← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 48

Sashe 48

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Wani irin É—agowa tai da idanunta, wanda sukai mata nauyi saboda jinta da take a gajimare, sheÉ—an na ta buga mata gangarsa a kwanyarta.

Kallon da tai masa ne yasa jin jikinsa yai wani irin sanyi, yaji gumi na karyo masa.

Kuma ta tsatsare shi da idanunta taƙi ɗaukewa.

Jin halin da yake shirin shiga ne yasa ya aro jarumta, ya haÉ—e rai yace "concentrate on what you are doing"

A hankali ta janye idanunta ta cigaba da note É—in, amma lokaci lokaci idan ya É—ago ido se su haÉ—a ido tana masa wani irin shu'umin kallo da be san dame ze fassara kallon ba.

(Ƙalubale gareku iyaye da malamai, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam ya hana keɓancewa da mace wadda ba muharramarka ba, a yanzu muharraman ma se ana sa ido sosai, saboda muna zamani ne computer age, wannan kallace kallacen fina finan wanda ya dace da wanda be dace dui matasan mu kallo suke, ga uwa uba litattafai wanda wasu suke taka muhimmiyar rawa, gurin gurɓata tunanin Young adults ɗin mu.
Sannan mace duk in da take komai girmanta ko ƙanƙartarta duk girmanka duk ƙanƙantarka zata iya jefaka a bala'i, 'ya mace tana da hatsarin gaske, Allah yasa mu dace"

Farhan tai zuruu da ido, kamar agola a rabon gado, gaba É—aya ta kasa sakewa. Gefe ga su Haseen suna ta karatun littafin su, da fari hankalinta baya kansu, tayi zurfi a cikin tunani, sedai jefi jefi kunnuwanta na É—aukar wasu abubuwan.

Tana nan zaune aka tashi, kowa ya bar ajin amma ita tana zaune ba ta tashi ba.

"Farhan" taji muryar Sadik ta daki dodon kunnenta.

Haɗe rai tayi sosai ta ƙi kallonsa.

Matsawa yai kusa da Ita, tai saurin matsawa daga in da yake.

"Farhan meyasa kike guduna kuma? Fushin kike dani haryanzu?"

"Dan Allah ni ka ƙyaleni"

"Bazan iya ba Farhan, dan Allah kiyi haƙuri"

"Dan Allah ka ƙyaleni"

"Kema kin san ba abune me yuwuwa ba, tsautsayi ne baze sake faruwa ba insha Allah, ki tashi mu tafi gida Please kiyi haƙuri"

"Bazan haƙurin ba, kawai kasa nayi abunda ban taɓa yi ba"

"Nima ban taɓa yi ba, amma ai nace ba zan sake ba"

Tsaki tai masa ta ɗakko jakarta, ta raɓa shi zata wuce.

Riƙota yayi ya haɗata a bango yana kallonta, kamar yadda yaga anayi a Bollywood 🙄🙄🙄.

"Farhan nike baki haƙuri kina min wulaƙanci, nasan nayi miki laifi but am sorry, dan Allah kiyi haƙuri" ya ƙarasa maganar a sanyaye.

Kawai idanunta suka fara zubar da hawaye.

Hannu ya kai ze share mata hawayen, amma ta riƙe hannunsa.

"Shikenan na gane ba zan taɓaki ba, zo mu tafi"

"Ni ba zan bika ba"

"Baki haƙura ba kenan?" Ya tambayeta a marairaice.

Gaba ɗaya ta rasa dalilin da yasa ta kasa jin haushin Sadik, yadda yake marairaicewa ne yasa wani irin tausayinsa ya shige ta, kuma tasan idan ta dena kulashi, bata da wanda zata cigaba da raɓarsa tana jin daɗi, babu wanda zata dinga raha da shi tana jin daɗi.

Yasa hannu ya karɓi jakarta, yace "muje ko"

Tabi bayansa suka fito, a harabar in da ake parking É—in motoci, suka haÉ—u da Mubarak Babba, ya kalli Farhan yana wani kashe ido yace "A'a yarinya ta zama 'yar hannu, delay É—in na meye haka baku fito ba, ko dai ana tisa wancan karatun ne da a kai ran Friday".

A take Farhan taji wasu hawayen na silalowa daga idanunta.

Sadik ya kalli Babba yace "Mubarak, ka sanni na sanka, ni da kai kar ta san kar ne, ko da wasa ba ruwanka dani da kuma Farhan, abunda ya faru ma tsautsayi ne, kar ka kuma na gaya maka"

Mubark yace "hmm to shikenan, na dena"

Yaja Farhan suka shiga mota suka tafi.

Seda suka kaita har inda take sauka Sannan Sadik yace "dan Allah ina ƙara baki haƙuri Farhan, kiyi haƙuri"

Ba tace Komai ba, tasa hannu zata buÉ—e motar ta fita.

Ya kuma riƙo hannunta, ta waigo ta kalleshi yace "baki cemin kin haƙura ba"

"Bakomai ya wuce" tai maganar tare da zare hannunta ta fice.

Shikam direba a ransa yace "Allah yasa yaron nan ba wata watsewar sukai da Yarinyar nan ba, naji yana bata haƙuri.

Sam Farhan ba taji wani abu ya ragu game da son da takewa Sadik ba, sema wani ƙara jinsa da take a ranta.

Idan ta kwanta bacci ba abunda yake yawo a ƙwaƙwalwarta se tunanin Sadik ɗin.

Tana cikin tunanin Ba tsammani taji wani irin yanayi yana bijiro mata, wanda ba ta san menene ba balle ta tantance baƙon yanayin da ke ji a jikinta!

FaÉ—in cakwakiyar da ke cikin littafin nan ba ta faÉ—uwa, hanzarta zuwa AREWABOOKS dan samun naku.

Or subscribe it at affordable price of
₦300 only.

(Saura acemin mara kunya, labarin ne yazo a haka🙄)

Mum Amnash ina godiya da sharhinki da kuma shawara, Nagode Allah ya bar zumunci 🙏

Domin gyara Sharhi ko shawara

07063065680.
Chapter 48 · 0% Book details