamar shine ango yayi kyau sosai.
Part É—in Mother ze nufa, amma yaga Nana a zaune kusa da Inna tana kuka.
Ya dawo da baya yace "lafiya kuwa? Nana ana ta shirin tafiya gurin biki amma kina zaune kina kuka?"
Duk da tana shakkar Inna amma tace "Inna ce tace ba zani ba"
Ya kalli Inna yace "Inna meyasa ba zata ba?"
Inna tace "bana son abunda baza'ayi shi ido na ganin ido ba, wane irin biki ne za'a tafi wata uwa duniya ayi shi da daddare"
Faruk yace "haba Inna, aina lokaci É—aya ne, yanzu kowa seya tafi a barta a gida, ai za taji ba daÉ—i, tashi ki sako kayanki mu tafi tare"
Inna tace "ki tashi daga nan kiga yadda zanyi dake"
Faruk ya ɗan marairaice yace "dan Allah Inna ki ƙyaleta, kinga kuka take fa"
"Ni bani da idon ganin kukan take ai, tayi kukan jini ma"
"Dan Allah Inna ki bari taje, kuka fa takeyi"
Inna tace "A'a yau naga ikon Allah, ka ƙyaleta tai ta kukan mana"
Faruk yace "wallahi Inna bana son inga mata suna kuka, kinga nan gidan bamu da ƙanwa mace, shiyasa idan naga yarinya ƙarama mace nake jin tausayin ta, dan Allah ki bari taje ko ta dena kukan nan"
ÆŠan tsura masa ido Inna tayi, ta tuna haka mahaifinsa ma yake, ba ya son yaga mace a damuwa ko ta na kuka, da irin wannan damar Matarsa tai amfani se yadda tai da shi, ta lura Faruk shine me sanyin hali a cikin su, duk da ga irin sunansa amma ba shi da zafi sosai.
Inna tace "Naji, amma sedai muje tare, in sa ido akan ta"
Faruk yai dariya yace "Hajiya Inna agurin dinner"
"Bana wasa da yara, ka sani ƙaniyar ka zanci ni"
Yai murmushi tare da miƙewa tsaye.
Ba'a tafi gurin bikin nan ba se kusan ƙarfe tara na dare, Faruk ya ɗau Inna da Nana zuwa gurin bikin nan.
Inna ta sha mamakin irin tsukewar da 'yan mata da iyayensu sukai, ba bu batun mayafai dama, kowa sabgar gabansa kawai yake yi.
Ga zabga zabagan baligan samari, wanda suka kasance dangin Amarya da na Ango, suna shiga suna fita.
Inna ba ta ƙara tsinkewa da al'amarin ba, seda aka fara cashewa, ba iyaye ba 'ya'ya, ana ta liƙa kuɗi ana raye raye.
matashiyar 'yar galar nan me suna Gimbiya Ameeea ta nishaɗantar da su agurin, da kala kala samfur daban daban na rawa, cike da ƙwarewa da burge al'umma (Wanda be san labarin Amira ba, ya hanzarta neman littafin WUTA A MASAƘA) Daga bisani dj Sultan, ya sanar da zuwan, Maman Ango da Amarya.
Zuwansu ba daÉ—ewa sega Amarya da Ango suma sun hallara.
Masha Allah, sunyi kyau matuƙa shi ya Sanya light blue ɗin shadda, ita kuma ta saka dark blue ɗin less.
Nan fa biki ya fara ɗaukar harama wajen ƙarfe goma saura na dare, gaba ɗaya zaman gurin ya ishi Inna, gashi ba ta san in da zata gano Faruku ba balle tace ya maida su gida ba, dan ba dan ya matasa ba ba abunda ze kawota gurin nan, dama ta zo ne saboda Nana, dan ba zata iya sakinta haka tazo wannan guri, ita kuma tana gida a zaune ba.
Tana cikin tunanin ne, taji ana wata shewa, ta É—aga kai ta hango wasu gungun samari da 'yan mata sun shigo, suna ta faman iface iface.
Zuba ido tai sosai, ta hango Sadik a tsakiyar su, sanye da coffee É—in shadda irin ta Faruk.
Mother da ke tsakiyar fili ta nawa Usman liƙi ta hango shigowar Sadik, tsayawa tai tana murmushi, yayin da Dj ya shiga koɗa Sadik ɗin yana masa kirari.
Da hanzari Sadik ɗin ya ƙaraso in da Mother ke tsaye, ya zura hannu a aljihun Rigar sa ya zaro bandir na kuɗi yana liƙa mata.
Juyi Mother ta dinga yi shima tana zuba masa kuÉ—in, ya rungumeta ana masa hotuna.
Inna kam tagumi tai tana kallon ikon Allah, can kuma aka sanar da cewa ana neman abokan Autan Hajiya Hauwwa, akan stage dan yiwa abokinsu kara na zuwa bikin Yayansa.
Aikuwa nan da nan suka cika stage É—in mazan su da matansu.
Ba kunyar iyaye ko manya da ke gurin, suka dinga tiƙa rawa ta fitsara a gurin nan, Taslim ta riƙo hannun Prince tana juya shi shikuma yana murmushi.
Rai a ɓace Inna ta kalli Nana da ta zubawa stage ɗin ido tana kallon ikon Allah, wanda ita kanta Nana a ranta abun da su Sadik ɗin keyi haushi yake bata, gaba ɗaya ba taga tsari ko dacewar Abun ba.
Inna tace "ke dan ubanki kin zura musu ido kina naɗar abunda suke ko? Wallahi ko da wasa naga makamancin wannan a tare da ke, se na shaƙe ki, ki mutu kowa ya huta"
Ɗan tura baki Nana tayi tace "To Inna ni me nayi?"
"Rufen baki, tashi mu bar gurin nan"
Nana tace "mu bar nan Inna muje ina? Ba mu san hanya ba fa"
"Zaki ta shi ko se na make ki"
Nana ta miƙe suka fita daga cikin hall ɗin, Inna na cigaba da banbami kamar Nana ce tai mata laifin.
Ko fa suka fito sha ɗaya saura na dare, babu ababen hawa ma, nan Inna ta shiga rarraba ido, ta ga ta ina za ta hango Faruk, dan da ya shiga hall ɗin se ta neme shi ta rasa, saboda da alama shike ƙoƙarin sallamar abokan sa da na Usman.
Suna nan tsaye a in da akai parking É—in motoci, sega Sadik ya fito shida abokan sa, suna hawa motocin da aka kawo su a ciki.
A hakan ma se rashin albarka suke.
Inna se girgiza kai kawai take, cikin sa'a kamar an jefo Faruku, se gashi ya nufo in da Su Inna suke.
Yace "Inna ba dai tafiya za kuyi ba?"
Inna tace "Aikam dan tun É—azu kai nake nema, ka maida mu gida"
Faruk yace "to shikenan, bari in É—akko motar"
Suna tafe a hanya, tunanin da Inna take daban har suka je gida.
Sadik kam kwana yai da É—okin washegari Mother's evening, Farhan za ta zo, ze gabatar da ita a gurin Mother, sedai ayi duk wadda za'ayi.
Da safe yana ta É—oki, yana son tabattar da zata samu zuwa ko kuwa?
Kasa haƙuri yai, ya ɗakko wayarsa ya kira lambar da Farhan ta kira shi da ita.
A daidai lokacin kuwa Huzaifa yana gidan su Farhan, kasamcewar cousin ɗin ta ne, ɗan wan Abbanta ne.
ÆŠaga wayar yayi tare da yin sallama.
Dumm Sadik yai jin muryar namiji, amma ya basar ya amsa sallamar yace "Amm Farhan nake nema ko tana kusa ka haÉ—ani da ita?"
Huzaifa yace "wace Farhan É—in?"
"Ta kirani da wannan layin shekaranjiya" Umma tsurawa Huzaifa ido tayi, tana sauraran abunda yake faɗa a wayar, ta ƙara saita nutsuwarta ne jin an ambaci Farhan ake nema.
Huzaifa yace "ok na tuna tayi waya kam, bari in kirata"
Huzaifa ya katse wayar, Umma ta kalleshi tace "ya akai ta karɓi wayarka ta kira wani?"
Huzaifa yace "Ai ban san wanda ta kira ba, kawai ta cemin za tai waya ne?"
Umma ta jinjina kai tace "kirawo ta"
Huzaifa ya miƙe ya kirawo Farhan, wadda ta duƙufa tana bitar Alƙur'ani.
Ta taso ta zo gaban Umma tace "gani"
"Waye yake kiranki a waya?" Umma ta tambayeta ta na kallon idon ta.
Farhan tace "Ni kuma?"
Huzaifa yace "wani ne ya kira wayata yace yana nemanki, wai kin kirashi a layina shekaranjiya"
Gaban Farhan ya faɗi amma ta dake tace "Yayan ƙawata ne, na kirata munyi magana ne, akan bikin da zamu anjima, ban san lambar wa ta bani ba"
Ba tare da ta kalli in da Farhan take ba Umm tace "tashi ki je"
Farhan ta tashi ta koma É—aki, tana jin yadda wani irin gumi yake bin cinyoyin ta na Rashin gaskiya.
Ita kanta tayi mamakin yadda wannan idea tai saurin zuwa kanta.
Seda Farhan ta bari Umma ta tafi É—akin Abba, sannan ta fito cikin sanÉ—a ta shiga É—akin Umman ta É—au wayar Umma, ta saka lambar Sadik ta kirashi.
Tai sa'a ya É—auka, yana É—agawa tace "call me"
Ba musu ya katse kiran, ya kirata ta É—aga tare da yi masa sallama.
Ya amsa yace "Princess, kewarki ta dameni, na ƙagu in anjima, fatan dai zaki zo ɗin"