← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 48

Sashe 35

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yayin da ita kuma Nanan ke manakin yadda Gaba ɗaya suke magana da iyayi, magana ɗaya biyu se anyi turanci, turancin ma me wuyar ganewa irin na turawa, ga yadda Jiddan ke zubawa Dr. Shagwaɓa a gabansu ba kunya.

Se bayan azahar, sanan Faruk yace Nana ta tashi su tafi.

Jidda tace "gaskiya uncle ka barmin Nana, idan zasu koma se ka zo ka tafi da ita"

Faruk yace "taɓ, ai wallahi kakarta ba zata yadda ba, ki bari in kin tambayi izinin Hajiya Inna, shikenan"

Nana ta shiga ran Jidda sosai, ta haÉ—a mata sha tara ta arziki, su kai hotuna sannan suka nufi komawa gida.

Sadik kuwa yana tafe yana masifa ya koma gida yace shi be ga Nana ba, gaba É—aya aka dinga jimamin in da Nana ta shiga, hankalin Inna ya gama tashi, Alhaji Abdullahi yana ko report za'a kai gun 'yan sanda.

Turo ƙofar ɗakin Nana tayi, hannunta rungume da kaya ta shigo da Sallama, gaba suka waigo suna kallonta.

Se yanzu ta sha jinin jikinta, ta tuna ba ta sanarwa da Inna zata fita ba.

A fusace Inna tace "daga ina kike?" Kafin ta amsa, sega Faruk ya shigo falon shima.

Ya kalli su Abba yace "Abba lafiya na ganku a nan?"

Abba yace "Nana ake ta nema, kuma se gaku tare"

Faruk yace "ai ni ne nace ta rakani gidan dr. Mu ka kai musu Abinci, daga nan kuma muka zauna se yanzu, laifina ne ayi haƙuri please".

Wani uban tsaki Sadik ya ja yace "wallahi wannan Yarinyar ba tayi ba, ta sa aka wahal da ni ina zaga layuka nemanta kamar ɓarawo"

Murguɗa baki tai tana hararar Sadik, ya ƙara harzuƙa yace "wallahi nazo gurin nan sena tataka ki, na tsani yarinyar nan tunda ta zo gidan nan take wahalar da mutane'

"Seka kasheni ai tunda ka tsaneni, masu gida na ga ma kunkuru da yake yawo da gidansa a ka, se ka naÉ—a gammi ka É—au gidan naku a bayan ka ai"

Inna tace "rufemin baki kan in zo in gurza wannan shegen bakin naki, kai kuma kayi haƙuri kaji zamu bar muku gida, ba kai kaɗai ba naga alamar matar gidan kanta mun isheta, zamu tafi Insha Allah, gara mu tafi ka dena ganinta kana ƙara tsanarta"

Mother tace "to ni kuma meye nawa a ciki?"

Faruk yace "dan Allah kuyi haƙuri, dul laifina ne wallahi"

Abba kam ya fusata sosai da abunda Sadik yayi, ya tabatta abunda Inna ke faɗa yaransa ba su da tarbiyya, dan haka yace "Sadik faɗan da nai maka ta dama ya shiga ya fita ta hagu ko? A gabana ka ke cewa ka tsani Nana ko, duk da matsayin ta a gurina, Nagode amma ka sani nafi ƙaunarta fiye da kai ɗan da na haifa a cikina, shashasha mara ɗa'a"

Da sauri Sadik ya É—aga kai ya kalli Abba, jin Abba yace wai ya fi son Nana da shi.

Nana kam sumsusm ta wuce masaukin su, Inna ma ba ta sake cewa komai ba ta bi bayan Nana, taje ta sameta a É—aki, ta dinga mata faÉ—a ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, dan seda Nana tai kuka.

A lokacin Inna ta saka Nana ta fara haɗa musu kaya, dan ta ƙudirce a gobe in Allah ya kaimu zasu bar gidan.

Da daddare Sadik ya buɗe ɗakinsa na cikin ƙaton falon da ke daf da ƙofar sashin Mother, saboda yanzu gidan ba kowa.

Ƙofar ɗakinsu Inna a buɗe tana jiyo hirar da Mother take da Sadik.

Sadik yace "Mother, nifa banji kin yaba sirikar taki ba"

Mother tace "ai sirikata son kowace ƙin wanda ya rasa, ga ilimi ga kyau ga gayu, ai Jidda tayi ta ko ina"

Sadik yace "Mother ba wannan ba, yarinyar da na kawo ku gaisa da ita Ranar Mother's evening fa"

Mother ta É—anyi shiru tace "wace yarinyar ce? Namanta wallahi"

"Mother, wata Fulani girl da na kawo miki, har kuka gaisa kina magana da su Anty Naja lokacin"

Mother tace "to ai Mutanen da yawa ba lallai in tuna ba"

"Please Mother ki tuna ta mana"

"Kai ka ƙyaleni, ni ban tuna ba, ya ma akai ta zama surikata?"

ÆŠan sosa kai yai yace "eh, in law É—inki ce to be in the next couple's of year's, not year's ma in next year Insha Allah"

"Wai tsaya, ba dai budurwar Faruk bace, aikuwa zeci ƙaniyarsa ze gamu dani, he better concentrate in his studies, karma ya ɓatawa 'yar mutane lokaci, shine y turoka da ita?"

Sadik yace "Ohhh my God, Mother she's my fiance, budurwata ce fa"

"What! Me kace?"

"Mother you heard me fa, and you are still asking me"

"Ai dole in sake tambaya, wace irin maganar banza ce wannan? Ina kai ina wata budurwa, ko secondary School ba ka gama ba"

Ɗan kwaɓe fuska yai yace "Mother, am finishing secondary School this year insha Allah, zan kammala secondary School a wannan shekarar, Abba yace in zaɓi kowace school nake so a duniya ze kaini, kan in gama degree ta kammala secondary ita, ni da ze yuwu ma, da se mu tafi can in da zanyi karatun ni da ita"

Wani banzan kallo Mother ta watsawa Sadik, ta ja tsaki ta maida hankali kan TV.

"Mother i meant what I said, Aure nake so inyi please, ki sa baki dan Allah, kinga ko da kuɗin plazar mu zan iya riƙeta, se Abba ya suponsoring karatunmu, ina son Yarinyar ne Please Mother ki sa baki, dan...

"Shut up Sadik!" Mother ta faÉ—a a tsawace.

"Kasan me kake faɗa kuwa, haryanzu ba ka cika shekaru goma sha takwas ba, uban waye ze maka Aure, me kai achiveing a rayuwar ka da har zaka fara tunanin wani Aure? Get out from my side, kaje ka kama litattafanka, kayi karatu ka zama wani abu kafin ka fara wata maganar aure, Allah ya ƙara nunamin kayi Wannan zancen"

Sadik ya ƙulu da jin zancen Mother, dan gani yake kamar kalaman nata na nisanta shi da mallakar Farhan ɗin.

Fuuuuu ya tashi ya bar falon a fusace, ya fasa kwana a É—akinsa na cikin gida da yai niyya.

Inna kam duk da taji hirar ta su girgiza kai tayi, da jinjina gaɓunta irin na wasu iyayen na wannan zamani,kamata yai yadda yaran suka zama na zamani, iyaye ma su zama na zamani a gurin tarbiyya.

Suna ta ihun ilimi ilimin zamani, amma takasa amfani da hikima da ilimin akan É—anta.

A fakaice yana wa mahaifiyarsa nuni da waye shi ne? Da kuma abunda yake so amma ta kasa ganewa, hakan yana faruwa a farkon a ƙuruciya, wanda wasu yaran kan zo musu da RUƊANI, idan ba su samu kyakykyawar kulawa da shawarwari ba se a samu matsala.

Yanayin Sadik, da abunda suka dinga yi shida abokansa a gurin bikin nan kawai, ya isa ya nuna maka waye shi, a É—an zaman nan nata tana ankare da halayyar yaron.

Ba dan gudun shiga abunda be shafe ta ba, da tayi abunda ya dace akan Sadik, amma tayi alƙawarin fita daga sabgar su gaba ɗaya, idan lokaci yayi iyayen Sadik zasu hankalta, da maida hankali akan yaransu, sedai zata taya su da addu'a Allah ya shirya mata zuriya ya tsaresu da taɓarɓarewar ƙarshen zamani da RUƊIN ƘURUCIYA!

Domin gyara Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.

Kar a manta a garzaya shafin Arewabooks, domin cigaba da samun littafai na, kuyi following É—ina @Ayshercool.

https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.

Sadik a fusace ya koma BQ, ya shiga ɗakinsa ransa na masa ƙuna.

"Wannan wace irin rayuwa ce? Boko boko boko! Kamar bokon nan ce tikitin jin daÉ—in duniya, shikenan dan mutum zeyi boko baze aure ba?"

Wani tsakin ya kuma yi, tare da fesar da iska daga bakinsa.

Meyasa Mother taƙi goya masa baya a wannan karon? Meyasa ita kullum take kallon shekarunsa da ƙanƙantarsa?

Ɗan gajeren tsaki ya kuma ja, ya haye gadonsa ya kwanta yai rigingine, take Farhan ta kuma faɗo masa, wani irin shauƙin sonta na ƙara ratsa shi sannu a hankali tabbas son da yake mata ba RUƊIN ƘURUCIYA ba ne, soyayya ce da ba ruwanta da girma ko yarinta.

Wayarsa ya É—akko yana kallon hotunan ta da yake wayarsa, she's cool and Beautiful, uwa uba ta na da tarbiyya da É—a'a a nutse take.

Ya shafi screen É—in wayar ta sa, ya lumshe ido yace "I love You Farhan" yai Maganar a hankali, yana sauke ajiyar zuciya.

Kamar wanda aka tsikara, ya tashi zaune, ya janyo system É—in sa, ya kunna, Series É—in nan da yake kallo ya nemo, ya kunna ya cigaba da kallon sa ba tare da fargabar Komai ba, a tunaninsa hakan ze É—auke masa hankali da rage masa damuwa.
Chapter 35 · 0% Book details