← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 48

Sashe 3

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadik kuwa bin bayan Farhan yayi da kallo, duk da ta ɗora ƙaton hijjabi akan uniform ɗin nata, seda ya dena hangota sannan Yace  "mu tafi gida"

Direba yaja mota suka nufi gida.

Suna zuwa tangamemen gidan, direban ya kutsa da motar yai parking, Sadik ya buÉ—e motar ya fito, kai tsaye cikin gidan ya shiga, sakamakon shriye shiryen bikin Yayansu da ake, mutane suna ta shige da fice a gidan nasu.

Yana kallon mutane a falo, amma ya hau bene, ba tare da ya kula kowa ba.

Yayar mahaifiyarsa ce ta hangoshi ta shiga kiran sunansa  "Sadik, kana kallon mutane amma ka wuce baka kula kowa ba?"

"Zan kulaku anjima idan kuka ragu, duk kun cika mana gida"

Be jira me zata ce ba ya ƙara gaba, ɗakin mahaifiyarsa ya shiga, ya tarar da ita tana ɗakko kaya a wardrobe ɗinta, ta dubeshi tace  "sweetheart, ka dawo ya school ɗin?"

Cikin shagwaɓa Yace "Am so much tired , gashi duk an wani zo an cika mana gida da hayaniya"

"Sorry, kasan shirye-shiryen bikin yayanka ake yi, dole mutane suzo amma ko zaka É—akinka na BQ ka kwanta ka huta?"

Girgiza kai yayi Yace  "No, a ɗakin Daddy zan wanka in kwanta, a kawomin Abincina nan"

Ta shafa sumar kansa tace  "considered it done my auta"

Yace  "Mother dan Allah a miƙomin jallabiyata, idan kin sauka ƙasa"

Ta jinjina masa kai, Sukayi murmushi tare, ta fita daga É—akin.

Banɗaki ya shiga ya watsa ruwa, ya fito daga shi se gajeren wando ya tsaya a gaban mudubi, yana ƙarewa kansa kallo, Farhan ce ta faɗo masa rai, a hankali ya lumshe idonsa, yana saƙawa da warware abubuwa da dama a ransa.

Buɗe ƙofar ɗakin akayi tare da yin sallama, ya amsa ba tare da waiga ba, saboda yaga me shigowar ta mudubi.

"Sadik manya, ashe ka shigo amma ba labari, ko neman mutane baka yi"

Murmushi yayi Yace "ai ban san kina gidan nan ba, na dawo kawai na tarar an wani cika falon, babu ma hanyar da zanbi in wuce É—akina, shiyasa kawai na taho nan"

Ta ƙarasa inda yake tsaye, ta ajiye kayan Abincin, sannan ta ɗora masa ash ɗin Jallabiyarsa a kafaɗarsa tace "gashi nan, Mother ce tace in kawo maka, sarkin rashin son Mutane"

Yai murmushi, yana ƙoƙarin zira jallabiyarsa, ta ƙura masa ido sannan tace  "Semi finalist, next year by now insha Allah an kusa grad, kaima ka wuce Dubai"

"Waye yace miki zanyi SS3, this year zan gama makaranta ni"

Tace  "meyasa zaka gama this year? Jumping zakayi kenan?"

Ya juyo ya fuskanceta sosai sannan Yace  'Khairat, jumping zanyi in kammala secondary School this year insha Allah, saboda Aure nakeso, Aure zanyi nan kusa"

Kwashewa Khairat tayi da dariya tace  'look at you, dan kaga kana da girman jiki? Secondary school fa zaka gama, Yaya Usman ma daza'ayi Aurensa Yanzu, seda yayi PHD, wakake tunanin ze maka wani aure yanzu?"

Ƙurawa khairat ido yayi sannan Yace "kina ganin nayi ƙanƙanta inyi auren ne?"

'ƙwarai kuwa, guda nawa kake zakayi zancen wani aure? Better build your future my friend, and stop talking this rubbish"

Tai maganar tana dariya, ta bar É—akin.

Sadik ya daÉ—e a tsaye a gurin yana tunani, sannan ya É—akko sallaya ya tada salla, bayan ya idar yaci Abincinsa ya kwanta.

Farhan ma harta koma gida, ta shirya ta tafi islamiyya, tunanin Sadik ɗinta ne a zuciyarta, tana tuna yadda yake yawan kyautata mata, amma abun tambayar anan shine, zasu iyayin aure kuwa ita da Sadik? Ita dai tana jin ƙaunarsa sosai a cikin ranta.

Se yamma sosai Sadik ya tashi, yai sallar la'asar sannan ya sakko ƙasa, har yanzu gidan da mutane sedai sun ragu ba kamar ɗazu ba, Yayyansa ne maza zaune tare da Yayar mahaifiyarsu, suna shirya atamfofi a cikin akwati, wanda za'a kaiwa Usman na lefe.

Sadik ya nemi guri ya zauna, yana bin kayan da kallo.

Mamansu Khairat ta kalli Sadik tace "dan ƙaniyarka ina maka magana ɗazu, amma kamin banza ko?"

Yai murmushi Yace 'na gajine, kaina na ciwo, gashi kuma an cika falon, shiyasa ban tsaya ba, wai wannan kayan duk na lefen ne?"

Maman Khairat tace  'eh gasu nan, jibi zamuje mu kai masa insha Allah"

Usman Yace "Autan mother Babu ko kara, ko 'yar sarƙa baka siya ka bani ba, a matsayin gudunmuwa"

Sadik Yace  "gaba ɗaya fa siyayyar nan kaɗan ce akayi maka a Nigeria, duk a waje aka yota, kowa yazo baka kuɗi kawai yake kaida Mummy, kuma kace Sena saimaka abu na  baka duk kuɗinka Bross"

Faruk Yace  'ji ɗan rainin hankali yaron nan dan Allah, duk gidan nan babu wanda ake sakarwa kuɗaɗe kamar ka fa"

Usman yace  "wallahi kuwa, yaron nan kuɗine dashi kamar banza a account bema san me zeyi dashi ba"

Sadik ya karkace ya gyara zamansa akan kujera yace  "aini na dena cin kuɗina, nima lefe zan fara tarawa, next year by now za'a kamin nawa lefen"

Maman khairat tace "Usman, dan Allah makemin mara Kunyan yaron nan"

Sadik yace "Nifa Mummy dagaske nake, aure zanyi nima, zamu yi magana da Daddy idan ya dawo gari, nifa banƙi a haɗa bikina dana Yaya Usman ba"

Umar ne ya kai masa duka Yace "yi mana shiru dan ubanka, mara kunya kawai, ubanwa ze maka auren? Ko dan kana ganinka ƙato haka? Better concentrate on your study, shikansa Bross Usy seda ya haɗa PHD ze aure balle Kai, da yanzu Balagar ta zo maka "

Harar Usman Sadik yayi Yace  "meye wani PHD?  Aure ze hanani karatune? Ai da sauƙi tunda balagara ta zo, Zan baku mamaki kwanan nan.

Ya miƙe yana zumɓura baki ya bar falon.

Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

                            Page2

Sadik na fita harabar gida, ya tarar abokansa sunzo wai zasu snuka, ya bisu suka fice dan yaje ya sarara.

Corper Nazir kuwa ya sha faɗa a gurin director, saboda ƙararsa da Sadik ya kai, ya dinga mamakin wannan lamari, shikenan dan yaran masu kuɗine baza'a basu tarbiyya ba? Yara duk ba ɗa'a? Ai makaranta ba iya gurin koyon karatu bane, hadda tarbiyya shikenan se a zuba musu ido su lalace, baza'a tsawatar musu ba dan kar iyayensu suji haushi?

Abun ya dameshi sosai, Tare da ganin rashin ma'anar wannan lamari akwai buƙatar a duba, idan bahaka ba rayuwar yaran zata ɓaci a banza.

Da wannan damuwar ya koma gidan daya kama, da yake ba'a camp yake a zaune ba, gida ya kama yake zaune a ciki.

Washegari ya shirya Domin zuwa makaranta, kamar kullum anyi assembly an gama, Farhan nata rarraba ido taga ta ina zata hango Sadik, sedai bata samu ganin nasa ba, ta duba inda yake tsayawa amma baya nan, duk setaji ta damu, haka aka sallamesu suka tafi azuzuwansu.

Sadik kam yau makara yayi sosai, corper Nazir yana harabar makarantar a tsaye yana zazzagawa, dan tabbatar da komai ya tafi daidai.

Motar gidansu Sadik ce ta kunno kai cikin makarantar, har Corper Nazir ze shiga cikin makaranta, yaga zuwan Sadik, dan haka ya tsaya.

Sadik ya fito daga mota, ya rufe motar ya saɓa jakarsa, ze shiga cikin makarantar.

Cikin shouting corper Nazir yace "hey come here'

Sadik ya juyo ya kalleshi, sama da ƙasa kamar kar yaje, sukuma yaje kiran, yana wani bossy walking yaje inda Nazir yake tsaye, Nazir ya kalleshi yace  "why are you just coming?"

Sadik ya kalleshi ya É—auke kai.

"Check your watch, what's the time now?"

Sadik ya É—auke kai kamar ba dashi ake magana ba, principal ne ya taho inda suke tsaye, yana faÉ—in"what's going on here?"

Nazir Yace  'Sir, wai Babu wani penalty na makara kowani laifi, idan yaran nan sun karya doka? Kalli lokacin da yazo makaranta, kuma na yiwa director magana akan haka amma ya nuna min is like you don't punish them"

Principal ya kalli Sadik yace  Yace  "Sadik, why are you late? Baka san lokacin da Yakamata kazo school bane?"

Tura baki Sadik ya shiga yi, yana hararar Nazir.

PC yace  "idan ka sake makara, sena baka punishment me wahala, ɗau jakarka ka bar gurin nan kafin in ci mutuncin ka"

Sadik ya É—au jakarsa fuuu yai cikin makarantar, yana tunanin yadda ze koyawa Nazir hankali.

Principal ya kalli Nazir yace  "ka manta da director, duk abunda yakama na hukunci a hukuntasu, shi yana la'akari da yadda ze samu kuɗine kawai, shiyasa baya goyon bayan hukuntasu, kuma wasu daga yaran iyayensu nada kuɗi yanzun nan se su ɗaureka, amma dan dai punishment wanda zasu iya, in sunyi laifi kar a saurara musu"

Nan suka cigaba da tattaunawa akan matsalolin yaran.

Koda Sadik yaje ajinsu da malami a ciki Yana lesson, amma babu neman izinin shiga ko makamancin haka, ya kunna kai cikin ajin nasu, yaje gurin zamansa ya zauna, Tare da ajiye jakarsa, fuskar nan tasa a É—aure yana ta jan tsaki.
Duk ajin suka waigo suna kallonsa, daga bisani malamin ya cigaba da Koyarwarsa.

Sadik be saurari me Malamin ke koyarwa ba, ya kifa kansa akan benci, zuciyarsa cike da jin haushn irin yadda Nazir ke zaƙewa da son cusawa hukumar makaranta wani ra'ayi na daban akansu, dole yayi maganin Nazir.

Malamin na fita su Amin suka zo inda Sadik yake, Nasir Yace"babban yaro ya dai? Meyafaru ne mun ganka Wani iri"

Sadik yayi tsaki Yace  "dan Allah ku rabu dani"

Amin yace "haba Sadik, Ya hakane? Mun tambayeka meyafaru kana wani cin magani"
Chapter 3 · 0% Book details