← Book details Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 48

Sashe 29

Rudin Kuruciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tai ringing harta katse be É—auka ba, gaba É—aya se taji ba daÉ—i, amma se tai masa uzurin ko yana wani abun ne.

Ta tattare litattafan, ta mayar cikin jakarta, ta maida jakar ma'ajiyarta.

Taita dakon ko Prince ze biyo wayara, amma shiru.

Ba ta gaza ba ta sake kiran layin nasa, a fusace ya fizgo wayar ya É—aga cikin masifa yace "Wai waye ne?"

Cikin sanyin muryarta, me sigar shagwaɓa tace "nice fa"

Wata irin ajiyar zuciya ya ja, tare da lumshe idanunsa, ba tare da yace komai ba.

"Ka na ji na kuwa?"

"Ina jinki Princess, ina tattaro kalaman ban haƙuri ne, na rashin ɗaga wayarki da farko, sannan kuma nai miki shouting, bari in kira ki"

Ya katse kiran, sannan ya kirata, seda ta kuma leƙawa tsakar gida ta ga ba kowa, sannan ta koma ta zauna ta ɗaga wayar.

"Ina fatan an karɓi ban haƙurina" yai maganar cike da kasala.

ÆŠan tura baki tai tace "naji muryarka wani iri, meke damunka?"

A shagwaɓe yace "Princess ɓatamin rai akayi zanyi kuka"

Dariya Sadik ya bata tace "Subhanallah, kuka kuma?"

"Eh mana"

"No, sorry kar kayi kuka, kaifa namiji ne kuka ai se mata"

"Khairat ce ta ɓatamin rai"

Tace "am sorry ni ban tambayeka ya kuka je gida ba?"

"Lafiya ƙalau, wandon nan da na siya, aka kawo nace ta ajiyemin ta bari akai mopping da shi, wai an zata tsumma ne"

Kwashewa da dariya Farhan tayi, dan sosai ya bata dariya.
Cikin dariya tace "to ai ba kowane yasan wannan wandon gayu bane, abu duk a yayyage"

"Au haka zakice ko? Shikenan"

"A'a kayi haƙuri kasa wani"

"Ai raina ya gama ɓaci, sena hukunta ta akan abunda tayi"

"A'a dan Allah kayi haƙuri, tsautsayi ne"

"A'a wannan ba tsautsayi bane, za ta gane kurenta"

"Dan Allah kayi haƙuri mana"

Sadik yace "ko zan haƙura se nayi tunani, duk da ita ma ina sonta, duk wadda Allah ya bani a cikin ku ina so, sedai na fi son ki, da ke ki kai laifin da tayi ba abunda zan iya"

Ɗif Farhan tayi taƙi magana, Sadik yace "ya dai Baby Princess, naji kinyi shiru"

"Ba ka cemin ƙanwarka ce ba?"

"Ai cousin É—ina ce, akwai Aure a tsakanin mu"

Take Farhan taji zuciyarta na tafasa, jiki a sanyaye tace "se anjima"

Sadik yace "Malama kar ki kashemin waya, ban gama Magana ba"

A É—an hasale tace "to ai aiki zanyi"

Rungume pillow yayi yace "na so ace am with you right now, in ga kishi na a kyakykyawar fuskar nan taki Baby, da wasa nake miki wallahi, tsokanar ki kawai nake"

Tura baki tai kamar yana ganin ta tace "to ni ina ruwana in ma dagaske kake"

"Ke ko kike da ruwa Yarinya, ba zaki tabattar da hakan ba, se kin ganni da wata, amma bana fatan hakan, ke kaÉ—ai kin ishi Prince, am sorry kinji Babyna wasa nake miki"

Motsi ta jiyo a tsakar gida, dan haka da sauri tace "se anjima"

Ta kashe wayar, kallon wayar yayi, tare da yin murmushi, ji yai duk damuwarsa ta gushe, ya ji daÉ—in yadda yanzu take sakin jiki harta faÉ—a masa abunda yake ranta, a hankali yana sake gane halayenta.

Sauka yai daga kan gadon yana murmushi, da jin daɗin yadda kishinta ya kasa ɓoyuwa.

Ita kam Farhan shiru tayi, tana sauraren wanda ke motsi a tsakar gida, Huzaifa ya leƙo ɗakinta yace "kin gama wayar?"

Tace "eh na gama, ga ta Nagode sosai"

Ya sa hannu ya karɓi wayar yace "ba batun godiya, kuɗin kati kawai zaki kawo"

Ba tace komai ba se murmushi da tai masa.

Shiru tai ta na nazarin maganganun Prince, yanzu idan dagaske yake mata fa, Khairat ma budurwarsa ce!.

Da ma ana ta masa gorin yana Soyayya da ita, tana abu kamar 'yar ƙauye, amma da gani dama Khairat wayayyiace kamar Prince, dan yakan yi mata hirar Khairat ɗin, amma ba ta taɓa kawo komai a ranta ba, saboda cewa yake ƙanwarsa ce.
Gefe guda kuma ga batun Sunusi, da ta tuno zancen Sunusin nan, se taji gabanta ya faÉ—i gaba É—aya se ta rasa sukuni.
Ba ta san da wani idon zata fara kallon tsabar idon Abbanta, idan lokaci yayi tace masa ba ta son Sunusi ba ita da wanda take so.

A hankali ta zame jikinta ta kwanta, ta lumshe idanunta tana sauraron yadda bugun zuciyarta ya ƙaru saboda damuwa.

Shikam Prince zuwa yamma tuni ya manta da batun wandon sa da Khairat tai masa asara, sema nemanta da yake suje taga gurin da ya kama, za suyi party da abokan sa.

Sedai ya nemi Khairat ya rasa, Mother ta sanar masa, ko ɗinkin ba taje ta karɓo ba, tunda yai mata tijara da safen nan, ba ta kuma fitowa ba.

Ɗan girgiza kai yai yace "lallai ma yarinyar nan ba ta da kunya, tai min laifi kuma ta hau fushi, Allah ya temaketa Princess ta bani haƙuri, fa sena tattaka ta"

Mother tace "wacece kuma Princess"

Ba kunya Sadik yace "sirikar ki ce" yai maganar yana nufar part É—in Mother.

Ɗan girgiza kai tayi ta cigaba da sabgoginta, dan bata ɗaukar maganganun Sadik ɗin da mahimmanci, tana barinsu ne a mazaunin ƙuruciya, Ina Sadik ina wata budurwa.

Duk wani shirye shirye Sadik ya kammala, daga kama guri kuÉ—in Abincin da zasu ci shi da abokansa duk ya kammala biya.

Ranar Laraba ya kama ranar da Sadik É—in zeyi tasa walimar, shida abokansa saboda ranar Alhamis za'a fara bikin.

Ɗan maidaidacin hall ne ya kama, yayi kyau sosai gurin, ƙarfe biyar motoci suka fara parking a harabar gurin.

Kallo É—aya za kaiwa matasan yaran, masu ji da tashen balaga kasan 'ya'yan gata ne.

'yan secondary, Mazansu da matan suna sanye cikin crazy jeans, da riguna me É—auke da sunan Amarya da Ango a gaba, baya kuma sunan mamammalakin rigar.

'yan makarantar sun wa Sadik kara, dan harda 'yan primary a cikin wanda suka zo partyn.

Shikansa uban gayyar duk da Asarar da Khairat tai masa, amma ya saka wani wandon, yayi kyau ya fito a ainihin ajebon sa, sumar nan tasa afro style ta sha wanki da mayuka, se wani irin ƙyalli take.

'yan mata sangan sangan se yawo suke a cikin maza da matsastun riguna da wanduna, duk sun matse halittun Jikinsu.

Tamkar jinsi É—aya suke, haka suke shiga suna fita a cikin mazan nan, ba ruwansu da wannan namiji ne waccan mace ce.

Ita kanta Khairat da taje gurin, seda ta sarawa rashin ji irin na 'yan makarantar su Sadik, duk itama ta su makarantar suna nasu rashin jin, amma su Sadik sun damesu sun shanye.

Nan aka fara raye-raye, da É—aukar hotuna, su Nas suna ta zuba rashin mutunci, da tanka 'yan matan in anjima su rungumo waccan, ko su kamo waccan suna rawa.

Shikansa uban gayyar haka 'yan mata suka baibaye shi, da sunan ɗaukar hoto suna rungumarsa, dan duk taƙadirancin Sadik a school, ba ruwansa da rungume rumgumen mata.

Kan stage suka janyo shi, suka dinga juyashi da sunan rawa.

Mubarak ne yace "mutumin nifa banga Farhan ba"

HaÉ—e rai Sadik yai yace "in ka ganta me za tai maka?"

"A'a bakomai, ai gani nai Yakamata ace tana gurin nan dan tayaka murna"

A taƙaice Sadik yace "ba ta zo ba"

Ba'a tashi daga gurin nan ba se goma na dare, amma anci an sha yadda yakamata, wanda aka gayyata da wanda ba'a gayyata ba duk sunci sun ƙoshi.

Wasu sukaiwa Sadik keyholders da Manyan kofuna na cas, da sunan couple's É—in a jiki, kowa da abunda ya bayar na gudunmawa saboda shima Sadik É—in meyi ne.

Seda aka watse za su taho gida sannan hankalin Sadik ya dawo jikinsa, Mother tai masa missed calls ba adadi.

Haka ma Khairat, itama wayarta kira ne rututu a ciki.

Khairat tace "Sadik kaga kiran wayar Mother, ga na Mummy bari in kira su inji ko lafiya?"

"No ƙyalesu in muje Gidan ayi duk wadda za'ayi"

Haka ya cigaba da driving, suka tafi gida.

Sedai suna zuwa gidan, a harabar gidan suka tarar da su Mother a tsaitsaye suna kiran layinsu, dan babu wanda yasan in da suka tafi, Sadik be gaywa kowa party ya shirya ba, dan karma asa wasu su bisu suje su hana su rawar gaban hantsi.

Ganin su Mother harda shi kansa angon a harabar gidan be dameshi ba, dan ko a jikinsa, amma idonsa na sauka a na Inna yaji gabansa yai wata irin mummunar faÉ—uwa!

Domin sauke manhajar AREWA BOOKS, Danna wannan link É—in.

https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f

Domin gyara, Sharhi ko shawara
Ayshercool
07063065680
[6/4, 4:21 PM] Jakadiyar Arewa: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️

RUƊIN ƘURUCIYA

PERFECT WRITERS ASSOCIATION

(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)

https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P. W. A

*Story and written by*
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Writer of

WATA KISSAR..(Sai mata)
ABDUL JALAL
AƘIDATA (paid book)
WUTA A MASAƘA
NOW RUƊIN ƘURUCIYA (paid book)

_Labarin RUƊIN ƘURUCIYA, na iya zuwa da wani salo, wanda baku saba ganinsa a rubutuna ba, hakan ya biyo bayan akan abunda aka gina labarin, wani abun ze ɓoyu wani Abun baze ɓoyu ba sakamakon labari ne akan teenegers, yara masu tashen Balaga, but hakan ba ya na nufin na sauka daga kan tsarin yadda nake Rubutu bane, ƙofata a buɗe take dan karɓar ƙorafi, gayra ko shawara_

⚠️⚠️⚠️ƘIRƘIRARREN LABARI NE, BAN YADDA A JUYAMIN SHI TA KOWACE SIGA BA SEDA IZININA ❌❌‼️

     

SHIN KUNA DA LABARIN MANHAJAR AREWABOOKS KUWA?
MANHAJA CE DA TAZO DA TSARIN DAN SAUƘAƘAWA MARUBUTA DA MAKARANTA SAUƘIN CINIKAYYAR LITATTAFAI.
TA IN DA ZAKU IYA SIYAN KOWANE FEJI AKAN KUƊI ƘALILAN, DAI DAI DA ALJIHUNKU.
INA FARINCIKIN SANAR DA KU CEWA, DA ZARAR NA KAMMALA FREE PAGES, ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABAN LITTAFIN RUƊIN ƘURUCIYA, AKAN MANHAJAR AREWABOOKS.
KARKU BARI A BAKU LABARI, AKWAI TARIN DARASIN RAYUWA A CIKIN LITTAFIN.

https://arewabooks.com/book?id=6220842688e1ec3a0410329f

21-22

Jikin Sadik yai sanyi da kallon da Inna take masa, wani irin kallo take ƙare musu tun daga sama har ƙasa.

Mother tace "Auta ina kuka tafi haka? Tun wajen goma na safe rabonku da gidan nan, ba irin kiran wayar da ba'ai muku ba amma ba kwa É—auka, ina kuka shiga ne?"
Chapter 29 · 0% Book details