← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 48

Sashe 20

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rumtse idonsa yai sosai yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya furta Farhan, yai ruf da ciki ya rirriƙe pillow ɗin da yake kai, a hankali ya dinga faɗin "Subhanallahi wabi hamdihi, subhanallahil azeem"

A haka bacci yai awon gaba da shi, sedai kasancewar ya saka abun a ransa, se ga Farhan a cikin baccin sa, a yanayi me wuyar fassara.

Yadda ya kwanta da wannan matsanancin tunanin, haka ya dinga mafarkai barkatai har Asuba, kiran farko ya buɗe idon sa, ya jiƙe sharkaf da gumi, duk da A.C da ke ɗakin nasa.

Tashi yai yayi shiru yana tunanin mafarkin da yai, jinsa yai somehow abnormal.

Tunani ya shiga yi yanzu se yayi wanka kenan? Amma ai mafarki ne kawai, shiru ya kuma yi yana tunani, ya É—akko wayarsa ya shiga yai searching, tabbas wanka ya kama shi since he has a dreams.

Tsaki ya ɗanyi, ya sakko daga kan gadon, a gurguje ya shiga banɗaki yai wanka yai alawala, ya fito ya zura rigarsa, sedai yana gamawa sega Faruk ya shigo ɗakin nasa, ya kalli Sadik yace "Au ashe ka tashi? Sarkin nauyin bacci, yau anyi abun arziki, dama Daddy ne yayo waya, amma ya nake ganin kanka kamar a jiƙe?"

Tsaki Sadik yai yace "Alwala nayi fa"

"Alwalar ce ka ke a jiƙe haka, kalli jallabiyar taka fa duk ruwa"

Banza Sadik yai masa, ya É—au turare ya fesa a jikinsa, ya saka hullar tashi ka fiye naci.

Faruk ya kwashe da dariya yace "inyee, Su Auta an girma, iyee sekace wani magidanci wanka da Asuba haka, Lallai ka girma ka isa Aure, na yarda da batunka na cewa da kake ka isa Aure"

Haɗe rai Sadik yai yaƙi cewa uffan, a falo suka haɗu da Usman shima ya fito, suka fito suka tafi masallaci, sedai suna tafe Faruk yana tsokanar Sadik, Sadik ya ƙulu matuƙar ƙulewa, amma yaƙi cewa komai dan kar Daddy ya fuskanci wani abu.

Da suka dawo daga sallar ma Sadik be koma bacci ba, ya nemi guri ya zauna yana ta tunani kala kala daban daban a zuciyar sa.

Haka ya zauna har gari yai haske, ya shirya ya fice dan tafiya makaranta, ba tare da ya shiga ko cikin gidan ba balle ya karya yai musu sallama, direbansa ya fara jan motar kenan ya hango Nana ta fito, se yanzu ya tuna abunda tai masa daren jiya, tabbas ba dan ya riga ya shiga mota ba da Allah kaɗai ze iya raba shi da ita yau, se kuma ya tuna yana taɓata ze sha tujara a gurin kakarsa, kuma Daddy ma ze masa faɗa, ƙwafa yayi dan ko me za'ai sedai ayi amma se yai maganin ta.

Haka ya tafi makaranta yana ƙananun sambatu.

Farhan ta shirya tsaf cikin Uniform ɗinta, sedai a jikinta tana jin tana ƙara ƙiba, dan skirt ɗin da ta sa tana jin yadda ya matse ta sosai, ta juya ta juya ta ƙarewa kanta kallo a madubi, ji take kamar ta cire shi ta canza wani, amma ɗaya skirt ɗin ba a goge yake va gashi ta makara sosai.

Ta ɗakko ƙaton hijjabin ta ta ɗora akan Uniform ɗin sannan ta fito tsakar gida, ta kalli Ummanta da ke kaiwa tana komowa a tsakar gida tace "Umma na tafi"

Ba ta kalli in da Farhan take ba tace "Allah ya kiyaye" cikin yanayin sanyin halin ta, ta wuce É—akin mahaifinta, se da tai sallama akai mata izinin shiga sannan ta shiga.

Tace "Abba ina kwana"

"Lafiya ƙalau Farhan, za'a tafi makarantar ne?"

"Eh Abba zan tafi"

Ya saka hannu a aljihunsa ya É—akko Naira É—ari ya bata yace "ga kuÉ—in makarantar ki, Allah ya tsare kin karya dai ko?"

"Eh Abba na karya"

"To shikenan, Allah ya kiyaye hanya, ki kula da kanki ki kula da addinin ki da mutuncinki kinji Farhan"

"To Abba insha Allah, nagode Sosai"

Ta miƙe ta fito, a soro ta tsaya ta buɗe jakarta ta ɗakko turaren da ta siya da kuɗin da Sadik ya bata, ta shashshafa a jikinta, dan tana matuƙar son ƙamshi a rayuwarta, sedai ummanta bata damu da ta ɗorata a hanya da yadda zatai amfani da kayan gyaran jiki ba, ko da yake yaushe ma ta kulata balle ta koya mata wani abu makamancin haka.

Ta gama shafawa ta maida shi jakarta, sannan ta fita ta nufi titi.

Gaba ɗaya Sadik yau kamar mara lafiya haka yake jinsa, yama rasa gaba ɗaya meke masa daɗi, duk yadda abokansa suka so jansa da surutu amma yaƙi magana, ƙyaleshi su kai, dan sun san haka yake yi wasu lokutan.

Ana ta shirye shiryen fara jarrabawa a makarantar, wasu malaman duk sun ƙarƙare darususskan su, wasu sunyi teses ɗin da duka zasu yiwa ɗalibai, zasu fara jarrabawa.

Farhan ta kasa fita daga ajinsu ma, gani take kamar ita za'a dinga kallo idan ta fita saboda yadda skirt ɗinta ya matse ta sosai, gashi bironta ya ƙare tana son siyan wani, haka ta daure ta fita siyan biron, sedai shop ɗin a kulle yake.

Kawai ta yanke shawarar zuwa gurin Prince ta karɓi aron nasa.

Ta É—au littafinta ta fita, taje ajin nasu sedai tana shiga ta duba gurin zamansa ta ga baya nan, ita ba iya sakewa take da 'yan ajinsu ba, dan haka ta nemi guri kawai ta zauna tana jiran dawowar Prince É—in.

Gudu gudu sauru sauri take hawowa step ɗin benen, jacket ɗinta na riƙe a hannunta ɗaya, ɗaya hannun kuma na riƙe da jarkar youghurt, yana daga saman benen a cikin malamai yake hangota tana hawowa, ilahirin jikinta na rawa, kanta a ƙasa ba tsammani tai karo da shi a tsaye yana kallonta.

Ƙoƙarin kaucewa tayi amma yaƙi ba ta hanya, yace "What did I told you last day?"

Kallon hannunta tai da ta riƙe jacket ɗinta, ta kalli jikinta ta ɗan yatsuna fuska tace "sir zafi nake ji shine fa na cire ta"

"Shut up! Bance karki sake cire jacket É—inki ki tafi haka ba?"

Ta yatsuna Fuska tace "kace"

"Shine kika cire rigar kike yawo da ita a hannu dan rashin kunya ko?"

Shiru tayi tana zumɓura baki taƙi Magana, yace "oya wear it back"

Tana harararsa ta gefe haka ta maida rigar, sannan ya batta ta tafi.

Tana barin gurin tace "É—an rainin hankali kawai" ta sake cire rigar ta tafi aji.

Corper Nura yace "Nayi matuƙar mamakin ganin irin wannan dress code ɗin na student, a garin Kano"

Nazir yace "ai ba kai kaÉ—ai ba, abun da mamaki kam kamar ba garin musulmi ba, kalli yadda suke yawo kamar ba musulmai ba, kuma babban abun takaicin an rasa me musu magana akan wannan shigar ta yaran, kuma su kansu iyayen suna kallo amma sun yi shiru"

Nura yace "amma hakan be dace ba, ze iya buɗe ƙofar ɓarna a tsakanin malami da kuma ɗaliban kansu"

Nazir yace "ai kai kaga haka, su ba wannan ne a gabansu ba, su makarantar burinsu yadda zasu samu kuɗi, su kuma iyayen burinsu ace yaransu na makaranta me tsada, amma ɓarna kam a makarantar nan sedai ai shiru kawai"

"Subhanallah, Allah ya kyauta"

Nazir ya amsa da "Ameen"

Farhan kuwa gajiya tai da zaman jiran Prince, ga shi 'yan ajin se fitsara suke kala kala a gabanta, dan haka ta tashi zata bar ajin, harta fito taji yace "See me here"

Ta waiga taga yana tahowa a hankali kamar mara lafiya, tai murmushi tace "ina ka tafi ne na daÉ—e ina jiranka fa"

"Naje cin Abinci ne ina jin yunwa, kuma nasan idan nazo ma nace ki rakani ba zaki bini ba"

Tai murmushi ta koma ajin nasu, tana gaba yana binta a baya, sedai shima ya lura da yadda take tafiya a kunyace saboda yadda skirt É—in ya matseta sosai.

Seda ta tsaya ya zauna sannan itama ta zauna, tace "dama pen nazo ka aramin, naje in siyo shop a rufe"

Murmushi yai yace "in baki pen dai ba in baki aro ba"

Ya zura hannu a aljihunsa ya ɗakko sabon biro ya bata ta karɓa tace "Nagode sosai Allah ya saka da Alkhairi"

Be magana ba se jinjina mata kai da yayi, ta zauna tana ta 'yan rubuce rubucen ta, da alama tana solving maths ne, shikuma ya ƙura mata idanun sa, ko ƙiftawar kirki ba ya yi, se wata irin ajiyar zuciya yake.

Ta kalleshi "baka da lafiya ne?"

Ya girgiza masa alamar a'a.

"Amma na ganka wani iri yau"

"Am sick" ya bata amsa a hankali.

"Meke damunka"

Be magana ba ya lumshe idanunsa, ya kuma buÉ—e su a kanta.

Cikin damuwa tace "dan Allah meke damunka?"

"Nothing, cigaba da aikin ki"

Jiki a sanyaye ta cigaba da rubuce rubucen ta, tana monitoring É—in Sadik É—in.

Can aka jima ya tashi ya bar seat É—in, ya koma baya ya kwanta akan wani benci.

Gaba É—aya Farhan ta damu, ta tashi ta bishi tace "Ko Clinic zan raka ka su dubaka?"

"No zan ware insha Allah"

"To kaƙi gayamin meke damunka"

"Idan na gayamiki zaki min wani kallo na daban, just forget about it, kije class É—inku kar Malami ya shiga"

Taslim ta kalli in da suke tace "lallai yau ana jin soyaya, sedai naga fuskokin masoyan É—auke da damuwa"

Kallonta kawai Farhan tayi, ta tashi ta bar ajin cike da damuwa tana tunanin meya sa Prince a wannan mood É—in haka?.

A ƙofar ajinsu taga Dodon nata wato Sir Nazir, ya tsareta da ido ta maze tare da ƙi ɓoye tsoronta, "Allah ya shiryeki, ina tausayawa rayuwar ki a nan gaba"

Farhan ba tace Komai ba ta wuce cikin ajin nasu, dan ita bata damuwa da duk surutun da Nazir ze mata akan Sadik.

Seda duk aka koma aji sanna Meena ta kalli Taslim tace "Ke nifa na tafi in je inga ta ina zan fara kaiwa gayen nan hari"

Taslim tai murmushi tace "jarababbiya idan me taurin kai ne kamar Naziru wahala zaki sha a banza a wofi"

"Shi ya isa ma, shi ma Nazirun dan ban dage bane, amma da shi É—in banza"

"Hmm to ai shikenan maji ma gani"

Meena ta miƙe ta gyagyara zaman Uniform ɗinta ta fice.
Chapter 20 · 0% Book details