← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 48

Sashe 22

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin Sadik kamar ɗan uwanta duk da kasamcewar alaƙar dake tsakanin su ba ta 'yan uwanta ka bace, wasu lokutan har ƙaguwa take gari ya waye taje makaranta su haɗu, ko ba komai Sadik akwai iya tsara kalamai masu kwantar da hankali.

Duk da irin wannan zama da take a gidan su, Farhan na matuƙar shakkar iyayenta, dan basu da sauƙi aguri tarbiyya sam, wani laifin idan tayi, da ido kawai za'a kalleta ta san tayi ba daidai ba ta hau tsma, dan a dunyta tsani ɓacin ran iyayenta dan kar ai mata faɗa, bata son faɗa dama rayuwarta.

Cin Abincin kawai take ba dan tana jin daÉ—in sa ba, dan ya riga yayi sanyi sosai, gashi Umman ta tashi ta bar É—akin gaba É—aya, ga tarin Magana da zata so ta tattauna da Umman amma babu fuska, ga damuwar Sadik ta dameta.

Haka ta tashi ta kai sauran Abincin Kitchen ta ajiye, ta É—au jakar Islamiyyarta ta tafi.

Shirye shiryen bikin dr. Nata nisa, ana ta faman shirin bikin su.

Gefe guda kuma kullum cikin rigima da tashin hankali yake da Nana idan suka haɗu, ita tsiwa shi rashin haƙuri.

A makaranta kuwa tuni sun fara jarrabawa, wasu suna maida hankali kan karatu, wasu kuma suna sharholiyar su kawai.

Wasu lokutan Farhan ajinsu Sadik take tafiya, dan suyi karatu yana kusa da ita, yana tamaka mata a wasu abubuwan, dan Sadik ba ƙaramin gifted bane.

Wasu lokutan kuma a Library suke zama, Farhan ba gifted ce kamar Sadik ba, she needs to read hard, amma 'yar dagiya ce sosai ga nacin karatu, ga son taga ta iya abunda ba ta iya ba.

Ko a aji idan akai abu bata gane ba, da ta tambaya gara ta bari in malamin ya fita, ta tafi gurin Prince ya koya mata.

Sedai a 'yan kwanakin nan, babban abunda yake ɓata mara rai be wuce yadda Mubarak Babba ke damun ta da kallo ba.

Kusan kullum idan ta zo ajin, se ta ganshi ya zo gurin Taslim, amma se ya dinga mata wani irin kallon ƙurilla wanda ko Sadik baya mata, gashi kallon yana damun ta sosai, sedai ta lura sam Sadik be san Mubarak na mata wannan kallon ba, ita kuma bata gaya masa ba saboda gudun buyagin sa.

Yanzu ma tana ajin, tana wani zane da Sadik ya koya mata, kasancewar za ta shiga jarrabawar basic technology bayan break, tafi gane karatun Sadik sosai akan wanda akai musu a aji.

Tana ɗaga kai tai ido huɗu da Mubarak, ya kashe mata ido tare da lashe lips ɗinsa kamar wani maye, hakan ya ƙular da ita ta ɗauke kanta da sauri ta cigaba da abunda take.

Sadik yace "Honey, waike a wani club zaki participating ne? Debate, quiz dancing competition ko kuma sport, kin san duk bayan exams Akwai wannan events É—in da za'ayi, ga end of term party da za'ai, a me zaki participating ne?"

"Ba kowanne" ta bashi amsa.

"Ban gane ba kowanne ba, ko quiz ba zaki ba?"

"Ai an É—au sunan wanda za suyi tuntuni"

"To meyasa ba'a saka da sunanki ba, naga You Are very brilliant"

"Ni nace kar a saka, ni bama son duk abunda za'ace inyi performing a gaban mutane"

"Ji ta dan Allah, kin fiye damuwa Farhan, I want you to be famous in this school, ya zaki dinga ɓoye baiwar da Allah yai miki? Yakamata ki dinga participating fa"

"Ni bana son a dinga kallona" tai maganar a shagwaɓe.

Be san lokacin da yace "wow" ba.

"Ina son shagwaɓar nan taki Farhan, tana ƙayatar dani fa"

Cikin wata shagwaɓa tace "Nifa ba shagwaɓa nai ba, kawai maganata ce a haka"

Yace "Awwn so cute, ɗan sake inji" yai maganar zuciyarsa na ƙawata masa ya rungume Farhan yai kissing ɗin lips ɗinta.

ÆŠan rufe fuska tai tana murmushi.

Yayin da shi kuma ya cigaba da bin ta da kallo, me ma'anoni daban daban.

Bisa kuskure Farhan ta É—aga kai, ta sauke akan su Mubarak da ke kissing É—in juna, shi da Taslim.

Wata mummunar faÉ—uwar gaba taji, take jikinta ya hau rawa dan abun ya bata mamaki, a makarantar nan ta fara ganin wannan watsewar muraran a zahiri.

Bata manta ranar farko da ta gani ba, a wani aji ba kowa ta hangi wani malami da wata yarinya suna kissing, se kuma yau da ake zahiran a gabanta.

Jiki na rawa ta miƙe ta kwashi litattafan ta, tace "Ni tafiya zanyi"

Sadik yace "Lafiya kuwa? Lokacin shiga exam É—in yayi ne?"

Shiru tai masa tana ƙoƙarin raɓashi ta wuce, waiwaya yai dan yaga abunda ya ɗaga mata hankali haka.

Take ya gano abunda ya jefata cikin wannan rawar jikin, se dai duk da ba yau su Taslim suka fara wannan ta'asar a gabansa ba, amma kawai yau se ya tsinci kansa a wani irin yanayi, mussaman da ga Farhan a daf da shi.

Ya tattara nutsuwarsa yace "Farhan calm down, forget about them ina jin daÉ—in hirar nan da muke, ki zauna Please"

Girgiza masa kai tayi tana son ficewa.

Yana ƙoƙarin comforting ɗinta ta zauna, amma ina jikinta har tsuma yake ta bar ajin.

Ganin Prince ba shi da niyyar bata hanya ta wuce, yasa kawai ta fita daga bencin, wanda garin fitar seda Jikinsu ya gogu da juna, wani shock suka ji a tare, wanda yasa Farhan saurin waigowa zaton ta ita kaÉ—ai taji abunda taji.

Sedai ta lura kamar shima yaji abunda ta ji, da sauri ta fice tana sassarfa.

Mubarak kuwa a hankali ya cika Taslim yana murmushi, Sadik ya kallesu a fusace  yace "kai Babba, dan kutmar.... Kar ka sake zuwar mana aji kana mana Iskanci, ka tafi ajinku ku dinga yi a can"

Mubarak yace "da can da muke a nan É—in meyasa ba kai magana ba se yanzu?"

"Saboda ba ze yuwu ku dinga takura nawa jin daÉ—in saboda iskancinku ba, Farhan Yarinya ce be kamata ta dinga kallon irin wannan abubuwan ba"

Babba yace "A'a ka manta, a cikin mahaifa take ƙarewar yarinta, shikenan dan kana wannan soyayyar 'yan ƙauyen kowa ma irinta zeyi, yarinya se kidahumancin tsiya, wataƙila ma duk ƙaryar banza ce, dan yaran nan suma sun san komai"

Sadik yace "what so ever dai, in ma zakuyi idan tana nan gaskiya ku dena, na gaya maka in ba haka ba za'aji kanmu da kai"

Nas yai dariya yace "Allah ya temaki Prince, Your royal highness"

Sadik yai tsaki yaƙi kulashi.

Taslim tace "kaifa Prince ka fiye abun haushi, kai kaƙi bari Yarinya ta waye, kuma ka hana wasu jin daɗinsu akan me?"

Wata uwar harara Prince yai mata, tai murmushi ta kalli Mubarak tace "one more time Dear"

Suka kuma rungume juna suna kissing, Amin yace "shegu ai baku burgemu ba, tun da ba kuyi wancan aikin a gabanmu ba"

Mubarak ya saki Taslim yace "ji shege, Allah ya shiryeka"  suka cigaba da dariya kamar ba suyi komai na damuwa ba.

Prince kuwa sake jefa masa wani tunanin su kai a zuciyar sa, yana sake kwaɗaituwa da Farhan, shi duk iskancin sa ba ruwansa da kowace 'ya, banda ma yanzu da ya fara soyaya iyakar sa da mata, ayi hira ai ciye ciye, ayi party amma ba dai ya taɓa 'yar wani da sunan aikata alfasha ba.

Da fari sam ba shi da feelings akan Farhan, yana dai sonta ne sosai, Amma zigar abokansa da RUƊIN ƘURUCIYA, sun fara ɗibarsa zuciyarsa na ƙawata masa ko sau ɗaya yai kissing ɗin mace.

Shi da fari kiss ƙyama yake ba shi idan su Nas  sunayi, yaita ce musu ƙazamai, amma akan Farhan yana matuƙar son ko sau ɗaya yayi, yaji me suke ji ne, zuciyarsa na fara kissa masa abubuwa marasa kyau akan ta.

Ita kam gaba É—aya mamaki ya hanata sukuni da damuwa duk suka addabeta, ta godewa Allah da yasa masoyinta baya cikin irin wannan masu muguwar É—abi'ar ta fitsara.

Ta shiga ajinsu tana zancen zuci, sedai abun mamakin suda suke daf da shiga jarrabawa, se ta tarar da 'yan ajin nasu sunyi group sunyi tsit.

Zaton ta karatu sukeyi, dan haka ta nemi guri ta zauna, sedai tana zama taji muryar Haseena, ba ta kai ga jin me take faÉ—a ba, taji sun kwashe da dariya suna shewa.

Ba ta damu ba, ta cigaba da abunda ke gaban ta, sedai suna gama shewar da sharhin, suka sake yin tsit, Haseena ta É—ora da abun da take.

Waya ce a hannun Haseenan, tana karanto musu wani abu, wanda da fari Farhan ba ta kai ga gane menene ba.

Sedai da ta ƙara natsawa, ajin yai tsit ta fara fuskantar me Haseenan ke karantowa, wata irin narkakkiyar batsa Hassenan ke karanto musu, ba kunya ba tsoron Allah ba saye komai, yadda yake a rubuce haka take karanto musu.

Lilly tai shewa tace "Kambu dama haka abubuwa ke wakana amma muna gefe? Dama akwai irin wannan zafafan Novels ɗin na hausa ban sani ba, ai ban taɓa zaton ana irin wannan abubuwa haka ba, kuma ban san ana karantawa a waya ba, na ɗauka se a bugaggen littafi ai"

Haseena tace "inji wa, bugaggen littafi da kenan, ai yanzu an samu marubutan yanar gizo, littafi se wanda ki ke son karantawa, irin wannan litattafan zaki same su kala-kala. A gurin ƙawar yayata naji suna hirar, ina nan na bazama ina ta tara mana su, wasu marubutan kiji nasu littafin zallar nishaɗi ne, wasu hikima da iya rubutu kamar a gabanka akeyi, wata kuwa litattafan na ta zakiga wa'azi ne kawai"

Yasmin tace "wayake ta wani littafin wa'azi, idan wa'azi ne ai kasan in da zakaji, amma ga irin wannan yadda ake fayyace komai, wanda idan tambaya za kai bame gaya maka, sedai ace maka kai yarone ba yanzu ba, amma ji yadda ake faÉ—ar abubuwa, kai ni gaba É—aya ma se naji kamar aimin Aure yanzu wallahi"

Lilly tace "to shegiya zalamammiya, kema kar dai ace sex addict É—in ce?"

"To wa ya sani ma, tunda kai bawa ba gwadawa kai ba"
Chapter 22 · 0% Book details