← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 48

Sashe 11

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lilly tace "wai, yau zamu gane wanda suka reaching adolescent period, a mata zamu ga wadda ƙirjinta ya fara tasawa da wadda har Yanzu take Small Baby".

Kwashewa su kai da dariya, wata yarinya tace "aikuwa maza kuma zamuji masu husky voice, da wanda suke da Baby voice har yanzu"

Lilly tace "ke Hasina masu babbar murya wannan ai se daga ajin su Prince zuwa sama za ki ji wannan, sedai in layi za suyi a leƙa hanmatar mu gani"

Hasina ta kwashe da dariya tace "ko muji in da wanda ya fara dreaming ba"

"Hmm yau zamu tantance adults da Babies, É—aya bayan É—aya zamuyi screening, muji wadda ta fara saka brezia, da wadda har yanzu take sahun yara, maza kuma azo a bamu labari wanda suka fara dreams"

Dariya suka kuma yi, Lilly tace "Yasmin ke fa 'yar iska ce wallahi, se su hau layi ki fara dubawa ai"

Suka cigaba da taɗin su, Farhan kuwa tai shiru tana tunani, wasu daga singns ɗin nan na adolescent period, already ta fara Experiencing ɗin su, amma ita banda yau ba ta taɓa sanin wannan alamomin balga bane, babu wanda ya taɓa gaya mata.
(Ƙalubale gareku iyaye)

Tunani ta fara yi meye wannan sexual feelings É—in, tasan shi ake nufi da sha'awa tun da sunyi a islamiyya, amma meye shi É—in? Ya mutum ze gane that he has sexual feelings towards his opposite sex?

Yanzu tarayyarta da Prince ze iya sa taji feelings akan sa kenan? Kuma hakan na nufin matsala ne kamar yadda Sir Nazir ya faÉ—a?.

Kai koma me ze faru, ta san ba wani abu da za taji ko ya faru, dan tana tare da Prince, kuma ma ai shika É—ai ne namijin da take kulawa, ai ita ba shiga sabgar maza take ba.

Da sauri ta tashi ta fita waje, ta nufi ajin su Prince.

Tana zuwa ta tarar 'yan aji suna fitowa, da alama wani gurin za su.

Mazan sun saka kayan sport wears, prince ya fito hannunsa É—auke da ball, yana buga ta yana cafewa.

Farhan ta zuba masa ido, ya É—aga kai suka haÉ—a ido, É—auke kai yai kamar be ganta ba ze wuce.

"Sadik" ta faÉ—a a sanyaye.

ÆŠaga kai yai ya kalleta, be ce komai ba.

Ganin ba za tai Magana ba, yasa shi yin gaba ze wuce, ba tare da shirya ba ta riƙe rigarsa.

Ya waigo ya kalleta, yaga idonta ya cika da hawaye.

Jiki a sanyaye tace "Am sorry please"

"Sorry for what? You don't need to apologise, ki je ki biyewa wancan ajawon kiyi watsi da soyaya ta"

"Dan Allah kayi haƙuri"

Prince yai wani irin murmushi da ke sanya Farhan farinciki, yace "ok shikenan my Farhan, ai ba zan iyayin fushi da ke ba, na ma fasa zuwa gurin ball É—in, hira zamuyi"

A'a kar ka fasa zuwa, tun da kayi niyya"

"No kin fiye min ball mahimmanci"

Amin ne ya dawo yana mita yace "wai dalla me kake a gurin nan, tun É—azu muna fili muna jiranka?"

Prince ya jefa masa ball É—in yace "ga shi nan kuje kuyi, ni na fasa zuwa"

"Kamar yaya?"

"Kamar yadda na gaya maka mana"

"Amma wallahi ka cika mara mutunci, wannan ai wulaƙanci ne, ya za'ai an shirya abu kuma kace ba za kai ba?"

Prince ya kalli Farhan yace "let's go inside my dear"

Suka shiga ajinsu Prince, suka bar Amin a gurin.

Amin ya juya ya tafi yana masifa, yana zuwa filin ƙwallon ya saki ball ɗin a ƙasa yana mita.

Nas yace "ahh ya haka? Ina Prince É—in?"

"Waccan mayyar yarinyar ce taje gurinsa, Shine ya jefomin ball É—in wai baze ba, ya tsaya a gurinta"

Taslim tace "wai dan Allah meya sa Prince yake wa mutane hakane?"

Meenat tace "ai shegiyar yarinyar ce mayya"

Amin yace "maganin ta zamuyi, idan har zata cigaba da rayuwa da Prince to dole za ta shigo clique É—in mu"

Nas yace  "ƙwarai kuwa, rabu da shi za muyi maganinsu daga shi har ita"

Daga nan suka fara ball ɗinsu a tsakanin maza da mata (😲🙄🤔).

"Farhan, ko kina doubting akan son da nake miki ne?"

Farhan ta girgiza masa kai.

"To meyasa kike guduna Farhan? Wallahi i really love you"

Shiru tai ta sunkuyar da kai, tana hawaye, Prince yace "ok I got you, is ok ki dena kukan"

Yai maganar yana ƙoƙarin kai hannu ya share mata hawaye, amma ta jabda baya da sauri"

Yace "ok sorry, karɓi hancky ki goge hawayen, ki dena zubarmin da su a banza"

Ta karɓa ta goge hawayenta, tana cikin gogen hawayen aka kawowa Prince Abincin da yai order.

Yaje ya karɓo ya dawo yace "My dear, me za'a kawo miki ne?"

"Nothing" ta faɗa a taƙaice.

"Why?"

Tace "Na ƙoshi"

"No baki ƙoshi ba, muci wannan tare"

Farhan tace ba zata ci ba, Sadik yai ƙasa da murya ya ɗebo a spoon ya kai bakinta, yana mata wani irin kallo Yace "dan Allah kici ko nima in ƙi ci"

Ji su kai an buɗe ƙofar ajin da ƙarfi, suka waiga gaba ɗaya.....

Free pages are not much, hurry up and subscribe yours.

Domin gyara, sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680.
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

                               7_8

Jikin Farhan har ya fara tsuma zaton ta Sir Nazir ne.

Shi kansa Prince ya É—auka Nazir ne, dan ya shirya tsaf dan maida martani ga duk wanda ya kuma kawowa soyayyarsa barazana koma waye.

Se dai ba ba yadda suka zata bane, wani É—an ss3 ne wanda ake cewa Babba.

Ya shigo ya kalli Prince yace "wai kai Prince wane irin banza ne? Ya za'ai an shirya abu da kai kace ba za kai ba meye hakan?"

Gyara zama Prince yai ya kalleshi Yace "an shirya yin abu dani, yanzu kuma nace ba zan ba, ba shikenan ba"

"Dalla kar ka gayawa mutane Maganar banza mana, wannan ai wulaƙanci da rashin mutunci, wai kai meyasa kake haka a rayuwar ka ne?"

Banza Prince yai masa, yaƙi ko kallonsa.

Babba ya dinga zazzagawa Prince jaraba, amma ya mirsisi yaƙi sake tanka masa, seda Farhan ta fara jin haushin abun da Babban yake wa Sadik.

Babba dai takaici ya isheshi, yai waje yana mita.

Yana fita Sadik ya girgiza kai kawai yai murmushi.

Farhan tace "Naga sun ji haushin abunda kayi, bari in tafi kawai kaje kai Ball É—in"

Sadik yace "No, ni kin fiye min ball É—in nan, maza muci Abincin nan kar ya huce"

Fafur Farhan taƙi cin Abincin nan, yai yai da ita amma ta ƙi yadda ta ci, se ƙyaleta yayi.

Yana cin Abincin suna ɗan taɓa hira, duk da Mafi yawa daga hirar shi yake mata, can tace "wai meyasa ake ce maka Prince ne?"

Wani kyakyawan murmushi Prince yai, da yai matuƙar birge Farhan, yace "Kinga ni ba sarki ba, ba ɗan sarki ba amma ana cemin Prince ko?"

"A'a kawai tamabaya nayi?"

"Kakana Hakimi ne, Kakata ma 'yar Hakimi ce, sannan babana yana da sarautu daban daban har a kudancin ƙasar nan, kwanan nan ma an masa wata Sarautar a Ghana, kuma ana ɗan cewa ina da jin kai, wanda ba hakan bane, kuma ni ne auta a gidanmu suna ji dani sosai wannan dalilin ne yasa ake cemin lil Prince"

Murmushi Farhan tayi tace "Sannu Prince"

"Yawwa matar Prince" ya faÉ—a yana kashe mata ido.

Haka suka cigaba da hira ita da Prince, tana jin wani farinciki maara misaltuwa kasancewar ya dena fushi da ita.

Da yake Friday ce, har aka tashi suna tare, ya raka ta har ajinsu ta É—akko jakarta, suka fito harabar makarantar.

Suna fitowa kuwa su kai arangama da Nazir, ya zubo musu ido yana musu kallon tuhuma, dan ba kowa a cikin makarantar se su, dan duk ana waje gurin wasa.

Gaban Farhan yai mummunar faɗuwa, amma ta dake ta ƙi kallonsa.

"Hey daga ina kuke!?"

Ya faÉ—a cikin shouting, wani Mugun kallo Sadik yaiwa Nazir, yaja hannun Farhan da sauri, wanda se da hakan yasa ta firgita, be tsaya ko ina ba se bakin motarsu, ya buÉ—e mata yace "shiga"

Ta waiga ta kalli Nazir ta kalli Prince, a hasale yace "shiga nace"

Da sauri ta shiga, shima ya shiga motar ya cewa direba ya ja su tafi.

Ta kalli Prince ta na so tayi magana amma taga ya wani haÉ—e rai, tilas ta ja bakinta ta tsuke, dan ko cikin kuskure ba tavsin sake aikata abunda zesa yai fushi.

Har suka sauke Farhan be kuma ce mata uffan ba suka nufi gida.

Shikuwa direban Sadik addu'a yake Allah yasa kar Sadik ya ɓata Yarinyar nan ganin yadda take masa biyayya kamar ubanta.

Sadik suna zuwa gida, ya tarar da mahaifinsa a harabar gidan, shi da wasu baƙi, watanni biyu kenan mahaifin nasa baya gari, se Yau ya dawo.

Da gudu Sadik ya sakko daga mota, ya nufi mahaifinsa da gudu, ga abokan mahaifinsa a gurin amma be bi takansu ba, ya rungume mahaifinsa yana faÉ—in "I miss You Daddy"

"Miss you too Auta na, how are you and how was your studies?"

"Fine Daddy, amma meyasa ba ka gayamin yau zaka dawo ba? Kawai se in dawo in ganka?"

"Eh mana, i warn Your Mum kar ta gaya maka zan dawo yau"

Murmushi Sadik yai, ya kuma kallon mahaifinsa yace "I really miss you"
Chapter 11 · 0% Book details