Sashe 17
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mother kuwa wani takaici ne ya ƙuleta, anyi abun nan ta bawa Inna haƙuri amma ta zaunar da Daddy tana maida yadda akayi.
Daddy yace "subhanallah, Sadik É—in ne yace be santa ba?"
"Zan masa ƙarya ne? Haka yace be santa ba, amma na tabbatar da a dangin mahaifiyar sa take baze ce be santa ba, gaskiya Abdullahi yana da kyau ka sake sa ido sosai akan iyalinka, wannan halin na Sadik sam be min ba, kun sangarta shi da yawa ba shi da ɗa'a sam"
"Ayi haƙuri Inna, insha Allah za'a gyara"
Ya kalli Nana yace "Amma ayimin afuwa, an takura Mamana da yawa, bari mu É—an fita tare da ita"
Inna tace "sekun dawo"
Yai murmushi yace "taso Mamana"
Da murna Nana ta tashi, Daddy ya riƙo hannunta, suka fito harabar gidan.
"Mamana ajinki nawa ne?"
Nana tace "Ajina shida, daga wannan hutun zan shiga Sakandire"
"Masha Allah, Yarinya ta girma, Allah ya temaka"
"Ameen" ta amsa tana kalle kallenta.
Alhaji Abdullahi ya É—akko wayarsa ya nemo lambar Sadik.
Sadik na É—agawa Daddy yace "kana ina ne?"
Sadik yace "Ina BQ"
"Fito waje ina son ganinka"
Mintuna kaÉ—an sega Sadik na tahowa, sedai yana hango Nana a kusa da Daddy ya haÉ—e rai hadda hura hanci.
Ya ƙaraso yace "Daddy gani"
"Sadik, wai baka san Nana ba?"
Sadik ya galla mata harara yace "Eh amma na tuno ta daga baya"
"A gaskiya banji daÉ—in abunda ya faru ba, Inna ta yi min complain da kai Sadik, gaskiya ban ji daÉ—i ba"
"Daddy nifa ba abunda nayi, kawai kasan dama ni ta tsane ni, ba ta sona kawai, tana son Dr. Da Faruk amma ni ta tsaneni kuma wannan 'yar ai itama ba ta da kunya"
Daddy yace "ba wannan na kiraka ka gayamin ba, na kiraka ne in ƙara jadadda maka, Nana ƙanwarka ce kamar Yadda Khairat take ƙanwar ka, bana son sake jin kunyi rigima ko ka gayamata wani abu mara daɗi ka ji ko?"
Sadik fuska a cunkushe ya jinjina kai, sedai yana ɗago kai Nana tai masa gwalo, sannan a ɗan sanyaye tace "kuma ma da ya shaƙemin wuyan hijjabi na, seda na dena numfashi, wuyana ma Ni yanzu ciwo yake min, da ƙyar nake haɗiye miyau"
Daddy yace "Ya Salam, kiyi haƙuri ze dena insha Allah, dan Allah ku dena faɗa 'yan uwa ne ku"
Sadik A ransa yace "Allah ya kiyaye wannan me kama da cartoon É—in ta zama 'yar uwata, shegen bakinta kamar ramin tsutsa'
Daddy yace "bari mu fita shan icecream tare, ku ƙara sanin juna a dena faɗa"
Sadik yace "Please Daddy, i scheduled to be with my friends by 5:00pm, if you don't mind i wanna be with them"
"We must go together!" Shine amsar da Daddy ya bashi.
Sadik kamar yai bindiga, haka yasa direba ya fito da mota suka fita tare, Sadik da Nana a baya, Daddy a gaban mota.
Suna tafe a hanya da ya waigo ya kalli Farhan, se wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarsa, Nana kuma suna haɗa ido zata murguɗa masa baki hadda fari da ido.
Ji yake tamkar ya turata waje ta window kowa ma ya huta.
Daddy yace "Mamana, idan kin girma me kike son zama ne?"
Seda Nana tai wani ƙasaitaccen murmushi ta ɗanyi fari da ido sannan tace "Ina son in zama 'yar jarida, in din ga aiki a gidan Radio ina karanta labarai, ko in dinga hira da mutane, in dinga karanta labarai da turanci"
Daddy yace "wow masha Allah, Allah ya cika miki burin ki Mamana, da kin kammala sakandare insha Allah za'a samo tsadajjiyar jami'a kije kiyi karatun insha Allah"
Murmushi tayi tace "Kasan a wace gidan radion nake son in dinga karanta labaran?"
Yace "A'a"
"Ina wannan radion da Hakimi yake kaiwa yana ji da Asuba? Da kuma da rana rana haka"
"BBC ko America?" Abba ya tambayeta yana murmushi, dan ya san Hakimi da son jin BBC.
Tace "Yawwa BBC, kasan da Asuba suke hira da hausa, idan haka rana ta ɗanyi idan aka kunna sekaji suna turancin turawa, to irin wannan nake son nima in dingayi, in dinga labarai da turanci ina maƙale muryata"
Sadik ya ja wani uban tsaki, dan gaba É—aya Nana ba ta gajiya da surutu, bakinta ko ciwo ba ya yi, tai ta zuba kamar wadda aka kunnawa ashana a ka.
A hankali Sadik yace "sedai aikin gidan radion jakai shi zaki, ba dai na masu hankali ba"
"Ai kai ne jakin" ta faÉ—a tana hararar Sadik.
Sadik yace "ke da wa kike?"
"Da kai nake, waye yace kace min Jaka?"
"Nike nace miki jakar?"
Daddy yace "A'a ya faÉ—a kuma a gabana? Ba yanzu na gama yi muku nasiha ba akan faÉ—an nan?"
Nana tace "cemin yai Jaka"
Sadik a buÉ—e baki yana kallon Nana, wato bayan hauka hadda makirci ma Nana ta iya, in ba haka ba yauhse yace mata Jaka.
Daddy yai ta musu faÉ—a, yayin da Nana ta cigaba da gallawa Prince harara hadda murguÉ—a baki.
Suka je wani babban store, Daddy ya saiwa Nana kayan ciye ciye, sannan suka nufi komawa gida, Sadik be kuma cewa komai ba, Nana ne da Daddy suke ta hirar su tana masa shirme kala kala yana biye mata.
Alhaji Abdullahi yana da son yara sosai, amma baya sha'awar ya tara su da yawa, sedai duk in da ya ga yaro ƙarami yana jansa a jiki ya kyautata masa.
Se daf da magariba sukaje gida, Nana ta rungumi kayan da aka siyo mata ta kasa da gudu.
Masaukin su ta nufa kasancewar ba ta ga Inna a falo ba, tun daga waje take ƙwalawa Innar kira, sedai tana shiga ɗakin kallon da Innar tai mata yasa ta nutsu.
"Gudun me kike yi haka?"
"Bakomai"
"Ban hanaki wannan guje gujen ba, a Wannan sakarcin naki kika zubawa wancan yaron miya a jiki, shine yanzu ma kike maimaitawa ko? Bari in sa a kira Hakimin ya turo a É—auke ki a maida ke gida"
"Dan girman Allah kiyi haƙuri, na dena ba zan ƙara ba"
Inna tace "da dai halinki ne ban sani ba, kiran me kike min?"
Nana tace "kinga abunda aka saimin"
Inna tace "kince masa kin gode dai ko?"
"Eh na masa godiya"
"To amma dai ki dena wannan guje gujen"
"To na dena insha Allah"
Da magariba ma Daddy yasa Sadik a gaba sukaje masallaci su kai salla, suna tafe yana masa Nasiha akan haƙuri da son zumunci, yai masa faɗa sosai yace masa Inna ba tsanarsa tai ba, amma ya dinga zuwa yana gaida Inna.
Shi dai Sadik be ce komai ba, yai shiru yana sauraren Daddy, amma shi duk wani abu da ze haɗa shi da Inna ba so yake ba, saboda ta fiye ƙaƙalen abun da za tai faɗa.
Da safe ya shirya tsaf ze tafi Makaranta, ya tuna kashedin Daddy, É—an gajeren tsaki yai ya É—au jakarsa ya kai mota, sannan ya tafi cikin gida.
ÆŠakin Mother ya fara zuwa, yaje ya gaisheta, ya zauna yai breakfast sannan ya fito, ya nufi É—akin Inna.
Yana zuwa ba Sallama ya shiga É—akin, ya tarar Inna tana lazimi, Nana kuma nata bacci akan gado.
"Ina kwana" shine abunda ya faɗa a taƙaice.
Inna ta ƙare masa kallo sannan tace "lafiya ƙalau" tana amsawa ya miƙe ya bar ɗakin ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Yau ya makara sosai a makaranta, dan har an kammala assembly sannan yaje school ɗin, miƙewa yai da nufin ya tafi ajinsu, yaji an masa tsawa daga bayansa.
Tsayawa yai ya waiwaya yaga wane ke masa wannan ihun haka.
"Why are you always coming late ne?"
Sadik ya watsa masa harar ya gyara jakarsa, ya cigaba da bin Nazir da kallon banza.
"Am i talking to robot? Ba Magana nake maka ba?"
"To me kake so ince maka, nifa gaskiya kana takuramin, ina ruwanka dani ka bi ka samun ido ka addabeni, kamar nikaÉ—ai ne É—alibi a makarantar nan, gaskiya bana son haka ka fita a sabgata na gaya maka"
"Ni kake gayawa haka?"
"To waye kai da baza'a gaya maka ba?"
Yana gama maganar ya nufi ajinsu yana tsaki.
Nazir yabi Sadik da kallo yana jinjina rashin tarbiyya na É—aliban makarantar.
Yana zuwa ajin nasu ya tarar ba malami a ajin, kowa se harkar gabansa yake, gaban aji kuwa Nas ne da wata 'yar SS3 suke wani dancing challenge ana musu video, se ihu ake ana musu tafi.
Sadik ya ajiye jakarsa ya zauna, yana kallon su Nas, Nas ya kalleshi yace "Prince, ranar bikin Brother É—inka Akwai casu wallahi, gaskiya yakamata ka shirya mana special party iya na 'yan school É—in nan"
Sadik yai murmushi yace "nayi wannan tunanin nima, dole ma ayi special party da za'a gyagije, kan kuzo Dinner bikin"
Amin yace "idan hakane kuwa, na ga tallan wasu wanduna, Yakamata muyi order É—insu latest crazy jeans masu kyan gaske"
Sadik yace "nunamin in gansu"
Nan suka zauna, Amin ya nuna musu wandunan, Sadik yace "gaskiya sunyi kyau, ni blue É—in nan nake so É—an 15k É—in nan, ku kuma zan muku order na 10k É—in nan kuyi ankon su"
Shewa suka É—auka a gurin, Taslim tace "omo What do you mean? Mu É—in kuma fa"
Sadik yace "in dai zaku sa se ayi order da ku"
Meena tace "mw ze hana? A siya damu"
"Shikenan duk wanda ze je partyn, a saka order da shi, zan sa a bugo riguna polo, amma kowa siyan riga ze dan ubanku"
Dariya su kai, Nas yace "nasan iya wuya ba tafi 5k ba, na saiwa mata goma riguna, amma fa se zafafa wanda suka cika mata, wadda idan ta saka kayan nan za'a ga kaya"
Taslim ta buga wani uban ihu tace "yeee ina cikin wanda za'a saiwa riga ko ba'a so, dan na kai mace wallahi"
Nas yace "ba ƙarya muma mun seda ai"
Shewarsu suka cigaba da yi, suna ihu, suna cigaba da tsara rashin jin da za suyi a gurin party.
Knocking ɗin ƙofar ajin akayi, Sannan aka shigo.
Director ne ya shigo, shida wasu 'yan bautar ƙasa, maza uku mata biyu, sedai matan kiristoci ne, dan kansu ya sha ƙarin gashi.