Sashe 37
Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mother tace "eh wani abu me ya faru, zaman kakarku a gidan nan, da wannan fitsarariyar yarinyar naga kana wani rawar kai, kana wani shishshsigi da neman suna, to let me tell you something, wallahi idan ma wani abu kake tunani game da Yarinyar nan gara ka cire shi daga ranka, ka maida hankali akan karatunka kar ma du fara tunanin wani abu ne a tsakanin ku suyi tunanin liƙa maka ita, ba zan amince da 'yar ƙauye a matsayin sirikata ba, dan naga su ba abunda suka saka a gaba banda Aure Aure, ko Aure za kai kafi ƙarfin wannan 'yar ƙauyen"
"Ohh my God Mother, what are you trying to say? Me nayi da ya nuna ina son Nana, idan alaƙata da Khairat be sa an kirata da Soyayya ba me ze sa alaƙata da Nana ya zama soyaya, wannan 'yar ƙaramar yarinyar, You know i just love female sister that's all, ban san meyasa kike zargin wani abu ba, she's a sister to me ina sonta saboda ita kaɗaice 'yar uwamu a ɓangaren Abba that's all, amma in kinji haushi ne am sorry for that, amma ba abunda kike Tunanin bane"
Duk haƙurin Faruk da alama yaji haushin maganganun Mother, Yain da Sadik shi abunda ya dame shi be wuce yadda Faruk ma me shekara kusan Ashirin da biyar ake cewa ya maida hankali akan karatu ba, balle shi da be ma cika shatakwas ba.
Gajeren tsaki ya ja ya bar Mother da Faruk a falon.
Mother ta dafa kafaɗar Faruk tace "am sorry my Faruk, ba na faɗa ne dan in ɓata maka rai ba, na faɗa ne dan in saka a hanya, ka maida hankali akan karatun ka ka zama wani abu a rayuwa, duk harkar matan nan shirme ne kawai, mutanen ƙauye da sunga kana nan nan da ita se suce zasu haɗa ku Aure da ita, But don't mind, zo ka kaiwa Mummy kayan nan"
Faruk be kuma cewa komai ba, ya karɓi ledar hannun ta, yai waje ba tare da ya kuma cewa komai ba.
Farhan duk damuwa ta isheta, duk a takure take sosai, tana son sake ganin Sadik ko ta kirashi a waya, amma ta rasa yadda za tai ta kuma samun waya ta kirashi, haka nan take jin kamar zuciyarta a takure take rashin Sadik É—inta, saura 1 week a koma school, amma ji take tamkar Shekara guda ya rage a koma makarantar.
Sadik yawonsa ya tafi, amma wajen tara na dare ya dawo gida, a falo ya tarar da Mother da Abba ga kuma Faruk suna kallo.
Abba ya kalli Sadik yace "kai daga ina haka?"
Sadik yace "na raka Salman ne gidan kakar su an aike shi"
"Mamanka ta san ka je rakiyar?"
Mother tace "A'a Abba ai naga abokinsa ne, kuma suna fita tare dama meyasa kake tambaya?"
Abba yace "bana son yawan yawon nan ne, gara ya zauna a gida yai karatu"
Sadik be ce Komai ba ya wuce ɗakinsa da ke cikin falon yana mita aƙasan ransa boko boko boko, an kasa fahimtar halin da mutum ke ciki se batun wata boko"
Ya ƙarasa Maganar yana rufe ƙofar ɗakin, ya jingina bayansa a jikin ƙofar yana sauke ajiyar zuciya.
A hankali ya taka ya zauna a gefen tangamemen gadonsa, wanda yafi na BQ girma da kyau, ya ƙurawa system ɗin sa ido, yana jin kunnawa ya ci-gaba da kallonsa, amma yana tuna halin da ze iya shiga a dalilin cigaba da kallon.
Miƙa hannu yai ya ɗakko remote ɗin TV dake kan fridge ya kunna, canza tashoshi yake yana neman wadda ze kalla.
Ya daɗe yana caccanza Channels, miƙewa yai da niyyar rufe tagar ɗakinsa, ya hango Mother kwance a jikin Abba, suna kallo yana bata popcorn a baki, su dai sam basa girma suna bawa junansu kulawa duk da shekaru sun fara ja, amma Mother ta kan maida Abban kamar ɗan shekaru talatin, basa ɓoye Soyayyar su ko a gaban yaran su ne.
Sakin labule kawai Sadik yai a hankali ya furta "When, When will you understand that am also human being?"
Ya koma ya zauna yana cije lips ɗin sa na ƙasa.
Farhan a hankali ta lallaɓa ta shiga ɗakin Umma, ta tarar Umman tuni tayi bacci, cikin sanɗa ta ɗau wayar Umma ta fito daga ɗakin.
Ta sa wayar a silent ta tafi É—akinta.
Ta turawa Sadik message kamar haka "Barka da dare, kwana da yawa ina fatan kana lafiya"
Wayarsa tai ƙara alamar saƙo ya shigo, ya kai idonsa kan wayar, yai ajiyar zuciya sannan ya janyo wayar, ya duba yai tozali da saƙon Farhan.
Hannu yasa a sumarsa yai murmushi, ya kwanta sannan ya kirata a waya.
"Dama idonka biyu ba kai bacci ba?"
Sadik yace "ke zan tambaya ba ki bacci ba?"
Farhan tace "eh nayi tilawa ne, na É—akko wayar Umma na kiraka"
Yai murmushi yace "gaba É—aya na koma kamar mara lafiya, saboda bana samun ganinki da jin muryarki"
"Nima haka ai"
"Dagaske kinyi missing É—ina"
"Umm" ta bashi amsa.
"Ok i understand, ya jikin naki?"
"Ni meya sameni?"
"Ba kince min kina ciwon ciki ba?"
Farhan tace "wallahi har yanzu yana min kaÉ—an kaÉ—an, wasu lokutan idan ya far sena dena duk abunda nake sedai in kwanta"
"Amma baki je Asibiti ba?"
"No ai ya dena"
"Karki min wasa da lafiyar ki Farhan please" ya ƙarasa Maganar muryarsa da rauni.
Farhan tace "lafiya kuwa, naji muryar ka na rawa?"
"Farhan Aure nake so" ya faÉ—a mata kai tsaye ba wata kunya ko shakka.
Jin maganar tai a bazata, wai Aure yake so se taji abun wani banbarakwai.
Shiru tai ta kasa Magana, Sadik yace "is sound somehow to you ko? Ban san a ya zan miki bayani ki gane ba, Farhan zanyi duk me yuwuwa in ga na Aureki nan kusa ba a nesa ba Insha Allah, ki kwanta kiyi bacci, dare yayi have a nice dreams Cwthrt"
A hankali ya ajiye Wayar ba tare da ya katse kiran ba, wayar Farhan ta bi da kallo, ta na maimaita abunda ya faÉ—a a ranta, cikin sanÉ—a ta tashi ta maida wa Umma wayarta, ta ajiye ta dawo ta kwanta, tana cigaba da jujjuya maganar Prince.
Kwanci tashi asarar rai, sati ya zagayo aka koma Makaranta, domin cigaba da gwagwarmaya ta neman ilimi, wanda ba'a samunsa da sauƙi, amma duk da haka a gurin neman ilimin Akwai bambanci me tazara tsakanin yaran talaka da na me kuɗi.
Farhan uniform É—inta a goge suke tsaf, se murna take za'a koma Makaranta, wanda a zahiri ba komawa makarantar ce ta sata farinciki ba, haÉ—uwa da Sadik take ta É—oki.
Shima nasa ɓangaren yana cike da shauƙin son ganinta, da kuma abokan karatunsa.
Ɗaliban sunji daɗin sake haɗuwarsu a zangon karatu na gaba, saboda akwai shaƙuwa ta mussaman a tsakanin ɗaliban.
Yana tsaye a cikin abokansa a gurin Assmebly tun daga nesa ya hangota ta shigo makarantar, ta cire ƙaton hijjabin jikinta, ta bar na makarantar da suka kasance tsangalallu.
Ta ƙara ƙiba tai fresh da ita, ta ƙara cika kayan makarantar nata, sosai alamun girma ke sake bayyana a tare da Farhan ɗin.
Be san lokacin da murmushi ya suɓuce masa ba, tare da lumshe idanunsa.
Guri ta samu ta tsaya a cikin 'yan ajinsu, ba wanda ya kulata se Lilly da ta miƙa mata hannu su gaisa.
Farhan ta miƙa mata suka gaisa, Lilly tace "An dawo lafiya"
Farhan tai murmushi tace "Lafiya ƙalau Alhamdilillah"
Nasir ne ya taɓa Sadik yace "dan Allah karka cimye Yarinyar nan da wannan idanun haba, wannan kallo haka"
Be ce Komai ba se cigaba da murmushi da yayi.
Har aka kammala Assembly ba ta gano shi ba sam, tai ta rarraba ido amma ba ta ganshi ba.
Haka aka gama ta tafi aji tana tunanin ko ya dawo yau oho.
A timetable period É—in farko, Sir Nazir suke da shi.
Ya shigo ajin suka miƙe tsaye suka gaishe shi, kan ya basu iznin zama ya dinga bin su ɗaya bayan ɗaya da kallo, ya ɗan tsurawa Farhan da ta sunkuyar da kanta ido, kan daga bisani ya janye idonsa zuwa kan Lilly.
Ta ɓalle botiran jacket ɗin ta, ana ganin ta cikin, gashi Masha Allah ta zama budurwa ita ma, duba da yanayin girman jiki na yaran masu kuɗi, ita ma ta fara cika.
A kausashe yace "Fatima, Allah ya dawo damu ko, close your jacket my friend"
ÆŠan tura baki Lilly tayi, sannan ta sa hannu ta rufe botir É—in rigar ta ta.
Haseena ta waigo ta kalli Lilly, ta sunkuyar da kai tana dariya ƙasa ƙasa, yai musu umarni suka zauna.
Daga bisani yai musu maraba da dawowa sabon zango, yai musu Nasiha sannan ya É—ora musu da lectures na ranar.
Kasancewar double period ne be fita daga ajin ba, se break yana fita Haseena ta kalli Lilly tace "to ƙarama 'yar air, daga dawowa zaki fara sa bawan Allah a gaba"
Lilly tai murmushi tace "gani ba taɓawa ba asarar ido"
Haseena ta ƙara samata da "taɓawa ba tafiya da shi ba asarar hannu"
Lilly tace "dan ubanki hauka nake zan tsaya a taɓa, ba wannan maganar sedai in ta gwara kan mutum"
Yasmin da ke ƙarasa kwafar note tace "za kiga ba me taɓawa, naga kin ƙaro wulaƙanci har wani chestout ki ke yanzu"
Lilly tace "to ke ya kika gani?"
Farhan na jinsu, amma ba ta ko motsa ba, ta cigba da danna carbin hannunta.
Ƙamshin turarensa ne ya mamaye mata hanci, tana ɗaga kai ya zauna daf da ita a hankali yace "shine ko ki neme ni ko? Anya kinyi missing ɗina kuwa?"
Murmushi tai tace "Ai na duba a gurin Assembly ban ganka ba, nayi zaton baka dawo ba"
"Meze hanani dawowa inga amaryata, ni tun lokacin da kika shigo na ganki ai, Kinyi ƙiba sosai, me Ummana take baki ne haka?"
Wani daÉ—i ne ya cikata jin yace Ummansa, ko ba komai yai mata kara ya girmama Ummanta.
"Tuwo take bani"
"Nima zan zo ta dinga bani gaskiya, karki fini ƙiba"
Ƙaramin tsaki Haseena ta ja tace "ban taɓa ganin munafukin mutum kamar wannan Farhan ɗin ba, ba wanda ta kula amma ga yadda take wata dariya"