Sashe 34
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aka dinga mata Nasiha da Addu'oi, sedai kana kallonta kasan itama 'yar boko ce, ba wani kuka da take yi, gashi a ƙalla ta kai shekaru ashirin da bakwai.
Inna ba tace komai ba, se mamakin yadda ake ajiye 'ya'ya sukai mizani kamar wannan ba aure da sunan boko, bayan mutane ne su ba ƙarafa ba, a haka ake lalacewa Garin zurfafa bokon nam, dan Akwai lokacin da tilas jiki na buƙatar abokin rayuwa, kuma ga uwa uba gurin yin bokon a cakuɗe ake maza da mata, dan itama dangin amaryar da 'yan makarantar ta su ba ƙananan shakiyayyai bane, irin abunda suka dinga yi a gurin bikin.
Da gani baza'ace Jidda miji ta rasa shi yasa ba tai Aure da wuri ba, saboda ta na da kyau sosai, ra'ayin Auren ne kawai ba'aiba se an gama bokon da suka ɗauketa kamar wani tikitun jin daɗin duniya, ba 'a taɓa cewa ba za'a aurar da 'ya se ta sauke Alqur'ani ba, da wasu litattafan addini ba sedai ace se ta gama boko.
Haka Inna tai ta zancen zuci ita kaÉ—ai, aka gama yi wa amarya nasiha aka tafi rakata É—akin miji.
Shikam Sadik ji yake dama shine yai wannan Auren haka, amma ace ba za'ai wa mutum Aure ba se bayan ya gama boko, idan kuma mutum ya mutu be gama bokon ba kuma beyi Auren ba fa?
Shikenan Allah ya yayewa Dr. An bar shi shida Faruk a wannan wahalar.
Ya dinga tsaki yana juyi, yai ta zuba ido ko Farhan za ta kirashi, amma shiru ba ta kira shi ba, kuma gashi tace idan ba ita ta kira ba karya kirata, gashi tace masa cikin ta na ciwo yana son yaji halinda take ciki.
Ƙarshe dai se haƙura yayi ya kwanta bacci.
Akai biki aka watse, amma Mother ta ga Inna taƙi tafiya, ta na so tai magana ta na jin tsoro, amma ita har ga Allah ta gaji da zaman Inna, dan wajen watan ta guda a gidan, tun da su kai Aure da Alhaji Abdullahi Inna ba ta taɓa zuwa ta kwana a gidan ba, se a wannan karon, kuma ita har ga Allah zaman na Inna ya isheta.
Alhaji Abdullahi na shan cofee É—insa da daddare kamar yadda ya saba, Mother na sake gyara masa shimfiÉ—a, tana saka turaruka tace "D mace ba kuyi magana da Inna yaushe zata tafi bane?"
Ya ajiye kofin hannunsa yace "kina da damuwa da hakane?"
"A'a, naga ba ta taɓa zuwa ta daɗe haka bane"
Yace "to se a kai yaya? Ba ta da ikon yin hakan ne? Ko kin manta gidan É—anta ne?"
"A'a ban manta ba, kawai na tambaya ne"
Be kuma ce mata komai ba ya cigaba da shan cofee É—in sa.
Bayan sallar Asuba, gari yai haske sannan Inna ta koma bacci, Nana na ganin Inna ta kwanta bacci ta tashi ta fito, ita gaba ɗaya kamar akan ƙaya take, ta gaji da zaman Gidan nan, ta rasa zaman me suke a gidan suka ƙi tafiya.
Zuwa yanzu ta saba da masu gadi da ma'aikatan gidan, saboda shegen surutun Nana da san gwaninta, gata da shiga rai dan haka duk sun santa.
Faruku ya fito hannunsa riƙe da kwando, da manyan flask na Abinci a kai.
Da sauri ta ƙarasa in da yake tace "ina kwana"
Yai murmushi yace "lafiya ƙalau, kina lafiya"
Maimakon ta amsa seta jinjina masa kai.
Tace "kawo in tayaka É—auka"
Yace "No ya miki nauyi, gidan amarya zanje kai musu Abinci, ko zaki rakani?"
Da sauri Nana tace "eh zan raka ka, dama banje ba"
Yace "ok let's go"
Ta bishi zuwa mota, ya buÉ—e mata gaba ta shiga, ya ajiye Abincin a bayan motar, ya kunna suka tafi.
Sun ɗanyi tafiya, kan su ƙarasa gidan Usman, suna tafe suna hira da Nana ta na zuba masa shirme kala kala.
Gidan babba ne, sedai be ka gidan su Girma, buzun da ke gadin gidan yana ganin Motar Faruk ya buÉ—e musu, suka gaisa da Faruk, ya shiga da motar.
Ta ƙarewa harabar gidan kallo, sannan ta kalli Faruk tace "gaskiya gidan nan me kyau ne, yayi kyau sosai"
Yace "dagaske?"
"Allah yayi kya masha Allah"
"Zan gayawa dr. Ince kin yaba gidansa, kimce yayi kyau"
Ɗan kwaɓe baki Nana tai, dan da Dr. Da Sadik ba suyi mata ba, Dr. Ba shi da fara'a Sadik kuma bashi da mutunci.
Ƙofar falon Faruk yai knocking, sun ɗan jira, 'yan mintuna sannan aka buɗe.
Dr. ne ya buÉ—e, da alama bacci suke, Faruk yace "wai haryanzu baku tashi ba?"
Uasman ya É—an yamutsa fuska yace "kai kullum seka dinga mana sammako haka, ka dena kawo Abincin nan haka Please"
Faruk yace "Ai nima Umarnin Mother nake cikawa, ita zaka cewa a dena kawo muku Abinci"
Usman yasa hannu ze karɓi flasan Abincin, amma Faruk yace "meye haka? Wallahi semun shiga, Nana wants to see your bride, semun shiga"
Ya ture Ussy ya shige, Nana tabi bayansa tana leƙa fuskar Usman, ko zeyi Magana, amma taga beba, se yamutsa fuska da yake alamar an takurashi.
A Falo suka zauna, Usman ya wuce bedroom ya barsu, Faruk ya kunna musu kallo yace "muna nan, ka gama kumburin ka, se Nana ta ga amarya"
Nana tace "naga kamar yaji haushi fa, ko mu tashi mu tafi ai naga gidan, kuma naga amaryar ranar biki"
Faruk yace "ba haushi yaji ba"
"Amma ai naga ya sha kunu fa"
"Ai shi haka yake, ba ya dariya sosai shiyasa ba'a fiye gane ɓacin ransa ba, koma yaji haushin ƙyaleshi kawa, a nan ma zamu karya muci har na rana sedai su fashe shi da amaryar"
Dariya Nana tayi tace "idan zasu fashe semu tafi"
Ya biye mata suka cigaba da hirarsu, kusan mintunansu talatin, sega Jidda ta fito ita da Usman, tana sanye da doguwar riga da hula akanta.
Tana ganin su Faruk, tai murmushi tace "Afuwan uncle, mun barku a falo ban san kunzo ba, be tasheni ba"
Faruk yace "ai dama nasan baze tashe ki ba, nikuma nace muna nan se kin tashi"
Tai murmushi tace "ya gida ya Mother na"
"Tana lafiya ƙalau, tana gaisheku, ima bacci na ta kirani a waya, wai inje Kitchen in ɗakko Abinci in kawo muku, mun kawo kuma mijinki se wani haɗe rai yake yi"
Banza Dr. Yai musu, ya zauna ya É—au remote yana canza chanel.
Nana ta kalli Jidda tace "Ina kwana"
Jidda tace "Lafiya ƙalau, ya kike?"
Nana a ranta tace "wai su wannan suyi hausa ma se sun mata iyayi" a fili tace "lafiya ƙalau"
Jidda tace "Uncle ina kuka sami wannan ne? Naga dai ba Khairat bace, Khairat ta girmi wannan, kuma gashi tana kama da ku"
"She's our little sister"
"Haba dai, dama Mother na da 'ya mace ne?"
"Cousin sister É—inmu ce, tana gidan Hakimi ne ita"
Jidda tace "Allah sarki, sannunki kinji"
Nana tai murmushi kawai, Usman yana ta canza tashoshi, ya kamo MBC3 ana film É—in up, Nana tai farat tace "laaaa cartoon dan Allah a bar mana"
Camzawa yai ba tare da ya kula Nana ba, Jidda cikin shagwaɓa tace "haba Baby, dan Allah ka bar mata mana"
Ba shiri Nana tace "subhanallahi Baby kuma"
Take dariya ta ƙwace mata, ta kalli girman Usman fuska duk gashi, amma ana ce masa Baby.
Dariya Jidda tai tace "it sounds strange to you ne? Yayi girma ince masa baby ko?"
Nana dai dariyarta ta cigaba da yi, dan babyn nan ya bata dariya sosai.
Faruk yace "mu fa gaskiya ba mu karya ba, dan haka a haÉ—a Abinci mu ci"
Jidda tace "eyya sorry, kar ace ina da rowa ban san ba ku ci Abinci ba ai, bari in É—akko plates se mu karya tare.
Ta ɗakko kwanuka a Kitchen, ta zuzzuba Abincin ta haɗawa kowa tea ta bashi, suka fara ci, sedai Nana ta kasa sakin jiki taci Abincin se ɗan tsakurar sa da take saboda su Faruk da ke gurin.
Maimakon da suka gama cin Abincin su tashi su tafi, se suka shantake a gidan dan Jidda ba ƙaramin dariya surutun Nana yake bata ba.
Inna kuwa tun bayan farkawarra ba ta ga Nana ba, ta zaci É—an fita falo tai zuwa harab zata dawo, amma taji shiru ba taga motsinta ba, Nan da nan ta fita nemanta da kanta, sedai ba Nana ba alamarta a gidan nan.
Hankalin Inna ya É—aga ta shiga tanbayr masu gadi, da masu aikin gidan amma suka ce ba su ga Nana ba.
Da hanzari Inna ta koma babban falo, wanda yai daidai da fitowar Alhaji Abdullahi, kallo É—aya yaiwa mahaifiyar ta sa ya fuskanci akwai matsala.
Cikin damuwa yace "Hajiya Inna, lafiya kuwa?"
"Yarinyar nan ce ban gani ba, tunda na farka ban ganta ba, bata gidan nan"
Yace "Subhanallah, garin yaya babu kuma wanda ya aiketa?"
"Bana tunanin hakan, dan ba in da ta sani"
Mother ce ta fito ita da Sadik, daga sashen ta, tai tozali fa su a tsaye cirko cirko.
"Lafiya kuwa?" Mother ta tanbaya.
Alhaji Abdullahi yace "Nana ce ba'a gani ba, tun É—azu ba ta gidan nan an tambayi masu gadi sunce ba su ganta ba, ka ga Sadik ka fita ka É—an zazzaga layu kan nan ko wani gurin ta fita.
ÆŠan buÉ—e baki Sadik yai yace "Abba ni ta ina zan fara neman ta? Ina zan nufa?"
"Koma ina ne ka nufa, kaje ka zazzaga ko Allah ze sa ka ganta"
Ran Sadik yai matuƙar ɓaci, ya bar falon yana ƙunƙuni, wai ya fita nemanta se kace wata Akuya.
Mother kamar za tai magana, amma ta fasa dan ta kula kamar kwanan nan Inna zuga Alhaji Abdullahi ta ke, da ta É—anyi masa kuskure kaÉ—an se ya fara mata masifa.
Nana kuwa tare suka shiga Kitchen da Jidda su kai girkin rana, suna yi Jidda na cin dariyar Nana, babban abunda ke ƙara bata mamaki da burgeta game da Nana be wuce yadda Nanan ke magana da manyance ba, a shekarunta wasu abubuwan tayi ƙanƙanta da faɗinsu, amma ba abun mamaki bane, tunda a hannun tsofaffi take.