Sashe 40
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da an fita break, Farhan ke tattara kayanta ta tafi ajin su Sadik, sedai can É—in ma da nasu kalar watsewar, ga Mubarak Babba da ke cigaba da takura mata, wani rashin mutuncin ma se sunga tazo ajin suke fara yin sa.
Haka nan take jin zaman makarantar ya isheta, mutum É—aya ke bata farinciki a makarantar Shine Sadik.
Kasancewar ta tare da shi ne kawai ke bata nishaÉ—i da É—ebe mata kewa, amma duk lamuran É—aliban har malaman sun ishe ta.
Nana ke zaune a gefen Hakimi ta na ta zuba masa surutu kala kala, yayin da yake kashingiÉ—e yana sauraronta, fuskarsa na bayyanar da tarin murmushi.
"Kaga Baba Alaji, da mukaje bikin nan kawuna ya tambaye ni me nake son na zama idan na girma"
"To ke me kika ce masa?"
"Ai ni kasan 'yar jarida nake son zama, me karatu da turanci, irin na turawan nan ina son inga na iya turanci sosai da sosai fa"
Hakimi yai murmushi yace "Ai Yanzun ma kin iya, tunda in anyi kina ji"
"Taɓ me na iya, ai idan ina ƙauyen nan na fi iya turanci, da mukaje birni duk se naji ba turancin, kaji irin turancin da suke kuwa kamar Turawa, ni bama na gane irin nasu turancin wallahi"
Hakimi yai murmushi yace "to Allah ya ida nufi, ya nuna mana kammala karatun naki"
Nana ta gyara zama tace "ina ga fa nima ƙasar wajen ze kaini, inyi karatun fa"
"Ba Gidan uban da zaki, kina gama Sakandire Aure za'ai miki, kya yi karatun a can, dama ba Jamilin Gidan me unguwa bane yake biyo ki idan na aike ki ba, da kin gama makaranta za'a ace ya fito" Inna ce take wannan bayanin a ƙofar ɗakinta.
Kwaɓe fuska Nana tayi tace "ni wallahi ba saurayina bane, dan Allah ki barni in karatu, wallahi ban isa Aure ba, kefa kike cewa Ni yarinya ce"
"Eh ke yarinya ce a yanzu ba, amma kan lokacin ai kin ƙara girma"
Nana ta kalli Hakimi tace "dan Allah ka sa baki, nima a barni inje inga ƙasar wajen nan inyi karatu"
Inna tace "idan kika je ƙasar waje karatu, ba bu me Aurenki za'ace idonki ya buɗe"
"Wallahi za'a samu me Aure na, kinga lokacin na zama 'yar gayu sosai, dama ni ba zan Auri ɗan ƙauyen nan ba, se ɗan gayu, ɗan birni wanda ya iya turanci"
Hakimi yace "Banda abunki, shi wannan turancin in kinyi Auren shi zaki ci ne, ai mutum Nagari ake nema"
"Eh to nagarin, kamar dai Farukun Gidan kawu"
Hakimi yace "shi kike so kenan"
Kamar wadda ake ce tayi zunubi tai farat tace "A'a ba haka ba, taɓ kawai dai ya iya turanci, kuma yana da kirki sosai, ba kamar wannan dogon mara kunya ba"
"Waye kuma dogo mara kunya"
Nana ta ɗan keɓe baki tace "wannan Sadik mana, wallahi na tsane shi ba shi da kirki kwata kwata, kaga yadda ya shaƙeni zemin duk ranar dan na zuba masa miya ban sani ba, ni kuwa na ɗau wandonsa me tsada na sa a ruwan datti"
Hakimi ya É—aga kai ya kalli Inna su kai ido huÉ—u, ya jinjina kai yace "Kar ki sake cewa kin tsani mutum, kuma kinga ai shi yayanki ne, karki sake"
"Baba Alhaji, yaro ne fa shi, tsawo kawai ya fini, dan haka ba wana bane, Faruk ne Yayana, me Kirki yaita saimin abubuwa da muna gidan"
"To uwar son abun duniya, dama saboda yana sai miki abubuwa shiyasa kike ta rawar kai a kansa, tashi ki bar nan uwar surutu, ko gajiya ba kya yi, kamar an kwance ruwa ki ta zuba"
Nana ta tashi, sum sum ta bar tsakar gidan, Hakimi yace "da kin ƙyaleta, a hirar ta ta nake fuskantar wasu abubuwan"
Inna tace "Na sani, nima a haka nake bugun cikin ta nake jin abunda ke ranta, amma wasu lokutan surutunta yai yawa, idan ba'a taka mata birki, a waje ma zata iya zuwa tai hakan"
Prince ya riga yai registration ɗin jarrabawar ƙarshe da wanda zasu gama a shekarar, zeyi tsallaken aji guda, duk a ƙoƙarin cinma burinsa na ganin ya shiga jami'a da wuri, dan ya samu ya mallaki abunda zuciyar sa ke so.
Sedai ɓangare guda idan ya tuna da ze bar makarantar, yai nesa da Farhan gaba ɗaya se ya ji damuwa ta mamaye shi, yana matuƙar jin Farhan a ransa.
Kamar kullum, Nazir ya kammala koyarwar sa a ajin su Farhan na ranar, ya bawa Class rep Umarnin ya tattara masa litattafan 'yan ajin ya kai masa ze duba notes.
Yana fita Lilly tace "kan bala'i, wai dagaske gayen nan yake checking note zeyi? Aikuwa kashi na ya bushe dan ba na wani note wallahi"
Haseena tace "Ubanki ze ci la'ada waje wallahi, kin raina mutumin nan kowa na tsoron sa amma banda ke"
Lilly tace "ke bari kawai, wallahi nima ina tsoron sa, ko kallona ya fiye yi se inji hantar cikina ta kaÉ—a wallahi, ni yanzu ya zanyi?"
Yasmin tace "to ki sauri ki ksrɓa kiyi mana"
"Ke wallahi ba zan ba, note É—in fa fa yawa, ba yi nake na Assignments É—in sa ma bayi nake ba, sedai ya kashe ni ya huta kawai"
Class rep É—in su yace "ba shakka kin shahara Lilly, mitumin nan ba raga miki ze ba"
"Aikuwa sedai ya kashe ni, ni bari ma in tattar maka litattafan, idan ka tashi sedai ka kai masa kawai"
"Aikuwa da kin kyauta"
Lilly ta tashi ta na karɓar litattafan 'yan aji, ta zo kan Farhan, ko littafin ba ta ɗakko ba.
Lilly tai murmushi tace "Sannu basarakiya matar Prince, a dole se an nuna mana sarauta, kina kallo ina haÉ—a litattatafai amma ko É—akkowa baki ba"
Kunya ce ta kama Farhan, tai murmushi tace "Yi haƙuri, ba wata sarauta wallahi, hankalina ne yana wani gurin"
"Eh hankalinki na kan tunanin sa ko?"
Murmushi Farhan ta cigaba da yi, ta É—akko littafin ta bawa Lilly.
Lilly ta karɓ ta fara buɗe littafin tace "Masha Allah, ke komai naki abun burgewa, kalli handwriting ɗinki me kyau kamar ke"
Murmushi ta cigaba da yai tana sunkuyar da kai, Lilly na cikin buÉ—e littafin ta tsinci takaddar haihuwar Farhan a ciki.
Farahn ba ta san takaddar ta na ciki ba, Lilly ta tsaya tana duba takaddar.
"Wow Masha Allah, Ashe akwai birthday me yaji a school É—in nan, saura sati É—aya birthday É—in ki Ashe?"
Da sauri Farhan tace "A'a ni ba na wani birthday, ban ma san takaddar na ciki ba, bani in ajiye"
Lilly tace "ke kin isa, budurwar Prince guda ace ba za'ai celebrating birthday É—in ta ba, wallahi dole ayi let me go and show him in case be sani ba"
Lilly tai waje da sauri da takaddar a hannunta, gaba É—aya Farhan ta rasa abunyi, sam ba ta so abunda Lillyn ke shirin yi ba, meyasa za tai mata haka.
Cikin sa'a Lillyn na fita, ta hango squad É—in su Sadik É—in, suna tahowa da alama zasu fita ne, Sadik na maga duk sun bashi attention É—in su.
Tun lokacin da Lilly ta bi Sadik, suka kai Farhan gida idan ya ganta ya kan ɗan sakar mata fuska, saɓanin da da ba ruwansa da su, hasali ma Juniors suna tsoron sa, kuma ta fanni guda ana son sa saboda yawan kyautarsa.
Ta ƙarasa in da suke, Sadik ya ɗan kalli Lilly, amma be ce komai ba.
Miƙa masa birth certificate ɗin tayi, ya karɓa yace "wannan na menene?"
Tai murmushi tace "nasan wataƙila ba ka sani ba, birth certificate ɗin Farhan ne, on 8th ne birthday ɗin ta, nasan maybe ka shirya wani abun"
Murmushi yai ya fara duba takaddar, yana bawa duk wani abu da ya shafi Farhan mahimmanci.
Ya shafi sumar kansa yace "Wow, naji daÉ—in wannan Albishir É—in, nasan ba dan kin gayamin ba ba zata faÉ—an ba, dole ai celebrating, kina da kyautar wannan Albishir É—in"
Lilly tace "godiya nake Allah ya raya mana Farhan, ya kaimu lokacin abun"
Sosai Sadik yai murmushi har seda haƙoransa suka fito yace "Ameen"
Ya kalli su Nas yace "guys kuyi gaba, let me go and see her first"
Aminu ne ya fara jan uban tsaki yace "what a shit! Wallahi tun fa Yarinyar nan ta zo school ɗin nan ka zama wani bita zai zai, ni na rasa uwar me kale bi a Yarinyar nan, ni banga wani abun burgewa a tare da ita ba, amma kai ta wani ɓare ɓare a kanta"
Wani É—an fito Sadik ya ja, me cike da rainin hankali yai gaba abunsa ya nufi ajinsu Farhan"
Nas yace "ƙyale shi, nasan abunyi, nasan dole ze haɗa mata birthday ai, tunda kuɗin banza gareshi be san cuwon su ba, da wannan damar zamuyi amfani musa shi a hanya"
Amin yace "what a good idea, shi banda wawanci ma, wannan 'yar talakwan kawai ya sarara ya watsar da ita, ko wani abun yai mata ba mataki zasu iya É—auka ba, amma ya kankane ya hana kowa wai shi Aurenta zeyi"
"Bar banza za muyi maganinsa ne"
Ya na zuwa ya tarar da Farhan ta cika tai fam tana zumɓura baki, Lilly na mata dariya.
Yana zuwa ya kaɗa paper a fuskarta, ta miƙa hannu zata karɓa amma ya ɗauke yana murmushi.
Yace "ke yanzu birthday É—in naki ya kusa, amma baki gayamin mu fara shiri ba"
"Ni ba wani shiri, ni bana wani birthday fa"
"Wannan karon zaki fara, hall zamu kama ƙarami ai shagali kamar ana bikinmu"
"Dan Allah ka bari, base anyi ba fa, ni a gida baza'a barni ba ma"
Tsuke fuska Sadik yai yace "in dan gida ne, ba matsala zan san yadda za'ai a fitomin da ke, amma sekin zo gurin nan, in kuma ba kya so ne ki gayamin"
ÆŠago fararen idanunta tai ta sa a nasa, amma ta kasa sake musa masa se shiru da tai ta sunkuyar da kai.
"Idan ina Magana, ko ince ayi abu kina mun gaddama, I will....."
Se kuma yai shiru, ya juya ya fita.
DOMIN GYARA, SHARHI KO SHAWARA
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa:  🎗ï¸ðŸŽ—ï¸ðŸŽ—ï¸ðŸŽ—ï¸ðŸŽ—ï¸ðŸŽ—ï¸ðŸŽ—ï¸ðŸŽ—ï¸
RUƊIN ƘURUCIYA
PERFECT WRITERS ASSOCIATION